shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 26 November 2016

Waye sanadi? 71 & 72


[11/21, 8:09 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣1⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com wani irin bakin ciki ya cikan zuciya tare da tahowar hawaye "na koyi uwaka in har zan yi kewarka zanyi kewar fitowata daga cikin wutar da na shekara ina shan azabar ta na fada a fili. haka na zauna babu abinda nake sai kuka babu kuka abinda yake tsaidani daga yinsa sai sallah tunda na idar da sallah isha'i na fara jin tsoro yar hayaniyar da nake ji da kuma surutan mutane a baya tunda akayi sallah ban kara jiba don haka duk hankalina ya tashi koh motsi naji sai na hau dube-dube har wajen karfe daya lokacin ina bakin kofar falon a zaune, kaina ya hau ciwo ga zazzabin daya rufeni ina zaune naga kofar tana budewa ya shigo kwata-kwata na kasa dago kaina na kalleshi. har yanzu baki bar kukan nan ba, kina nema ki haifar wada kanki ciwo ki daga min hankali. ganin ban dago kaina ba yasa ya karaso ta tsugunna a gabana mu wife me yake faruwa? ya kai hannunsa kaina yana kokarin dagawa iya karfina nasa na hankade shi na dago fuskata idanuna da kyar naiya daga su nace. kada wannan munanan hannunka su kara karambanin taba jikina na tsaneka wallahi imran da na bude ido na ganka gara ace idanuna sun dauwama a rufe ka kauce a gabana bana kaunar ganinka," ina fadar haka naja jikina na shiga cikin dakin. **** **** **** **** **** *** Don Allah rukayya kiyi hakuri ki bar kukan nan karkija wata cutar ta kama ki tunda kuka dawo kullum kina cikin kuka da damuwa, insha Allahu safiyya tana nan lafiya, kuma zata dawo duk irin damuwar da kika shiga baki kai yaran nan ba hajiya hassana (mahaifiyar rukayya) ta dago idonta cike da ruwan hawaye ni dai don Allah hajiya ku barni na koma can na dubo ta, ki taimaka kisa baki abba ya barni wallahi yaya salim ba zai dubata sosai ba... kuka yaci karfinta ta kasa karasawa gaskiya ba zan saka baki ya barki ba, kiyi hakuri insha Allah salim ba zai dawo ba sai tare da ita, kina ganin alhaji da kawunki har can suka je suka bada cigiyarta kina ganin jiya kawunki ya dawo aka tura salim rukayya yanda kike kaunar safiyya haka muke kaunarta, wallahi inason safiyya kamar yanda nake sonki ki duba kiga yanda hankalin kawunki ya tashi kamar ke kika bata. hajiya ni dai ki min taimakon nan kisa abba ya barni koda kawu ne mu kara zuwa na san sadiya za a bar ta muje mu kuma bamu san halin da imran yake ciki ba, tun ranar da yazo muka gaya masa ya suma aka kai shi asibiti washe gari muka kirawo wayarshi baya shiga ina tunanin ko ranar da ya fadi yan makaranta suka zare masa abu ina ganin harda wayansa. in har kinaso nayi wa alhaji magana sai kin daina wannan kukan to wai me zana ki gayawa iyayenta halin da ake ciki kinga yau sati biyu kar suyi tunanin har yanzu baku dawo ba, hajiya su iyayen safiyya suna tunanin tafi shekara da bata saboda tun ranar dazamu tafi har muka zo nan ta kwana ta bar gidansu da zummar bazata koma ba." cikin rashin fahimta hajiya hassana tace ban gana ba, nan take ta zayyane mata labarin da safiyya tabata, Allah sarki baiwar Allah dole yarinyar nan ta shiga damuwa, amma wannan kakar tata batayi mata adalci ba data gaya mata wannan labarin ita kuma safiyya tayi wauta da bata tsaya ta saurari abinda mahaifiyarta zata gaya mata ba nasan ita kanta mahaifiyar tata baza taso haka ya faru a kanta ba, kuma ita safiyya bai kamata ta yanke hukunci cikin bacin rai ba, data bari ta saurari bayanin ummanta idar har vai gamsheta ba sai tayi tunanin mafita wallahi hajiya kullum haka nake nuna mata tun muna makaranta amma taki ganewa ku... kema da laifinki rukayya hajiya hassaja ta katse ta hajiya wani irin laifi? me yasa tun ranar da kukazo kuka kwana baki gaya min ba??? 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/22, 8:29 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣2⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.abbagana.cf hajiya nima a lokacin bata gayan ba sai da muka je makaranta take gayan halin da take ciki, to me yasa baki bugo waya kin gaya min ba har kukazo duba alhaji amma baki gayan halin da take ciki ba? ni fa hajiya nayi zaton fadan dana yi mata ta hakur yanzu ke kina tunanin safiyya tafiya tayi da kanta ko dauke ta akayi? gaskiya hajiya tunanina yafi karkata a kan dauke safiyya akayi, saboda ana gobe zamu taho mukayi fada ta dawo tana bani hakuri da kanta kuma harda ita muka hada kayanmu fitarmu da sadiya bamufi munti goma ba muka dawo bata nan. Dan Allah hajiya ku barni na nemo safiyya ban san a wani hali take cik.... kuka yaci karfinta ta kasa karasawa hajiya ta juyo ta jikinta tana shafa kanta kamar karamar yarinya tare da gaya mata maganganu dazasu kwantar mata da hankali haka har barci ya dauketa. hajiya hassana ta rafka tagumi ta fada cikin tunani wannan wace irin kauna rukayya takewa safiyya yarda batanta yake neman wargaza farin cikin yata mace guda daya bama ita daya ba harda ni kaina da duk wasu makusantanmu. ya Allah ka bayyana yarinyar nan, kasa tana hannun na gari don girmanka. ta durt a fili tare da zubowar hawaye a fuskarta. sai wajen karfe biyar rukayya ta tashi ta ganta a falo ita daya dakinta ta shiga. tana toilet wayarta tayi kara data kammala alwala sannan ta fito tana fitowa aka kara kira tayi saurin dagawa hello kawu' daga can barin da akayi kira aka amsa mata cikin katuwar mury ba kawunki bane, muna bukatar miliyan biyar in har kina kaunar kawarki kina kuna kaunar taci gaba da shakar numfashi mun baki kwana uku, ana fadar haka aka katse jikinta na rawa ta fito tana kiran hajiya sukaci karo da kawunta yayi saurin rike ta yana girgiza ta lafiya rukayya, tana mayar da numfashi kamar tayi gudun shekara tayi mishi bayani. ina number ta aka kira dashi? tayi saurin bincikar received call tana dubawa taga hidding number bata san lokacin datayi wurgi da wayar ba tana kuka daidai lokacin hajiya ta fito tana tambayar lafiya ganinta da kawu ta tsaya tana kallonta sannu da zuwa tace wa kawu bai samu damar amsawaba har sai daya lallabata tayi shiru tare suka zauna akan kujera yana cigaba da lallabata ya juyo wajen hajiya hassan yana tambayarta alhaji ibrahim yana ciki? kanta bashi amsa yashigo bayan sun gaisa ya maida kallonsa ga rukayya wadda take ta faman share hawaye har yanzu kukan kike koh? bazakiyi hakuri ba abba kirafa akayi ta waya wai na bada miliyan biyar a kawo safiyya don Allah ku hada kai da kawu a ba su har imran zanwa waya shima ya bada wani abu a hada son Allah ku taimaka abba yace ina number da aka kiraki muyi magana in har zasu kawo ta ko miliyan nawa ne sai a basu kawu yace nifa ina tunanin wasu macuta ne suke so su karbi kudi a banza, hidding number sukayi suka kira hajiya hassana tace ni kam ina ganin a bari in suka kara kira sai su fadi inda suke a kai musu su bamu safiyyan ko hankalinmu zai kwanta, shi kenan rukayya kiyi shiru bana san kukan nan zamuyi shawara da kawun inyaso har in sun kara kira kice suyi miki kwayancen inda za a same su sai a kai musu kudin. sun jima suna lallabata har sai datayi dariya ta mike kawu bara na debo maka hotunanmu tana shiga dakin ta dauko jakarta ta zaro hotuna cikin album ta fito bata kula da farar takarsa ta fado ba sai bayan sallar magariba ya tafi tareda yaya isa hajiya ta mike bara na kaiwa alhaji abinci tana shiga dakinta taci karo da yar farar takardar har ta wuce ta dawo tq dauka ganin rubutun yasa tayi saurin warwarewa don taga me aka rubuta. ta dora idonta akan rubutun. ta fara karantawa:...... 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Waye sanadi? 67---70



[11/14, 7:58 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣7⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com ga safiyya tana so ku gaisa "hello aunty' aunty kin manxe dani ba kya kirana a waya can barin safiyya tace kiyi hakuri kanwata ban cika kunna wayata ba shikenan aunty na hakura yaya ya gaya miki ummata ta haihu baki min barka ba, an min kanne har guda biyu aysha bai gaya min ba da har suna zanzo lah! aunty kizo daman gobe ne sunan tana dariya tace aysha kinga lokaci ya kure da sai nazo amma ki mata barka duk ranar da nazo zanzo naga kannenmu a,a ba zan yarda ba bara na baki kiyi wa umman barka to a bata inyi mata kada kanwata tayi fushi dani ta mikawa umma waya tana dariy umma ga kawata ku gaisa ta karbi wayar tare da yin sallama kirjin safiyy ya buga da sauri daidai lokacin network ya hau rawa muryar nana ta dauke umma ta mikowa aysha waya tare da gaya mata bata jin magana tayi saurin sawa a kunnent hello aunty hello aunty ba kyaji ne ta katse wayar, ina zaton network yana da matsala nasan zai kara kira sai ku gaisa salima tace umma wannan kamar su daya da khalil aysha tace ni kum nafi ganin kamar su da abdul, da yaya imran kalli irin giransu daya ita dai umma kallonsu take tana dariya daga suce suna kama da wane sai suce suna kama da wani. washe gari karfe takwas alhaji nazo gidan tare da khalifa sai kanin hajiyarsa khalifa ne ya shigo umma da matar malam mado suna aiki bayan sun gaisa ya shigo rumfar. fitowa ta kenan daga wanka sai aysha tana sawa hassan kaya hussaini kuma yana hannun salima suka gaisa ya karbi hussaini. ya juyo yana kallon aysha ina umman? kan tayi magana salima tace tana daki don Allah kanwata dauki tabarma ki kai zaure salima ta mike da saurinta tana fita umma ta fito aza khakifa ne nine umma an tashi lafiya? lafiya klau khalifa ya mutanen gida? duk suna lafiya tare muke da kawunmu daga adamawa yazo za a kai masa yaran ya gani" duk da ba wani taro akayi ba mutanen unguwar sun shigo sosai sai wahe garin suna su aysha da salima suka tafi. tun bayan suna wani waye wan gari sai alhaji nasir yazo sau biyu wajen yaransa in banda gaisuwa babu abinda yake hada mu tun babah tana yimin fasa har ta gaji ta hakura sai dai ita ta zauna suyi hira. haka aysha duk ranar asabar sai tazo wata ran har da Dr khadija ake zuwa, duk ranar da aka zo sai an kira yaya imran mun gaisa wata ran har mamansu sai da aka ban muka gaisa da su khalil. ranar danayi kwana arba'in gidansu aysha na fara zuwa tare da taimakon zuwaira yar autar malam mado ta goyi hassan muka tafi, murna wajensu aysha har ta rasa inda zata sa kanta haka mamansu Dr. khadija sai yamma Dr. khadija dasu aysha suka kawo mu gida. cikin wata uku inka gansu bazakace watansu uku ba sai kayi tunanin sun kai shekara, sunyi kiba sosai kamar ya'yan karabawa kayan wasa da kayan sawa har mamakin alhaji nasir nake kwata-kwat baya jin zafin kudin. har yar aiki ya kawo mana din kula dasu. **** **** **** **** **** cikin farin ciki ta shigo cikin dakin nasu, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin tsananin farin ciki sanye take cikin material light pink an masa diniki mai kyau na riga sa siket. siket din ya fito da shape din kugunta farin ciki kike haka tun dazun sai dinple sinki ne yake motsawa haka inda labari bani in sha momy ba wani labari bane kawai ina murnar gama karatune kamar yau safiyya ta shiga B.U.K wai yau safiyya ta gama abin da ya kai ta har tana shirin karbar matsayi gaskiya dole muyi murna ina sadiya ne? tana tare da oniya momy tace kizo ki fara hada kayanki ina tunanin gobe zamu bar nan gobe kuma momy? a,a to zamu cigaba da zamane bayan mun gama abinda ya kawo mu. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/15, 8:30 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com nayi saurin zama a katifa na dago fuskata wadda har ruwan hawaye sun fara sallama nace nikam momy bazam koma na bar kano har abada ta dago tana hararata wai ke meyasa baki da hankaki in baki kima ba ki gayan ina zaki koma da zama? zan shiga duniya har abada bana fatan na kara ganin ummata in da kin san zaki shiga duniya da tun farko baki batawa kanki lokaci ba tunzuwanmu kinyi abinda zuciyarki take gaya miki wallahi momy bazan koma wajem umma b gara ma ki rabu dani na riga ba gama yankewa kaina hukunci babu kaffara in har kika dau shawarar zuciyarki zakizo kiyi dana sani lokacin da bashi da amfani lokaci ya kure kuma a lokacin zaki san ni rukayya mai kaunarkice. wallahi safiyya daga yau har abada ba zan kara gaya miki gaskiy ba kije ji yi duk abinda zuciyarki ta gaya miki tana fadar haka ta mike ta fit nayi saurin mikewa na karssa wajen loka na bude duk wasu muhimman takardu na debo su na zuba cikin jakar hannuna na. na riga na gama sakarwa kaina mafita. ina cikin daki momy ta shigo na tsugunna na bara hakuri tana murmushi tace baby ya riga ya wuce daman kekike jan abinda zamuyi fada , ina gaya miki gaskiya ne ki bari muje kano ki saurari maganar umma ki kuma nemi gafararta don wallahi kin daga mata hankali shekara daya ba kasan inda yarka take ba. na daga mata kai sadiya suka shigo tare da oniya yanzu daman gobe zaku tafi baku gaya min ba? oniya ta fada tana share hawaye na matso kusa da ita ina murmushi kiyi hakuri yar uwata kwanan nan zamu dawo. karfe takwas imran yazo lokacin su momy da sadiya basu nan na mike tare da bude jakar momy na zura mata envelop ina hawaye nabi dakin da kallo nayi saurin goge idona na fita ta baya don karmu hadu dasu momy, na kirashi ta waya nake gaya masa ina bayan makaranta. banfi minti uku ba yazo ya fito daga mota fuskanshi dauke da murmushi kanwata unguwa zaki? na girgiza kai cikin sanyin murya nace imran yaufa zamu rabu ina fatan zaka yafemin a zamanmu in na saba maka cikin razana yace ban gane nufin kiba, ba gobe tare dani zamu tafi kano ba? na girgiza kai ni ba zan koma kano ba na bar kano har abada ina tunanin kamar ganin karshe kake min. haba safiyya ki bar fadan haka don Allah idan kika tafi ina zan saka rayuwata don Allah ki rufan asiri karki guje ni safiyya duk inda zaki tafi ba zai kai darajar gidan mahaifinki ba, na dago idona mai cike da hawaye nace imran kace dui inda zani ba kamar gidan mahaifina bako? ya ma kasa magana sai kai ya daga nace to imran ni banda mahafin da zanje gidansa kamar yaya baki da mahaifi dazaki wajensa mutuwa yayi? imran nima bansani ba, ya mutu ko yana raye Allah masani zaman da mukayi da kai ina jin zuciyata tana yi min babu dadi dazamu rabu me yuwa ne tana kewar sabon da mukayi na dago kaina ina kallonsa abindana gani cikin idonsa yasa nayi saurin sunkuyar da kaina . naji muryarsa cikim amwani irin yanayi mai wuyar fassarawa yace safiyya ki taimakawa rayuwata karki tafi ban san halin da zan shiga ba bana magana biyu zan tafi imran ya daga kansa sama yana neman mafita cikin dakika biyu ya samawa kamsa mafita imran Allah ya hada fuskokin...."kan na karasa naji kamar an buga hankici ya daki fuskata nan take hankalina ya gushe nayi baya zan fadi naji an tare ni ana kyalkyala dariya iya abinda zan iya tunawz kenan . A hankali na shiga yunkurin bude idona naji sun min nauyi sosai hannuna na daga na kai zuwa idona don su taimakan har nayi nasarar bude su. wata irin razana nayi na mike tsaye ina kallon jikina kan na gama tantance kayan jikina wata kofa ta bude ya fito daure da tawul daya kuma yana tsane kansa fuskarshi dauke da murmushi amarya kin tashi?..... 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/16, 8:36 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com yana maganar yana mikon riga ta nayi saurin kallon jikina wata razananniyar kara na saka lau tayi zata fadi yayi saurin taro ta nan take ta sume a hannunsa. yayi saurin shimfide ta a gadon da sauri ya zura doguwar jallabiya ya fita ya nufi cikin mota. kayan jikinsa ya debo duk taimakon daya dace yayi mata ya fita yana murmushi har ya dawo tana barci ganin bata farka ba yasa hankalinsa ya dan tashi jikinsa a sanyaye ya karasa gefen tafkeken gadon ya zauna tare da dire ledan da take hannunsa. wayarshi ta hau kara ya zaro tare da jan tsaki ya daga ba tare da yayi magana ba cikin shagwaba tace hello yaya imran kana ina tun dazun dady yake nemanka ka daga mana hankali. cikin tsawa yace haba khadija na gaya muku ina lafiya akwai aikin da nake shiyasa ban kwana a gida ba yana fadar haka ya katse wayar. tsawarsa ne ya farkar da nana daga suman datayi, jin kukanta yasa imran juyiwa da sauri duk wani karfinta ta tattaro ta mike tsaye hannunta ta kalla tayi saurin fincike karin ruwan hawaye babu abinda yake zuwa a idanunta, kanta kamar zai fashe haka takeji ga wani irin zazzafan zazzabi da yayi mata sallama. karo na biyu ya kara miko mata rigarta yana murmushi. sai lokacin ta kalli jikinta tayi sarin rarumar bargo ta kare kirjinta ta dafo idonta tana kallonsa babu abinda ya hanga cikin kwayar idonta sai tsantsar kiyayyarsa bakinta take motsawa tana san magana amma ta gaza durkushewa tayi a wajen tana wani irin kuka. meye abin kuka safiyya? ina son kidayawa shi yasa na nuna miki kaunata farin ciki zaki imran ya hada jiki da keh, kin zauna kina kukan da bashi da amfani cikin wata irin murya na shiga magan ka cuceni imran kaci amanata ka wargaza duk wani farin cikina ta keta martabata ka tarwatsa duk wani burin rayuwata nayi bakin cikin tashina naso ace kana gama cika burinka ka kashe ni na huta da ciwon zuciya. imran ka gama da rayuwata, don Allah ka taimakan ka kasheni na huta ka taimaka ka kashe ni ba zan taba yafe maka ba, na tsane ka bana kaunar na ganka ka tashi a gabana" safiyya abinda kike so nayi miki kina maganar zaki shiga duniya nasan kuma in kin shiga duniya abinda zakiyi kenan don haka nace gara nina fara aikatawa nasan kuma zaki fadi haka, nikam ba zan kashe kiba ina sonki cikin tsawa nace baka son baka kaunata! har abada ba zan taba kaunarka ba kayi min tabun da har abada ba zai taba gogewa daga zuciyata ba, kaje Allah yayi min sakayya da gaggawa. ina fadar haka na fincike riga ta jiri na dibana kamar zan fadi nayi saurin dafe garon dakin. haka nabi bango har na kai kaina toilet na zura riga ta har na fito yana tsugunne inda na barsa naje kofar dakin don na bude na fita iya karfina na hau jan kofar amma na kasa na juyo ina kallonsa muryata a dashe nace kazo ka bude min zan fita yana wata irin dariyar mugunta yace safiyya kin shigo dakin nan kenan bazaki fita ba har sai kin amince zaki auren muyi rayuwa mai kyau da... kan ya karasa na katse shi wallahi imran dana aure ka gara na auri bakin maciji wanda kullum zai sare ni sau dubu zan zauna dashi da dai na zauna da kai. ina fadar haka na tsugunna a bakin kofar naci gaba da kukana ledar da ya shigo da ita ya ajiyen a gabana. ga abinci nan kar yunwa tayi miki illa' yana fadar haka ya tafi gado ya kwanta. a wajen na kwana ina kuka har gari ya waye kin yarda da imran gashi ya cuce ni yayiwa rayuwata karan tsaye. na mike jiri na diban na shiga toilet na dauro alwala, lokacin dana fito har lokacin yana barcinsa hankali kwance na karasa inda naga an shimfisa sallaya na juyo mayafi na tadda sallah bayan an idar naji wata azababbiyar yunwa wadda take shirin illata cikinta yayi wata irin murdawa ban san lokacin dana saki kara ba ya farka a gigice lafiya? ya fada yana murza ido ko muryarsa bana kaunar naji sautunta. nayi saurin toshe kunnuwana naci gaba da kukana babu magiyar da baiyi min ba don na gaya masa me yake damuna karshe ma sai na rufe fuskata naci gaba da kukana. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/18, 8:41 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com ya mike ya shiga toilet wanka yayi ya fita baifi minti goma ba ya dawo dauke da flask din shayi. zama yayi y hadan sannan ya mikomin kisha mu tafi na juyo ina kallonsa don gaskata abinda ya fada ya kara dagan kai ki sha mu tafi na maida ke na karba ina gama sha naji cikina yana hargitsewa amaine ya tason nayi saurin mikewa don na shiga toilet ina mikewa jiri ya debe ni na dawo zan fadi yayi saurin tare ni nayi yunkurin kwace kaina daga rikon da yayi min amma ya rike ni kam ga amai ya cikan baki, ki zauna karki fadi ganin ba zai sake ni ba yasa na sakar masa ama a fuska har na gama bai sakeni ba sai faman sannu yakemin ji nake kamar wuta yake zuban idan yayi min magana. gaba daya jikinsa ya baci da aman shayin danayi iya karfina na yunkur na hankadashi yayo baya kansa ya bugu, wata yar karamar kara ya saka ya kai hannunsa inda ya buge yana dubuwa yaga jini. safiyya kinga kin fasan kai koh? wallahi imran inda zan iya kashe kada sai na kashe ka dana ji muryarka gara kunnuwana su daina ji har abada. toilet ya shiga ya dauraye jikinsa da wajenda yaji ciwo da kansa ya zauna yayi gyaran waken ya juyo wajena. ga magani kisha karki wahala yana maganar yana mikon ban ko kalleshi ba nace ina jakata? mikon yayo na karba nayi saurin zazzagawa wayata ta fado nayi saurin dauka na kunna naji muryarshi karki sha wahala kinga layin wayarki dago kai na ganshi a hannunsa gabana ya karya shi ya kuma watsar. ga kayan break nan zan fita nemo kayan auran safiyya yana fadar haka ya mike nima nayi saurin mikewa ina zaki? yana bude kofar naga mun fito wani tafkeken falo ya sha kujeru ya karasa ya zauna yana dariya. zarcewa nayi wata kofa zuciyata cike da farin cikin ganinta a bude kan na karasa naga tana rufewa ba tare da an taba ta ba, abin ya ban mamaki na juyo ina kallonsa hannunsa dauke da dan remote. na gaya miki ba zaki taba barin gidan nan ba har sai kin amince zaki aure ni na kira malamai su daura mana aure. na dafo kai idona cike da hawaye imran dana aure ka gara na kare rayuwata cikin gidannan har na mutu, kasa hannu ka yanke duk wata alaka da ta fara ginuwa a tsakaninmu nafi son Allah ya sa na mutu na huta. ban so ka! bana kaunarka!! ko baya na gaya maka bazak taba samun soyayyata ba ballantan yanzu daka shayar dani tsantsar kiyayyark. ina rokon ubangiji yayi gaggawar yi min sakayya, banyi tunanin haka daga wajenka ba, ina tun farkon zuwanka me ka gaya min kan na karasa ya katseni cikin tsawa karki kara magana kunnuwana bazasu iya juran munannan kalamunki ba nayi tunanin haka kike so kiyi in kin shiga duniya to don imran ya fara meye abin damuwa? ina in na aure ki na taimake ki duk wanda zai aure ki zai goranta miki duk daran dadewa ni daya ne ballantan bazan goranta miki ba" bana kaunar taimakonka wallahi har abada ba zan taba auranka ba da na aure ka gara na auri kasurgumin kafiri bashi da addini, na san ba zai iya aikata wannan muguntar ba, wallahi gara na mutu banyi aure ba"' shikenan safiyya mu zauna a haka har karshen duniya yana fadar haka ya mike yayi cikin dakin da muka fito. a wajen na zauna naci gaba da kukana har barci ya dauke ni karfe sha biyu na fark naganni kwance a kan doguwar kujera, kwata-kwata banyi tunanin waye ya dora ni a kan kujerar ba da kuma yar guntuwar takardar data fado daga jikina ba, na mike jikina yana rawa sakamakon kyakkyawar yunwar da nakeji. nayi cikin dakin na debo kayan shayen daya kawo min na dawo falon na hada ina gama sha na lura da yar guntuwar takatdar na dauka naga rubutu kamar haka:" NANA SAFIYYA NA FITA NEMO KAYAN AUREN KI DA FATAN BAZAKIYI KEWATA BA GA KAYAN KALLO NAN KI KALLI INDIYA KI KOYI SOYAYYA DAZAMU SHIMFIDA IN MUNYI AURE KI KUMA KALLI MASU KAMA DAKE. NA KI A KULLUM A KODA YAUSHE ""IMRAN SALIS"". 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Tuesday 15 November 2016

WAYE SANADI? 58--66


[11/1, 9:10 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com karya kike kinaso ki karasa da imran koh? lah momy ai shi baice yana sona ba, kawai gaisuwa kawai muke kinga shi ba maye bane. oho miki dai wallahi ki iya kanki, zan iya momy amma ba yanzu ba. sadiya ce ta shigo yanzu muka hadu da imran zai fita nace har an gama soyayyar Allah sadiya bakya ganewa waya gaya miki soyayya muke? ana gobe abba zaizo bayan mun gama waya na mike na shiga toilet bayan na shirya na juyo ina kallon momy nace"momy zanje unguwa tayi saurin dago kai ina kika sani da zaki unguwa? kai momy me kika daukeni ina tare da oniya tana nunamin gurare kuma yau nidaya zan fita nayiwa hajiya tsaraba na bana abba ya kai mata. **** **** **** **** **** ** Rakiya!! Rakiya!! ta shiga kwala mata kira tayi saurin fitowa tana daura dankwali 'gani babah' gani nayi lokacin zuwanki asibiti yayi baki fito ba kin ta sana'ar taki" yanzu nake shirin fitowa ina gyara kayanmu dana wanke ne dana gama zan tafi. bara naje nayi barka kanki gama, tana maganar tana yafa mayafi bayan fitarta baifi minti biyu ba naji sallama na amsa tare da fitowa ina karasawa mukayi ido hudu dashi nayi saurin juyawa zan koma naji muryarsa babah tana nanne? a ciki na bashi amsa na shige cikin kallon fuskarsa babu abinda ya karan sai bakin ciki ina shiga daki na zauna wani irin hawaye ya zubomin wannan auren ba karamin ya karamin ba face bakin ciki tunda sanadin sa na rabu da farin cikin zuciyata, wayyo Allah na safiyya ina kika shiga kika barni da tunanin ki a raina bazan taba farin ciki ba muddin bakya tare dani, a wani hali kike shin tana raye tsahon wata uku ban sata a idona ba nayi saurin kauda tunani tana raye tabbas jikina yana ban safiyya tana raye ki dawo gareni na miki bayanin da zaki gamsu wallahi safiyyata ba shegiya bace kizo na gaya miki gaskiyar waccece ke, kuka yaci karfinta tafi minti biyar tana kuka jin muryar babah a waje tan gaisawa yasa tayi saurin tashi ta fada ban daki, wanka tayi ta fito babah zan tafi ta zaro kudi ta mika mata ki biya ta bakin asibiti ki siyomin kayanmiya. tana fitowa bakin titita samu mota ta shiga ta zauna kusa da wata yarinya wayartane tayi kara tayi saurin dagawa hello aunty na dawo can kuma tace a,a tun jiya na dawo na baro su lafiya. ta kara cewa aunty zaman lagos da dadi karatu yazo gangara sai dai innazo zaki sha labarin karatun safiyya umma tayi saurin dago kai tana kallon yarinyar, ita kuma ta cire wayar da ke kunnenta tana dariya nan take umm ta shiga tunanin tata safiiyan. hajiya ba a nan zaki sauka ba? tayi saurin kai dubanta kofar asibiti ake ta zaro kudi ta mika masa ta shige cikin asibiti. tafiya take amma ba sosai take ganin gabanta ba, babu abinda yake ranta sai tunanin safiyya har ta kusa karasawa dakin taji muryan asha mama sannu da zuwa nayi saurin juyowa ina murmushi, aysha antashi lafiya? lafiya klau mama. ina maman taki tana gida cewa tayi nazo na tafi dake gidanmu yau ba zata samu zuwa aiki ba, nama dade da zuwa harna fito saina hangeki. banyi musu ba na bita muka tafi dan na riga na saba da ita kusan yanayinsu daya da nanata illa wannan bata da taurin kan nan gata kuma da hakuri sabanin nana. babu wsni nisa tsakaninsu da asibitin muna tafiya tana jana da hira har muka karaso gidansu, wani falo ta kaini bai kyan tsari mama ki zauna bara na kira momy ina zama ta kwalawa yar aikinsu kira lami ki kawo ruwa anyi baki tana fadar hak ta hau bens wanda mattatakalarsu take cikin falon da nake zaune. tana hawa wata budurwa ta shigo hannunta dauke da tire an dora lemun kwali da ruwan roba sai wani kofi mai kyau............ 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/2, 9:00 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com sannu da zuwa hajiya yauwa sannunki ta ajiye har ta juya ta dawo dan Allah hajiya na tambayeki abin ya ban mamaki amma na hadiye nace Allah yasa na sani. muryar a hanki kamar tana tsoro kar wani yaji abinda take san fada tace dan Allah kema irin mutanen nan ne da ake nunawa a talabijin naga kuna kama kum gashi kinsa hakori ance daman a garin ake sawa nace daman a wani gari ake ganinsu a talabijin? da sauri tace naji aunty aisha tana cewa makka abin ya ban dariya nace bi ba,a makka name ba na dai taba zuwa sau daya' ta hau dariya amma wallahi kuna kama babu abinda ya rabaku dasu keda alhajin kegos shima kamarku daya kan ta sake wata magana taji saukowa tayi saurin fita tana dariya. ta karaso fuskarta a cike da nishadi sannu da zuwa kina tare da lami tana miki shirme koh? bance komai ba illa murmushi muka gaisa kin ganni yau bana jin dadin jikina ba zan samu damar zuwa ba shine na tura aysha ta taho dake dan karkizo bana nan. nim de yau banzo da wuri ba, tace bari na shiga kitchen tunda ta tashi na fada tuniyar tunani har ta dawo ta hau kiran sunan. rukayya!! rukayya!! nayi saurin dago kaina kamar wadda ta tashi daga barci ta zauna kusa dani haba rukayya me kika rasa kikeso ki jawa kanki wata cutar, kullum kina cikin tunani ki tuna kina da ciki kullum in an auna miki jininki baya sauka sai kara hawa yake, ki cire tunanin komai a ranki. me yake damunki? duk wanda ya kalleki ba zai ga alamun damuwa a tare daka ba' tayi kasa kasa da murya wallahi rukayya in wata ta gaya miki halin da take ciki sai kinga ke a aljanna kike. na numfasa tare da goge fuskata likita matsalat ta zarce yanda kike zara lik....kan na karasa tayi saurin cewa sunana khadija dahie ta fadi hakan ne dan na daina gaya mata sunan danake kiranta dashi. murmushu nayi mata kawai sannan naci gaba da cewa Dan Allah in bazaki damuba ina so na miki wata tambaya tace Allah yasa na sani dan Allah aysha yarkice ta cikinki? karkiyi mamakin tambayan kokiji haushin amsar ki nake jira gaskiya aysha ba yata bace yar yayanace uwarmu daya ubanmu daya danayi aure na jima ban haihu ba dan haka ya barmin ita har kawo yanzu da nake haihuwa inada yaya hudu duk suna makarant to yanzu khadiya in aysha ta bata yaya zakiji a ranki? ta dafe kirji tare da zaro ido ai sai na kusa mutuwa Allah kada ma ya nunamin wannan ranar" khadiya yata ce ta bar gabana yau tsahon wata uku me yasa ban mutu ba? na tsaya ga yawaita tunani ta dago kai cikin tausayawa rukayya ya akayi tabar gabanki? kan wani dalili ne wanda ya zama sirrina khadiya ita daya na haifa sai wannan abinda yake cikina. gaskiya rukayya dole ki shiga cikin damuwa amma kiyi hakuri duk wsni tsanani yana tare da sauki, insha Allahu zata dawo gareki rukayya me yasa baku kai gidan radio ba kinga ba bata tayi ba ita ta tafi da kanta lokacin ya rage saura kwana daya ta tafi lagos karasa karatu au karatu take? tana karatu mana shekara uku tana zuwa jami,a to rukayya bakya tunanin koh tana can tana karasa karatun me zai hana kisa abbanta yaje can legos din ya dubo koh tana can, babanta ya mutu kuma wanda nake aure kan mu rab...." yanzu baki da aure? na daga mata kai yasa kawarta ta dubuta tunda sukaje take nemanta har wasu makarantu taje bata ganta ba nasan hakin safiyya tana da wani irin zuciya in dai ta fadi abu saita aikata nayi imani inda muka rabu tana cikin wannan halin zayyi wuya ta dawo gareni ko safiyya bata rantse ba indai tace ta bar abu to ko ta barshi har abada bare kuma ta rantse nariga nayi rashin safiyya babah da abba sun min SANADIN rabuwa da yata" bata san lokacin data furta haka ba cikin mamaki dr khadija tace suwaye? babah da Âbba 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/3, 8:43 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com nayi saurin dago kai dan kwata-kwata ban san na furta hakan ba khadija bari na tafi. a,a ki bari na gama abinci nayi zaton yini zaki yi. sai karfe uku na fito daga gidan khadija ina shiga na tadda babah tana shara ni magajiya, rakiya kin daga hankali baki taba dadewa haka ba nayi murmushi nace babah yau akwai mutane kuma malaman lafiyar bata zo da wuri ba shiya sa kikaga na dade na jawo kujera na zauna ban jima da zama ba jummai ta shigo harkin dawo rakiya? ehh hajiya na dawo. **** **** **** **** **** A hankali yake rukin motar cikin nishadi ya shigo cikin makarantar , kamar ance juyo bayanka ya hangi mata sanye da likaf tana nunawa wasu samari motarsa yana kokarin ya dawo baya wayarshi yayi kara ya duba cikin screen my Dady dan haka yayi saurin dagawa bayan ya gama wayar ya juyo yana kallon wajen da yaga an nuna motarsa amma babu kowa a wajen, kai kawai ya girgiza yayi gaba. yana karasowa ya tadda momy ta fito a,a aunty momy ina zuwa? bansani ba na gaya maka ka dinga kirana da rukayya in ba haka ba zamu samu damuwa yan dariya ya fito daga motarsa sanye yake da rantsatsiyar farar shadda ta kamfanin chetex kanshi babu hula sai lallausan bakin gashinsa da yasha gyara sajensa kwance luf a kyakkyawar fuskarsa, bakin ya riga ya saba amma zanyi kokarin gyarawa bari na kira maka safiyyar tana fadan haka ta juya ciki tare muka fito momy tace imran bari naje cikin makaranta wajensu sadiya minti uku. wai safiyy baki iya gaisuwa ba? ban iya ba kuma ba zan koya ba' kiyi hakuri kanwata ki mayar da wukar kar a yanka yaya imran, murmushi nayi ina kallonsa abin kamar a mafarki yau safiyya tayiwa imran murmushi insha Allah daga yau harara ta kare. kanwata mun wuni lafiya? ba gani ba wai ma me ya dawo da kai ina ba jiya kazo ba? dan kuma na baka dama shine kullum sai ka zo" kai kanwata abin harda kari jiya banzo ba ina zaton tun ranar da abbanmu yazo muka gaisa sai yau na dawo. waye abban naka? kan babba kana karya kiya saida kazo har naki zuwa mu gaisa saida momy kuka gaisa, yana dariya yace kinga aikin bawa kanki amsa dana zo naki fito mun gaisa ba sai da momy muka gaisa, har na zo mata da budurwata suka gaisa naso ki ganta kiga yayanki koh ya iya zabe" na dago kai ina hararansa wsi kai wacece kanwar taka?? safiyya ce kanwar imran Allah ya kiyaye na juya zan tafi naji muryarsa hab yar kanwata kiyi hakuri naci darajar umma nayi saurin juyowa ina kallonsa ji nayi hawaye yana taho min nayi saurin tsungunawa, ya karaso da sauri fuskarshi dauke da tashin hankali ya tsuguna safiyya lafiya kike hawaye? nan take nasa masa kuka ya shig tsananin tashin hankali meya same ki? wani abinne yake miki ciwo? ni na bata miki rai? dan Allah kiyi shiru ki gayamin kaina girgiza mass to me yasa ki kuka? imran ummata na tuna to kiyi hakuri gobe tunda weekend ne sai muje kano kiyi kwana daya na girgiza kai ina kuka ba zani ba!! bazani ba!! ina fadar haka na mike cikin hostel ya tsaya sororo cikin mamaki har momy ta dawo yan a ganka kai daya ina safiyyar? hum momy lamarin safiyya yana bani mamaki cikin rashin fahimta tace ban gane ba, imran meye yake faruwa? muna hira daga nace mata dan darajar umma shine ta samin kuka, na tambayeta tace ummar ta ta tuna daga nace gobe zamuje taga ummanta shine fah ta hau kuka tana bazata ba tayi saurin shigewa ciki. yayi saurin bude motarsa ya dauko mata jakar rubutun, momy ga rubutun zan kiraki an jima naji me yasa kuka." 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/4, 8:32 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣1⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com karka damu imran lamarin safiyya sai addu'a momy hankalina ya tashi sosai bana so naga tashin hankalin safiyya please rukayya ki lallasheta kar kanta yayi ciwo yana fada fuskarshi cike da damuwa. ta shigo dakin ta samen na hada kai da gwiwa ina kuka ta karaso da sauri ta dago kaina safiyya me haka? ta fada cikin rudewa cikin dashewar murya nace momy umman ' to ba imran yace zai kaiki ba kince bakya so me kuma za,a miki? cikin kuka nace momy bana iya barci kullum ina cikin kewar umma amma bana fatan na kara ganinta, momy ya zanyi? hmm safiyya wallahi kiji tsoron Allah mahaifiyarki kike cewa bakya fatan ki kara ganint kan wani banzan tunanin ki da bashi da amfani. na dago ido duk sun canza kala saboda kukan dana sha yanzu momy bakya tausayin halin da nake ciki, ya zanyi da rayuwata, momy banda jigon rayuwata, banda mahaifi dan Allah ki gayan momy ya zanyi da rayuwata gashi bana fatan na kara ganin umma duk wani bakin ciki da nake ciki itace SANADI, me yass tabi hanyar da Allah ya haramta ta haifeni ki gaya min ina zansa rayuwata? nasha gaya miki in har zaki daka ta zuciya wallahi zata kaiki ta baroki, na gaya miki baki da shaidar da zaki tabbatarwa kanki ke shegiya ce in kuma kina da ita ki gayamin, momy kakatace ta gayamin to kakarkice ta haifeki?? na girgiza kai meyass baki saurari ummanki ba ? momy in na tsaya zuciyata zata iya bugawa kinga babban kuskure da kikayi kinga safiyya mu tafi a baki da uba kin isa ki canzawa kanki kaddara?? na girgiza kai to tunda kinsan da hake me yasa kika kasa cinye jarrabawar da ubangiji yayi miki kina abu kamar ba musulma ba, ko me umma tayi miki baki da abinda zaki saka mata, safiyya kiyi hakuri ki barwa Allah komai zakiga komai yazo miki da sauki. to momy ya zanyi? wa zai aureni banida uba? baki da shaidar da zaki tabbatarwa kanki baki da uba ki bari mu koma kano kiji bayanin da umma zatayi miki in har baki gamsu ba sai ki dau matakin da zaki dauka. kaina naji ya sara nayi saurin dafe shi tare da kiran sunan Allah cikin sarkewar murya nace' momy kaina zai cire ki taimakamin ta maso kusa dani tare da cire hannuna daga kaina sannu kiyi hakuri bara na kama miki a hankali naji rage zafi, barci ya soma daukana ta mike ta tsiyayo ruwan rubutun da imran ya kawo mata, ta shafa a fuskanta sai lokacin ta tuna da katin wayar data siyo ta dago tare da sawa daman abbanta zata kira taji yaje gida kira daya tayi aka daga hello abba' muryar hajiya taji bayan sun gaisa tace hajiya ina abba? kanta bata amsa taji ana cewa ya jikin Alhaji usman din "hajiya abbane bashi da lafiya? waye ya gaya miki? hajiya yanzu naji ance miki ya mai jiki kigayan me yasamu abba? ganin ta daga hankalinta tace karki rada hankalinki ranar daya je wajenku hanyar dawowa shida direbansa sukayi hatsari amma basu ji wani ciwo ba yanzu ma dan yana barci ne da saina bashi ku gaisa. cikin kuka tace hajiya ya za ayi ace sunyi hatsari baiji ciwo ba? gobe zanzo naga jikin abba haba rukayya na gaya miki baiji ciwo ba kiyi zamanki. Allah hajiya sainazo tana fadar haka ta katse wayar kukantane ya tasheni momy lafiya kike kuka? ta juyo wajena sadiyy abba sunyi hatsari wani irin zabura nan take na mance da ciwon kaina na hau kuka mundi rabin awa muna kuka babu mai bawa wani hakuri muna jin wayoyinmu suna kara bamu ko kallesu ba. sadiya ta shigo da gudunta tana sariya ganin halin da muke ciki yasa tayi saurin tsayawa sisters lafiya kuke kuka? cikin sanyi jiki ta karaso gaban momy aunty rukayya lafiya kuke kuka keda kike babba a cikinmu mune zamuyi haka kiyi hakuri dan Allah kiyi shiru kun dagan hankali dakyar ta iya bude baki tace sadiya abba nane yayi hatsari what? ta durta tare da mikewa daga tsugunen da tayi aunty rukayya yanzu yana ina? yana kano kuyi hakuri momy gobe saimu tafi muga jikin nasa, tafi minti biyar tana lallashinmu sannan mukayi shiru. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/8, 8:01 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣2⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com waya tayi kara a fusace na daga mallsm ka rabu dani ina fadar hama na katse, naci gaba da kukana sadiya ta mike bari na gawaya farida bayan fitar ta momy ta kalleni ki bar kuka dazu kika gama kukan ciwon kai, cikin dasj hewar murya nace momy kizo mu tafi yau ta girgiza kai yamma tayi ki bari gobe mu tadi shigowar sadiya ce ta katse maganar aunty ruky kizo inji imran" momy tace ki goge fuskarki muje koh. yana tsaye jikin motarsa sanye da bakar jallabiya kanshi babu hula muka karasa cikin rudewa ya tare mu rukayya yaushe abban yayi haysari? cikin saekewar murya tace wallahi imran ban sani ba tun ranan daya tafi bamu kara waya ba sai yau na kira wayarshi naji hajiya ta daga shine take gayamin ta karasa maganan cikin kuka. kiyi hakuri ya dago fuska cikin damuwa kuyi hakuri kukan bashi da amfani gobe sai muje a ga jikin nasa yanzu bari naje airport nayi mana bukin momy tace na gode imran bari na dauko kudi muje ta juyo tana kallon sadiya kan tayi magana imran yace 'wane kudi zaki dauko rukayya gani kawai ku shiga mota muje ita dayan yar uwanku ba zata bane? duk na duba ban ganta ba muje kawai, har mukaje muka dawo ina kuka fakin daya yi yasa na dago kaina duk sun fita saini daya ina kokarin fita naji muryarsa ya kira sunana cikin kasalalliyar murya safiyya!! na dago kai ina kallonsa kiyi hakuri ki bar kukan nan karki jawa kanki wani ciwon don Allah kinfi awa kina kuka kiyi hakuri kinga gobe zamuje ki ganshi, hankali na tashi in naga kanwata cikin damuwa bare kuma naga tana kuka sai naji kamar zan mutu kiyi hakuri kanwata ki bar kukan nan yana taban zuciya. ya jima yana lallashina sannan ya samu nayi shiru na zaro kafata zan fita naji muryarsa safiyya ki min alkawarin ba zaki kara kukan nan ba , na daga masa kai haba yar kanwata kimun magana naji dadi muryata a dashe nace zan tafi na kwanta. yanzu zakiyi barci? kaina ciwo yake kinga gobe in munje kuka ya kare kiga Abba da umma nayi saurin dago kai bana son kana kiran ummata kana sa zuciyata tana bugawa ka kiyaye ina fadar haka na fita daga motar. farida na hanga tana ganin na fito tayi saurin shigewa na karasa dakin na jiyo masifar farida. har na karasa taba fada ko kallonta ban ba na karasa kan katifa na kwanta bayan ta fita na juyo ina kallon sadiya me kukayi wa farida take fada? rabu da farida rashin mutunci takeji dan Allah ba a gabanku na fita nemanta na gaya mata abban ruky yayi hatsari ba har zuwan imran ban ganta ba duk cikin makarantan nan na duba ban ganta shine tazo tana fada rashin mutunci take ji wallahi dan bana biye mata da sai munyi fada. sadiya ta mike bari naje daki na dauko kayana danni wallahi ba zan kwana a dakin ba, nasan yanzu kwana zatayi tana mita. washe gari karfe takwas mun gama shiri imran kawai muke jira momy tace wai yau bara muyi break bane? watace tayi kara sadiya ta mikon na daga kanwata an tashi lafiya na amsa da lafiya klau da fatan kun shirya tun dazun muka shirya kai muje jira okey ku fito mu tafi najuyo ina kallon sadiya yazo. yana zaune a gaban mota ya zuro fuskarsa har muka karaso idonsa yana kanmu fuskarsa dauke da murmushi da suka dada masa kyau hada da kwarjini aunty an tashi lafiya? gani mukayi an bude murfin motar wata kyakkyawar budurwa ta fito fuskarta dauke da murmushi sannun ku ta furta tana kallon imran. tunda muka shiga mota take hira dan naji kaunar yarinyar a raina. sai dataga jirginmu ya tashi sannan taja motar ta tafi. