KIGYARA KANKI
Yanda Amarya ya kamata ta kasance. ranar da
za'a
kaita dakin Angonta
*************************************
Yanada kyau Amarya tayi fesss da ita tayi kwalliya
sosai tayi tsaf-tsaf
Sannan tayi duk wata Addu'a da ta iya don kare
kanta daga shidanu
Musamman ya kamata Amarya ta karanta
Qulhuwallahu Ahad, da Falaqi da Nasi, da Ayatul
kursiyyu, da Amanarrasulu da sauransu
Bayan duk ta karanta wadannan a gidansu kafin a
kawota gidan miji da niyyar kariya daga shaidanun
mutane da aljanu!, to yanada kyau ta daura Alwala
irin ta sallah sannan A rankayo zuwa gidan
mijinta,
Bayan duk tayi haka da anzo da ita kofar gidan, to
ta shiga gidan da qafar dama tare da (isti'aza da
basmalah don neman tsari) sannan tayi sallama in
zata shiga gidan koda kuwa ba kowa
Haka kuma ta shiga da dakin nata da sllama in
zata
shiga wanda zata zauna a ciki
To shi ango fa?
______________________________
Shima yakamata ya caba Ado wanda yasan ze
qayatar da Amaryarsa sannan shima ya shigo
gidan
da qafar dama sannan yayi mata sallama ya shiga
Amma fa Ango kar ka manta ba hakanan zaka
shiga ba ba wata 'yar leda a'a yana daga cikin
tsarin musulumci ka shiga da wani abu na ci Ko
nama, ko kifi, ko Naman kaza, ko tsire, da dan
kayan tsotse-tsotse me dadi wanda za'a ci a sha
ayi Nishadi ayi hira irin ta masoya
Amma fa kafin ayi wannan ciye-ciyen da shaye-
shayen A tsarin Musulumci bisa koyarwar Manzo
(s.a.w) Ango da Amarya zasu fara yin Alwala ne
suyi sallah raka'a 2 ta nafilah don godewa Allah
idan suka idar sai ya dafa kanta yace; Allahumma
inniy As'aluka khairuha wa khairu ma jabaltaha
alaihi wa a'uzu bika sharraha wa sharru ma
jabaltaha alihi
Fassara (ya Allah aina roqonka Alkhairinta da
Alkhairin da ka ginata akansa, kuma ina neman
tsarinka daga sharrinta da sharrin da ka ginata a
kanshi)
Anan zamu tsaya se a darasi na gaba zamu dora
daga inda muka tsaya da yardar Allahu
Allah yasa mu dace Ameen
Daga Zamantakewar Aure ga ma'aurata/whatsap
Jazakul Allahu khair
ReplyDeleteAllah ya saka ameen
ReplyDeleteALLAH YASAKA DA ALKHAIRI KUMA ALLAH YABIYAMAKA DA BUKATUNKA
ReplyDeleteMUNGODE
ReplyDeletemun gode
ReplyDelete