shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

QARIN**********JINI--17

qarin-jini.jpg

QARIN JINI 17

Baba baicemin komaiba yaja hannuna mukaje
palo ya zaunar dani yace min lafiya,? naci gaba
da kuka kiyi magana mana!, baba inasonsa zan
aure shi wllhy inasonsa, aljanin barcinki kike
magana ko kuma wani daban kike samo? naji
wani faduwar gabah, Aah baba Abdullah nake
magana akai, nayi ta baiwa baba haquri akan
zan aureshi, qarshe baba yace min yaji Allah
yamin albarka na rungume babana inata kuka
baba yagayamin cewa yayi magana da yayan
abdul akan yau zasu hadu yaqayamasa anfasa
auren sai gashi kinzo da wannan maganar Allah
ya miki albarka..... naji dadi na tashi banyiwa
kowa sallamaba dan naga yaya habeeb shirye
yake da ya dakeni naje gida sumi sumi kamar
munafuka na jaa motatana sai gidan yayata ban
cemata komaiba naci gaba da al'amurana, tunda
nasan cewa aure yananan nayi waya na gayawa
benaxeer aurena yakusa saura kwana biyar taji
dadi waye angon nagayamata wanine taji dadi
taki kamar itace, inason in tambayeta ina A.A
amma ina girman kaina ya hanani har munyi
sallama tacemun jiya naga aliy abokin A.A yana
gayawa wasu qawayensu cewa A.A zaiyi aure
nan daa sati daya wani jiri naji ya kamani
bansan lokacinda wayan ta fadiba nafara kuka
sai da nayi mai isata sannan nayi shiru. Araina
nace dama mafarkinda nayi kace zaka kashe
kanka duk yaudarane? dama ashe aure zakayi?
wllhy da in aureka muyi tarayyarka da wata qara
in mutu banyi aureba? ko kuma in auri wani
namijin Allah na godemaka da kasa babana ya
zabamin miji dana tabe.! meena slow babbar
aminiyata itace gaba wajen raba katin buki aka
kawo min calendar aure da duk wani abu da ake
rabawa a gurin aure amma ba wanda na kalla
sabida radadi da zafi da kishin da zuciyata take
fama dashi, gobe zan zama mallakin wani ba
dream guy dina ba.! Lallai na yaudari zuciyana,
amma sai haquri anata shirye shiryen bikin
aurena an gyaramin gidana, naji su zainb khalifa
da zainb ibraheem sunata gulma wai basu taba
ganin gida irin wannan ba kayana daga Turkish
aka baiwa baban Zainb khalifa yasiyomin da
yake achan yake aiki kaya naji da fada abin sai
wanda ya gani meena slow sune qirjin biki sai
shiga da fita sukeyi sun shirya party kala kala
amma ba wanda najee bani ba ango suka
chashe abinsu. Sun shirya wata walima ARAB
DAY mata zallane naje walimar, sunyi shigane
manto da wandon Jeans da kuma wani farin
qyale shigar ta burgeni sosai, 20/5/20... an
daura auren OUMULKHAIR
MUHAMMAD&ABDULLAH AL-MUSTAFAH gaskiya
an taru wajen daurin auren mu benaxeer ta
aikomin abin gyara jiki da kuma HQ dina ashe
bena tsohuwar macece tasan komai, gaskiya
mijinta ya more nidai ba abinda nayi sai zubar
da banxaye nayi da yamma aka shiryani nafito
tsab dani nasha kitso da qunshi umma tayi min
fada sosai babama haka, yayata naziah ma
tamin fada fadanta yafi shiga raina fiye da fadan
da kowa yamun ina kuka aka kaini gidan mijina
Abdullah..
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive