shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 22 July 2015

WACE CE**********ITA? 75

computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 75
Na ABBA-GANA
Armiya'u tace Wallahi kuwa hafsa taso farhaan
kamar rayuwarta ta bashi kanta sabida tana
gannin kamar zai aureta, kai ai hafsa tayi jinyar
rabuwa da farhaan, iffaat ta gyara zama tace ai
yace min tanada jarumta sosai, armiya'u tace
uhum Ashe dai kinsan komai kena,? nama daina
jin tsoron fada, iffaat tace eh duk ya fadamin
yace har matarsa ta farko tananan yana tare da
ita yace har gida yake kawota.! armiya'u ta
gyara zama za'ayi gulma ai iffaat in gaya miki
yanda hafsa ta bani labari mijinki akwai tsananin
buqata kuma yanason jarumta matuqa gurin
harka, idan kika kiyaye haka wallahi zaki
sameshi a hannu shiyasa ma hafsa ta daga tuta
duk cikin yan matanshi yafi ji da ita, idan kika
kiyaye sai yanda kikayi dashi.!
Iffaat dai duk da qunan da zuciyanta keyi bai
hanata saurareba, wai har wata tasan asirin
mijinta Allah wadaran halin farhaan, Kinga mijin
ki Dan gayu ne, so wallahi sai kin kasa kin tsare
yanda yan mata sukayi yawa idan ma Allah ya
tsareki bai miki kishiyaba to zai nemi mata a
waje amma idan kika gyara kanki kin gama
komai Dan maganin matannan kinasha kwalliya
duk ki riqayi kissa da kisinsina ki zama first
class gaki da gashi kiyi yanda kikasan mijinki zai
ji dadi, Dan girkinnan duk ki xama kece kan
gaba, wallahi nasan yan matan da suke son
mijinki ba adadi kuma duk sun fiki girma da
wayo, ko wacce tasan yanda zata sace zuciyar
namiji so ki zama very careful iffaat kam ta
sassauto da kishi tana sauraren jawabin qawarta
Aysha armiya'u mada lallai ita tasan inda duniya
ta Nufa kuma itace qawa ta gari....
Armiya'u tace ki duba yanxu ina kallo mijinki ya
shigo baki gaisheshiba kuma ko ruwa baki
kaimasaba bare abinci, iffaat tayi murmushi
batace komai ba
Armiya'u dai ta baiwa iffaat darasi kuma ya
shigeta matsalar batasan yanda zata fara bane,
bayan sunyi sallama ta tafi saiga farhaan ya fito
a daki dama jiran tafiyarta yake yaxo yayi tsaye
yana kallonta wannan yarinya akwai kwarjini sau
da yawa idan ta masa Abu ya tunkareta sai ya
kasa..yaga idan ma masifa zai mata aikin banxa
zaiyi don ba jin masifar takeyiba so gara ya
mata magana cikin ruwan sanyi....
Ya kira sunan ta tana kwance ta dago ta
kalleshi, ki tashi zaune batace komaiba ta miqe
zaune yace ki ijiye waya, zamuyi magana kafada
inajinka kawai.
Ya kira sunanta, Iffaat tace na'am ki ijiye waya,
sai ya bata tausayi ta ijiye waya ta fuskanceshi
dakyau yace iffaat abinda kikayi kina ganin kin
kyauta? Ta xaro ido mi nayi kuma? Kin fini sani,
aah Malam kada amin sharri ina zaune lafiya mi
nayi?? mi kika yiwa yaran mutane? Ta bone
kuwa wayanni yara kuma ?? Yace abokan aikina!
Uhum yy kenan abokan aikinka kuma? Ya za'ayi
nasan abokan aikinka? Iffaat wannan serious
issue ne, miyasa kika aikata hakan?? Nifa yaya
ban gane mi kake fadaba kamin dalla dalla
kawai, yaga zagaye zagaye ba nashi bane yace
yaran da kika yiwa aski da bille Kuma kika
dakesu....!!by muhd Abba Gana


mu hadu a kashi na gaba
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive