WACE CE******ITA? 61
WACE CE ITA..??61
Na ABBA-GANA
Suna tsaka da labarin su saiga farhaan ya shigo
ya gaida surukansa yama ummanshi ya jiki ya
shige dakin abbansa,
Bayan ya wuce ne maman Suhaila take cewa
Allah sarki yaronnan har yanxu bai nemi
mataba? Umma tace kedai bari gashinan
Bansan mi yake jiraba, niko ga shawara, mizai
hana a hada farhaan da iffaat aure. Mama tayi
dariya kai hajiya kulu ina kika taba ganin rigima
da rigima sun hadu duk sukasa dariya umma
tace lallai kam Dan farhaan da iffaat basa zama
guri daya. Mama tace koda yake shi aure daban
ne wata qila sai kiga sun zauna lfy.
Gaskiyar magana dukansu sunyi na'am da
shawarar hajiya kulu maman Suhaila sun tsaya
akan zasu shawarci mazajensu suji,
Suna zaune suna tadi saiga iffaat da ta ciki
kyale da su mangoro da gwaiba umma tace um
um mai hali baya barin halinsa..! duk suka saka
dariya, taje ta wanko ta kawo musu suka
farasha, dama ita qa'idarta idan zatasha
mangoro saita mulmulashi yayi laushi yayi ruwa
sannan tasha. Ta kuwa miqe qafafu ta saka
basket dinda ta saka kayan a ciki ta fara shan
mangoronta tana zaune saiga farhaan ya shigo
ya kalleta, xaman da tayi ya bashi dariya ya
tuna mai da lokacin da take qarama sai yaji bari
ya tsokaneta komai ta fanjama fanjam.!!
Wai umma wannan Yar taki ba university take
xuwaba? Umma tace eh chan take kaga yata an
zama yan mata ko..!! Inafa yan mata har yanxu
bata wayeba! Kalli Dan Allah yanda take shan
mangoro kamar wata Yar ruga,! ruwan
mangoromangoro suna bin hannu, ya kwashe da
dariya hadda buga qafa ya gama quleta ya kalli
umma anya kuwa zata sami miji a haka??
Umma tace ka sakawa yata ido dayawafa miji
kam sai ta xaba Dan ma bakaga yanda ake
layiba dukansu suka dara nima dai jabo na dara
kuma Masu karatu sai Ku dara.!!
Iffaat tace umma ki barshi, ta dago ta kalleshi
ido cikin ido tace mijina sai ka Ganshi wayayye
na gaske ba irin wayewarkaba, ba Wanda yagane
habaicin da ta masa sai shi damu Masu karatu.
Yadan Sosa kai yayi murmushi qarfin hali mama
bari na tafi tunda kun hanani mangoro, umma
tace sai kace wacce da debo ta sammaka, yace
waa ai wannan tafi dijee rowa.! da zai fita ya
hada da gefen chinyarta ya take saida tayi qara
ta jefeshi da qallon mangoro......
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.