WACE CE******ITA? 55
WACE CE ITA..?? 55
Na ABBA-GANA
kaiiii..! Ya na sauke hannu itama ta wanke shi
da nata Marin, kamar daga sama saiga Suhaila
taga an mari mijinta tuni ta wanke iffaat da mari
tofa iffaat ansha mari ta daga kai ta kalli yayarta
taga yanda tayi wani iri haushi ya qara kamata,
dama ita iffaat duk bala'en da takewa farhann
da biyune ga kishin abin da ya aikata ga baqin
cikin rashin samunsa. Yayar ta fara mata masifa,
bata cewa yayar komaiba taci gaba da yimai
masifa da fitsara yayar tanata cewa ta bari tana
rufe mata baki Amma inaaa saida takai aya ta
zazzagemasa kwandon rashin mutunci Suhaila
abin ya qara kwabe mata baqin ciki kamar ta
hade rai ta mutu, ta qare tamai tsaki ta murguda
baki ta juyo gun yayar ke kuma ki zauna yana
qunsa miki baqin ciki kina shiga daki kina kuka
kamar wata doluwa.!
ta kama hanyar fita Suhaila ta bita tanason tace
kada ta fadawa mama farhaan ya daka mata
tsawa akan ta dawo, ta rasa yanda zatayi, taxo
gabansa ta tsuguna tana bashi haquri abin
mamaki yace ba komai ya wuce laifin sane
shima dama baiji dadin abinda ya fada mataba
nan dai suka shirya hmmm mata da miji sai
Allah hardai suka aikata aikin lada nan take,
farhaaan yasan bala'en iffaat yafi nashi nesa ba
kusaba cox shi yasan WACE CE ITA baisan
miyasa yake shakkartaba.!!
Ta isa gida a fusace amma kuma saita tsinci
kanta da kasa fadar abinda ya faru, ta rufa masa
asiri chaiiii soyayya bala'ece nan ma qarya ta
xubawa mama tace wasu samarine suka bata
haushi. mama tace nidai zanso naga mijinki
kullum cikin korar samari waike yarinya, tayi
murmushi ta wuce dakinta,. Tana shiga ta kulle
qofa ta fara kuka tayi nadamar dukan farhaan
koba komai ya girmeta kuma gashi mijin yayarta
haka kuma masoyinta ta tsinewa kanta yafi sau
dubu amma ita kanta batasan lokacinda ta
aikata hakan ba.!!
Farhaan kuwa duk ya damu yayi nadamar
abinda ya aikata qarshe yasa Suhaila ta kira
iffaat tana bata haquri itama ta bata haquri tana
ce mata ga yy farhaan zaiyi magana da ita ta
kashe wayar farhaan yace ta kyaleta amma ya
damu matuqa...
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.