shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 27 July 2015

WACE CE***********ITA? 95-96-97

computerimages1.jpg

Hmmmm.
Wai har sun shirya an yafi juna sunci abincin
tare...
Wata sabuwar soyayyah ce a Gidan ma'auratan
gwanin bansha'awa suna kula da junansu yanda
yakamata.
Yanxune iffaat take fahimtar abinda armiya'u ta
taba gayamata na cewa farhaan bamuqacine na
gaske lallai hakane kullum dai yajishi ciki
uhummm.
Abin ba'a cewa komai.
Iffaat ta cika alqawari takai goggo makka kuma
ta dauko qawayenta na qauye dije da rukayya an
baiwa mazajensu lebaranci a companyn su
farhaan suna shanawa suma ga dukkan alamu
suma su waye su xama yan gayu, amma bana
tunanin dijee zata waye Dan har yanxu tana nan
sai a hankali..
Bayan shekara 7
Koda naxo naga iffaat da yara uku mamaki ya
kamani naso naga iffaat da ciki amma ina
banganiba sai yayanta na gani..
Mace daya namiji biyu
Macen taci sunan Suhaila sai maxan dayan
sunan mahaifin iffaat mahmoud dayan sunan
mahaifin farhaan habeeb.
Farhaan ya zama kamilallen mutum kamar
bashiba, iffaat kam har yanxu saidai idan
ba'asamu damaba..
Dan Ko yau da ni abbagana naje muku gidan, saman bishiya
na ganta tana tsinkowa tana wurgowa qasa
yaranta suna cabewa sunata jin dadi, farhaan ya
shigo ya duba bata yasan ina taje ya girgixa
kai, yaje ya kirata tana ganinsa ta diro saman
bishiya saida naji tsoro na dauka ta karye sai na
tuna fiye da wannan ma tayi..
taje ta rungume shi tanamai oyoyo yace bawai
na hanaki hawa saman bishiya ba, ta kanne ido
tace waya iya raba monkey da hawa bishiya
dariya yayi ya tuna lokacinda tayi mai fitsari
saman bishiya yace monkey ne,
Suhaila ce ta shigo itada habeeb cox shi
Mahmoud jinjirene, Suhaila da wayo tace Abba
mu anti amarya mukeso.! gidansu hameed na
uncle Ali an musu anti amarya kullum sai yace
mana mu bamuda anti amarya, muma munason
anti...kaji jaraba!. iffaat tace kiji yarinya da gulma xanci
gidanku yanxu, ba anti amyaba anti ango bace
min da gani, sakarya kawai...!!
Suhaila ta wuce tana gunguni,
Farhaan kam dariya yakeyi sosai, iffaat ta
kalleshi miye haka.?? Daga jin anyi xancen
amarya sai wani washe baki kakeyi...toh fah zai karane kodai?muh-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive