QARIN**********JINI----19
QARIN JINI 19
Jikinta yai sanyi tace eh nice, kunya ta kamashi
na yarda jakan da yayi a gabanta, yadauki
jakarsa ya wuce daki ya zauna bakin gado, sai
hawaye ya daqa hannuwansa sama yace Allah!
kaine mai fitar da matacce acikin rayayye ka
fitarda rayayye acikin matacce, Allah nagode
maka da kahadi da abinda nafison aduniya!,
dream baby na! wacce nake so nake qauna
wacce itace burin rayuwa da ita nake kwana da
ita nake tashi! yau gata a gidana a matsayin
matata Allah nagodemaka, baisan lokacinda yay
sujada ba dan murna, sai dai baisan yanda zai
bullowa al'amintaba yasan dai ta tsaneshi tun
lokacinda ya kwasheta da mari a gaban mutane,
shi baya buqatar wani abu a gurinta kawai ya
riqa ganinta tana mishi mur mushi yafiye mashi
komai a duniya, ta ina zai fara,? ya dauko
wayarsa ya kira abokinsa aliy, ya gayawa aliy
cewa matar da ya aura dream baby dinsace Aliy
abin yabashi mamaki sabida farko bai yardaba
saida yaji A.A yana rantsuwa sannan ya yarda
amma abin da daure kai.!
Tashiga daki kamar yanda Abdul yay godiya
haka tayi godiya wa Allah da kuma iyayenta da
suka hadata da dream guy dinta!,
Bayan kwana hudu, tafito daga kichin sukayi
karo shi zai shiga ita kuma ta fito, ta tsorata
sosai tana jiran taji saukar mari shiru, ina
rudewa yay yana bata haquri tawuce gefensa ta
wuce dakinta... yau sati uku da gane junansu
yadaina zuwa office 24hrs yana gida yana
kallonta ya rasa yanda zaiyi ya mata magana
iya tunaninshi ta tsaneshi kuma bayason ya
takura mata itama nata bangaren haka abin
yake.... Tagaji da zaman da suke haka tana
zaune wata dabara ta fadomat wacce taji a
gurin benaxeer uwar iyayi, tajiqa barkono a ruwa
saida ya jiqa sosai ta shanye ruwan tazo falo ta
kwanta bayan minti 20 jikinta yayi kamar wuta
idonta suka kada sukayi jajir tanajin motsinsa ta
fara kuka adimauce yazo gurinta ya dagota
lafiya my DREAM BABY..!!!
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.