shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

QARIN**********JINI--4

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 4
********by**********

muhd-Abba~Gana


Tunda oumulkhair taji saugi ta dawo gida take
wani mafarki mai ban mamaki da ban al'ajabi,
kuma kullum saitayi mafarkinnan kuma iri daya
kuma na abu daya, tun abin baya damunta har
yafara damunta, tun bata baiwa abin
muhimmanchi har ta fara bashi muhimmanchi
takai ta kawo idan khair batayi wannan
mafarkinba sam bata jin dadi ajikinta ahankli son
wannan mafarkin ya kamata, bawani abu bane
illah wani GUY da take gani kullum acikin
barchinta, sonshi ya kamata har yana neman
illatamata rayuwa har yanzu yakai idan batay
mafarkinsa sam bazata taba samun sukuniba
idan wani abu kakeso gurin khair sai ka roqa
abaka albarkacin dream guy dinta, batada tadi
sai na dream guy dinta tun tanayi tsakaninta da
qawayenta harta gayawa yayarta naziah, da
farko ya naziah abin wasa da taukeshi har tana
tsokanan yar qanwarta da dream guy dinta, idan
tanason aiki sai ta hadata dashi nan danan zata
mata aikin kuwa, har yakai ya kawo naziah
tagane abin na khair azimunne, baranarda zata
fito ta koma ga mahallinta batare da khair tayi
zancen dream guy dintaba, tun yayarta na mata
fada ahankali hartakai fada sosai take mata
amma khair ko a jikinta kullum wutar son
Wannan guy dada ruruwa yake a cikin zuciyarta,
duk wani saurayi nata ta koreshi yanzu batada
saurayi sai dream guy dinta, gashi son dream
guy dinta sai qara azabtar da ita yakeyi har
yafara mata illa ajiki dama ita ba tada wata
qibar azo agani sai qara lalacewa takeyi (takoma
kamar wata abokiyar karatun abba wato
maryam wacce bakomai ajikinta sai qashi
kamar abusa ta fadi su maryam anji haushi, lol)
haka khair itama ta koma yau shekara biyu da
wata shida oumulkhair nafama da wannan
mummunar lalurar wacce ba wanda yasan ina ta
dosa.....


muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive