shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 28 July 2015

sireenah---2

muhd.jpg

Sireenah 2********by**********

muhd-Abba~Gana

{sharifin~Zamani}


Duk wanda ya Kalli fuskar Sireenah baya
marmarin yakara kallonta sai dai dan karamin
bakinta da siririn Karen hancinta sune suka dan
taimaka mata tayi dan dama dama. Koda ta isa
school she is already late don ta tararda har
lecturer yashiga Kuma da alamu yayi nisa a
darasin dayake koyarwa, kai tsaye tashiga hall
din don tasan baza a hanata shiga ba saboda
kusan kullum ne sai tayi lattin tun ana hanata
shiga har malaman suka gaji da ita, wasu Kuma
sunayi mata rangwame albarkacin ilmin dake
gareta, sai dai yau kash kamar tazo a rashin sa a
domin Malam Tanko ne ciki gashi bayada
mutunci ko kadan amma hakan ta daure tashiga
yaga sanda tashiga hall din baiyi mata magana
ba saida yabari takai tsakiar hall din Kafin yace
Hey you black monkey where the hell do you
think u are going by this time around? Sireenah
wadda duk ta dabirce dalilin tsawar da Malam
tanko yayi mata takasa furta komai kallonsa
kawai takeyi da manyan fararen idanuwanta
wanda mommy tarasa yadda zata canza musu
launi tsabar hassada amma fuska kam babu kyan
gani dalilin (artificial black colour )da tashafa.
Malam tanko yakara kuluwa rashin maganarta
saboda haka ya koreta daga hall din students
suka fara daria wasu Kuma sun tausaya mata
(kunsan daman rayuwa dole ne mutum yana da
enemies da lovers ) balle ma Sireenah dasuke ma
Kallon kaskanci su aganinsu bai dace a ce
wannan kucakar yar aiki ce course mate dinsu ba
abin da ke kara basu haushi kenan gata always
cikin saka kalan tufafi daya! (basu san itama ba a
son ranta take sa Kala daya kullum ba ) Koda
yake dole suce haka saboda Nile University Abuja
babban makaranta ce wanda sai ya yan masu
hannu da shuni (richies ) zaka gani a ciki wasu
dalibban ma daga kasashen waje suka zo karatu
kunga dolene ayi mamakin karatun Sireenah a
wannan school wasu haushinta sukeyi duk cikin
makarantar babu wanda yakaita sa kaskantattun
kaya kullum tufafi daya ne a jikinta dalilin haka
aka samata one colour wasu Kuma black monkey
suke ce mata sauran dalibai suna mata lakabi da
gifted may be shiyasa 70% din daliban sukayi
hating dinta(ni kaina abba gana na tausaya wa
Sireenah saboda tana ganin abubuwa iri iri a
school da gida)!
Sireenah dake zaune bakin hall tazuba uban
tagumi tana kukan zucci dataga bazai fisshe ta
ba dole ta fidda wayarta wata lalatacciya kirar
Nokia c2 ce wanda yasha bandeji tayi logging on
social network, 2go chat ne takeyi tana shiga ta
tarar da sakonni kusan 20 saura na friends dinta
ne wanda suke 2go trivia tare while sauran
sakonnin na wani abokinta ne wanda suka shaku
sosai dashi, yana mata korafin rashin hawanta na
kwana biyu yayi missing din jokes dinta etc, Allah
sarki Lover boy nima nayi missing dinka rashin
data ne yahana ni hawa gashi yanzu na hau kai
Kuma baka nan balle nasamu wanda zai debe
mani kewa tana cikin wannan zancen zucci sai
gashi online (dayake sunada wireless a school
din)! Haba Funny girl nayi missing dinki kin
wahalar dani sosai gashi banida numberki balle
nakiraki koda yake kece kika hanani, am so sorry
loverboy I was out of data shiyasa kadaina
ganina. Hmm kin gani KO ga amfanin bani
numberki nan ai da tuni na aiko miki, a a habadai
kai da kefama da kanka ina zaka samu kudin aiko
mani? Hmm haka dai kike gani indai akan ki ne
zan iya hana ma kaina don nafaranta maki Kinsan
ke ta daban ce ko cikin friends dina! Toh nagode
sai dai nikuma banason kahana ma kanka! Yanzu
dai mubar zancen tunda gani nahau online muje
2go trivia muyi game ko yaka ce?
Gaskia yau bana ra ayin zuwa can hirarki kadai
nake bukata oya kibiyani bashin jokes dina na
kwana biyu da nayi missing. Haka sukayi ta
debema junansu kewa har lokacin isuwar lecturer
na biyu da zai gabatar da darasi nagaba suka
rabu badon sun so ba!
Wacece Sireenah? Ya matsayin ta yake a wurin
mommy Tee? Kodai yar aiki ce kamar yadda
dalibbai ke fada? Wanene wannan Loverboy?
Meye dangartakarsu da Sireenah?muhd-Abba~Gana
Share:

sireenah----1

muhd.jpg

Sireenah 1
********by**********muhd-Abba~GanaYarinya(budurwa) ce yar kimanin shekara
shatakwas(18) sanye da tufafin ma aikata irin na
(house maid) tana goge-goge tunda sanyin Safia
tafara wannan aika ce aikace saboda gudun kada
tayi lattin zuwa school. Tana cikin moping
mommy Tee tafito daga dakinta sanye da rigar
bacci alamun yanzu ne tashin ta daga barci, Kee
Sireenah idan kingama aikin da kike yi kije dakina
ki gyara shi daganan kiwuce dakin su yan biyu
shima ki gyara akwai wankin su a ciki kihado su
kije ki wanke tufafin tas kada ki daga har sai sun
bushe ki goge su duka amma yanzu kifara hada
mana breakfast, kada ki kuskura ki dandana
(tsabar mugunta taya mutum zaiyi girki ba
dandane?) Mommy Tee don Allah ina neman
rangwame zanyi duk abinda kika umurceni amma
wankin kibari har nadawo daga school gudun
kada nayi latti. Lallai Sireenah wuyanki ya isa
yanka wato yanzu ban isa nasa ki aiki ba sai kin
kawo mani naki excuse KO? Toh bara kiji aiki
bafashi dolene kiyi dukkan abinda nasaki ban
damu da lattin da zakiyi ba idan ma da hali a
koreki mana naga batun bokon yarinyar banza
Wallahi da akwai yadda zanyi da tuni nasa
ankoreki daga makaranta badon Kina cikin
dalibban da minister of education ke sponsoring
ba masu kwakkwaran securities Sireenah bata
kara cewa uffan ba banda hawaye dake ambaliya
a fuskar ta har mommy tee tawuce bangarenta!
Jikinta bawani kwari har taga ma goge gogenta
idan da sabo tariga tasaba da musgunawar
mommy Tee bayan tagama hada breakfast tana
cikin jerawa saman dinning table sai ga yan biyu
sun fito shirye cikin kaya masu Shegen tsada
amma duk da haka basu da babbanci da wasu
ugly monkeys komai tsadar kaya baya yi musu
kyau farin dake garesu nema yadan taimakesu
koda yake harda farin kantin Hassana ce ta fara
magana Sireenah fatar kin gama girka mani
abinda nace? Eh Hassana gashinan yana jiranku
kan dinning, Ke miss kuku kinfa san ni bana son
irin wanda kika girkawa Hassana nawa nake so
daban cewa Hussai, don Allah Hussai Kiyi hakuri
kici na Hassana inada sauran aikin da zanyi gashi
bakiyi magana tun farko ba, nidai nagaya maki
bazan ci ba ko kije ki girka mani wani ko nacanye
na mommy tee yi hakuri basai kinci nata ba
yanzu zan girka miki daidai wanda kike bukata
bayan wucewa war Sireenah yan biyu suka tafa
hadi da dariar mugunta sannan sukaci breakfast
dinda ke gabansu daman tsabar mugunta ce yasa
Hussai tace bazata ci na Hassana ba bayan
komai nasu iri daya ne hatta under wears basu
babban tawa saboda sun kasance irin yan biyu
nan masu masifar kishin junansu suna gama yin
breakfast suka wuce school domin daukar
lectures koda Sireenah tazo bata tarar dasu ba
don haka takoma kitchen taci abinta daman
yunwa take ji Kuma bata isa taci abinci ba sai
sun rage Kafin taci itama mommy tee tafito cikin
kaya masu tsadar gaske but katon ciki da uban
duwawu yahanata yin kyau a cikin tufafin ta
zauna tayi break dinta kafin tawuce companyn
mijinta domin aiki! Daman ma aikatan gida jiran
fitar Hajia Tee suke yi suna isowa tabangaren da
Sireenah take suka ce ma ta maza Fulani Kiyi
sauri kema kije ki shirya duk zamuyi miki aikin
gidan har da abincin rana zamuyi Kafin ki dawo,
Nagode sosai Allah yabiya ku.
Bayan Sireenah tagama shirinta a maimakon
tashafa powder tagoga shoe shiner baki
(black )wanda itama ba a son ranta take shafawa
ba dokar mommy tee ce tagoga wani bakin abu a
hakoranta kace haka Allah yayi ta gashi takara da
bakin a baya ga himmar baki (nikaina abba
dana ganta sai da naji tsoro lols) Kamanin ta
gaba daya yacanza har wani walkia fuskar ta keyi
tsabar yaji shoe shiner amma zaka zata is
natural a yadda tayi masa daman tariga ta rufe
hannayenta da Kafafuwa with black socks! Allah
yayi mana kariya da masu hali irin na Mommy
Tee
muhadu a kashina gaba

muhd-Abba~Gana
Share:

WAEC MAY/JUNE

bana.jpg

WAEC Threatens To Withhold 19 States Results
Over Debts

visit www.examstaiwo.tk
Hundreds of candidates who sat for the May/June
West African Senior School Certificate Examination
may not have their results released in the next two
weeks, the West African Examinations Council has
announced.
No fewer than 19 states of the federation owe the
council about N4bn examination registration fees.
The WAEC Head of National Office, Lagos, Mr.
Charles Eguridu, announced this on Monday at a
briefing in Lagos.
He, however, failed to make public the affected
states.
Eguridu said, “A total number of 19 states in the
country owe the Council in respect of entry fees for
state government sponsored candidates for the
May/June 2015 WASSCE. Some states also still owe
the Council registration fees for the May/June 2014
WASSCE.
“We have written to the affected state governments
without any response. The poor response of the
debtor states is threatening the smooth operations
of the Council.
“We, therefore, want to publicly plead with the
affected states to off-set the registration fees of
their candidates as soon as possible, as we cannot
guarantee that the results of their candidates for the
May/June 2015 will be released along with others.”
may/june WAEC RESULT 2015
TO BE RELEASED WITHIN 2_WEEKS
The news is from punch newspaper...
All waec 2015 candidates
wish you all the best of
luck....9_credit BY GOD GRACE IF U BELIEVED type
# Ameen via comment box
WWW.EXAMSTAIWO.TK Remain The Bes In Giving
Information About Exam In Nigerian
Share:

CHIPS SALAD

banaio.jpg

Dankali, heinz beans, salad cream, egg, mai,
attarugu, albasa, gishiri, nama, maggi ki fere
dankali ki yankashi atsaye, kisa gishiri ki soya, ki
yanka namanki kanana ki dafashi, idan yayi laushi
sai ki dan bashi tsoro acikin mai da dan attarugu
da albasa, ki dafa kwai ki yankashi atsaye, Sai ki
dauko plate mai fadi ki fara zuba dankalin, sai ki
sa sauran kayan gaba daya, kwai da nama da
beans din, amma jerasu zakiyi yadda zaiyi shaawa,
sai kisa salad cream din daga karshe, SAI CI
Share:

MEAT & RICE IN EGG

banna.jpg

MEAT & RICE IN EGGKAYAN HADI
(2)Shinkafa
(3)Awai
(4)Nama
(5)Peas & carrot
(6)Albasa da lawashi
(7)Attaruhu da tattasai
(8)G/oil or maggrine
(9)Tafarnuwa
(10)Maggi da gishiri
(11)Thyme
PROCEDURE:-
Ki sami markaddaden naman ki, Ki zuba a
tukunya.Ki
samu curry, Tafarnuwa,Lawashi,Thyme,Maggi da
gishiri ki zuba ki juya sannan ki barshi ya
dahu.Sannan
ki wanke shinkafa kiyi mata rabin dahuwa
Sannan ki kara wanke ta ki tsane ta da matsami
Sai kuma ki daukko wannan naman ki zuba a
kasko
mai fadi ki zuba mai ko margin ki soya sama²
Sannan ki dakko shinkafar ki ki zuba akai sai ki
sami
attarugu ko tattasai ki jajjaga ki zuba akai ki juya
Sai ki samu carrot da peas ki goge bayan carrot
din ki
yayyanka
Sai ki zuba ruwa ki juya sosai
Sai ki barshi zuwa yan mintuna
Sannan ki sami kwai ki fasa akai ki juya sosai
Sai ki barshi ya dan dahu
Sannan ki sauke
Sai ki wanke hannu ko cokali ki hau ci.
Share:

QARIN************JINI---22(KARSHE)

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 22

Sunyi shiri na minti biyar chan ya janye jikinsa
daga nata ya tashi ya shig daki ta bishi da kallo
cikeda bayyanannar qauna, yaje bayan kamar
minti 10ya fito yace mata ni na gano dalilin da
yasa muke qaunar junanmu,!! Ya kalleta yawani
lumshe idonsa saida taji wani yarrrr ajikinta,
infada kin bani gari, eh fadi ina saurarenka, ya
matsa kusa da ita ya rungumeta sosai yace
mata sanadiyar QARIN JINI..!!! Tace QARIN
JINI???ta tambaya shi, yace eh QARIN JINI..!!
Lokacinda nafadi a AYNN nanemi taimakon jini
nace gurin dan nigeria nakeso kuma musulmi
yanzu na duba takarduna naga wacce tabani jini
macene yar nigeria kuma musulma kuma yar
garinmu sokoto, ba kowa bace illah matana
uwar yayana insha Allah OUMULKHAIR
MUHAMMAD sanadiyar QARIN JINI aka zuqo
qaunarki aka zubamin inda tabi jinina takamani,
kamar yadda lokacinda yayana ya kadeki da
mota na baki jinana, hadi da qaunata aka saka
miki, kinyarda da cewa sanadin soyayyarmu ta
QARIN JINI ce ko yaya??? Ta qara kwantawa
akan faffadan qirjinsa ta lumshe ido tace eh na
yarda.. ya tallabo fuskarta yana kallonta yana
murmushi yace kina sona miyasa baki
gayaminba? saima mari da kika bani?
Hmmmm..!!! ta bude baki zatayi magana saitaji
ya zura mata harshensa acikin bakinta ya fara
kissing dinta a hankali, batasan lokacinda itama
tafara bashi amsaba saida taji qafafuwanta sun
kasa daukarta sannan tay qoqarin janye jikinta
lallai Abdul ya rude sabida har idonsa sun sauya,
tay qarfin hali ta jawo hannunsa suka zauna..
kowa na fadin abinda yayi lokacin suna ta dariya
har akayi sallah magrib sukayi sallolinsu sukaje
suka kwanta shima ya dauko blanket dinshi yayo
dakinta, yace yau kinyi baqo, dama tasan za'ayi
haka ya umurceta tatashi suyi sallar godiya
sukayi sallah sukazo suka kwanta Abdul yafara
kawomata hari da qananan makamai tun tana
kaucewa harya fara samun nasara akanta yayi
mata lilis ko numfashi dagyar take fitar dashi
anan ya auka da babban makami mai linzami
mai tarwaza duk wani missing din juna da akayi,
Lallai ranar farko Abdul yasamu nasarar shiga
gonarsa da kew inda yayi yanda yakeso aciki.
Khair anji jiki sosai amma daurewa tayi kar ta
nunamasa cewa taji jiki class dinta ya ragu, nan
yaga alamar kamar bata gajiba yasake kawo
mata second hari da taga zatasha wahala sosai
saitafara kukan kissa irin na mata tuni ta ijeye
zancen clss gefe dataga zatasha wahala nikaina
jabo naga qoqarin khair sosai, gari ya waye
yadan gasamata jikinta....
soyayyah mai inganchi taginu tsakaninsu kula da
juna baiwa juna hakkinsu sai wanda yagani...
duk iyayensu sunsan cewa ABDULLAH shine
DREAM GUY din OUMULKHAIR shima ansan
cewa itace DREAM BABY dinsa abin ya basu
mamaki da al'ajabi sosai harma idan sukaji cewa
sanadin QARIN JINJ wannan abun yafaru....
khair taji dadin zabin da babanta yay mata haka
shima yaji dadin zabin da yayansa yay masa,
Yaudagobe batabar komaiba, yau ga khair dauke
da cikin Abdul ta haifa masa namiji aka saka
masa suna mahmoud kai in taqaitamuku
oumulkhair saida ta haifi yaya biyar wa Dream
guy dinta suna burgeni sosai wllhy yanda suke
nuna kulawa ga junansu tana qoqarin gyaran HQ
dinta da abubuwan da tsohuwar qawarta
benaxeer take bata kullum, dame take kamar
sabuwa budurwa har yanzu Abdul yakasa gane
komai kullum ji yake yau kinfi jiya.....
ALHAMDULLILAH godiya ga dinbin
makaranta littafaina ina muku fatan alkhairi.
Share:

Monday 27 July 2015

QARIN**********JINI---20

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 20

Yanda taji ya kira sunan ya daure mata kai
dream baby kamar yaya??? Ya akai tazama
dream baby dinsa kodai yataba jin tace mishi
dream guy ne idan ma yan gidansu suka
fadamasa gaskiya sun zubar mata da clss,
yanata tambayarta mi yake damunta ita kuma
tashiga kogin tunani ya girgizata da qarfi ta bude
idonta da suka chanza kala daga fari zuwa jaaa,
bari in dauko key muje asibiti, nan akeyinta
karsujee Dr yace lafiyarta lau tunda tasan cewa
ba wani ciwo dayake damunta, tace bazataje sai
yasami kansa mai bin umurninta yace to sai
wani zabura take kaman tayi bacci tana
qanqameshi shima yana rungumeta abinda
kowannensu yakeso kenan da ciwon qaryarta tay
bacci shiko sai wani kallonta yake abin nema
yasamu yau ga dream baby dinsa akan cinyarsa
tana barci, murmushi hadida wasu zafafan
hawaye suka qanqaro a kumatunsa suka fada
cikin hancinta nandanan ta bude ido ta kalleshi a
dimauce lafiya my DREAM GUY? Sam batasan ta
fadi sunanba yaji wani iri dream guy ko yayansa
ya tona masa asirine an gayamata ita yakeso kai
amma yaji dadi, ka daina kuka naji sauqi ta fada
tana sharemasa hawaye, sai mai maita sunan
yake aranshi har yafito waje taji, ta kalleshi, tace
miyasa kacemun DREAM BABY ??? Ya kalleta
yace miyasa kika cemim DREAM GUY ???
Share:

QARIN**********JINI---21

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 21
Kowanne yai deeef kamar ruwa ya cinyesu, na
tsawon lokaci abdul ya daqo kansa karo na biyu
yasake tambayarta miyasa tace masa dream
guy? batace komaiba, ya tallabo fuskarta wacce
take cike da hawaye da jan ido na ruwan
barkonon da tasha ya kafamata ido, ido cikin ido
har saida dukansu hawayen da suka maqale a
idonsu suka qarasa qanqarowa, ya matseta qam
a jikinsa yana shinshinar qamshin jikinta har
yafara fita hayyacinsa, ta dawo dashi ta hanyar
tambayarsa miyasa kacemin dream baby!,
yasaketa ya zauna dai dai yana kallonta yafara
bata labarin cewa tun wata faduwa da yayi a
AYNN US kaishi ya daki wani qarfe aka kaishi
asibiti tun da yaji sauqi ya fara mafarkinki kala
kala, da haukarda aka cinna mishi, har ana cewa
aljanace ta shafeshi duk akanki da irin azabar da
yasha dss akanki na baro AYNN nadawo gida
nigeria, amma ina dawowa naija sainayi karo
dake bayan na baroki US, abin yabani mamaki
matuqa, haka na qara komawa US nanma
naqara ganinki anan natabbatar da cewa ke
aljanace, sai ranarda kika mareni kina min
magana na tabbatarda cewa ke mutum ce ba
aljanaba, nasha azabarda bantaba tunanin
samun mafita akantaba!, nay alqawarin ko nayi
aure bazan taba hada jiki da wata mataba,
matuqar ba dream baby dina bace, ana saura
sati daya aurenmu nay mafarkinki kinzo kina
kuka mai tsanani kina cewa idan baki aureniba
to zaki kashe kanki!!. hankalina yay matuqar
tashi na farka bacci nacewa yayana nafasa
aurenki, dagyar aka samu nadawo hayyacina na
yarda aka daura min aure dake, duk wani party
da walima bansamu halartar ko dayaba, dan
banajin dadin jikina, wllhy dai dai da rana daya
bantaba tunanin cewa bazan aurekiba kuma
gashi tunanina ya zamo qaskiya oumulkhair
nasoki kamar in kashe kaina akwai lokacinda
idan abin ya mitsoni zanfara kuka tun safee har
zuwa dare baci ba sha sonki ya dade yana
wahaladda zuciyana..!!! Nima kusan abun da ya
faru dakai shi ya faru dani, nan tabashi labarinta
daga accident har qarshe amma ita shekaranta
HUDU tana dandanar azaba shikuma shekara
DAYA, ya tausayamata fiye da kansa sabida shi
shekara daya yayi amma ya yakasance, akan
itada tayi shekara hudu tabbas lamarinsu abin
dubawane to amma miyasa haka ta faru dasu
tambayarda suka hada baki lokaci daya sukace
TO MIYASA HAKAN TA FARU DAMU???...
Share:

QARIN*********JINI----18

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 18

Ankai amarya gidan mijinta su zainab khalifa sai
wani iyayi akeyi ko za'asamu miji amma banajin
cewa andace,dota zainb Ibrahim kuma ba
ruwanta baiwar Allah da ita meenah slow sune
agaba benaxeer kuwa damuna take dawaya
nasan zatace inama itace, su samira malami
giwa su Aysha armiya'u ma sun samu zuwa
aurena gaskiya nayi jama'a, anyi komai na
al'ada aka bar amarya da angonta hmmmm..
abdul yasan bazai iya kusantar wata mace idan
dai ba dream baby dinsa bace, gaskiya zai cuci
Wannan yarinyar da yayansa ya hadashi aure da
ita acewar yayanshi yanada yaqini akan idan
yaqanta zai sota, amma yayanshi baisan cewa
akwai wata aranshiba, yakasa yi mata magana
sai ya fita ya turo mata sms cewa... kiyi haquri
kici abinci gashinan saida safee!, taji dadi sosai,
da safee ya shigo tana bacci yafita abinshi ya
mata sms cewa yaje gurin aiki, taji dadi yanda
shima bayason matsamata tunda tay aure bata
qara mafarkin dream guy dintaba yau sati daya
bata saka mijinta a idoba taji dadin haka tagane
shima yanada hankali bazai matsamataba tana
waya da iyayenta da iyayen mijinta... Benaxeer
kuwa kullum sai ta kira taji miya faru amma
shiru takeji harda tambayata a cikin abubawan
da tabani wanne yafi kew nagane nufinta sai
kawai na wayance nace duka suna da kew,
benaxeer uwar gulma bata gane komaiba .... yau
satina uku a gidannan ban saka mijina a idoba
ina zaune a falona wanda yaji kayan gayu naji
da fada gidana ya burgeni sosai kayana
wayanda aka siyomin daga turkey komi na qasar
ya hadu tsarin gidan yana burgeni., naji qarar
mota araina kuwa nace baqi nayi haka ba waya
ba komai, ina nan zaune har yashigo fallon
waigawan da zanyi wazan gani A.A ko kuma
ince DREAM GUY dina...!!! Ya tsaya gabana ya
daure fuska kamar an aiko masa da uwarsa ta
mutu ina oumulkhair take araina nace kardai
shine mijina? zansha wuya agurinsa sabida
nasan cewa ya tsaneni amma kuma zuciyata
zata samu natsuwa kai Allah nagode maka da
ka hadani da dream guy dina biyayyah ga iyaye
ta janyo min cimma burina, dake nake magana
kin saka mutane gaba kina kallo...!! Na dawo
hayyacina na sunkuyar dakai qasa nace nice, ai
nice oumulkhair, jakarda ke hannunsa ta subuce
masa ya qara nuna ne kece oumulkhair? kece
matata? Kece yayana ya dauramin aure da ita?
Tofa....
Share:

QARIN**********JINI----19

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 19

Jikinta yai sanyi tace eh nice, kunya ta kamashi
na yarda jakan da yayi a gabanta, yadauki
jakarsa ya wuce daki ya zauna bakin gado, sai
hawaye ya daqa hannuwansa sama yace Allah!
kaine mai fitar da matacce acikin rayayye ka
fitarda rayayye acikin matacce, Allah nagode
maka da kahadi da abinda nafison aduniya!,
dream baby na! wacce nake so nake qauna
wacce itace burin rayuwa da ita nake kwana da
ita nake tashi! yau gata a gidana a matsayin
matata Allah nagodemaka, baisan lokacinda yay
sujada ba dan murna, sai dai baisan yanda zai
bullowa al'amintaba yasan dai ta tsaneshi tun
lokacinda ya kwasheta da mari a gaban mutane,
shi baya buqatar wani abu a gurinta kawai ya
riqa ganinta tana mishi mur mushi yafiye mashi
komai a duniya, ta ina zai fara,? ya dauko
wayarsa ya kira abokinsa aliy, ya gayawa aliy
cewa matar da ya aura dream baby dinsace Aliy
abin yabashi mamaki sabida farko bai yardaba
saida yaji A.A yana rantsuwa sannan ya yarda
amma abin da daure kai.!
Tashiga daki kamar yanda Abdul yay godiya
haka tayi godiya wa Allah da kuma iyayenta da
suka hadata da dream guy dinta!,
Bayan kwana hudu, tafito daga kichin sukayi
karo shi zai shiga ita kuma ta fito, ta tsorata
sosai tana jiran taji saukar mari shiru, ina
rudewa yay yana bata haquri tawuce gefensa ta
wuce dakinta... yau sati uku da gane junansu
yadaina zuwa office 24hrs yana gida yana
kallonta ya rasa yanda zaiyi ya mata magana
iya tunaninshi ta tsaneshi kuma bayason ya
takura mata itama nata bangaren haka abin
yake.... Tagaji da zaman da suke haka tana
zaune wata dabara ta fadomat wacce taji a
gurin benaxeer uwar iyayi, tajiqa barkono a ruwa
saida ya jiqa sosai ta shanye ruwan tazo falo ta
kwanta bayan minti 20 jikinta yayi kamar wuta
idonta suka kada sukayi jajir tanajin motsinsa ta
fara kuka adimauce yazo gurinta ya dagota
lafiya my DREAM BABY..!!!
Share:

QARIN********JINI--- 16

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 16

Yaya naziah dai tasan mafarkine kawai nay
sabida haka tacemun shikenan za'afasa auren
kidaina kuka gobe zanyi magana da baba ta
lallabani har barci ya sake awon gaba dani
mafarkin dazu dai na sake mai mai tawa amma
a cikin mafarkin nawa sai na tambayeshi address
dinsa yagayamun, bayan natashi daga barci
koda na tuna address din sai naga address din
gidanmu ya bani, tun safee yaya naziah tazo
gurina ta ganni curko curko dani a daki.! na
maimaita abinda na gayamata dadare naqara da
cewa idan kuma ba hakaba Wllhy ZAN KASHE
KAINAH...!!! Hankalin ya naziah yay balaeen
tashi dajin maganar kisa bashiri ta kira babana
tagayamishi, baba bashiri yazo gidan, yaya ta
kirani nazo nagaisheda baba, yace oumulkhair
bani nazo miki da maganar aureba ke kikazomin
da ita, kuma ban aminceba saida na baki lokaci
nace kiqara tunani kikace kinji kin amince,
tabbas mutunchina wani abune da bana wasa
dashi duk abinda zaisaka mutumchina ya zube
zan barshi na farko duk wanda yaji kin kashe
kanki zaice auren dole na miki sabida haka ni da
kaina zanje gidansu Abdullah in basu haquri su
janye maganar auren Allah ya hada kowa da
rabonsa, ya miqe zai tafi natashi na russuna
gabansa ina kuka, baba dan Allah ka yafeni
wllhy ashirye nake da in maka biyayyah koda
kuwa zan rasa raina wllhy zan auri Abdullah
kuma harga Allah ba abinda zan aikatawa kaina,
baba kaci gaba da yimin addu'ah, baba ya shafa
kaina Allah ya miki albarka oumulkhair amma
aure anfasa bazanso in rasakiba akan abinda
bakyaso, ya qara gaba inata kiransa amma ina
baiko waigoba ya tafi, yan kwanakinnan naci
kuka har saida zazzabi mai qarfi ya kamani
kwanana biyu ina kwance ran na uku na warke
yau saura kwana bakwai aurena amma ba wani
shirye shirye da naga anayi yaya naziah
kolokacinda banida lafiya ba wani kula dani
takeba, haka dana warke ko magana batamun
umma kuwa tunda na fara zazzabi ko ya jiki
balle Allah qara lafiya abin duniya ya isheni
narasa inda zansa rayuwata inji dadi, na shirya
najee gidan mu natarar baba bayanan yafita
umma ina mata magana ko kallo ban ishetaba,
da taga na fara kuka sai tatashi tabar min palon
ina zaune saiga yaya habeeb ya shigo ko kallona
baiyiba ya wuceni nagaisheshi yayi banza dani
zai fita naqara gaisheshi ya juyo ya makamin
wata arniyar harara saida naga jiri,yace
mahaukaciyar yarinya wacce haukarta
tafiyemata mutunchin mahaifinta, daga yau karki
qara kiranada yaya niba yayanki bane wawuya
kawai hankalinki ya kwanta baba yaje gidansu
Abdullah yagamasu kinfasa auren yay tsaki
yafita, baba yaje gidansu Abdul tashin hankali..!!
haka nazauna a palon ummatata amma ba
wanda yake mun magana yaya saeed ma da
nakebi dana gaisheshi ashar ya duramin, narasa
abinda yakemin dadi ina zaune naji qarar motar
baba da gudu naje gunsa fuskarsa a daure naje
na fada jikinsa ina kuka...
Share:

QARIN**********JINI--17

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 17

Baba baicemin komaiba yaja hannuna mukaje
palo ya zaunar dani yace min lafiya,? naci gaba
da kuka kiyi magana mana!, baba inasonsa zan
aure shi wllhy inasonsa, aljanin barcinki kike
magana ko kuma wani daban kike samo? naji
wani faduwar gabah, Aah baba Abdullah nake
magana akai, nayi ta baiwa baba haquri akan
zan aureshi, qarshe baba yace min yaji Allah
yamin albarka na rungume babana inata kuka
baba yagayamin cewa yayi magana da yayan
abdul akan yau zasu hadu yaqayamasa anfasa
auren sai gashi kinzo da wannan maganar Allah
ya miki albarka..... naji dadi na tashi banyiwa
kowa sallamaba dan naga yaya habeeb shirye
yake da ya dakeni naje gida sumi sumi kamar
munafuka na jaa motatana sai gidan yayata ban
cemata komaiba naci gaba da al'amurana, tunda
nasan cewa aure yananan nayi waya na gayawa
benaxeer aurena yakusa saura kwana biyar taji
dadi waye angon nagayamata wanine taji dadi
taki kamar itace, inason in tambayeta ina A.A
amma ina girman kaina ya hanani har munyi
sallama tacemun jiya naga aliy abokin A.A yana
gayawa wasu qawayensu cewa A.A zaiyi aure
nan daa sati daya wani jiri naji ya kamani
bansan lokacinda wayan ta fadiba nafara kuka
sai da nayi mai isata sannan nayi shiru. Araina
nace dama mafarkinda nayi kace zaka kashe
kanka duk yaudarane? dama ashe aure zakayi?
wllhy da in aureka muyi tarayyarka da wata qara
in mutu banyi aureba? ko kuma in auri wani
namijin Allah na godemaka da kasa babana ya
zabamin miji dana tabe.! meena slow babbar
aminiyata itace gaba wajen raba katin buki aka
kawo min calendar aure da duk wani abu da ake
rabawa a gurin aure amma ba wanda na kalla
sabida radadi da zafi da kishin da zuciyata take
fama dashi, gobe zan zama mallakin wani ba
dream guy dina ba.! Lallai na yaudari zuciyana,
amma sai haquri anata shirye shiryen bikin
aurena an gyaramin gidana, naji su zainb khalifa
da zainb ibraheem sunata gulma wai basu taba
ganin gida irin wannan ba kayana daga Turkish
aka baiwa baban Zainb khalifa yasiyomin da
yake achan yake aiki kaya naji da fada abin sai
wanda ya gani meena slow sune qirjin biki sai
shiga da fita sukeyi sun shirya party kala kala
amma ba wanda najee bani ba ango suka
chashe abinsu. Sun shirya wata walima ARAB
DAY mata zallane naje walimar, sunyi shigane
manto da wandon Jeans da kuma wani farin
qyale shigar ta burgeni sosai, 20/5/20... an
daura auren OUMULKHAIR
MUHAMMAD&ABDULLAH AL-MUSTAFAH gaskiya
an taru wajen daurin auren mu benaxeer ta
aikomin abin gyara jiki da kuma HQ dina ashe
bena tsohuwar macece tasan komai, gaskiya
mijinta ya more nidai ba abinda nayi sai zubar
da banxaye nayi da yamma aka shiryani nafito
tsab dani nasha kitso da qunshi umma tayi min
fada sosai babama haka, yayata naziah ma
tamin fada fadanta yafi shiga raina fiye da fadan
da kowa yamun ina kuka aka kaini gidan mijina
Abdullah..
Share:

QARIN***********JINI---15

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 15

Tun da na dawo gida nasamu baba nagayamasa
abinda yasa nadawo gida, yace inje inqara tunani
shima zaiyi tunani bayan sati biyu da maganar
da nayiwa baba yakirani nazo,
Oumulkhair dama nakirakine akan maganar da
kikazomin da ita sati biyu da suka wuce, nace
kije kiyi tunani mikikayi tunani akai?? Khair tayi
shiru batace komaiba na tsawon minti uku...
kinyi shiru, baba ni nariqa na bar komai a
hannunka duk hukunchinda ka yanke shirye nake
da in karba,!! Kanta aqasa ta bashi amsa. Allah
yay miki albarka dama tun lokacinda wannan
mutumin ya kadeki da mota ya cemun yana
nemawa qaninsa aurenki nace masa yayi shiru
sabida yanzu andaina auren hadi, yan mata da
samari sun waye sabida haka sam bazasu yarda
da auren hadiba ya dade yana min maganarki
qarshe nace ya bani lokaci inyi shawara jiya
muka hadu dashi a saman gidana, sai gashi ya
dawo min da maganar yanaso aba qaninsa dama
yazo gurinki dan ku dai daita kanku ke kuma
gashi kinzo da wannan maganar inaga shikenan
sai a baiwa yaron dama yazo ku dai daita
kanku. Nidai baba idan kayi bincike akan yaron
ka tabbatarda cewa yaron kirkine iyayensa
mutanen kirkine basai yazoba kawai adaura
auren na amince.! aah oumulkhair bazamuyi
hakaba kibari kawai yazo kema kiganshi yafi
nidai baba basai yazoba..! To shikenan Allah ya
miki albarka.. bayan sati daya da maganar
dangin gidansu Abdullah sukazo gidanmu ganin
amaryarsu, tabbas danginsa mutanene masu
kirki da girmama jama'a yaya naziah ta tarbesu
tarba ta mutunchi da girmamawa nikaina naji
dadin ganinsu ko bakomai naga dangin mijina
suna da mutunchi zanji dadin zama dasu, chan
wata mata wacce ina kew tata zaton matar
yayanshine ko kuma inche mutumin da ya
kadenice tace, ashe Abdullah jinin da yabayar wa
matarsa ya baiwa jinin gatanan Allah yayi shi
zai aureta duk akai dariya harnima saida na
murmushi, abinda yafi bani mamaki shine
maman Abdullah sai ina ganin kamar na santa
sosai, har inajinta acikin rayuwata amma narasa
inda nasanta maganar aure ta kankama ansaka
rana da sadaki da komai amma kuma har yanzu
bansan wazan auraba.. Yau watana daya da
dawowa daga AYNN tun da nadawo dream guy
dina na daina mafarkinsa sai daren yau nay
mafarkinsa mafarkinda yay balaeen daga min
hankali naganshi ya durqusa aqasa yanata kuka
kuka mai tsuma zuciya nazo kusa dashi amma
na kasa masa magana, yacemin yanzu sabida
girman kai irin naki yasa kika tafi kika barni
yanzu sabida son zuciya irin naki kika gujeni da
kinsan yanda sonki yake a cikin qirjina da baki
barniba haba. Khair ki tausayamin mana wllhy
ina qaunarki fiye da tunaninnki inason
kasancewa tare dake har qarshen rayuwata karki
barni.. na kallesa nace masa sai dai kayi haquri
yau saura kwana tara adauramin aure
WHAT..!!!??? Wllhy duk ranarda kika auri wani
baniba KHAIR zan kashe kaina..!! saina kashe
kaina..! rayuwata bake batada amfani zan masa
magana sai naga ya juya ya dauko wuqa zai
dabawa kansa a figice na farka daga barci na
kwarma ihu da kuka mai qarfi yaya naziah
tashigo lafiya oumulkhair?? Yaya na fasa aure ni
dream guy dina nakeso....
Share:

QARIN*********JINI--14

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 14
Aliy yanzu yazamuyi ne pls,wllhy nakasa sukuni,
ina magana kazauna kana kallona haba aliy
yakakeson inyi da rayuwatane?? Bazaka taba
gane minake filling ba.!! Haba A.A, bansan cewa
abinda kake fada qarya bane sai yau..zakazo
kana kuka kana ciwo kana barin qasa kana qin
zuwa clss duk akan yarinya sannan kazo ka
mare yarinya ganban mutane kace min wai kana
sonta in yarda sam ni na tsinke da al'amarinka
tun dazu. Aliy ni kaina bansan yanda akai na
aikata abinda na aikataba bansan lokacinda na
maretaba! bansam lokacinda na gayamata
maganar da na gaya mataba.! aliy kadaina
maimaita abinda yafaru kawai kamun mafita
abokina banida wanda zan gayawa abu ya bani
shawara sai kai nan yasake fitarda wasu zafafan
hawaye dagani suna tareda azaba ya dafe
qirjinsa ni kadai nasan mike going anan aliy
bazai iya barin abokinsa cikin Wannan tashin
hankaliba, sukayi shawara yasama masa mafita
sannan suka kwanta amma ba barci a idon
A.A....
Khair kam murna agurinta babu kama hannun
yaro koba komai tagane cewa dream guy dinta
ba aljani bane mutum ne kuma tafi kewtata
zaton cewa ya rama abinda ta mishine ataqaice
taji dadi sosai, sai tunanin yanda zata bullowa
al'amarin tasan kozata mutu bazata zubarda
class dintaba taje gunsaba, sannan abin yanzu
yana dada yimata tasiri a zuciya tasan tanada
girman kai anya zata iya ijiye girman kanta ta
nuna mishi sonda take mishi? kai ina bazan
iyaba!! gaskiya sai dai inmutu wllhy bazan kai
kainaba harmadai yanzu da naga ya tsaneni ina
ganin tsanata qarara a cikin idonsa... miye
mafita??? Kodai in gayawa benaxeer ne?? aah
wannan sirrinane bazan gayawa benaxeer ba ta
fallasani a internet, kawai bari in koma gida in
ijiye karatunnan haka nagaji da shan axaba, zan
cewa baba yasami duk wanda yake ganin ya
dace dani ya hadani aure dashi, zan amince
koma waye, ga dukkan alamu bazan taba kaiwa
ga burinaba, nagayawa benaxeer cewa zan koma
gida aure za'ayimin itadai bata yardaba sabida
tasan cewa banida wani tsayayyen saurayi da
taga ina soyayyah dashi, so kawai tace min
tajine dan tasan koda za'amutu bazan
gayamataba. nashirya komai nawa nasayi ticket,
sai naija gaskiya inason benaxeer koba komai
tana sani dariya kuma tana bani shawara iya
gaskiyanta ko in karba ko kar in karba Allah
sarki bena sai mun hadu naija....!!!
Share:

QARIN*********JINI--13

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 13

Takai minti daya akan qirjinsa. ta janye jikinta
da qarfi ta waskeshi da mari tasssss...! kai
bakada hankaline?? idan kuna tafiya bakwa
kallon gabanku? sai kuzo kuna ture mutane. da
yake bakusan darajar mutaneba, sokoko yai yana
kallonta tabbas yau ya tabbatarda DREAM BABY
dinsa ba aljana bace mutum ce gashi har tayi
masa magana wai bai san darajar mutaneba
kenan itama mutumce kenan? shikam buqatarsa
ta biya tunda har ta mishi magana ko kasheshe
zatayi bazai daina sontaba sabida jinta yake
kamar tare aka haliccesu kominsu daya.. baice
mata komaiba tabi gefensa ta wuce ya bita da
kallo cike da farin ciki mara iyaka...
Cike take da baqin ciki da danasanin abinda ta
aikata wai itace a qirjin DREAM GUY dinta amma
takasa tantace komai wai hannuntane ya daki
abinda tafiso fiye da kanta a duniya,abinda
rashinsa yake neman hallakata Lallai dasake to
miyasa bai mata maganaba? lallai aljanine da
mutumne yanda yan school dinnan kowa keji
dakansa yakeji ubanshi wanine a duniya ba
namijin da zata mara Wllhy ya qyaleta, tay
kukanta har ta godewa Allah tay shiru ba nasara
atare da ita khair dai tazama yau ciwo gobe
lafiya..
Yau za'ayi general meeting a school dinsu bayan
antashi daga meeting din cikin mutane ta dauko
wani qaton cake tana tafiya zata karya kwana
kena benaxeer ta kirata ta waigo lokaci daya tayi
karo da wani mutum bata ankaraba taji
ankwasheta da wani wawan mari saida ta fadi
qasa.. ya nunata da yatsa ke mahaukaciyar
inace? idan kuna tafiya bakwa kallon gabanku?
Dayake bakusan darajar mutaneba ko? duk sai
mun muku hankali a school dinnan Wllhy, ya
juya ya wuce abinshi.. shikam aliy mamakin
duniya ya kamashi ganin yarinyarda sonta yake
wahalladashi yake fama da jarabar sonta ya
gane mutunce ba aljanaba, itace har yake
marinta anya lafiyar A.A lau kuwa??.
Benaxeer taji haushin abinda akayiwa qawarta ta
dagata tace zasu kaisu qara amma khair tace ta
shareshi bashida hankali.. a cikin zuciyarta kuwa
murna take ganin cewa wanda take qauna
mutunne ba aljaniba har yana magana yau
kwanan farin ciki tayi.. shiko A.A kwanan baqin
ciki yayi da danasanin abinda ya aikata,
shikanshi baisan dalilinsa na aykata hakaba
anya lafiyarsa qalau kuwa?? Dole ya nemi dream
baby dinsa gafara ko yasamu kwanciyar
hankila...
Share:

QARIN*********JINI--11

qarin-jini.jpg

QARIN JINI. 11


Yauda murnarta tafito zuwa lecture, sun kama
hanya zasu lecture sai girjin khair ya fara
bugawa nan tafara waige waige amma bataga
komaiba, tacewa bena su zauna suka samu wani
guri suka zauna bena tace bari in siyo mana
ruwa mushako tatafi sayen ruwa,sai gashi yazo
ya wuce A.A ya rude yacewa aliy Wllhy itace,
narantse da Allah itace muje kaganta batayi
kama da drawing dinda yake dakinaba kadubeta
da kew itace muje kusa da ita kagani tunda khair
ta hango dream guy dinta tasha jinin jikinta iya
tunaninta mafarkinda tasabayine yauma takeyi
sabida haka kallonsa takeyi bako motsa ido
sarkin gulma bena kuwa taje kawowa khai ruwa
datagayamata cewa shine tagani mai kama da
yayanta. Sannu yan mata, aliy yace da khair
amma khair ko motsi hasalima ita tunanin takeyi
mafarkinta ne takeyi, shiyasa kwata kwata bata
ga aliy da yake mata maganaba, batasan
dagaske bane aliy yay magana haryagaji Amma
khair ko motsi batayiba har aliy yaji haushi yace
Wllhy wannan ba mutum bace aljanace yaja
hannun A.A da qarfi ya tafi sabida kar shima
abin yashafeshi, suna zuwa gida A.A yafara kuka
ni kawai gida zan koma wllhy nagaji da rayuwar
qasarnan bazan iya haquri da dream baby naba
tun ina ganinta a bacci har na fara ganinta a fili
amma kuma bata magana aliy yay iya bakin
qoqarinsa akan ya haqura zai bincika masa
amma ina A.A har ya hada kayansa ya sayi
ticket sai naija..
Benaxeer zanje gida hutu ina yawan mafarki a
gida kamar akwai abinda suke boyemin haba
khair kullum fa sai kinyi waya da gida kuma
duka wata daya yarage afara exam kawai kibari
bayan exam mutafi tare,inafa oumulkhair harta
sayi ticket ta hada kayanta ta sai naija..
Yan uwa sunyi , murnar ganinta amma kuma duk
tay baqi ta lalace nandai ta fadamusu ita bazata
koma makarantaba ta bagayamusu ta hadu da
dream guy dinta a US amma wasu na mata
dariya wasu kuma suna cewa aljanin yanzu
harfito maki yake,? kowa da irin abinda yake
fada bata kulasuba sabida tasan abinda takeyi
itakam..
A.A yagayawa iyayenshi dalilin dawowarsa gida
Nigeria amma kowa dariya yake masa yaso a
gufula amma sai yace sunada gaskiya sabida
aikinsa yafi kama dana mahaukata.
Bayan kwana hudu da dawowata gida neda
qawata meena slow munje saloon mun fito zamu
shiga mota sai kawai naganshi nace meena ga
dream guy dina nan, wllhy shine yay sokoko
yana kallona, har meena slow tajani takaini
mota.. A.A yafara tunani tabbas yarinyarnan
aljanace yaza ai in barota U.S kuma inganta a
naija a naijama a garinmu agarimu ma a
unguwarmu nayarda dream baby na aljanace zan
haqura kawai in koma makaranta in barwa sarki
Allah komai...
Meenah kin ganshiko? Wllhy shine kamansu daya
da drawing dina.. Ke wai bakida hankaline??
Baki aiki da tunaninki? Ina iliminki ya tafi
khair? ?? kiga mutum ya tsaya kaman gumki ko
motsi bayayi sannan kice min wai mutunne kince
kin baroshi U.S sannan yau kwana hudu da
dawowarki sannan kiganshi naija a naijarma a
garinku, agarinkuma a unguwarku, sannan
kicemin mutunne in yarda nandanan khair
tayarda da maganar meena slow 100% gaskiya
tafada ko banza meena slow logically take
magana, ta yanke shawarar haqura ta koma
makaranta dan itama ta yarda da cewa dream
guy dinta ba mutumbane aljanine...
Share:

QARIN********JINI--12

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 12

Tagayawa iyayenta ta gano dream guy dinta ba
mutum bane aljanine ta kawo dalilajnta na hakan
kuma tace zata koma school kowa yaji dadi
ganin ita dakanta tagano abinda ake gayamata
shekara kusan hudu da suka wuce haka ta
tattara kayanta sai U.S dan chi gaba da
karatunta bena taji dadin dawowar khair school..
Oumulkhair tana tafiyarda rayuwarta cikin qunci
amma a boye bawanda yasani haka A.A shima
yana tafiyarda rayuwarsa shikin qunci da zafi da
radadi da azaba irin na soyayyah amma tin da
yadawo bai yiwa abokinsa aliy maganar dream
baby dinsa shima aliy bai masaba iya tunanin
aliy anyiwa A.A maganine da yaje gida shiyasa
bai taso masa da maganarba....
Kwana tara da dawowar A.A daga naija yay karo
da dream baby dinsa wacce yasakawa suna
aljana a ransa.. tabbas itace yaganeta da yake
ance aljanu sunada sauri tabishi naija, yadawo
nanma ta biyoshi amma koda aljanarce Wllhy
yanason ganinta kullum, shi tama shiga jikinsa
yafiye masa rahama yasan yana tare da
aljanarsa amma ina.. haka itama data ganshi
yanda yay tunani haka tay tunani qarshe tace
yashiga cikinta yafiye mata kwanciyar hankali
akwana atashi har sun saba da ganin junansu
wanda sun saka lokacinda koda basuda lecture
daya zaizo yabi ya wuce dan kawai suqa juna
bena tanason tayi gulma amma natakamata birki
kuma tana fuskantar wani abu sabida Lallai
Wannan pic din da yake dakinsu shine
mutuminda suke haduwa dashi kullum wanda
tun lokacinda ta fara ganinsa tagayawa khair
amma khair taqi aminta, yanzu sun dan rage
mafarkin juna sunga juna a zahiri kuma kowa ya
gane dayanshi. Ba abinda yake qara
tabbatarmusu da cewa aljanune sai duk
lokacinda daya ya fito to dole sai yaga daya a
hanya wanda idan ba aljaniba wazaisan randa
kake fita kullum da lokacinda kake dawowa yau
oumulkhair ta dauki alwashin cewa qarfe biyar
na safee zata fito idan ma aljanine ko mutum
sai ta gani kuma idan taganshi wannan lokacin
to koda kuwa zai kashetane saita yi mishi
magana.. abinka da jini daya A.A ma ya yanke
wannan shawarar yau zai fito kuma idan yaganta
sai ya mata magana.... da qarfe biyar dukansu
sunfito kowa ya biyo hanyar da yasaba biyowa
haka kuwa tariqa jin gabanta na faduwa idan
taganshi yanzu anya kuwa zata iya yimasa
magana? kanta a qasa tana wannan tunanin taji
tayi karo da mutum tangal tangal kamar zata
fadi ya riqota ya rungumeta....
Share:

QARIN*********JINI---10

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 10

Ta daga yatsa ta nunashi shima ya daga yatsa
ya nunata lokaci daya duka numfashinsu ya
tsaya anan suka zube sumammu.! Farkawan da
zaiyi yace Wllhy aliy yau na hadu da DREAM
BABY na.!! Wllhy naganta.! Miyasa bakwa yarda
da abinda nake gayamuku ne? miyasa kukeson
ku qaryatani? alhalin naganta da idona!, Wllhy
naganta aliy, bawai namaka gardamabane A.A
kawai kabari har kaji sauqi sai anemomaka ita,
ni na warke.!!! Loakaci daya ya fada hadi da
cewa.. Wllhy azabar da nakeji na rashinta ya
fiyemin zafi da radadi da ciwo akan duk wani
ciwo na duniya ya danne qirjinsa yace aliy kaga
nan? Yana tattare da wani wani dafi da azaba
da radadi da guna wasu zafafan hawaye suka
qanqaromasa, abinda nakeji bazan iya fadarsaba
a bakiba, bawanda zai iya gane mi nake fada sai
mai irin nawa ciwon wllhy aliy ina matuqar shan
azaba wayyo dream baby na...!!! aliy ka
taimakeni pls...!! Ya sake fashewa da kuka
kamar qaramin yaro aliy kuwa sai aykin rarrashi
har yaqaji amma bazancen yin shiru agun A.A,
yay kuka har barci yay awon gaba dashi anan
yay mafarkinta kamar yanda yake mafarkinta
wata tara da suka wuce sai dai yau sabanin
kullum da yake ganinta nesa dashi tana
nemansa, yau yaganta kusa dashi hartana masa
murmushi, tabbas yaji dadin ganin ta yau
yaganta a fili yaganta a zahiri, yafarka yacewa
aliy yau mutumiyar tawa harda murmushi tamun,
shidai aliy yana biyewa A.A ne dan kawai
azauna lafiya, amma yafi kewtata zaton cewa
yayi gamo da aljanane wacce take wahaladdashi
haka. Waya isa ya fada A.A yadaina yimasa
magana...
Wai lafiyanki kuwa tunda kika farfado kika rige
wannan drawing din na yayanki kina kuka kina
wasu magan ganu wayanda sam bana gane mi
kike fada, ki gayamin mana ko nasamu
kwanciyar hankali, benaxeer nagayamiki ba
komai kawai missing din gidane yake damuna
dan Allah kimin bayanin miyake damunki qarshe
tashige blanket dinta tabar bena tana zare ido
kamar wata mayya..
Hmmmm,
Tashiga duniyar mafarki taqanshi yana mata
murmushi karo na farko kenan da ta fara ganin
murmushinsa har wushiryarsa ta bayyana, yau
shekara uku da wata tara tana fama da azabar
sonsa, yay mata illarda duk wani ciwon so
yakewa masoyinsa,yay mata illarda koda
taganshi azahiri bazata taba amincewa dashiba,
tana balaenn son Wannan dream guy dinta
hartanajin cewa ta matsa kusa dashi amma ta
kasa, haka dai mafarkinta na yau ya gudana
wanda yasha bamban da kowane irin mafarki
nata tatashi cikeda farin ciki da jin dadi, abin ya
daurewa bena kai sosai yarinyar da ta kwanta
tana kuka kuma tatashi tana farin ciki anya kuwa
khair batada komai a cikin kanta? anya aljanu
basu shafetaba?
Nafi kewtata zaton jinnine bena takira
oumulkhair tagayamata abinda take tunani
gameda ita, khair tay dariya sosai harda kwalla
aranta tace (dama kinsan cewa ga abinda yake
damuna da kinfi gane cewa lallai aljanu sun
shafeni gida har ruqiya sukay min) khair
tagayamata cewa missing din gidane yake
damunta kuma tay mafarkin gida yanzu data
kwanta shiyasa tatashi da walwala..
Share:

