shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday, 26 July 2015

WACE CE********ITA? 78

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??

78
********by*********



muhd-Abba~Gana





Ya kalleta chike da mamaki yaga batama kula da
mamakinsaba sai shima ya basar.! sun shiga
gida ta kawo mai abinci abinda bai taba samuba
tunda ya aureta yasan ba ita ta girkaba amma
duk da haka yaji dadi ya zauna yaci yana chi
tace, nasan police station ba abincin kirki shi
yasa na kawo maka wannam, lokaci daya har ya
hargitse, tayi dariyarta ta mugunta ya dago ya
kalleta tace kaima ka dandana kwana Gidan yan
sanda ko? Ta qara yin dariya tace dadi ko??
Baice mata komaiba ina tambaya.! ya kalleta
wai ya akayi kikasan ina chan ? Tayi murmushin
mugunta tace sabida ni na saka a kamaka..!
Ya zare ido Kamar ya? Tace Kamar haka.!
Please kimin bayani ya akayi kikasan ina gurin?
Wallahi Nina tura a kamamin kai, kuma yanxu na
fara duk lokacinda na ganka da wata mace
wallahi saina kulleka. Mamaki yakeyi dukda cewa
yasan iffaat fiye da hakama zata iyayi amma ta
bashi mamaki, miyasa duk motsinsa akan
idonta,? Ya akayi kikasan gunda nake zuwa?
Tace sabida ina iffaat, baice komaiba aransa
yace Ko ta saka a riqa bibiyarshine? Kallonta
kawai yayi Dan gaskiya tamai yawa,!! yana
zaune wayanshi tayi qara ya daga abbanshine
ya gaisheshi anan abba yake gayamai zai
aikeshi Thailand, kuma ya tafi da matarsa,
bayan ya qare waya ya mata bayani ido bude
tace baxataba karatunta zai sami matsala kuma
tafiya har wata biyu ko uku, yaso ya tafi da ita
wataqila ma achan su shirya amma taqi.
Farhaan yama Abba bayanin abinda ta masa
bayani Abba yace ba komai...
Tunda tun cikin Daren yabar gida yaje Kaduna
yana shirye shiryen tafiya, mai sami kansaba har
ya tafi,
Farhaan dai an tafi Thailand yabar iffaat ita
kadai a gida an kawo mata wacce zata tayata
zama kamin mijinta ya dawo...by Abba~Gana
Tunda matar maman nargees tazo ta kula iffaat
abincin take siyo musu, tanason tayi magana
amma dai tana tsorooo ace tayi shishigi.....


muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive