shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 28 July 2015

sireenah----1

muhd.jpg

Sireenah 1
********by**********muhd-Abba~GanaYarinya(budurwa) ce yar kimanin shekara
shatakwas(18) sanye da tufafin ma aikata irin na
(house maid) tana goge-goge tunda sanyin Safia
tafara wannan aika ce aikace saboda gudun kada
tayi lattin zuwa school. Tana cikin moping
mommy Tee tafito daga dakinta sanye da rigar
bacci alamun yanzu ne tashin ta daga barci, Kee
Sireenah idan kingama aikin da kike yi kije dakina
ki gyara shi daganan kiwuce dakin su yan biyu
shima ki gyara akwai wankin su a ciki kihado su
kije ki wanke tufafin tas kada ki daga har sai sun
bushe ki goge su duka amma yanzu kifara hada
mana breakfast, kada ki kuskura ki dandana
(tsabar mugunta taya mutum zaiyi girki ba
dandane?) Mommy Tee don Allah ina neman
rangwame zanyi duk abinda kika umurceni amma
wankin kibari har nadawo daga school gudun
kada nayi latti. Lallai Sireenah wuyanki ya isa
yanka wato yanzu ban isa nasa ki aiki ba sai kin
kawo mani naki excuse KO? Toh bara kiji aiki
bafashi dolene kiyi dukkan abinda nasaki ban
damu da lattin da zakiyi ba idan ma da hali a
koreki mana naga batun bokon yarinyar banza
Wallahi da akwai yadda zanyi da tuni nasa
ankoreki daga makaranta badon Kina cikin
dalibban da minister of education ke sponsoring
ba masu kwakkwaran securities Sireenah bata
kara cewa uffan ba banda hawaye dake ambaliya
a fuskar ta har mommy tee tawuce bangarenta!
Jikinta bawani kwari har taga ma goge gogenta
idan da sabo tariga tasaba da musgunawar
mommy Tee bayan tagama hada breakfast tana
cikin jerawa saman dinning table sai ga yan biyu
sun fito shirye cikin kaya masu Shegen tsada
amma duk da haka basu da babbanci da wasu
ugly monkeys komai tsadar kaya baya yi musu
kyau farin dake garesu nema yadan taimakesu
koda yake harda farin kantin Hassana ce ta fara
magana Sireenah fatar kin gama girka mani
abinda nace? Eh Hassana gashinan yana jiranku
kan dinning, Ke miss kuku kinfa san ni bana son
irin wanda kika girkawa Hassana nawa nake so
daban cewa Hussai, don Allah Hussai Kiyi hakuri
kici na Hassana inada sauran aikin da zanyi gashi
bakiyi magana tun farko ba, nidai nagaya maki
bazan ci ba ko kije ki girka mani wani ko nacanye
na mommy tee yi hakuri basai kinci nata ba
yanzu zan girka miki daidai wanda kike bukata
bayan wucewa war Sireenah yan biyu suka tafa
hadi da dariar mugunta sannan sukaci breakfast
dinda ke gabansu daman tsabar mugunta ce yasa
Hussai tace bazata ci na Hassana ba bayan
komai nasu iri daya ne hatta under wears basu
babban tawa saboda sun kasance irin yan biyu
nan masu masifar kishin junansu suna gama yin
breakfast suka wuce school domin daukar
lectures koda Sireenah tazo bata tarar dasu ba
don haka takoma kitchen taci abinta daman
yunwa take ji Kuma bata isa taci abinci ba sai
sun rage Kafin taci itama mommy tee tafito cikin
kaya masu tsadar gaske but katon ciki da uban
duwawu yahanata yin kyau a cikin tufafin ta
zauna tayi break dinta kafin tawuce companyn
mijinta domin aiki! Daman ma aikatan gida jiran
fitar Hajia Tee suke yi suna isowa tabangaren da
Sireenah take suka ce ma ta maza Fulani Kiyi
sauri kema kije ki shirya duk zamuyi miki aikin
gidan har da abincin rana zamuyi Kafin ki dawo,
Nagode sosai Allah yabiya ku.
Bayan Sireenah tagama shirinta a maimakon
tashafa powder tagoga shoe shiner baki
(black )wanda itama ba a son ranta take shafawa
ba dokar mommy tee ce tagoga wani bakin abu a
hakoranta kace haka Allah yayi ta gashi takara da
bakin a baya ga himmar baki (nikaina abba
dana ganta sai da naji tsoro lols) Kamanin ta
gaba daya yacanza har wani walkia fuskar ta keyi
tsabar yaji shoe shiner amma zaka zata is
natural a yadda tayi masa daman tariga ta rufe
hannayenta da Kafafuwa with black socks! Allah
yayi mana kariya da masu hali irin na Mommy
Tee
muhadu a kashina gaba

muhd-Abba~Gana
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive