BAYYANA KWALLIYA.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
'Yar uwata karki karaya, wallahi ke kyakkyawa ce
mai dadin kallo, mai dadin qamshi, mai dadin
murya, mai dadin mu'amalla, komai naki dadine
dashi.
Haka Allah yayi ki, duk daya saka miki rauni qasa
da namiji, amma fa raunin nan naki shine qarfinki.
Domin babu wani da namiji da zai gagare ki, sabo
da Allah yabaki sirrin juya zuciya kamar yadda
yabawa namiji sirrin juya wani da qarfi, don haka
babban taimakon da zaki yiwa kanki shine kiyi
nesa da girman kai, kisan cewa kinada wannan
qarfin koda yaushe.
Son suna da alfahari yana tafiyar da mutuncin
mace.
Shiyasa in tanada sha'ani take binciko qasan
akwati, amma a gida sai daurin qirji, ko tsohon
riga wanda in za a shayar da yaro nono kota
wuyan rigar ana iya finciko shi.
Idan mijin yanason yaga lalle a jikinta to yayi
fatan sha'ani ya taso.
Buqatarta kowa yace tayi kyau alabashi mijin
karya gani, idan ta qarasa wajen sauran matan
tace:
"Su wane da wane sun cika kallo, saisu Qura
maka ido har karasa yadda zakayi tafiya"
Bayan kuwa tagama hado shika-shikan tayarda
hankulan maza, kuma tace ita wallahi ba tallar
kanta take yiba.
Duk macen data kamu da irin wannan matsalar
ba abin da zata iyayi domin mai gidanta, kuma
zuciyarta zatayi nisa qwarai daga tunanin irin
shigar da zata yiwa mutum Daya kacal alhali idan
tafita mutane ne dayawa zasu yaba, mazansu da
matansu.
Ashe mijinta tunda shi Daya ne sai a saka masa
na maneji, ko kwalliyar ma ba dolene yariqa gani
ba.
Mace tagari dukiyarta da iliminta da shekarunta
basa hana tayiwa mijinta hidima, ina sha'awar
matar da wata zatace:
"Mu sayi kaza"
Ita kuma tace
"Maigidana bayaso"
Ba wai tace
"Tabdijan zansha fada kuwa" .
Manufa ba tsoron fadansa take yiba, tsoron ta
sayi abinda ransa bazai soba.
Yakike ganin Khadija (R.A) data auri mai gidanta
(S.A.W) sai abin da yace za ayi!
Yakike ganin biyayyar da tayi masa duk da
kasancewarta mai kudi shi talaka, amma ta
saukar da kanta domin yi masa hidima har ta
amsa kiran Rabbana ?
Yakike ganin saye zuciyar da tayi masa da har
tsufanta zuwa rasuwarta bai da kamarta a
zuciyarsa ?
Ke me zaisa bazaki kwatanta ba ?
Idan aka ajiye maganar daraja agefe guda.
Me Allah yabata a jikinta wande ke bai bakiba ?
Tafiki matsayi, amma ki karanta tarihi kiga
qoqarin da tayi da zuciyarta da jikinta wajen
tabbatar da mijinta a surar data rasu ta barshi.
Yi amfani da duk abin da Allah ya hore miki
wajen biyayya ga mijinki.
Kiduba kigani Allah yayi miki halitta ta ban
sha'awa wace dole a kalla, toki nuna masa,
Yamiki murya mai dadi, toki jiyar dashi, Yabaki
damar yin kwalliya kala daban-daban toki bar
masa shi kadai, karki yarda wasu su riqa haduwa
dashi a kanki.
BAN DA GIRMAN KAI.
Kiyi qoqari ki manta duk sifofin gidanku ko naki
na kanki, kiyi tunanin irin sifar da kikeso mijinki
ya sifantu da ita, da irin matsayin da kike so
yakai.
Allah yabamu ikon yin aiki da abin da muke
karantawa.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
allah yasakamuku amin
ReplyDeleteAllah ubangiji yasa mudace ameen
ReplyDeletedaga fatima usman bashir gumel