Ina masu Girman kai toku saurara kuji.
KUDUBI IRIN AZABAR DA ALLAH YAKE YIWA
MASU GIRMAN KAI:by ABBA--GANA
1. AADAWA (mutanen Annabi Huud a.s.):
Yayin da Manzo yaje musu da gargadi daga
Ubangijinsu sai sukayi girman kai suke ganin
cewar:
Su sunfi Qarfin wani mutum yayi musu wa'azi.
WAI DON ME BA ZA'A TURO MUSU MALA'IKU
BA!!!
Saboda Qarfin jiki da da kuma Girman halittar da
Ubangijinsu yayi musu.
Sai sukayi jayayya da ayoyinsa, suka Qaryata
Manzanninsa, suka bi son zuciyarsu.
Daga Qarshe sai Ubangiji ya tura musu wata irin
iska daga gareshi MAI QARFIN GASKE, mai
tsananin Sanyi.
Har tsawon Darare Bakwai da wuni Takwas
wannan Masifaffiyar iskar tana bugawa akansu.
Ta rurrushe gidajensu da katangun da suka
kewaye garin dashi, Sannan ta Tsintsinke
Kayuwansu, Tayi rugu-rugu da gangar jikinsu, nan
ta barsu ayayyashe tamkar guma-guman
bishiyoyin dabinai..
Allah yana bamu labarinsu ne domin mu
wa'azantu mu gyara halayenmu karmu aikata irin
laifukansu.
Tabbas Girman - Kai sutura ce ta ALLAH.
Allah ya riga ya rantse cewa duk mutumin daya
ara ya yafa, to saiya Qaskantashi ya azabtar
dashi.
Allah ka rabamu da girman kai.
Ameen
ReplyDeleteAmiin
ReplyDelete