Rikicewar jinin Haila.
SHARHI NA FARKO:
Rikicewar jinin Haila.
Idan mace taga jini yanayi mata wasa wato yazo
yau gobe sai kuma ya dauke bayan kwanaki uku
sai kuma yadawo to abinda zatayi anan shine:
Ta tsaya tayi karatun ta natsu, saita lissafa
kwanakin da jinin yazo sune kwanakin Haila, sai
kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune
kwanakin tsarki domin da hakane zata cika
kwanakinta na al'ada.
Misali kwanaki tara, sai yazo a rana ta farko data
biyu sai bai zoba a rana ta uku data hudu sai
yazo rana ta biyar amma bai zoba a ta shida da
ta bakwai sai yazo ata takwas data tara.
To anan sai muce tayi al'adar kwana biyar a cikin
kwanaki goma, wannan matar ita ake kira (Al-
Mulaffiqa) a larabcin mata masu al'ada.
Idan ya zama ansami tazarar kwanaki takwas ko
sha-biyar tsakanin daukewarsa da dawowarsa to
na biyun zai zama sabon jinine kenan, ba nada ne
ya dawoba.
Kutara a darasi mai zuwa zamuyi bayani akan
yadda ake gane daukewar jinin Haila.
Insha Allah.
Assalamualaikum menene maganin
ReplyDelete