NASHA NONON MATATA MENENE MATSAYIN AUREN MU ???
MALAM NASHA NONON MATATA MENENE
MATSAYIN AUREN MU ???
Don Allah malam ya matsayin mutumin da yasha
nonon matarsa, ya aurensu yake ?
(Daga Hamza Sa'eed).
AMSA:
======
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi
da dukkkan bangarorin jikin matarka, in banda
dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take
haila.
Saboda haka ya halatta ka tsotsi nononta
mutukar babu ruwa aciki, amma idan akwai ruwa
aciki, to malamai sunyi sabani akan halaccin
hakan zuwa maganganu guda biyu kamar haka:
1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake
haramta aure shine wanda aka sha kafin yaro
yacika shakaru biyu, saboda fadin Annabi (S.A.W)
.
“Shayarwar da take haramtawa, itace wacce yaro
yasha saboda yunwa”
Kuduba Sahihul Bukhari hadisi mai lamba ta
:5102.
Ma’ana.
Lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono,
saboda shine abincinsa, shi kuma wannan ya
farune bayan mutum ya girma don haka ba zaiyi
tasiri ba wajen haramta aure.
Wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Bai halatta ya shaba, saboda koda yaushe
mutum yasha nonon mace tota haramta a
gareshi, domin Annabi (S.A.W) ya umarci matar
Abu-huzaifa data shayar da Salim, don ta
haramta a gareshi, kamar yadda Muslim ya
rawaito a hadisi mai lamba ta: 2636, tare da
cewa a lokacin Salim yariga ya girma, wannan sai
yake nuna cewa idan babba yasha nono to zai yi
tasiri wajan haramcin aure.
Zancen da ya fi karfi shine ya halatta miji ya sha
nonon matarsa, saidai rashin shan shine yafi,
saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau,
don neman Karin bayani kuduba:
Bidayatul-mujtahid mujallady na 2\67.
Allah shine mafi sani.
Allah y tsare gaba
ReplyDelete