shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 20 July 2015

WACE CE******ITA? 54

computerimages1.jpg

.: WACE CE ITA..??54
Na ABBA-GANASuhaila anachan ana barsar amarci da
angonta...
Iffaat kuwa ananan ana fama da axaba gwanin
ban tausayi....
ko wata Biyu ba'ayi farhaan ya fara chanza wa
ya gama da ita kenan, ya koma Neman
matanshi duk qoqarin Suhaila na kyautata mishi
ta ko wace hanya duk abinda tasan zaiji dadi
tana masashi iya qarfinta kuma qaryane yace
bata gamsar dashi cox a dare daya sai yayi
round biyu haka take haqura duk da tana jin jikii
burinta ta faranta masa, amma abanza takeyi su
farhaan kam ba hali.. dama mai hali baya barin
halinsa abin dai ba dadin ji sau tari takan
qyanqyasawa iffaat amma tace kada ta fadawa
mama.....
Ranar Suhaila ta kama farhaan yana waya da
wata akan zasu hadu wani guri, ranta ya baci ta
mai magana kuma tace sai ya fada mata ina
zaije sannan ta barshi ya fita...
Habawa kamar jiranta yake ya wani taso mata
kamar ya cinyeta hadda su gori wai albarkar
qanwarsa takeci ita tasa ya aureta, ba itace
choice dinsaba inda yake shiga banan yake
fitaba, maganganun farhaan sun qona Suhaila
matuqa ta shige daki tana kuka...!
Allah sarki Suhaila.!!
Kamar daga sama saiga iffaat yan mata dama
iffaat bata cika xuwa Gidan ba cox abinda take
gani ranta yana quna, idan dai kaga tazo Gidan
to aikota akayi, yanxuma wani tsimine aka kawo
mata daga sokoto shine akace ta kawo mata
aka aiko iffaat...
tin tsakar gida take kiran yy Suhaila har tashigo
palo bata nan, tashiga daki taganta tana kuka
hankalinta ya tashi tayi ta tambaya amma taqi
fada mata dagyar ta fada mata Ashe yana bakin
qofa yana jinta tana qare fada ya shigo a
fusace.. Kin gayawa uwata sai ta kasheni ko ta
hanani yin abunda naga dama wawuya kawai.!
Ashe bazaki iya rufawa mijinki asiriba..?? yayi
tsaki ya koma Palo tofa masu sayen fada da
kudin su bare an sami dalili,ta miqe tsaye ta
tsallake Suhaila ta fito Palo...
Taxo gaban sa ta riqe kunkumi amma wallahi
Yaya farhaan ka bani mamaki, ashe har yanxu
kana wannan mugun halin naka?? Koda ba abin
mamaki bane hali zanen dutse. Ta nunashi da
hannu abin kunya namiji kamilalle a fuska amma
xuciya ta shedan tirr da hali irin naka, koda ba
komai bane wayewace!!! Amma Allah wadaran
wayewa irin taka wacce akeyinta da Neman
mata ni wall...... Kamin ta qare farhaan ya miqe
ya kwashe ta da mari kuuut.....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive