shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 26 July 2015

WACE CE********ITA? 83

computerimages1.jpg

WACE CE ITA.??83


********by*********

muhd-Abba~Gana


Yana fitowa wanka ya saka tufafin data ijiye
masa ya feshe jikinsa da turare yadauki waya
ya kira abba ya gaya masa ya iso anjima zaizo
ya kawo mai report din komai, Abba yace ya bari
sai gobe idan ya qara hutuwa,ya kira mama da
umma da hajiya kulu duk ya gaishesu ya gaya
musu ya iso, iffaat ce ta shigo tace Au har ka
fito? Ya kanne ido yana Neman janyota jikinsa
yace nayi missing dinkine Dan shiga bayin da
nayi shi yasa nayi saurin fitowa, bata bari ya
kamataba ta zille, tayi murmushi, tace sai tsara
zance, nidai muje kaci abin ci tana gaba yana
Binta baya sun Isa Palo ta zasu fara chin abinci
farhaan yasa rigima shi dole sai ta bashi a baki
idan ba hakaba bazaiciba, aranta tace anya xan
juri Wannan shiriritar kuwa? Mutum da girmansa
yana Wannan Abu, yaji shirun yayi yawa yace
bari naje na kwanta, ta kalleshi da dara daran
idonta abincin fa? Ba kinqi bani abakiba, yanda
yayi ya bala'en burgeta kuma sai taji wani
sonsa ya ninku a zuciyanta Allah ya shirya min
kai mijina!, tace to bari na baka ya kuwa gyara
zama tafara bashi duk taje saka mai loma sai
rabi ya shiga rabi ya xube hakadai taga chi da
chokali shirititane ta ijiye tafara bashi da hannu
nan ma da gangan ya riqa chijeta wai ya dauka
kifine, suna tsaka da wannan drama saiga
maman Nargees ta dawo, ta wangale baki taji
dadi ba kadanba, ga dawowar farhaan ga kuma
abinda tagani wai iffaat tana baiwa farhaan
abinci a baki, hmmm.
Ta gaidashi, iffaat nason ta daina bashi shi kuwa
sai haaaaa yake mata baki yake irin na yara,
haka dai ta bashi sama sama.
sun gaisa yake mata godiyar xaman da tayi da
iffaat tace ba komai yiwa Kaine. Ta wuce kitchen
ta jera kayan data siyo ta wanke kayan da iffaat
tayi aiki dasu tsab sannan ta fito koda ta fito
sun tashi gurin duk yayi abinci tayi murmushi
tace sai kace an baiwa jinjiri abinci, ta share
tsab, ta gyare.!
Iffaat bayan sun qare chin abinci farhaan yasa
wata rigimar wai wallahi bayan sa kamar ya
bude Dan gajiya, taxo ta masa tausa, tace
bakyau ana qare chin abinci a kwanta Dolensa
yayita zagayawa a daki har yaji ya gaji kuma ya
hanata tafiya bayan ya qare ya kwanta bacci..


muhd-Abba~Gana
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive