JURIYAR MACE TAGARI
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Mace tagari fa tsayayyiya ce, tasan yadda zatayi
maganin matsalarta da kanta, a maimakon
neman a saketa ko kuwa lallai wata ta fita, zatayi
bakin qoqarinta ne domin taga rayuwar aurenta
taci gaba ta hanyar warware matsaloli da sa6ani.
Takan jure bushewar zuciyar mijinta, ta daurewa
daukar kura kuransa, domin kar gidanta ya6aci.
Mace tagari takan lura da duk canjin da tagani
daga mai gidanta, don haka sai tafara binciken
yadda zata warware matsalar.
Bana mantawa a rayuwar makaranta nata6a
zama da wata 'yar ajinmu wace aka gaya min
wani abu maras dadi game da ita, nayi qoqarin
6oye mata, amma da muka hadu saida tagano ni
duk kuwa da dariyar dana riqa yi, wannan abu
yajawo hankalina na tambaye ta yadda tagane,
sai tace min itafa MACE ce kuma tana tare dani,
kar nazaci surutu kawai takeyi dani batasan
komai daya shafe niba.
Sai nayi mata nasiha akan abinda aka gaya mini.
Don haka nake ganin ba macen da zata zauna da
namiji batasan abin da yake sakashi fushi, murna,
tunani, sha'awa ba sai bankaura.
Mace tagari takan zauna da maigidanta a lokacin
sa6ani don gyara baya, takan manta da
MUGWANCIN da yayi mata idan ta tuna da irin
wahalhalun da yakeyi da ita da 'ya'yanta, takan
gano cewa saki ba shine mafita na farko ba, sai
an rasa yadda za'a yi tukun.
Annabi (S.A.W) yana cewa:
ﺃﻳﻤﺎ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺳﺄﻟﺖ ﺯﻭﺟﻬﺎ ﺍﻟﻄﻼﻕ ﻓﻲ ﻏﻴﺮ ﺑﺄﺱ ﻓﺤﺮﺍﻡ
ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺭﺍﺋﺤﺔ ﺍﻟﺠﻨﺔ .
Duk macen data roqi mijinta saki haka kurum to
qamshin aljanna ya haramta gareta.
Ahmad,Abu Dawoud, Tirmithiy, Ibn Maja da
Darimiy suka fitar.
Ya Inganta.
Kaga kenan mace tagari takan nemi sakine a
lokacin da kowa ya tabbatar da cutarwar da yake
mata, amma ba don kawai tagaji da zama dashi
ko batason wani abu da yakeyi ko don yaqi cika
mata wani alqawari ba.
Aure sunna ce da Annabawan Allah duk sukayi, ya
kamata mugaya matansu suka zauna dasu ???
Bai dace ba kowane mutum ya riqa jin matsolinki
da mijinki, sai in abin yafi qarfinki.
Mace tagari mijinta shine komai, koda bai iya
soyayya ba.
Bata zama a gabansa ko gefensa saida yardarsa,
takan cika da ladabi aduk inda yake, takan nuna
masa qauna sosai ta gaskiya ce ko qirqira ce
kawai.
Idan zai fita qafarsa-qafarta, idan taji yashigo ta
tarbo shi cikin fara'a da annushuwa, nan da nan
tafesa turare ta shafawa lallenta mai yafito sosai
ta danyi kwaskwarima, ta canja murya tareda
yawan murmushi da fari.
Idan zai fita addu'a, in yadawo godiya da murna
da farin ciki.
Mace a kullum mai sanyaya raice ba mai jiran a
sanyaya mata ba, farin cikin maigidanta shine
nata, komai yabata takan gode, ga fadin yi haquri
kamar nunfashinta.
Tana fama da baqin ciki amma tayi dariya,
tanajin zafin abin da mijin yayi mata amma tayi
tunanin yadda zata faranta masa rai.
'YAR UWA IN KINA BIYAYYAR AURE DON MIJINKI
NE TO KITSAYA HAR SAIYA GODE, IN KUWA
KINAYI DON ALLAH NE TO YANA GANIN ABIN DA
KIKEYI BAZAI WATSAR DA AYYUKANKI BA.
Allah kabamu ikon yin amfani da abinda muka
karanta.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
favicon.ico
Jazakallahu Khairan
ReplyDeleteallah yskama da alkairinsa
ReplyDelete