INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWATA
INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN
BUDURWATA ?
Tambaya:
Malam koya halatta na kalli gashin macen da
nakeso in aura ???
Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaimin
bayanin abunda ya halatta in kalla a jikin macen
dazan aura kafin muyi aure.
Nagode.
Allah ya gafarta maka.
(Daga abba gana)
AMSA.
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kakeso
ka aura.
Kamar yadda yazo a cikin hadisi, inda Annabi
(s.a.w) yake cewa:
"Idan dayanku yana neman aure, to in yasami
damar kallon abin dazai kira shi zuwa aurenta,
toya aikata hakan"
Abu dawud a hadisi mai lambata: 2082.
Amma malamai sunyi sa6ani akan wurin daya
kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da
yaje neman aure:
1. Akwai wadanda sukace zai kalli fuska da tafin
hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna
ni'imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna
kyau.
Saboda haka sai a takaita akansu, wannan itace
maganar mafi yawan malamai.
2. Nabiyu kuma sukace, zai kalli duk abin yake
bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da
hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.
3. Malamai na uku sun tafi akan cewa:
Zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta
fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya
kalleta.
Wannan ra'ayin shine yafi dacewa, saboda ta
haka mutum zaisan yanayin matar dazai aura,
yadda ya kamata.
Saidai ba'a son yawaita kallon saboda duk abin
da aka halatta saboda bukata, toya wajaba a
tsaya a gwargwadonta.
Wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin
waya, zai iya zama haramun saboda yana iya
tayar da sha'awa, sha'awa kuwa tana iya kaiwa
zuwa barna.
Wal iyazu billa.
Saboda haka matasa ku kula dan kunji ance ya
halatta, kada mutum kuma ya wuce gona da iri a
wajen kallon.
Mai neman Karin bayani, yaduba:
Al'insaf 8\15 da Muhallah 9\161.
Allah shine mafi sani.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.