QARIN**********JINI--5
QARIN JINI 5
********by**********
muhd-Abba~Gana
09039016969
Yauma kamar kullum da wuri ta kwanta bayan
yaya naziah taymata fada sosai yanzu har ta
saba da fadan batajin komai tama qagara ta
qare fadan nata taje takwanta, ta kwanta bacci
bay dauketaba ta qagara ya dauketa tay bacci
ko zata hadu da masoyinta, burin rayuwarta,
abin qaunarta, dream guy dinta, takai qarfe
Goma na dare tana mulmula akan gado amma
bacci yaqi daukarta sai rufe ido take tana
budewa, da tasan inda zataga bacci data kirashi
yazo ya dauketa koda da kudine xata siya, dan
kawai taga burin rayuwarta a haka har tay
bacci. Yauma kamar kullum taganshi a wani
lanbu da suka saba haduwa dashi,yauma sam
bai kulataba, dama chan idan taganshi sai dai
tayi ta kallonsa tana murmushi amma baya mata
magana bata mishi magana wannan ganin da
take mishi ya fiye mata komai dadi a duniya bata
taba jin muryarsaba bata taba ganin dariyarsaba
sai dai taga yana lilo abinshi hakan na matuqar
burgeta kuma tunda take mafarki dashi bai taba
waigowa ya kalletaba saidai ita tayi ta kallonsa,
a haka har akayi kiran sallar asuba tatashi tay
sallah takoma bacci gari ya waye taje tagaida
yayarta, tatararrda har tafita ko ina tajee oho.?
Har qarfe biyu na yamma bata dawoba ta shirya
abinchi taci ta ijeyewa yayarta sauran guraren
qarfe uku tadawo bayan ta gaida yayarta yaya
naziah tace kije gida umma na nemanki, tace to
bata damuba sabida tasan mamarta bata mata
fada sosai dadai big boss ne wato baba to kuwa
da ta shiga uku sukai hira ita da yayarta kamar
ba komai a tsakaninsu har dare yay taje ta
kwanta da wuri dan taga dream guy dinta....tab! za'ayi masoya a mafarki
muhd-Abba~Gana
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.