shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 20 July 2015

WACE CE******ITA? 59

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 59
Na ABBA-GANA
Mama tayo kanta tana tambayar lafiya amma
ina iffaat ta riqa ta suma,
Yy Ali ne ya dauki wayan ya kira number Yy
Suhaila, Dr. Ya masa bayanin da ya yiwa iffaat
yace babbar motace ta shiga gabansu suka
yanka daji anan motar ta wuntsila rai yayi
halinsa Yaya Ali ma dashi da qarfin halinsa sai
da yayi kuka, ya yiwa mama bayani tuni gida ya
rude da koke koke Yy Ali yayiwa baban Suhaila
waya ya fada Masu abinda yake faruwa kamin
kace kwabo labarin rasuwar Suhaila ya baje
family namu kowa yaji mutuwar Suhaila cox
Suhaila mutunce mai mutunci ga haquri da
kawaici, bata shiga harkar da ba nataba kai
mutuwa tana dauke nagari. farhaan kam da ya
samu labari mutuwar tsaye yayi bai samu damar
maganaba saida yaga gawar Suhaila, sannan ya
fara kuka kamar qaramin yaro kamar wani
zararre, lallai ta tafi tana binsa basussuka cox
bayajin tayi wata biyu yana kyautata mata
kullum cikin muzguna mata yake, su farahnax
kam haka ta dawo kamar mahaukaciya, mutuwar
ta ratsa kowa a gidannan musamman iffaat da
farhaan da maman Suhaila.!!!
Iffat koda ta farfado har an kai Yy Suhaila
makwancinta wayyo Allah, mutuwa mai raba da
da mahaifi miji da mata Yaya fa qanwa aboki da
aboki. Mutuwa tayi yankan qauna a wannan
family...
cikinta ma anciroshi da ranshi amma da yake
wata7 ne kwana biyu yayi yabi uwar shi, cikin
da farhaan yayi burin ta zubar tun tana amarya
zan iya cewa ma bayason cikin.
Sauda yawa Suhaila tana kiran iffaat qanwarta
ta fada mata abinda farhaan yake mata amma
tace kada ta fadawa kowa, kuma bata taba
fadaba
Mutuwar Suhaila yasa iffaat ta qara tsanar
farhaan gani take kamar shiya kashemata Yar
uwa! amma fa still sonsa yana cikin zuciyarta,
hmmm soyayya manya..!
***
Arba'en din Suhaila yayi daidai da fara jarabawar
su iffaat mutuwar Suhaila tadan natsar da ita
kadan dama iffaat ta iya matsuwaa idan Abu ya
faru da ita! sunyi neco da waec lfy sai jiran saka
mako, xubi xubi iffaat tana zuwa gidansu
farahnax ta gaida mamarshi da farahnax din da
kuma qawarta Yar baqa zainb khalifa,
Ranar tana zaune dakinta taji sallamar farhaan,
da yake Gidan idan aka shigo dakinsu yana daga
gefe ne sai dakin mama, tanaji ta gane tayi
banxa dashi.
Sunyi hira da mama, tanaji yana tambayar ina
iffaat tace tana daki,
Har ta manta da wani farhaan yazo gidan. Chan
taji sallamar sa a dakina, Dan amsa sallama
wajibine da nasan iffat ba zata amsa maiba, taci
gaba da aikinta, ya zauna ya fara sun batunsa,
yaga ba nasara, yace iffaat.......
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive