Menene hukuncin mai zuwa gidan abokinsa yana hira da matarsa ???
Assalamu Alaikum
Malan menene hukuncin mai zuwa gidan abokinsa
yana fira da matarsa alhalin abokin nasa
bayanan ???
(Daga Abdullahi Baban Saifalah).
AMSA
====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
A'a wannan bai halatta ba, yin hakan kusancine
ga aikata zina.
Saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) wanda
yake cewa:
"LAA YAKLUWANNA AHDUKUM BI IMRA'ATIN
ILLA MA'A ZY MAHRUMIN"
Fassara
"Kada dayanku ya kadita da wata mace sai
tareda zu maharruminta.
Ma'ana
Dan uwanta wanda babu aure a tsakaninsu,
kamar wanda suke uwa daya ko uba daya ko
kuma uwa daya uba daya ko makamancin haka.
A Wani hadisin kuma yana cewa:
" ﻻ ﻳﺨﻠﻮﻥ ﺭﺟﻞ ﺑﺎﻣﺮﺃﺓ ﺍﻵﻛﺎﻥ ﺛﺎﻟﺜﻬﻤﺎﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ "
Abinda hadisin yake koyar damu shine:
"Duk wanda ya kadaita ma'ana ya ke6anta da
wata mace wacce ba muharramar saba, to zai
kasance na ukunsu shaidanne.
To kaga kuwa wata rana idan sha'awarta ta
motsa komai zai iya faruwa kasancewar babu
mai dauke mata sha'awar tata a kusa.
Saboda haka bai halattaba, aikata hakan
zunubine mafi girma.
WALLAHU A'ALAM
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.