shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 19 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 25

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 25 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- ina shiga na kankame ta ina kuka hannu ta daga da kyar ta shafa kaina wahida ba dai abin sa sukai miki ko? a daran yaya shahid dani muka kai anty wani babban asibiti kudi basu yi wata-wata ba suka shiga da ita emergency likitoci sunyi nasarar cire mata bulet din ina zaune na hada kaina da gwiwa ya shigo taso mu tafi yace min na mike na bishi muna isa muka tarar su abba mom atu baba rabiu duk sun zo har anyiwa daddyn wanka kukan da nake yine yasa abba yayi min magana tashi ki koma daki ina kallo shahid na kwararawa mahaifinsa addu'a waya naiwa haidar cewa maza ya taho gida bbu lafiya kan kice meye wannan gidan ya cika da mutane tashin hankali, haidar ya iso ya tadda ana shirin fita da mahaifinsa daga dakinsa lokaci daya ya birkice da kyar aka shawo kansa yaiwa mahifin nasu addua,amma sumansa uku koda za,a dauke shi kukan kura yai ya rike makarar ya dinga duka masu rike da ita,shahid shi ya dauki haidar yasa shi a daki ya kulle sannan aka samu damar fita da mahaifin nasa a asibiti kuwa sunce basa bukatar dan jinya sai dai anti da kanta ta roki a bata wahida saboda haka wahida ce a gurinta.bayan sati daya ba laifin jikin antin yana sauki ranar shahid da haidar abba da baba rabiu anty ta soma yi musu magiya hadda kukanta su fada mata gaskiya ina mijinta yana raye ko kuma ya rasu kukanta ya daga hankalinmu ainun,haidar yace anty sai dai hakuri amma maganar gaskiya daddy ya rasu yaune kwanansa bakwai gaskiya ta girgiza domin bbu wanda ya ankara sai ganinta akai wanwar a kasa ta fadi tuni jini ya balle haidar ne ya kira likita,likitoci sukai hanzarin dauke ta wani likita ne ya dinga fada kun gani kun wargaza mana aiki shi yasa muka fada muku bamu.....kan ya karasar bom boy ne cikin fushi ya dakatar dashi ya dinga yiwa likitan bala'i da kyar abba ya ja shi suka tafi.tsakad dare ina zaune kan abin sallah tace wahida ban ruwa insha na mike na dauko robar swan na tsiyayo a cup na dago kanta na bata tasha sosai har tace ya ishe ta na maida ita ba kwantar tace sannu wahida nace yauwa wahida Allah yai miki albarka ubangiji Allah ya raba ki da sharrin makiyanki amin,wahida ki taimaka ki bawa dan uwanki ishassun hadin kai shahid yana tsananin sonki anty ba wai bana sonsa bane ina son karatu ne to wahida Allah ya taimaka ameen,ta koma ta kwata ina jin ta tana ta jero kalmar shahada koda inda saboda yace na saba jin irin wannan saboda koda yaushe sannan duk irin baccin da anty take yi muddin akayi kiran sallah ta kan ce in taimaka mata tayi alwala tai sallah yau ma ina zaune har akayi sallar asuba sai dai nayi mamakin yadda har aka idar anti na bacci komawa nai na kishingida bacci ne ya soma daukata sallamae abbana naji shi da ya shahid. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).