QARIN********JINI---9

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 9

Ke dan Allah kimin shiru kin isheni da surutan
banza marasa ma'ana..!! yayana shi daqiqine
dazai zo gurina bai gayaminba,?? koshima
irinkine baqauye, ke wllhy kina US amma har
yanzu baki wayeba, mtswww.!! Benaxeer batace
komaiba sabida ita abin ya dauremata kai ta
tabbatar wanda tagani yanzu drawing dinsa a
dakinsu, itako khair tunanin da takeyi yaza'ay
taga mutumin da kwata kwata bashi a duniya,
b'ahalicceshiba sam, ta zana pic din dream guy
dinta ta manna ko ina a jikin dakinta, duk wanda
ya tambayeta sai tace yayantane, shiyasa sarkin
surutai da iyayi benaxeer tace taga mai kama
dashi, bena dai tanaso ta gamsar da qawarta
oumulkhair cewa taga mai kama da yayanta tay
alqawari daukarsa hoto dan ta nunawa
oumulkhair, tafito waje ta hangosu tazo dai dai
ta saita wayanta zata dauki hotonsa sai kawai
taji kukan mage dama benaxeer akwai tsoron
mage bashiri zata ruqa sai kuwa snow dinda aka
yi jiya yayi santsi sosai ya kwasheta kaji
teeeeeem..!! benaxeer a qasa samarinnan suka
fara yi mata dariya taji haushi sosai, kunyatai
kunyatai tatashi to koma gida bata gayawa khair
abinda ya faru da itaba dan kar ta mata dariya
ta fuske abinta, amma nasan benaxeer sarkin
gulma anji jiki,
Tashigo tun daga waje ta farajin sheshkar kuka
abin ya bata mamaki sabida tasan duk abinda
ya saka wannan mutakabbirar,mishkilar qawarta
mai girman kai kuka ba qaramin abu bane, nan
da nan ta rudee lafiya khair tay juyin duniya
akan ta gaya mata abinda yake damunta amma
taqi fada garshe da tagaji da nacin bena sai tace
mata tay missing din gidane a dole bena ta rabu
da ita.. tabbas yanzu dream guy dinta yay mata
illarda ko karatu bata iyayi, tanajin jiki sosai,
(tabbas abbana gayamin cewa soyayyah
nada balaen zafi kullum sai gasganta maganar
ta nakeyi,) takai ta dawo khair ta daina zuwa
class bena tai iya qoqarinta tagayamata abinda
ke damunta amma ta kasa ita iya saninta
oumulkhair batada wani saurayi wanda suke
soyayyah dashi balle tace soyayyah takeyi, kuma
iya fahimtarta tagane cewa khair soyayyah ce ke
damunta, tunda take da khair bata taba ganin ta
kula saurayiba ko tay tadin saurayiba, sai dai
kullum karatu kamar Al huda huda amma kuma
yanzu tadaina karatu miye dalili oho? Kodan
gulma tanason taji dalilin kukanta da kuma
dalilin rashi zuwanta clss, yan kwanakinnan sai
dada ramewa take yanzu hartafi (abokiyar
kararun hauwa jabo ruqayya ramewa) sai ido
abin sai wanda yagani, tabbas ina tsananin
tausayawa khair halinda ta samu kanta a ciki na
soyayyah da wanda bata saniba, yau benaxeer ta
lallabata zasu tafi lecture amma kuma kwata
kwata badason ranta zatajeba, ana tsakiyar
lecture kawai taji ta gaji tafito zata koma hostel
tana tafiya kamar wacce qwai ya fashwa aciki
sai taji wani abu ya daki qirjinta wanda bata
taba jin makamancin irinsaba sai kawai ta dago
kai har ya wuce shima ya dago kai lokaci daya
suka kalli juna....
Share:

QARIN*********JINI---8

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 8
Na muhammad
Laaah khair..!! kalli a notice bord abinda ake
nema, ke wllhy benaxeer kin cika kalle kalle ki
riqa jan clss dinki mana, mtsww..!! sai tay shiru
batace komaiba,
Yau kusan kwana hudu kenan muna wucewa
muna ganin wannan takardar a ko ina an liqa,
yau takardar ba kamar sauran takardunba ba an
fadada takardar, anyi kira najan hankali da
kalamai na tausayawa laa khair kalli wannan
abun na duba ina dubawa naga ana neman jinine
a qarawa wani kuma ma wanin dan qasatane
dan garinmu kuma group blood dinmu daya,
yanzu su turawa duk iyayinsu sukasa yin wata
dabara sai sun nemi jini a gurin mutane lokaci
daya idona sukakai qasan takardar akecewa wai
jinin dole yazama na dan Nigeria kuma musulmi,
haba nai mamaki ace turawa su rasa yanda
zasuyi ashe sharudda yasaka bari muje muyi
sadaukarwa ai dole in tai makamasa naija ba
wasaba, naja benaxeer mukaje clinic din
makarantar nagayamusu dalilin zuwana suka
dibi jinina roba uku suka karbi sunana da komai
nawa na qara gaba ban qara jin labarin
mutuminba wanda yanzu na tabbatarda cewa ya
warke haka kawai naji inason sanin waye mai
irin jinana? waye aka sakawa jinani? Harnagaji
da tambaye tambayena..,
yan kwanakkinnan nacika mafarkin guy dina
wanda a mafarkin nake ganin shima yana
nemana maimakon ada da nake ganin sa kawai
a zaune yanzu ko yanata nemana amma kuma
nay masa nesa baya ganina. sai daga masa
hannu nakeyi amma baya ganina, mafarkina
gabadaya ya chanza yanzu abun yana balaeen
damuna na rasa yanda zanyi sabida wanda nake
muradi gashi yana nemana amma ya kasa
ganina kullum sai nay kuka akan wannan abu
sabida wllhy nafi shiga tashin hankali akan da,
da kwata kwata baya ganina ni kawai nake
ganinsa amma yanzu shima gashi yana nemana,
wata zuciyar tacemun duk shedanne yake
jaqulamiki tunani ina tsaka da kuka saiga sarkin
surutunnan benaxeer tashigo da sabon labari
sam ban kulataba sabida nasan tasaba da
surutanta,tace wai yau khair wllhy yau naga mai
kama da drawing din yayanki a school dinnan,
kizo ki ganshi gashichan gaban hostel dinmu
kadan, my be yayankine yazo miki visiting wllhy
kamansu daya, oumulkhair kizo kiganshi
mana....
Share:

QARIN*******JINI---7

qarin-jini.jpg

QARIN JINI .7
Na ABBA GANA
Duk wani shiri da yakamata inyi na wucewa US
nariga nayishi visa, ticket, komai na hannuna,
nashirya tsab abina murna kuwa agurina
ba'amagana haka kawai Allah yasakamin son
AYNN ta US tun ranarda naga tallar school din a
internet sunayi naji inason tafiya school din
shekara uku kenan daidai da shekarun da nay ina
mafarkin GUY dina.,
Nayi bankwana da yan uwa da abokan arziki,
dangi na jini har airport suka kaini garfe 5:40am
jirginmu ya tashi sai US amma gaskiya mun
zaunu, na isa Florida a US ana sanyi wanda
bantaba tunaninsaba nay waya a numbr da aka
rubuta a jikin admission letter dina akazo daga
school aka daukeni na isa school din iya haduwa
school din ta hadu, duk wani iskanci idan kana
nemansa a school din zaka samu abin mamaki
yayan musulmai baka tantancesu da yayan arna
wllhy kowa abinda yaga dama yakeyi ba wanda
yake musu fada, dole babana ya hanani zuwa
wannan makarantar dan gudun gurba cewar
tarbiyata Allah ya tsareni daga sharrin maza da
mata ilahee ameen...
Yau wata na daya da zuwa AYNN. Mafarkinda
nake da dream guy dina ya chanza dan yanzu
yana kusa dani sosai yana lillonsa, naji dadin
haka sosai, tun danazo school din nay wata
qawa mai suna benaxeer kwata kwata yarinyar
batamun ba amma sai wani lilleqemun take
bayanda zanyi sabida ko banza itama akwai
riqon addini kuma tanada ra'ayin kanta, amma
batada clss sosai ga surutun tsiya kai ni badan
kartace na qitaba da bazanyi qawance da
benaxeer ba wllhy, amma ko ba komai benaxeer
tana son karatu sosai wanda yasa nake dan shiri
da ita amma ni banason surutu, rayuwar
makaranta tamun dadi wanda yanzu kullum
sainay mafarki da guy dina kuma kusa dani
kadan...
Yauma kamar kullum nashirya nida qawata da
yake ba course dinmu dayaba amma muna wasu
gens tare da ita, muna tsakiyyar tafiya sai taron
mutane muka gani sun tsaya sunyi circle suna
kallon wani abu muna kawowa benaxeer tace sai
munje muga mi yake faruwa nikam nace ta
sameni a hall bazanjeba haka kuwa bena ta
kwashi jiki ko kunya taje kallo tana university
amma tana harkar yan primar, sai da ambulance
tazo da daukeshi sannan tadawo, tazo duk
jikinta a mace tabani labari wai wanine ya saka
takalmin taya bai iyaba ya fadi, kanshi ya daki
wani qarfe shine ake kallo danina da bena akwai
tsoro, nace Allah ya tsare gaba...
Share:

QARIN**********JINI--6

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 6
*********by**********
muhd-Abba~Gana


Gari ya waye ta shirya ta dauki key din motarta
tacewa yaya naziah zata wuce gida don jin kiran
mamarta,
Taje gida tagaida yayyenta da masu aikin gidan
tana shiga dakin mamarta taga wani malami da
uban rawani akansa da kuma littafai a gefensa
ga wata jaka a hannunsa ta gaisheshi cike
damamaki mi malami yakeyi a pallon ummarta
tunda safee,? ta wuceshi taje gun ummarta tana
zuwa ta fada jikin ummarta tafara shagabar da
tasaba, ga mamakinta sai taji umma tana kuka,
lafiya ummah,.!!?? Umma batace mata komaiba
ta goge hawayenta tace mata taso muje, tun
qarfe shida na safee malam isuhu yake jiranki,!
Waye kuma mlm isihu ummah,?? nidai taso
muje zaki san ko wayeshi yanzu, ta kamo
hannuna muka fito, muna zuwa tacewa mlm
isihu gatanan malm, nidai cike nake da mamaki,
tanuna masa ni ya quramin ido sosai chan sai
yace hajiya yarki lafiyarta lau, aah mlm kaduba
dakew dai kagani my be boyewa sukayi, sabida
gaskiya suna damunta dayawa, ni bangane mi
suke magana akaiba, na saka musu ido inga ikon
Allah, mlm isuhu yay hayaqi a dakin ya fara
karatun qur'ani awarsa daya yana karatu, amma
nikam ko gezau qarshe dai yacewa ummah
dama yasan lafiya ta lau, akace na shiga daki
sukai maganarsu ta sallameshi ta dawo daki,
ummah ta fara tambayata mi yake damuna bana
mugayen mafarkai? araina nace (nikam dream
guy dina kawai nake gani a marki) nace aah,
ummah tace to waye dream guy..? Gabana yay
mummunan faduwa wato ana nufin aljanune
suka shafeni kenan ? Wato ruqiyyah akamun
dazu kenan ? To wllhy lafiyata lau ba wani
aljani, wato yaya naziah qarata takawo gida
kenan.! ANan mukay maganar da umma
nagayamata abinda yake damuna tun farko har
garshe tun lokacinda na fara mafarkin mutumin
har zuwa yau ta bani shawarwari tace kuma duk
zan kwanta in riqa addu'a nace mata tooh na chi
abinchi nadawo gida gun yayata mai qaunata
naziah 
Kwaniki sai dada gaba sukeyi a family dinmu
kowa yasan dream guy dina hatta baba yayi
fada har yagaji ya barni, abinda yafi baiwa
iyayena haushi rashin kula samarin da nakeyi,
yauma kamar kullum naje zana jarabawar shiga
university karo na uku kenan, yauma bata
jarabawar nay nadawo gida abina sabida ni
AYNN nakeso a rayuwata idan bachan aka kaini
karatuba bazanyi karatuba gaskiya meena slow
har takai 300lv a university amma ni gani gida
ala dole sai AYNN...
Bayan result din exam ya fito akaga banciba,
amma kuma AYNN sunkarbeni sai kawai baba
yace ya amince inje Aynn din Allah ya taimaka
amma da sharadin inmasa alqawarin zan kama
mutunchina banda kula samari araina nace;
(Inada saurayina dream guy dina mizan yi da
wasu samarin)...muhd-Abba~Gana
Share:

QARIN**********JINI--5

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 5

********by**********

muhd-Abba~Gana

09039016969

Yauma kamar kullum da wuri ta kwanta bayan
yaya naziah taymata fada sosai yanzu har ta
saba da fadan batajin komai tama qagara ta
qare fadan nata taje takwanta, ta kwanta bacci
bay dauketaba ta qagara ya dauketa tay bacci
ko zata hadu da masoyinta, burin rayuwarta,
abin qaunarta, dream guy dinta, takai qarfe
Goma na dare tana mulmula akan gado amma
bacci yaqi daukarta sai rufe ido take tana
budewa, da tasan inda zataga bacci data kirashi
yazo ya dauketa koda da kudine xata siya, dan
kawai taga burin rayuwarta a haka har tay
bacci. Yauma kamar kullum taganshi a wani
lanbu da suka saba haduwa dashi,yauma sam
bai kulataba, dama chan idan taganshi sai dai
tayi ta kallonsa tana murmushi amma baya mata
magana bata mishi magana wannan ganin da
take mishi ya fiye mata komai dadi a duniya bata
taba jin muryarsaba bata taba ganin dariyarsaba
sai dai taga yana lilo abinshi hakan na matuqar
burgeta kuma tunda take mafarki dashi bai taba
waigowa ya kalletaba saidai ita tayi ta kallonsa,
a haka har akayi kiran sallar asuba tatashi tay
sallah takoma bacci gari ya waye taje tagaida
yayarta, tatararrda har tafita ko ina tajee oho.?
Har qarfe biyu na yamma bata dawoba ta shirya
abinchi taci ta ijeyewa yayarta sauran guraren
qarfe uku tadawo bayan ta gaida yayarta yaya
naziah tace kije gida umma na nemanki, tace to
bata damuba sabida tasan mamarta bata mata
fada sosai dadai big boss ne wato baba to kuwa
da ta shiga uku sukai hira ita da yayarta kamar
ba komai a tsakaninsu har dare yay taje ta
kwanta da wuri dan taga dream guy dinta....tab! za'ayi masoya a mafarki


muhd-Abba~Gana
Share:

QARIN**********JINI--4

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 4
********by**********

muhd-Abba~Gana


Tunda oumulkhair taji saugi ta dawo gida take
wani mafarki mai ban mamaki da ban al'ajabi,
kuma kullum saitayi mafarkinnan kuma iri daya
kuma na abu daya, tun abin baya damunta har
yafara damunta, tun bata baiwa abin
muhimmanchi har ta fara bashi muhimmanchi
takai ta kawo idan khair batayi wannan
mafarkinba sam bata jin dadi ajikinta ahankli son
wannan mafarkin ya kamata, bawani abu bane
illah wani GUY da take gani kullum acikin
barchinta, sonshi ya kamata har yana neman
illatamata rayuwa har yanzu yakai idan batay
mafarkinsa sam bazata taba samun sukuniba
idan wani abu kakeso gurin khair sai ka roqa
abaka albarkacin dream guy dinta, batada tadi
sai na dream guy dinta tun tanayi tsakaninta da
qawayenta harta gayawa yayarta naziah, da
farko ya naziah abin wasa da taukeshi har tana
tsokanan yar qanwarta da dream guy dinta, idan
tanason aiki sai ta hadata dashi nan danan zata
mata aikin kuwa, har yakai ya kawo naziah
tagane abin na khair azimunne, baranarda zata
fito ta koma ga mahallinta batare da khair tayi
zancen dream guy dintaba, tun yayarta na mata
fada ahankali hartakai fada sosai take mata
amma khair ko a jikinta kullum wutar son
Wannan guy dada ruruwa yake a cikin zuciyarta,
duk wani saurayi nata ta koreshi yanzu batada
saurayi sai dream guy dinta, gashi son dream
guy dinta sai qara azabtar da ita yakeyi har
yafara mata illa ajiki dama ita ba tada wata
qibar azo agani sai qara lalacewa takeyi (takoma
kamar wata abokiyar karatun abba wato
maryam wacce bakomai ajikinta sai qashi
kamar abusa ta fadi su maryam anji haushi, lol)
haka khair itama ta koma yau shekara biyu da
wata shida oumulkhair nafama da wannan
mummunar lalurar wacce ba wanda yasan ina ta
dosa.....


muhd-Abba~Gana
Share:

QARIN**********JINI- 3

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 3
********by**********


muhd-Abba~Gana


Sanadi.......
Ranar khair tafito daga wani super market zata
tsallaka titi tashiga motarta kirrrrr..!! Kikaji wata
motar tay sama da khair wace tuni tasuma agun
hannunta na hagu ya karye dama ita bawani jiki
mai kwariba nandanan ta karye a hannun sauran
jikinta yaji ciwo sosai,, jikin mutumin yana rawa
wanda garin sauri yaje yakai qaninsa airport zai
koma hutu yau, Wannan mummunan al'amari ya
faru, tuni ya dauketa ya nemi police daya yakaita
hospital aka admtn dinta anyi treating dinta
yanda yakamata, aka daure kariyar da hannunta
yayi, Dr yace sai ansaka mata jini sabida jininta
ya zuba sosai, duk aka zagaye hospital dinnan
ba jinin da yake mata mutumin ya dauki
wayanta ya lalubo numbrs din iyayenta yakira
gidansu yagayamusu abinda yafaru bashiri suka
rabazo asibiti duk family dinta ba jinin ko daya
da yake mata abin duniya ya ishi wannan bawan
Allah daya kadeta gashi Dr yace nanda 24hrs
komai zai iya faruwa idan dai ba'asaka mata
jininba sabida jininta ya zuba, gashi duk saurinsa
na xuwa airport saida qanin nashi yay missing
fly, sauri ya haifi nawa kenan, yace agwada
nashi jinin shima yaqi yayi, haka jiki ba qwari ya
koma gida yagayawa matarsa da iyayensa
abinda ya faru nandanan hankalinsu yatashi
basuda mafita, sai qaninsa abdullahi yace
agwada nawa mugani ko zai mata? yayanshi ya
banka mishi harara, yace ai duk kai ka jawo,
kuma konawa jinin baimataba naka zai mata
abdul yace ai dama group din jininmu ba daya
bane da naka, nandanan sai yayanshi yace eh
hakane kuma muje a gwada nakan mugani, suka
kwashi jiki sai hospital aka auna jinin abdul abin
mamaki nan danan ya dace da jinin khair, aka
dibi leda uku aka saka mata,bayan awa biyar ta
farfado ai kuwa yayan abdul yaji dadi sosai
ganin ansamu jinin da yay mata jinin ma na
qanenshi, khair dai tay jinya har tawarke sarai ta
koma gida....


muhd-Abba~Gana
Share:

QARIN**********JINI 1 &2

qarin-jini.jpg

QARIN JINI MARUBUCI MUHAMMAD ABBA GANA

QARIN JINI 1


Na abba~gana
Rufemin baki wawuyar yarinya wacce batasan
abunda takeyiba..!! Wllhy oumulkhair idan bakiyi
hankaliba sai na gayawa umma abinda kikeyi
wawuya kawai..!! ana miki magana kin sakowa
mutane ido kamar wata mujiya, ki tashi kibani
guri mashirmaciyar yarinya kawai..! Yaya naziah
wllhy...... Wallahi me!? rufemin baki duk abinda
zaki fada maimaitawane na dade kina gayamin
haka, tafada cikin fushi.. kawai niki bacemun da
gani.!
Sumui sumai tatashi tay dakinta...
Tabbas nima nasan abinda nakeyi yasabawa
hankali kuma bawanda zaiji ya saurareni har ya
bani uzuri idan har mai hankaline, toni ina zan
saka rayuwata.? Banida abokin da zangayawa
matsalata ya saurareni hatta meenah slow
qawata wacce muka tashi tare da ita
nagayamata matsalata, amma sai dariya kawai
tamun, sun maidani mahaukaciya wacce batasan
mitakeyiba, kumafa hakane banida maraba da
mahaukaciya, garama mahaukaciya tasan cewa
haukan takeyi nifa ata qaice dai mahaukaciya
tafini..
Cox ni abinda nakeyi bashida dalili ko kadan,
wasu zafafan hawaye suka gangaro akan
kyakyawar fuskata wacce rabon datasaka mata
powder tun kamin mota ta kadeta akaita asibiti,
naci gaba da kukana wanda yazamomin sabo
yanzu, har akay kiran magriba sannan natashi
na dora arwula nai sallah da addu'oena dana
sabayi bayan duk sallar magrib har akay esha
itama nayi sannan nazo nakwanta inyi barci da
wuri ko zanga DREAM GUY dina......!!

QARIN JINI.2


Na abba~gana
OUMULKHAIR yarinyace kyakyawa wacce basai
natsaya muku bayanintaba duk inda ya mace
takai a kyau oumulkhair takai inda Allah yayta
mara qiba amma akwai hips sosai a tare da ita,
in shot oumulkhair tanada kew na jiki dana fuska
tubarkallah masha Allah khair ta hadu wallah, da
kunsan wata qawar jabo ummu rubab, dasai
nacee muku oumulkhair tafita girman kai, daji
dakai, da daukar kai, da yanga da gayu, da
kwalliya, tabbas khair akwai girman kai sosai
wacce idan tanason abu saidai ta mutu bazata
iya cewa abatashiba ita dole kar mutunchinta ya
zube ko clss dinta ya ragu hmmmm. khair
kenan....
A gurin yayarta naziah tagirma wacce suke uwa
daya uba daya, nazia bayan aurenta da shekara
takwas Allah baibata haihuba sai ta dauko
qanwarta oumulkhair tadawo gurinta tun tanada
shekara goma har yanzu da takeda shekara 18
agurin yayarta take, iya gata mijin yayarta yaya
rabiu yana nunamata,baya bari amata fada ko
kadan wanda kullum ya naziah ke cewa shiya
batata, babanta kuwa dama kaman bayasonta
kullum fada yakemata dukda cewa itace autar
gidansu amma sai fada shiyasa banatason zuwa
gida dan gudun fadan su baba,
Taqare secondary school dinta shekara biyu da
suka wuce, yanzu tanason tay applying a AYNN
US.amma babanta yaqi barinta taje karatu
aqasar, wai ba addini a gasar tofa kaji iyayen
addini baban su oumulkhair.
Yanzu dai shekara ta biyu kenan tana zana exam
na shiga university a naija nata rubutawa ba dai
daiba dan kar taci kuma tana faduwa, amma
AYNN Kuwa wannan shekaran ma sun karbeta
amma tsohonta yaqi yarda da tatafi qasar
karatu tofa.....

muhd-Abba~Gana
Share:

SHIN KUN SAN ABINDA YAKE YAWAN SHIGAR DA MUTANE WUTA???

shyk-muktar.jpg

Daga Dawud bn Yazid, daga babansa ya ji Abi
Huraira yana cewa: Manzon Allah (SAW)
yace :"Shin kun san abin da yake yawan shigar
da mutum wuta? Sahabbai suka ce: Allah da
Manzonsa ne suka fi sani, Sai yace: su ne
Al'aura da Baki/ciki..
Kuma abinda yafi yawan
shigarwa Ajannah sune: Tsoron Allah da
kyawawan dabi'u". [Adabul Mufrad hadith 289].
Kenan yana da kyau mu kula da abin da muke
kaiwa bakin mu, mu tabbatar halal muke zuba
ma cikin mu. Sannan mu kare kan mu daga
shiga gonar da ba namu ba, mutum yayi aure
idan yana da halin yi, idan kuma ba yi da halin
yi sai ya bi koyarwar Annabi don ya kare kansa
daga zina. Allah ya aiko Manzonsa ne (SAW)
don ya koyar da mutane kyawawan halaye da
dabi"u. Don haka mu zama masu kiyaye
dukkanin dokokin musuluci.
Allah Ya sanya mu
daga cikin bayinsa masu rabo. Allah ya sada
mu da dukkanin alkhairiai da albarkatun da ladan
da yake cikin wannan Rayuwa.
Source:
muhammad abba gana
Share:

WACE CE****ITA? 98-99-100 (karshe)

computerimages1.jpg

*********by*********

muhd-Abba~Gana


To amaryaf taxo ina daidai da ita, yadan
muskuta dama akwai wata yarinya Dana gani ta
kwanta min arai inaga xan kawoma su Yy
Suhaila ita tunda tanason anti amarya, Yy
Suhaila suke kiran Yar tasu da ita.
iffaat hararanshi tayi tace wallahi baka isaba,
yayi dariya yace kefa kika ce taxo kina daidai da
ita,! Ta fuske tace eh ta murguda baki, farhaan
yayi dariya ya tashi ya shige, har yakai qofar
bayi bari nayi wanka xan kawo miki ita ki
ganta..
Iffaat kam taji ba daidaiba, harya fara wanka ta
kasa haqura ya fito ta bishi bayi Yy farhaan
waida gaske kakeyi? Yayi dariya sosai sannan
yace eh mana ya wanke ko ina xai dauraye jiki
ta kashe fanfo ta fara bala'e wallahi baxai
yiwuba, ai wannan sharrine, yace aah kinji
yarinya ke kinxama chuss dole na dauko sabuwa
a Leda na bare ta kenifa sai nayi mace hudu Dan
ki sani, kii kunna min ruwana mana, ta fara
kuka, wallahi sai ta gayawa umma yace umma
ai xataso a kawo mata sabuwar suruka ta haifo
mata jikoki, ba kece kin daina mini wankaba ai
dole na nemo mai mini wanka Dan ni Dan lelene,
cikin kuka tace xan riqa maka wanka wallahi,
yace to ki fara yanxu, ta kuwa kunna ruwa tamai
wanka Tass suka fito ta shirya shi sai yan
hawaye takeyi, abin yabana bashi dariya ba
kadan ba, tana zaune saiga Yy Suhaila ta shigo
iffaat tace ke get out masu tsokane tsokane
kawai, yarinya tayi tsaye bata gane dawan
gariba, farhaan yace Yy Suhaila kuje wasa kinji
yarinyar anti amarya tace yeeeeeeeee ta tafi da
gudu, farhaan yaga yanda iffaat ta hade fuska ta
miqe da qarfi zata fara yankomai bala'e ya
janyo ta ta fado jikinsa haba Yar gidan umma ni
na Isa na qara aure yanda nake da mace kamar
ki ai kin wuce 1 of 4 ke ta dabance kullum sweat
kike qarawa, ya fara kissing dinta, tace bayan
kace min chuss yace wallahi wasa nake miki
kinfi komai daraja a gurina kece sanadin
shiryuwata kuma kin haifomin Yaya masu kyau
masu kama dake, ta qara shigewa jikin sa tana
mai nata salon nidai sai na fito na basu guri
suci soyayyah kar na makance,....
TAMMAT BI HAMDILLAH....
Qarshe wannan littafin kenan
Ina godiya ga dinbin masoya da suke bibiyar ta a
wannan Dan qaramin littafi na WACE CE ITA.. ina
godiya ga masu bani shawara da Masu mini
gyara hadda masu zagi ban barku a bayaba ina
godiya matuqa Allah ya saka da alkhairi,
Nasan hausar tawa sai a hankali kuna qoqari
gurin karantawa...
... sai mun hadu wani book mai
suna..........."QARIN JINI"
nagode sosai
Don shawara ko gyara ga number ta +2349039210365
Banda tambayar wane guri nake please...
MUHAMMAD ABBA GANA ke muku fatan
alkhairi.
Share:

WACE CE***********ITA? 95-96-97

computerimages1.jpg

Hmmmm.
Wai har sun shirya an yafi juna sunci abincin
tare...
Wata sabuwar soyayyah ce a Gidan ma'auratan
gwanin bansha'awa suna kula da junansu yanda
yakamata.
Yanxune iffaat take fahimtar abinda armiya'u ta
taba gayamata na cewa farhaan bamuqacine na
gaske lallai hakane kullum dai yajishi ciki
uhummm.
Abin ba'a cewa komai.
Iffaat ta cika alqawari takai goggo makka kuma
ta dauko qawayenta na qauye dije da rukayya an
baiwa mazajensu lebaranci a companyn su
farhaan suna shanawa suma ga dukkan alamu
suma su waye su xama yan gayu, amma bana
tunanin dijee zata waye Dan har yanxu tana nan
sai a hankali..
Bayan shekara 7
Koda naxo naga iffaat da yara uku mamaki ya
kamani naso naga iffaat da ciki amma ina
banganiba sai yayanta na gani..
Mace daya namiji biyu
Macen taci sunan Suhaila sai maxan dayan
sunan mahaifin iffaat mahmoud dayan sunan
mahaifin farhaan habeeb.
Farhaan ya zama kamilallen mutum kamar
bashiba, iffaat kam har yanxu saidai idan
ba'asamu damaba..
Dan Ko yau da ni abbagana naje muku gidan, saman bishiya
na ganta tana tsinkowa tana wurgowa qasa
yaranta suna cabewa sunata jin dadi, farhaan ya
shigo ya duba bata yasan ina taje ya girgixa
kai, yaje ya kirata tana ganinsa ta diro saman
bishiya saida naji tsoro na dauka ta karye sai na
tuna fiye da wannan ma tayi..
taje ta rungume shi tanamai oyoyo yace bawai
na hanaki hawa saman bishiya ba, ta kanne ido
tace waya iya raba monkey da hawa bishiya
dariya yayi ya tuna lokacinda tayi mai fitsari
saman bishiya yace monkey ne,
Suhaila ce ta shigo itada habeeb cox shi
Mahmoud jinjirene, Suhaila da wayo tace Abba
mu anti amarya mukeso.! gidansu hameed na
uncle Ali an musu anti amarya kullum sai yace
mana mu bamuda anti amarya, muma munason
anti...kaji jaraba!. iffaat tace kiji yarinya da gulma xanci
gidanku yanxu, ba anti amyaba anti ango bace
min da gani, sakarya kawai...!!
Suhaila ta wuce tana gunguni,
Farhaan kam dariya yakeyi sosai, iffaat ta
kalleshi miye haka.?? Daga jin anyi xancen
amarya sai wani washe baki kakeyi...toh fah zai karane kodai?muh-Abba~Gana
Share:

WACE CE*******ITA? 94

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??94
na ABBA GANA
kuka take tamkar ranta zai fita,
Yaxo yana lallashinta yana bata haquri ya samu
ya mata wanka da gashin jiki yayi toweling dinta
ya kawota daki gaskiya taji jiki ba kadan ba
bakinnan nata haka ya mutu murus kamar ba
itaba, ba'ajima ba sai xaxxabi, farhaan shi
kanshi yasan bai mata dakyauba yama manta
sabon shigace an saba da masu wakeken abu
shiga daya kamar an kada guga a rijiya, wannan
kam a tame take fam shima da gyar ya samu
shiga, ko Suhaila ma kusan haka take but na
iffaat yayi yawa,
Ya kira Dr. su yamai bayani ya kawo mai yan
magunguna ya tayar da ita ya bata taqisha yayi
yayi amma taqisha sai rawar dari take ga
xafinda takeji a gurin, itakam ji take kamar ma
ya yageta, farhaan dai anyi jinyar iffaat bata mai
magana Sam, ko kallonsa ma batayi idan yaxo
rufe idonta takeyi yaxo yayita surutansa ya gaji
ba amsa...
Kwananta uku a kwance ko lecture bata xuwa,
ranar na hudu ta tafi skull, bayan sun fito lecture
ta hadu da armiya'u suna tadi armiya'u dai
kullum maganarta daya a kyautatawa miji a sha
Abu Dan qara ni'ima, iffaat ta kalleta, ke kullum
xance daya abinda ko dadi babu! Armiya'u ta
kalleta tayi murmushi yarinya baki maida
hankalinki bane abinda kawai zance miki wallahi
so sweat, iffaat kam bazata iya fadar cewa sai
yanxu ta shigo system ba sai ta basar da
maganar...
Ta dawo gida taga farhaan zaune batako
kalleshiba ta wuce daki tayi wanka ta fito taje
tayi girki, ta kawo mai yace dauke abinki
baxanciba kamar bataji mi yake fada ba ta kama
hanya ta wuce abinta janyota yayi da qarfi nace
ki dauke baxanciba, kallon mamaki tamai taga
yanda ya daure fuska aranta tace ai tunda ka
biya buqatarka shikenan banida daraja. har
zatayi magana kuma sai ta fasa da duqa zata
dauki abincin farhaan ya janyota wato daukewa
zakiyi ko? Bazaki tambayeni dalilin yin hakaba,?
Haba iffaat miyasa kike min hakane? kuka ya
kubce masa iffaat miyasa kike min hakane
eeeh ? Kullum kina azabtarda zuciyarda ta
damfaru da qaunarki, Dan kawai Kinga na damu
dake matseta yayi sosai jikinsa itama dai
hawayen suke xuba a idonta, ta fara magana
tana kuka basai na kawo mukuba kawai akan
Neman matanshine shi kuma yace tuni ya daina
koda bata aminta 100% ba amma taji ta
gamsu....
Share:

WACE CE********ITA? 93

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??93
Na ABBA GANA
Tamai sannu da zuwa, ya amsa bayan ta juya
ya kalleta mace kamar hawainiya sai chanxa wa
takeyi, yaje yayi wanka.
ta kawo mai abinci Dana safe Dana rana na
yamma ma Dan ba yanxu yakeciba da sai ta
hado mai dashi kuma duk sai ya cinyeshi, ta ijiye
tace yaci wai ya qoshi, tamai kallon banxa kasan
Allah wallahi sai kacishi, ya kalleta yanda ta
hade fuska hakadai yayita durawa yana qarewa
yaje yayita amai ko sannu bata cemaiba yana
fitowa tace Allah yasa dai matan basu maka
cikiba!! dagachin abinci sai amai ta bashi dariya
sosai wai ciki, ya nemi guri ya zauna, bai
tankataba haka dai iffaat take da farhaan kullum
cikin yi masa habaici take, da rana taci uban
kwalliya da dare ta saka arnan kayan bacci ta
kuma fuske abinta, ranar da ya qara nemanta
tace sai yaje asibiti an duba shi idan bashida
rashin lafiya, farhaan kam ya shiga uku kullum
cikin baqin cikin yarinyar nan yake, lallai yanxune
yake sanin haqiqanin WACE CE ITA... dama
hausawa sunce Dan hakin daka raina shi yake
tsole maka ido, ai kuwa ga iffaat tana wanashi
Son ranta, farko yace bazaije asibiti ba daga
baya da yaga jan ran nata yayi yawa sai tsingau
yakeyi haka ya daure yaje aka dubashi, lafiya
lau yake ya kawo mata result tana kwance da
kayanta na daukar allhaki ta tashi zaune ta
duba taga lafiyanshi lau tace saura Abu daya
kuma yace bayason yaji ko miye wallahi sai ta
bashi haqqinsa, iffaat taga da gaske yakeyi
idonsa sunyi jaa sai xuba masifa yakeyi
hankalinta ya tashi tasan ba hanyar guduwa
amma ta fuske ta nuna kamar bataji tsoroba
farhaan kam matseta yayi ya cire mata kaya
duka cizo duk yasha amma ina saida yayi
nasarar kawar da budurcinta Allah sarki iffaat ta
bani tausayi.....
Share:

WACE CE*********ITA? 92

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??92
Na Abba gana
Yana shigowa ko kallonsa batayiba, duk kunya
ta kamashi, gashi ma abinda yajeyi ya kasa
aikatashi ya Dan Sosa kai yace bakiyi bacci ba!?
Tace nayi faarkawa nayi yanxu, yaga kamar
batayi fushiba sai ya matso kusa da ita zai
zauna tayi xunbur ta tashi kada ka kuskura ka
matso kusa dani tamai kallon raini kamar taga
wani kashi,
Ta kalleshi ai shi mai hali baya barin halinsa
tunda ka saba da Neman mata wallahi ba abinda
zaisa ka daina, ya xa'ayi na iya bacci bayan na
auri miji manemin mata, ido cikin ido ta kalleshi
tace farhaan nayi Dana sanin aurenka, nayi
baqin cikin kasan cewa tare dakai, babban abin
godiya ga Allah shine ba'abinda ya shiga
tsakaninmu, bare ayi xancen hada zuri'a na
tabbatar da yarana sai sunyi baqin ciki da
samin uba mazinaci irinka.!! Amma yanxu kaga
Hankali kwance zan nemi wani miji nayi aurena
kuma wallahi saina fadawa umma halin da kake
ciki..
Farhaan zuciya tayi xafi waishi take gayawa zata
nemi miji tayi aure, yaso ya mammaketa amma
sai ta wuce shi nan ya zauna yana Allah
wadaran halinsa yayi tsaki yafi sau dubu ya kasa
shiga dakin har bacci ya saceshi, iffaat kam ko
dar bata ga bacciba gari ya waye kamar kada
tamai breakfast Amma ta daure ta hada mai
taxo tasa qafa ta shureshi ya tashi, ta kalleshi a
wulaqance tace to aje ayi wanka a tsarkake jiki
ayi sallah, a karya aje gun Neman wasu matan,
aranshi yace wai dan wulaqanci da qafa xata
tayar dashi yaji bala'en haushi Dan kuwa da
atayar dashi da qafa gara a gyaleshi, kuma ga
magan ganun banxa tana gayamai ya kalleta
waike waya gaya miki Neman mata naje?! Cikin
isa da tsabar rasjin kunya Tace sabida ba
namijin kirkin da xai bar gidansa 12 na dare ya
dawo 3 sannan yace ba gun banxa yake
zuwaba, bare kaida akasan halinka na Neman
mata....
Farhaan dai ya kasa magana yayi wanka ko
karyawa yakasa yi ya Dan saba tana bashi a
baki yau kam yasan koxai mutu bazata bashi
abakiba,
Haka ya dawo office guraren yamma ta qare
girki tayi kwalliyarta kamar ba itaba.
Share:

WACE CE*******ITA? 91

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 91
Na abba gana
Abin sai Wanda ya gani, farhaan har tausayi
yake bani wai wannan kudin da ya kashe duk
Dan cika umurnin Mrs purhuuun ne, anyi komai
cikin jin dadi da kwanciyar hankali su mama kam
sai fada sukeyi wannan bidi'a haka aure na
Neman shekara amma sai yanxu ake wani
qaqale qaqale iffaat kam taji dadin komai d
farhaan ya mata hatta kayan aure saida ya mata
sabbi akwatuna kamar dai sabuwar amarya koda
ai sabuwarce tunda har yanxu, wane yare da
sukecewa ((dast na khurde )) budurwar kenan
wacce batasan mazaba,
An sallami kowa cikin aminci inda amarya da
ango suka dawo gidansu farhaan kam hadda
shan maganin qara qarfi irin yau za'a suburbudi
iffaat...
mutuniyar kuwa ko a jikinta Dan tasan batada
tsarki, su farhaan anxo ana lalabe lalabe iffaat
ta dakatar dashi ta hanyar gayamai batada
tsarki kuma ta gaji ya barta tayi bacci, ga injin
dinsa ya riga yadau zafi, farhaan Dan takaici ya
rasa abinda zaiyi sai daukar key yayi ya fita yaje
kozai samu gunda xaiyi aiki yanda yayi tsingau
dinnan, iffaat ta gane ina ya nufa amma Sam
bata kulashiba.
farhaan bayan ya tafine yaje kuma yakasa
Neman matan banxar, haka ya samu daki ya
kwanta yanata juyi har bacci ya daukeshi bai
farkaba sai guraren 3 Subhanallahi, ya tashi da
sauri ya dawo gida koda yaxo ya tarar da iffaat
zaune tana kallo abin ya bashi mamaki kallon
iffaat cikin dare....
Share:

WACE CE*****ITA? 90

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 90
Na ABBA GANA
Ya biyo ta Palo tana sauraren waqarda kusan
kullum saita saurareta koda waqar hausa bata
burgeshi amma har ya haddace wannan wai
kuma baiti dayane yakejin tana maimaitawa
kullum shine na badi ba rai soyayyah jigon
rayuwa ana cewa " itadai soyayyah maiyi bai
samun sauqi, a jini take yawo wasu gunsu tana
hanin aiki, na shiga cikinta ta xafar tamkar doki,
na shaida sone mahadi gun rayuwa"ya kalleta
yayi murmushi iffaat sarkin rigima normal
xatamai duk abinda yakeso amma da xaran ya
buqaceta sai taqi, ya zauna kusa ida ya daura
kanshi akan chinyoyinta yana wasa da jelar
gashinta, yace yakamata amin tafsirin wannan
baitin waqar kullum shine a bakinki tun kina
qarama nakejin kina yinsa, tace kace dai tun ina
Yar aikinka nakeyinsa, tayi murmushi, nidai abba
da zasu ce na musu tafseer din wannan baitocin
waqar da zanyi page 100 dashi amma basu bani
damaba, iffaat ya kira sunanta ta kalleshi mi
yasa kike guduna? Tace gudu kuma? Yace eh
mana, tayi murmushi tace Sabida lokacin auren
mu ba'ayi su dinner, su party su lunching ba
wani Abu da akayi kaga kuwa kamar ba'ayi
aurenbane ya miqe zaune yanxu kinason ayine?
Tace eh ayi, shine matsalarki?? Eh to yanxu dai
shine na farko, yayi murmushi wallahi duk
abinda kikeso xa'amiki ya miqe zaune ya shiga
dakinsa ya kira abokinsa wannan da iffaat tayi
wa fitsari farhaan yace monkey din gidansune,
yamai bayanin komai kuma yana son ayi komai
cikin satinnan..
Bayan kwana biyu farhaan ya kawo mata IV
yace ta rabawa qawayenta taji dadi sosai ta
shiga rabo, duk Wanda ya tambayeta ba tayi
aureba sai tace na jin dadin aurene wannan.
tayi qayyar mutane farhaan ma haka su umma
dai kam saidai su saka musu ido Dan sunga abin
nasu wasane farahnax taxo su ZZ duk an hallaro
Yar baqa ma haka hatta su dijee da rukayya
ba'abarsu a bayaba.....
Share:

WACE CE********ITA? 88 & 89

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.??

88


*******by*********

muhd-Abba~Gana


Okay.! zauna muyi kallo ya zauna suna kallo har
guraren 1 na dare iffaat idonta gyam akan TV ko
motsi yanayi yana satar kallonta amma batada
niyyar tashi, ya fara gyangyadi, ya karbi remote
ya kashe dole sai sunje sun kwanta, iffaat kuwa
ta fuske tace yaje xatazo yaga dai batada niyyar
tashi sai ya wuce yace yana jirinta tace mai OK,
iffaat dai anan ta gyangyade sai bacci da asuba
farhaan ne yaxo ya tayar da ita bacci yana Dan
shashafata har ta bude ido tamai murmushi ta
tashi taje tayi alwula tayi sallah ta dawo Palo
zata kwanta farhaan yasha gabanta yace idan
dai dannine ki kwantar da hankalin ba abinda
xan miki murmushi kawai tayi ta rabashi ta
wuce, taje taci gaba da baccin ta qarfe 9 ta
tashi ta hada mai breakfast ta shirya a D table
ta dawo tayi kwanciyarta sai goma ta tashi da
yake ba lecture ta Dan dima abincin a taje
taganshi yana sharar bacci wanka ta shiga ta
fito ta dandasa kwalliya ta saka wasu arnan
kaya cikin kayan da tasiyo ita kanta tasan tayi
ta fesa turare taxo kusa dashi ta shafa
kumatunsa a hankali ya bude ido ya kalleta
tamai murmushi ya janyo ta jikinsa sosai yayi
kissing dinta a kumatu, tadan goce ka tashi
muje kayi wanka, yayi miqa hadi da salatin
annabi ya miqe yaje wanka bayan ya fito tazo
tayashi goge jiki da shafa mai, daxai chanxa
kaya sai ta miqe xata fita ya janyo ta ina
xakije,? ta Sosa kai xan dauko abune a Palo yayi
murmushi aranshi yace mata da mijinta amma
tana guduwa. Ya saketa bata dawo ba saida ta
tabbatar da ya saka kayan sannan ta shigo.....
WACE CE ITA..?? 89


********by*********

muhd-Abba~Gana


09039016969

Ta kalleshi ta riqe kunkumi iyeee kaganka
kuwa.!? Kayi kyau kamar sabon ango, ya kalleta
ya kanne ido yace ai angonne ko kinmanta har
yau baisha maiba,! Ta gane mi yake nufi sai ta
basar da zancen muje kayi breakfast kaje ka
gaida su Abba da umma, yace to my princess,
sun zauna ta kawo breakfast nan ma yasa
rigima har yanxu bai warwareba sai ta bashi a
baki, haka ta riq biye mai tana bashi yana chi
idan ya cijeta tace sai ta rama haka zata samu
wani guri shima ta chije shi har suka kammala,
ta rakashi har mota ta dawo ta tattara kayan
gudu gudu cox tanada lecture 12 gashi 11:30 ya
wuce ta qare ta wuce skull.
*******
Zaman iffaat da farhaan dai xan iya cewa lafiya
lau duk wani kula dashi tanayi ba abinda za'
nuna mata tun daga kwalliya har girki da tattalin
miji saidai har yau taqi bada hadin kai farhaan
yayi yayi amma taqi..
Ranar dai ya tirketa tana baccin rana a daki
yaxo ya dabai bayeta ya fara yan shafe shafensa
chan ta farka ta bude ido ta kalleshi tace miye
haka?? Yace mata sunnace haka, tace sunna
kuma? Yace eh bakisan annabi yace duk Wanda
ya aikata Wannan sunnatawaba daidai yake da
Wanda yayi jihadi ya kashe arna dububa. Ta
kalleshi ta kyalkyale da dariya har saida tayi
kwalla, sannan tace Yy farhaan watana hudu
gidannan watanka uku muna kwana daki daya
gado daya bargo daya bakasan da a kashe arna
ba sai yanxu farhaan kam ya fara nisa ba wani
jinta yakeba tuni tasa qarfi ta tureshi gefe ta
miqe zaune ta kalleshi rai a bace wallahi kada
ka qara kuskura kace zaka kusanceni! Ya kalleta
ido sun wani Kada haba iffaat mi yasa kike min
hakane? So kike na koma abin farko da nakeyi?
Wannan kuma ya rage naka ko yanxu waya sani
ko ana lallabawa dubunka ce bata cikaba na
kamaku, ko kuma anji tsoron cell shiyasa ake
kama kai amma dai badan iffaat ba kuma ba
Dan tsoron Allah ba.!.
Ta wuce Palo ya zauna saman gado yayi tsaki
wannan yarinya mayaudariyace wallahi, ta
koramin yan mata kuma ta hanani kanta kuma
gata kamar aljana duk abinda nakeyi tana gani,
yayi tsaki yadan kwanta akan gadon qafafunsa
suna qasa ya dafe kai miye abinyi??
Da gaskiyar ta Dan tsoron cell naqi Neman
matana amma yakamata na bari Dan Allah
badan kowaba. Yayi ajiyar numfashi...


muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
Share:

WACE CE*******ITA? 86 &87

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.??
86


*******by**********

muhd-Abba~Gana


Data gane kallonta yake tace a bari sai gobe
yace ai bai gwada ya ganiba ko ya iyaba, ta
riqoshi tana nuna mai ya bata wahala ba
kadanba amma fa shima yasha ruwa....
Hmmm , soyayyah cikin ruwa dadi wallahi, tana
Neman fita ya kamo gashinta saida tayi qara
tana waigowa ta zabgamai cizo shima saida yayi
qara tace ka tsani gashinnan nawa kodan ina
aske na yan matankane kakejin haushin nawa.!?
ya tun karo ta da qarfi tuni tayi wani super a
ruwa ta gudu yasan idan ma ya bita wasu
ruwan zaisha sai ya gyaleta, ko banxa tayi
tsokana bare ta sami abin fada, yana kallon ta
ta fita ruwan ya qurawa halittarta ido iffaat
akwai chinya, ga uban hips dinnan ta take
juyashi kamar me yayi murmushi ya lashe lebe
aransa yace Allah yayita bani sa'arki, har ta
wuce ta juyo taga yana kallonta tasan dama zai
kalla yanda ta saka wannan kayan haka tamai
bye tayi sauri ta wuce ya Dade a ruwa yana
tunani sannan ya fito ya shiga gida koda yaje ta
shiga kitchen daura abinchin dare, yaje ya saka
tufafi ya biyo ta kitchen ya rungumeta ta baya,
yayi kissing din wuyanta. Tace Dan Allah kaje ka
kalli ball dinka gashichan an fara. Yace au
korana ma kikeyi ko??
Ta baxan tafiba, tace yi haquri mana, yace kibar
girkin anjima sai mu fita muci tace itakam ba
inda zata chin abinci. Haka yayita damunta
kuma ya qi sakinta, saida yaga ta daure fuska ya
kama kanshi, ya dan samu tana sake mai idan
ta daure mai ai ya shiga uku yace tayi sauri ta
qare yana jiran ta,
Ayanda iffaat takeda saurin aiki yana burgeni
cikin lokaci kadan zatayi aiki ta qare dama tasan
farhaan akwai chin amala kamar Dan yarbawa
cox lokacin da tana mai aiki kusan kullum sai
anmai amala, ita kuma lokacin komai aka bata
chi take dukda bata gane abincin amma haka
take chinyiewa, to itama amala ta hada mai da
miyan agusi yaji kayan ciki yana qamshin
attarugu da carry ta hada mai fruit salad ta
kawo ta ijiye...
Uhummm su farhaan fa za'a fara dandana dadin
aure...


WACE CE ITA..??
87*******by**********

muhd-Abba~Gana


Bayan ta qare girki ta ta fito yanata mata sannu
murmushi kawai tayi, ta shiga bayi ta watsa
ruwa tayo alwula sannan ta fito shima yayi
alwula ya tafi masallaci ta zauna saida ta qare
kwalliyarta tsab sannan tayi sallah, nima ta
burgeni Allah ya qaro min yawan gashi nasamu
na kuri irin iffaat... Ta fito tsab da ita taje Palo
farhaan ya dawo kenan ya ware hannu irin taje
dinnan ta murguda masa baki abin ya bashi
dariya ita iffaat komai sai ta murguda baki...
Akaxo chin abinci nanma yace baxai iyaciba
itama tace bazata iya Chiba tofa sai Yaya wai
sai dai ya bata ta bashi haka sukayi kuwa
wannan karon bata batamai tufafi sosai ba, Dan
tana kallon yanda yake bata sai itama tana yin
hakanan suna chi yana bata labarin Thailand har
suka kammala suka tashi suka Dan zaga palon
Dan abincin ya fada musu, bayan sun qare
iffaat ta zauna farhaan yaje ya bude kayan da ya
siyo abinda yafi bata dariya hadda kayan baby
kuma bana babyn farahnax bane wai na babyn
da zasu haifane nan da wata Tara a yanda yace
murmushi kawai tayi ta tattara kayan ta saka a
wardrobe ta dawo ta zauna, yayi miqa kixo muje
ki kwanta mana, ta yatsina fuska kaje kawai
zanzo, habadai kizo muje kin gaji, tayi fari da ido
kaje mana idan naji bacci zanxo, ya dawo ya
zauna ni bazan kwanta idan bakiba...muhd-Abba~Gana
Share:

Sunday 26 July 2015

WACE CE********ITA? 85

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 85
Na ABBA GANA
Tana ganin yazo kusa da ita kunya ta kamata
Dan kayan sai a hankali komai na jikinta suna
nunawa gasu irin masu hade da wandone, yayi
qoqarin kamata amma yana xuwa kusa da ita ta
gudu ya kuwa biyota sai ji yayi kamar ana jansa
tuni ya nemi nutsewa a ruwan tana mai dariya
sai taga da gaske yakeyi yanda yake dukan
ruwa, ba shiri tama manta da wani kayan jikinta
da boyon da takeyi kada ya ganta tayi sauri ta
rungume shi ta janyoshi bakin ruwa farhaan duk
ruwan dayasha bai hanashi jin laushin fatar
jikinta ba jikinsu ya hadu sun kawo bakin ruwa
amma farhaan da iskanci yayi lamo a jikinta yaji
fresh fata ba irin ta gardawan yan matansa ba,
ta kalleshi ta jijjigashi ya bude ido a hankali tace
mai sannu ko? Ya harareta ya murguda baki
yanda yake murguda baki ya bata dariya ta
kuwa dara, yace dariya ma kike min ko bayan
kin wahaladda ni, tace to ai Kaine kasan baka
iyaba ka biyoni, ya qara narkewa a jikinta to
yanxu ka fita waje kamin nazo yace ba inda zaije
saima ta koya masa yanda takeyi, tayi tayi
amma ya nace ba inda zaije sai ta koyamai
yanda ya maqalqaleta ne ba yafi damunta tace
to sakeni sai muje! Yace wayo zaki min ki gudu
tace zan koya maka amma ba yanxuba yace
shiko idan har bazata koya mai yanxu baisaidai
su kwana chikin ruwa, Tace to, ya maqalqaleta
har suka kai gurin sannan ya saketa, ta fara
nuna mai farhaan kam kallonta yakeyi ba kallon
abinda take koya masaba....
Share:

WACE CE********ITA? 84

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.. ??84
Na ABBA GANA
Bayan ya kwantane Ya nace saita mai tausa
gata bata iya tausaba haka dai tayi ta dannawa
tun yana wash wash har dai baccin gaskiya ya
kwashe shi, tana tabbatar da yayi bacci ta janyo
bargo ta lullubeshi, ta zauna akan madubi tana
kallonsa, tana tunani,
Dama ana cewa namiji daidai yake da jinjiri idan
kana mai abinda yakeso to ka gama dashi,
saidai ita kam nata mijin mayen mutane Allah
dai ya shirya matashi hakadai tayi ta tunani...
chan ta tuna da maman Nargees tayi sauri taje
Palo koda taje ta hada kayanta bayan ta gyara
palon, iffaat ta kalleta Dan Allah kiyi haquri
wallahi na manta kin dawo! Ya naga kin hada
kaya ina xuwa??
Zani gida mana aikina ya qare gashi tun ba'aje
ko inaba har an fara mantawa dani, iffaat tayi
dariya tace wallahi ba komai mukeyibafa ! nace
wani Abu kukeyi?
Naji dadi sosai wallahi nan dai maman Nargees
ta qara bata wasu shawarwari sannan tace duk
da haka ta riqa ja masa aji ba komai bane jiki na
rawa zata masaba, tayi dariya taso ta bari
farhaan ya tashi ya sauketa amma tace ya gaji
kuma ta hanata itama ta kaita wai idan ya tashi
bata ba zaiji dadiba, uhummm maman Nargees
dai ta gyara aure sosai ta tafi...
Bayan maman Nargees ta tafi iffaat kayan da
aka shigo daso ta musu muhalli bata budeba
Dan tasan bata aikesaba!!
Ta gaji Dan aikinda tayi ta zauna tanata tunanin
yanda xuwan farhaan ya chanza ta tayi
murmushi tasan dai har yanxu bazata iya bari
suyi wani abubua Dan tsabar kishi irin nata, bari
tayi wanka har zata shiga bayi sai tace bare taje
S.P ta dauko Yar figaggiyar rigar wankanta ta
saka taje ta fara wanka,.
Ashe farhaan ya tashi yana kallonta ta window
yana murmushi yanda take wasa da ruwa kamar
kifi, Yaji bari yaxo shima ayi dashi tana cikin
ruwan kawai jin tayi mutum ya fado ciki da yake
tafi shi iyawa shi farkon ruwan yake tsayawa ita
ko har gurin xurfin take tafiya..
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive