sireenah---2
Sireenah 2
********by**********
muhd-Abba~Gana
{sharifin~Zamani}
Duk wanda ya Kalli fuskar Sireenah baya
marmarin yakara kallonta sai dai dan karamin
bakinta da siririn Karen hancinta sune suka dan
taimaka mata tayi dan dama dama. Koda ta isa
school she is already late don ta tararda har
lecturer yashiga Kuma da alamu yayi nisa a
darasin dayake koyarwa, kai tsaye tashiga hall
din don tasan baza a hanata shiga ba saboda
kusan kullum ne sai tayi lattin tun ana hanata
shiga har malaman suka gaji da ita, wasu Kuma
sunayi mata rangwame albarkacin ilmin dake
gareta, sai dai yau kash kamar tazo a rashin sa a
domin Malam Tanko ne ciki gashi bayada
mutunci ko kadan amma hakan ta daure tashiga
yaga sanda tashiga hall din baiyi mata magana
ba saida yabari takai tsakiar hall din Kafin yace
Hey you black monkey where the hell do you
think u are going by this time around? Sireenah
wadda duk ta dabirce dalilin tsawar da Malam
tanko yayi mata takasa furta komai kallonsa
kawai takeyi da manyan fararen idanuwanta
wanda mommy tarasa yadda zata canza musu
launi tsabar hassada amma fuska kam babu kyan
gani dalilin (artificial black colour )da tashafa.
Malam tanko yakara kuluwa rashin maganarta
saboda haka ya koreta daga hall din students
suka fara daria wasu Kuma sun tausaya mata
(kunsan daman rayuwa dole ne mutum yana da
enemies da lovers ) balle ma Sireenah dasuke ma
Kallon kaskanci su aganinsu bai dace a ce
wannan kucakar yar aiki ce course mate dinsu ba
abin da ke kara basu haushi kenan gata always
cikin saka kalan tufafi daya! (basu san itama ba a
son ranta take sa Kala daya kullum ba ) Koda
yake dole suce haka saboda Nile University Abuja
babban makaranta ce wanda sai ya yan masu
hannu da shuni (richies ) zaka gani a ciki wasu
dalibban ma daga kasashen waje suka zo karatu
kunga dolene ayi mamakin karatun Sireenah a
wannan school wasu haushinta sukeyi duk cikin
makarantar babu wanda yakaita sa kaskantattun
kaya kullum tufafi daya ne a jikinta dalilin haka
aka samata one colour wasu Kuma black monkey
suke ce mata sauran dalibai suna mata lakabi da
gifted may be shiyasa 70% din daliban sukayi
hating dinta(ni kaina abba gana na tausaya wa
Sireenah saboda tana ganin abubuwa iri iri a
school da gida)!
Sireenah dake zaune bakin hall tazuba uban
tagumi tana kukan zucci dataga bazai fisshe ta
ba dole ta fidda wayarta wata lalatacciya kirar
Nokia c2 ce wanda yasha bandeji tayi logging on
social network, 2go chat ne takeyi tana shiga ta
tarar da sakonni kusan 20 saura na friends dinta
ne wanda suke 2go trivia tare while sauran
sakonnin na wani abokinta ne wanda suka shaku
sosai dashi, yana mata korafin rashin hawanta na
kwana biyu yayi missing din jokes dinta etc, Allah
sarki Lover boy nima nayi missing dinka rashin
data ne yahana ni hawa gashi yanzu na hau kai
Kuma baka nan balle nasamu wanda zai debe
mani kewa tana cikin wannan zancen zucci sai
gashi online (dayake sunada wireless a school
din)! Haba Funny girl nayi missing dinki kin
wahalar dani sosai gashi banida numberki balle
nakiraki koda yake kece kika hanani, am so sorry
loverboy I was out of data shiyasa kadaina
ganina. Hmm kin gani KO ga amfanin bani
numberki nan ai da tuni na aiko miki, a a habadai
kai da kefama da kanka ina zaka samu kudin aiko
mani? Hmm haka dai kike gani indai akan ki ne
zan iya hana ma kaina don nafaranta maki Kinsan
ke ta daban ce ko cikin friends dina! Toh nagode
sai dai nikuma banason kahana ma kanka! Yanzu
dai mubar zancen tunda gani nahau online muje
2go trivia muyi game ko yaka ce?
Gaskia yau bana ra ayin zuwa can hirarki kadai
nake bukata oya kibiyani bashin jokes dina na
kwana biyu da nayi missing. Haka sukayi ta
debema junansu kewa har lokacin isuwar lecturer
na biyu da zai gabatar da darasi nagaba suka
rabu badon sun so ba!
Wacece Sireenah? Ya matsayin ta yake a wurin
mommy Tee? Kodai yar aiki ce kamar yadda
dalibbai ke fada? Wanene wannan Loverboy?
Meye dangartakarsu da Sireenah?
muhd-Abba~Gana
distinction
ReplyDelete