shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 3 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 15

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!15MUHD-ABBA~GANAya amin yace mom zamu gudan anti to amma kar ku dade kun san abbanku ya kusa dawowa nace anty mahida zo muje mana ta kara makalkale mom tace wallahu naji dadin kwanciyar bacci zanyi nace mom ki ture ta kar ta karasa ki min isa gidan bom boy a falo tare da small suna kallon kwallo mu kai sallama suka amsa na zauna kusa da ismail yaya amin yace ina anty? anty ta tafi katsina gaisuwa amma yau zata dawo inji bom boy, ya amin ya kale ni nina so na manufarsa amma sai na share,bom boy ya taso ya dawo kusa dani yace anti wahida ba gaisuwa? na kalle shi ya rame sosai yayi wani irin kyau yace me kike so in kawo miki ne nai masa banza haba my dear daure mana ki min magana caraf ya kamo hannna ya murza Allah ba dan na tuna maganar ya amin ba da tuni na tofa masa yau,cikin kasa da murya kamar yadda yake min magana kasa-kasa nima nace "bana so kana tabani,no ki barni in samu nutsuwa....... Allah sai dai kar ka samu muddin sai ka........shut up kina so tara min tawage ne kike daga murya,ai gani nai irinku sai da daga murya........me kike nufi wallahi wahida ki shiga taitayinki muddin kika shigo hannu sai kin.....Allah abbana ko ince Allah Al'amin kanina ne Allah ya kyauta kaine ka girmi ya Al"amin? to ki tambaye shi mana na mike domin ya ishe ni ni lambun gidan na wuce nai kwanciya iska na kada gashin kaina duk saiya lullub min fuska.
jin motsi kusa dani sai na tattare gashin tsugunne yake gabana ya zuba min mayatattun idanunsa na hararw shi yai murmushi yace sahiba tunanin me kike? wace sahibar kaje ka nemi sahibarka ba dai wahida ba wahida me yasa kike garani kike gasa min gyada a hannu? saboda BANA KAUNARKA! inda wanda nake so,ko ka gane? keh! wallahi na fara gajiya da wannan wulakancin na ki ko don kinga ina sonki? to kayi zuciya mana ka sake wata zan baki mamaki ba zan sake wata ba amma zaki gane kuranki,aikin banza ai na dauka zaka yi zuciya ashe ba a da ita,ya finciko ni cikin zafin nama sai gani wanwar a jikinsa sai kawai na saki kuka ya hankade ni ya barni gun a zuciyata na ce Allah ya isa mugu kawai na mike na goge fuskata.
kicin na shiga na dan yi wa anti girki kasancewar na san dadin su bomboy yafi son tuwo sai nai tuwan shinkafa nayi sa,a tuwan yayi kin yadda nake so na nannade shi a leda sannan na daura miyar agushi wadda ta amsa sunanta domin taji nama ina gamawa sai na daurawa shahid nasa domin sam baya cin tuwo miya ina soya sannan na dafa shinkafa na yanka salat na ajiye gefe sai dana kammala nasa sannan na hada lemuka kala uku nasa a firij kasancewar na san shahid na son gashasshen nama sai na gasa sannan na yanka kanana-kanana daidai yadda zai iya hada da abincin koma wa nai na gyara falon domin gaba dayansu suna dakin small na kunna turaran wuta.

MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz


Abbagana hausa novels
@ facebook
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).