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/10, 8:12 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com karfe sha biyu mua sauka a kano momy ta kunna wayarta zata yi kira ya juyo rukayya wa zaki kira? zan kira hajiyane ta turo a daukemu tun kan mu taho nayi way gidan mamam miji...kanya karass wayarsa tayi kara ya zaro ya daga bayan ya gama magana kuzo mu karasa ga motar can mijin mama nane. yana maganar yana nunam mana wata farar honda. mufa asibiti zamu fara zuwa momy ki kira ki tambayi wani asibiti ne ku bari muje gida in mun huta in yaso sai mu tafi. sadiya tacs gaskiya mu fara zuwa can asibitin koya kika gani aunty ruky, ni dai a ganina mu fara zuwa mu hadu tunda dai munzo kano din zuwa can ba zai bada wuya ba. muka karasa wajen motar dureban motan ya fito da sauri ya bude mana sannunku da zuwa gaba imran ya shiga mu kuma muka shiga baya wayar momy tayi kara hello hajiya nazo kano a wani asibiti kuke to shikenan wai suna nassarawa yayi saurin juyowa muma nassarawar zamu kunga babu nisa. har muka karasa babu wanda ya kara magana muna yin parking yara suka fito da saurinsu su hudu oyoyo yaya ya bude mota ya fita yana dariya hi babies ina momy? mai wayo daga cikin su tace taje aiki to ina ayshata? tana ciki wai fushi take bakazo da wuri ba. aunty ku fiti mu shiga suna gaba muna bayansu yaran sai surutu suke masa tana zaune ta rufe idonta ya karasa gabanta yana dariya am sorry lovely sister nasan nayi laifi cikin shagwaba tace bazan bude idona ba sai ka goyeni lala sister kinyi girma yanxu bakya ganin inda kika koma ai sai ki karyani ta kara rintse murya Allah bazan hakura ba saika goye ni ko na kira abban salima nace kazo kana dukana karki min sharri hau na goyeki tayi saurin dane bayansa tana dariya ya mike yana zagaya falon to bude idonki, tana bude kamar a mafarki taga yan mata a zaune suna murmushi wata irin wuntsulowa tayi daga bayansa yaran suka hau dariya. Allah yaya ba zan yarda ba sai na gayawa momy shine baka gayamin kuna tare da baki ba sannunku da zuwa momy tace yauwa yar gatan imran kinsha goyo kai aunty Allah naji kunya bari na kawo muku ruwa ta mike tana kiran lami. cikin mintina biyu suka cika gabanmu da kayan marmari har kasa suda yaran suka tsunguna suna gaushemu ta juyo wajensa. yaya baka gaya min sunan su ba yana murmushi yace ki gaya musu sunanki dana kannanki suma su gaya miki nasu. ta juyo sunana aysha ta nuna wata yarinya wannan kuma salima ga salim toh ni sunana safiyya wannan kuma sadiya sai kuma aunty mu rukayya. lah yaya kusan irin muryarku daya . saida mukayi sallah muka tafi har wannan lokacin mamansu bata dawo ba muna gidan ta bugo waya tayi mana sannu da zuwa. babu wani nisa tsakanin gidan da asibiti muna shiga momy takira hajiya tana ganinmu ta hau murna na gaya muku ba wani ciwo yaji ba kun bi kun daga hankalinku. sadiya tace hajiya dole mu daga hankalinmu abba shi kadai yake zuwa mana yayi hatsari mu kasa zuwa ta juya tana kallon imran yayi saurin zubewa yana gaisheta, momy tace hajiya surinkine saurayin safiyy ne sunansa imran shi ya biya mana mukazo hajiya karya take saurayintane tana murmushi tace an gode, hajiya ba komai . tana gaba muka shiga dakin tare da yin sallama su biyune a dakin yana zaune a kan gado ba wani ciwo yaji ba illa hannunsa daya da aka dora. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/10, 9:26 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com sannu abba ina maganar ina hawaye yayi saurin rike hannuna meye abin kuka safiyya kinga naji sauki, su momy suka karaso su da imran da sadiya suka gaishe shi, momy ta tashi da sauri ta karasa wajen daya mutumin da yake zaune kawu ya jiki maganar datayine ya sa ya dago idonsa muna hada ido naji zuciyata ta buga nayi saurin sauke idona kasa na tsuguna ina gaisheki hannu yasa ya dagonu sannu yata kunzo lafiya? cikin sanyin murya nace lafiya klau abba ya mai jiki? momy ta jawo kujera muka zauna. babu abinda yazo a raina sai tunanin ima nima ina da uba wata irin soyayya ce baran nuna masa ba amma umma tabi ta hanyar da ubangiji ya haramta ta sameni ban san lokacin da hawaye ya dinga zubomin ba, hajiya ta matso kusa dani meya saki kuka safiyya? tana fadar haka kamar ta turani na hau kuka abba yace safiyya meye ya saki kuka ko baki da lafiyane? na girgiza kai sadiya tace wai ke meyasa kike haka kin fi son kullum ki daga mana hankali. shi ko imran yama kasa motsi ya mike jikinsa a sanyaye ya fita dan zuciyarsa zatq iya bugawa in har ya ci gaba da sauraron kukanta waje yayi ya samu waje ya zauna ya rafka tagumi ya fada duniyar tunani meyeke damun rayuwar safiyya?? ita ina nata iyayen? me yasa bata so ayi mata maganar ummanta? meye dangantakarsu da rukayya da sadiy meyasa kullum cikin damuwa da kuka take? tambayoyin da ya kasa bawa kansa amsa kenan koma mene in Allah ya yarda safiyya sain zama SANADIN sanyaki cikin farin ciki nazama SANADIN kawai miki da duk wata damuwarki, nayi SANADIN gyara tsakaninki da mahaifarki, koma meye sai na zama SANADIN gyaruwar rayuwarki ina sonki safiyya son tsakani da Allah tun kan na ganki na kamu da sonki zan soki ko a wani haki kike, ko wacece ke zan aureki na zauna daje insha Allahu safiyya sai mafarkina ya tabbata a kan.... maganar rukayya ce ta katse masa tunani ya dago imran ya ka fito ka zauna anan? rukayya bazan iya zama ina sauraron sautin kukan safiyya ba please rukayya ki gayan meye yake damun rayuwar safiyya, na fuskanci rayuwar safiyya tana tattare da matsla kuma momy nasan kinasane da matsalar kuma kinsan abinda yake damunta ki gayamin dan Allah waje ta samu ta zauna gaskiya imran bazan iya gaya maka damuwar safiyya ba damuwarta ta bani amana kaga in har na gaya maka naci amana kayi hakuri imran bazan iya gaya maka ba amma karka fidda rai ita safiyyar zata gaya maka damuwarta da kanta na fuskanxu imran kana da sa,a cikin mamaki yace rukayya saboda me kikace haka? imran rayuwar safiyya babu abinda ta tsana sama da tsaya tana magana namiji amma gashi rana tsaka kazo ka karya wannan kiyayyarar har ku tsaya kuna hira wani abin ita daya in tana kwance zakaga tana murmushi in na tambayeta dalili sai tace in ta tuna kiranta da kake kanwarka shine yake bata dariy na tabbata gaba kadan zaku shaku da safiyya zata iya gaya maka damuwarta. to yanzu ta daina kuka? tun yaushe tayi shiru yanzu haka ma dariya take kawauna yana bata labari ya saki murmushi momy bara na shiga muyi sallama da abba naje gidan mamana anjima zan dawo tare suka shigo yana fita yaya isha ya shigo (yayan rukayyane) ga dukkan alamu bashi wasa yaje gaban mahaifinsa sun jima suna hira sannan yatafi karfe takwas imran ya dawo hannunsa rike da babban flask bayansa aysha tare da mahaifiyarta lokacin da suka shigo muna waje muna sallah sun jima sannan ta fito aysha tace yay inaso aunty rukayya ya hango sadiya yayi saurin karasaws wajent har kasa ta tsugunna ta gaishesu yace sadiya ina su rukayya? imran yanzu suka fita su da yaya salim aysha tace naso momy kiga me kama dani murmushi tayi tace wata rana zan ganta. basufi minti goma da tafiya ba muka dawo hajiya ta fito kuzo mu tafi tunda ga me kwannan yazo hajiya bari nayi wa abba sallama na shiga tare da yin sallama ya amsa fuskarshi cike da murmushi har kun dawo safiyya? na daga masa kai. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/14, 7:24 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣5⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Na daga masa kai har na juyo zan fita abba kawun ya tafine? kwata kwata ban san lokacin da bakina yayi tambayar ba yaje gida tundazun yake jiran dawowarku amma yace gobe kanku tafi zaizo kuyi sallama nace Allah ya kaimu muma zamu tafi yace to saoda safe zakuje can gidan kune? na girgiza masa kai ban san lokacin da hawaye ya taho min ba nayi saurin fita ya tsaya yama kallon ikon Allah meye yake damun safiyya ya tambayi kansa ko rukayyace take bata mata rai Allah ya kaimu gobe zan tambayeta. ina fitowa na tarar da imran ya dawo nayi saurin goge hawayen fuskata imran yace hajiy ku taho mu tafi, tunda muka shiga mota babu wanda yayiwa wani magana har muka karasa bayan sun fita naji kiran imran sai da hajiya tasa baki sannan na fita yana jingine jikin motar da mukazo sanye yake da kananan kaya wanda sukayi matukar dacewa da kalarsa kanwaya ba muyi sallama ba, to dole ne sai munyi sallama na fada cikim fushi Allah ya bawa kanwata hakuri kana cin darajar alkawarin da nayi maka amma naga kana son wuce gona da iri kana neman takurawa rayuwata tun farko na gaya maka bazan taba sonka ba babu soyayy a tsarin rayuwata tun kan lokacinka ya kure ka kama gabanka kaje ka nemi me sonka bari na fada maka wani magana wallahi imran bazan taba sonka ba daga yau ma mun daina gaisawa na juya zan shiga gida naji muryarsa kiyi hakuri safiyya ban juyo ba ya karasa gabana ya tsunguna dan Allah safiyya kiyi hakuri ki bari muci gaba da gaisawa a maysayinki na kanwata shikenan zamu cigaba da gaisawaa amma wallahi ka kara takuramin har abada ba zamu kara gaisawa ba ina fadar haka na shige ciki. washe gari karfe sha biyu muka tafi kawun momy da salim ne suka kaimu airport, saida sukaga tashin jirginmu sannan suka tafi. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. 💘WAYE SANADI?💘 6⃣6⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com **** **** **** **** **** cikin ikon Allah yau kwanan umma uku da haihuwa. ta sauka lafiya Allah yayi mata kyautar kyawawan yayanta guda biyu duk maza kullum alhaji nasir yana gidan farin ciki har ya rasa inda zaisa kansa har mahaifiyarsa sai da khalifa ya kawo ta ga yara tayi murna sosai. da yake haihuwar gida tayi. Dr khadija da aysha zuka zo wa umma barka, lokacin alhaji nasir yana gidan yana ganin aysha ya dago kai tare da saurin mikewa yana fadin safiyya! safiyya! babah tayi saurin fitowa daga kicin tana kallon ikon Allah ya kara cewa safiyya! aysha tace ba ita bace ni sunana ayaha ta tsunguna tana gaishehi cikin mamaki uace sunanki aysha kuma? khadija tace wajen rukayya mukazo babah tace ku shiga tana ciki suna shiga umma ta hau murmushi sannunku da zuwa aysha har dake kan tayi magana babah ta shigo rakiya kinga wani ikon Allah yanzu don Allah me ya raba yarinyar nan da safiyya wallahi sai da tayi murmushi naga bata da hushirya sai kuma safiyya dana lura tafita tsayai umma tace itace likutan dana gaya miki ina zuwa awo wajenta, suka kara gaisawa da babah ta fita fita dan kawo musu ruwa aysha tace umma karmarku day da wannan ta nun daya daga cikin yaran wanda yake hannun mamanta ta dago kai tana murmushi ta hau dariya mama don Allah bani wayarki na kira yaya imran na gaya masa ta zaro wayar ta mika mata kyaji da shirmemki . yini sukayi a gidan aysha ta bawa umma imran suka gaisa yayi mata barka, da daddare alhaji nasir yazo bayan sun gaisa sa babah ya shigo dakin tare da sallama na amsa kaina yana kasa ina bawa hyssaini nono ya zauna tare da daukar hassan rukayya ya kira sunana a ciki na amsa don kwata-kwata bana kaunar yayi min magana sai wani rawan kai yake akan yayansa ni yayi SANADIN rabani da tawa yar. maganarshine ta katse tunanin da nake nayi niyyar canzawa su hassan suna ki gayan wane suka kike so ni dai na sawa hussaini "salisu" sunan ubangidana ke kuma ki gayan wane suna kike so a sawa hassan a sa masa sunan baffana "yusuf" ya mikon manyan ledoji guda bity ga kayan nan nasa aka dinko miki yana maganar yana mikewa. ana gobe suna da daddare dr khadija ta kawo aysha har ma da salima duk zasu kwana da kuma kayan barkansu umma tayi murna sosai zuwan aysha ko ba komai in suna tare da aysha tana debe mata kewar safiyya, wanda bata wuce minti biyar ba tare da tunaninta ba. wayar aysha ce tayi kara tayi saurin dagawa hello yaya imran kana lafiya? lafiya klau yar uwa. Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Friday 4 November 2016

Waye Sanadi?? 53--57


[10/24, 8:15 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Cikin sanyin murya nace na gode kuma insha Alllah zanyi amfani da shawaranki. Ta juyo wajen yarinyar da ta kira da aysha suna hada ido tayi saurin fita. Bayan ta gama dubani na dawo kujera na zauna tana murmushi tace kinga muna ta kallonii koh? Ina zaune aysha tace taga mai kama da dady kamar kanwarsa ni kaina dana ganki nayi mamaki sosai ina son yayana sosai dan haka da naga kuna kama kema sai naji ina sonki a raina" nace haka lamarin Allah yake sai kaga baka san mutum ba amma in wasu suka ganka sai suce kana kama da wani, wanda suke fadan baka sansuba ba ka kuma taba ganinsa ba ta zaro wani dan kati ta mikamin ga wannan duk ran daki kazo ki dinga nema na ba tare da kin bi dogon layi ba na karba ina godiya mun jima tana ban shawarwari. Ina fitowa na samu a daidaita sahu na shiga har kofan gida ya kaini babah tana zaune tana kada abu na shigo ta hau raba ido baba me kike kallo ina alhajin da kuka tafi tare ai tunda ya kaini ya taho na karasa na zauna a kusa da ita ta mike bara na miko miki abinci. Bayan na gama na juyo wajen baba nace nayiwa alhaji magana kan ya rage zuwa kinga babu aure a tsakaninmu bai kamata ya dinga shigemin ba har ma ya dinga kaini unguwa maganar mutane bata da dadi in haka nayi masa magana ga mallam nan shine wakilina tunda daman a wajensa ya aureni duk wani hakkina ya dinga bashi. Babah tayi saurin katse ni kice kin koreshi ya barki da wahala kinyi daidai kin kyauta bab...." kinga yi min shiru har kinda da maganar da zaki gayamin wayasan abinda ki kayiwa alhaji mukhtar ya barki da yarki gashi yanzu ta gudi ta barki shine wannan ma kike so ki cuci abinda zaki haifa, kina ganin nan gaba haka zaki zama mana tashin hankali ina hawaye na dago babu auren na kuma ga kullum yana gidannan zai iya zama matsala ayi mama mummunar zato Sannu wadda bata so ayi mata sharri ke gak...." kan ta karasa mallam ya shigo naji duk maganar da kuke rakiya tafiki gaskiya tasan meye rayuwa kuma yanzu alhaji nasir ya bar wajena mun gama magana don haka ban san na kara jin kina wata magana mara amfani ya juyo wajena ke kuma maganar da zsn gaya miki karki dora SANADIN batar safiyya a wuyan alhaji nasir ki dora SANADIN batan ta a wuyan magajiya, to inda bata gaya mata wannan mummunar zancen ba babu abinda zaisa tabar gabanki kuma kici gaba da kai kukanki wajen ubangiji har Allah ya juyo da hankalinta ta dawo wajenki. Ya miko min kudi munyi da alhaji nasir duk wata zai dinga kawo kudin abincinki gashi kuma ya bayar wannan ko bakida lafiya za'a dauka a sai magani sannan kuma da zuwa awo, don haka dukk wata zai dinga zuwa ya kawo. Ni dai bance komai ba nasa hannu na karba dan basune a gabana ba tunanin yata ya cikemin zuciya. Ina kika shiga safiyya ki taimaka ki dawo ina maganar cikin zuciyata ashe har ta fito fili maganar babah naji daga baya tace: yanzu ko kunyata bakya ji kike fadar haka? Nayi saurin juyowa babah ba magabar da nayi ta hau salati yanzu bakin san kina maganar safiyya ba? To Allah ya kyauta miki wallahi in baki rage tunaniba, sai ciwon zuciya ya kamaji tana fadar haka ta shiga cikin daki. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [10/25, 9:16 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com www.abbagana.blogmr.com **** **** **** **** *** waike malama ba kya jin wayarki na karane? na dago fuskata a hade nace ina jinta toh zaki daga bane? momy bana raayin dagawa in kinsan bazaki daga ba meyasa kika bada lambarki? wa nake bawa numberta? wannan dinnan ne da yake kirana wai bashi da sunane? ta fada tana haranta wanda yazo ranan oh muhammad na daga kai, mikomin wayar banyi musu ba na miki mata; Assalamu alaikum, muhammad kana lafiya? lafiya klau aunty momy safiyya bata nan ne? muhammad tana toilet ne ya akayi? aunty momy daman ce mata zanyi yau zanzo mu gaisa ta kuma ki dagawa" kayi hakuri kasan babyn tawa sai na kaita an duba kwakwalwarta ina tunani akwai matsala me yasa kikace haka aunty momy? to muhammad inna gaya mata magana bata yarda ga dan banzan taurin kai, dan haka dole na kaita a dubata yana dariya yace shikenan innazo sai muyi maganar inta fito ki mikamin gaisuwata okey muhammad muna jiranka ka gaida mutanen gida tana gama wayar ta juyo tana kallona banda ruwan hawaye babu abinda yake bin fuskat kan tayi magana na katset momy ni kike cewa banda hankali zaki kaini a dubani koh? kai tsaye taban amsa to kina da hankalinne? na girgiza mata kai na mike zan fita jinayi kamar zan fadi nakai hannuna na dafe kaina da sakin wata razannaniyar kara wannanda harnima ya razanani🙂. A hankali na dinga kokarin bude idona naji na kasa hannu na kai fuska naji wani sassanyar murya ta doki zuciyata sannu safiyy. kin tashi abin kamar a mafarki naji muryan ba shiri nayi saurin bude idona ina kallonsa tare da juyaw ina kallon inda nakw kwance ban wahalar da kwakwalwata ba wajen gane inda nake ba wata asibiti to waye ya kaw....... maganarshi ce ta dawo dani daga tunani sannu safiyya bara na kirawo likita ya dubaki momy ce ta shigo najuyo wajen tare da fadin me ya kawoni asibiti, bakya jin dadine shine na kira muhammad ya kawo mu asibiti inajin haka nayi saurin mikewa ina kokarin saukowa daga gadon ta karaso da sauri"meye haka bakya ganin drip ne a hannunki. na juya ina kallon hannu na kai zan cire naji an rike hannun "karki cire safiyya ki bari ya kare." na zabga masa harara bazan bari ya kare ba meye ruwanka da rayuwata." 🅰bbagana hausa novels @ faceebook. [10/25, 9:41 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣5⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com na juyo wajen momy nace ce miki nayi banda lafiya da zaki dauko mara hankali ku kawo asibiti ta rike hannuna tana murmushi am sorry nasan nayi laifi a min afuwa. na juyo wajensa kasake min hannu ko nidin ba yar isaka bace irinka nika dakain zan bada shaidar haka amma kiyi hakuri ki bar drip din ya kare kyaji karfin jikinki, dan Allah ki taimaka safiyy yana maganar yana girgiza kai cikin tsawa nace to hannunka ne da ba zaka sakar min ba? to kimin alkawarin bazaki cire ba ki taimaka kanwata. waye kanwartaka? kiyi hakuri don Allah kibar drip din nan momy tace muhammad sakar mata hannun bara na kira abba shi yayi mata magana. ta zaro wayarta tare da kiransa kira daya a dauka hello Abba bayan sun gaisa take gaya masa tana gama gaya masa ta sa wayar a kunnen naji muryansa safiyya kiyi hakuri ki bari ya kare. abba ce min tayi fah bani da hankali kinga ki rabu da ita ranar monday zanzo amma ki bari ruwan ya rake saiku tafi kinji yat ina kuka nace to abb yayi saurin cewa bana son kukan nan kiyi shiru kar kanki yayi ciwo ina jin ya katse na kaudar da kaina na kwanta momt tace har kun gama banko tankataba na mayar da idona na rufe baby bara naje na samo miki abinci. ya karaso ya tsugunna kiyi hakuri safiyya me nayi miki kike min haka? ki tausayamin safiyya duk wanda yake nuna maka kulawa bai kamata ya zama abin gudunka ba dan Allah ki tausayamin na yarda bakya sona amma ki amince na zama dan uwanki ki ban matsayin yayanki koh kaninki na miki alkawarin maganar soyayya ba zata taba shiga tsakaninmu ba har abada, dan Allah ki tausayamin duk maganar da yake idona suna rufe sai da naji muryarsa tana rawa yasa na bude idona cikin dabara ba tare da ya gane ba, ji nayi kirjina yana bugawa sakamakon ganin ruwan hawaye a kwance cikin kyakkyawan fuskarsa. Dan Allah kiyi magana safiyya ko zanji dadi ki gayamin kin amince mu dinga gaisawa. bansan lokacin da bakina ya furta na amince, yaji maganar kamar cikin barci yayi sauri dago kai yana murmushi safiyya na gode, na gode ya mike da sauri bara na kira likita. momy ta shigo tare dasu sadiya. farida tace yanzu wannan ce mara lafiya? ruky kika wani daga hankalinki haka, na juyo ina haranta sadiya tace sannunki kam nasan ciwon love ne kawai tana kunyar gaya mana amma ba komaii ni zan shigar dake, ban ko mata magana ba. sallama yayi tare da shigowa shi da wata nurse, ta karaso wajenta bayan ta gama ta fita sadiya ta juyo wajen muhammad tana dariya yau daiga muhammad angon safiyya rike baki yayi yana dariya sadiya bar fadan haka kar kisa ta janye amincewa da mukayi yanzu yana maganar yana kallon agogo dake jingene a sama. karfe takwas ruwa ya kare na azakzali momy taje takirasu a ciremin.... 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [10/31, 8:01 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣6⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com bayan ta gama waya ta juyo waike malama ba zaki bari ya kare ba kin..... kan ta karasa nasa hannuna na cire da kaina, na shiga uku me yasa kika cire na mike tsaye niba ce miki nayi banda lafiya ba kuka kawo ni nan, wai ya akayi kuka kawoni ina barci? abin ya baya momy mamaki ta tabbatar abinda zuciyarta take gaya mata tabbas saffiya tana da matsalar aljannu ina mafita ta tambayi kanta kan ta samu mafita maganarta ne ta katse mata tunani. momy ya akayi kika daukoni ina barci? toma ya akayi nayi barci kinga bara na kira dr a dubaki tana fita muhammad ya shiga safiyya har ya kare na daga masa kai ina aunty momy ya tambayeta taje kiran likita okey bari nayi sallah nazo mu tafi. momy ce ta fito bako sallam ta juyo tana kallon muhammad tace gaskiya muhammad ina ganin ciwon safiyya bana zuwa asibiti bane cikin mamaki ya juyo rukayya saboda me kikace haka? nan take ta gaya masa maganganun da sukayi da safiyya ya girgiza kai to momy wannan wani irin ciwone? kan ta bashi amsa ya cigab sa cewa ina ganin tan da mutanen boye, nima haka nake tunani yaceto ina mafita tace kaine zaka samar mana mafita mu din wa muka sani a garin nan? yadi minti uku baiyi magana ba can yaja dogon numfashi shikenan rukayya zanyi duk wani kokari don neman lafiyar safiyya.shikenan muhammad na gode rukayya me abin godiya? muhammad sole na maka godiya yana dari yace aunty momy imran shine sunana na gaskiya ina amfani da muhammad ne dan kada safiyya ta ganeni tace ban gane ba au momy baki da labarin aljani imran da yake kiran safiyya lokacin da kuke makaranta, ta rike baki tana dariya kaine imran aljanin wayar safiyya? kai ya daga amma kaban mamaki kaine mutumin da ya haukata baby gaskiya saina gaya mata anty momy ki rufan asiri karkija a janye alkawarin da aka min. wani alkawarine daban sani ba? na gaya mata babu maganar soyayya tsakaninmu da ita za dai mu dinga gaisawa hmm lallai imran har yanzu baka san wacce safiyya ba bara naje daki kada ayi minu fushi okey aunty momy gobe zanzo hudu na yamma amma kan sannan zanje wajen wajen malami nayi masa bayani. ina sallah ta shigo toilet ta zarce ta dauro alwala ta fito bayan ta idar ta juyo shine kika wucw bako salkama? to momy dole ne sai nayi sallama? babu sole amma kin masa alkawarin zaki dinga sauraransa ku dinga gaisawa kuma kinsan muhimmancin alkawari to inya dawo wata rana zan masa sallama momy yunwa bakeji toh waye zai fita a wannan darwn ga take away dinda imram ya siyamana nima shi zanci na kwanta. sai karfe uku na fito daga dakinmu kai tsaye na wuce cikin makaranta sanye nake da doguwar riga baka na nade fuskat da dan mayafina babu komai a hannuna sai book guda daya muryar momy naji daga bayana tace sai yanzu akaga damar zuwa class din? kuka kama hanya koh jirana kunkiyi, keh dakika tsaya shiritanki shine zamu jiraki? kai momy kefa aunty nace kuma abba yace ki dinga lallabani'zan lallabaki ko dan darajar yaya imran kai momy har yafi abba matsayi? ba haka nake nufi ba kowa da matsayinsa. karfe biyar wayata ta hau kara ina dubawa labar na wayar imran ne na ajje can wata zuciyar ta tunamin alkawarin da nayi masa nayi saurin daukan wayar 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [10/31, 8:36 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣7⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 09039016969 www.MuhdAbbagana.blogspot.com safiyya kina lafiya? can kasan makokorona na amsa da lafiya kuna cikin makaranta ne? na girgiza kai kamar yana ganina baki ban amsa ba ina tambayarki, bana girgiza kaiba to ai safiyya kin san ba ganinki nake ba ballantana na ga kin girgiza kai kiyi hakuri ki ban amsa ni ina hostel momy kuma tana cikin makarant su dasu farida shi kenan amsar da kake so na baka. shi kenan kanwata nima gaya miki zanyi nazo mu gaisa ina jiranki cikin makaranya da fatan kina sane da alkawarinmu na zuwa muna gaisawa yana fadar haka ya katse nabi wayar da kallo. wannan mutumin zai dinga fakewa da nayi masa alkawari ya takurawa rayuwata gaskiya sai na taka masa birki, hijabi nasa na na fito yana zaune cikin motarsa tunda na tawo ya kasa dauke idonsa akaina babu wata kwalliy a fuskata amma hakan ta masa wani irin kyau mai makantar da zuciya gabaki daya, yana yin komai na yana burgeshi ya Allah ka mallakan safiyya ya furta a hankali tare da lumshe ido ta karaso fuskanta a hade. jin alamun an tsaya a ganansa yayi saurin bude ido yan murmushi muka hada ido nayi saurin dauke idona"safiyya ki shigo mana? nan ma ya isa sauri nake ina aiki a daki fitowa yayi daga cikin motar ya dawo kusa dani sanye yake da kananun kaya wanda suka dace da kallar fatar jikinsa, tunda bazaki shigo ba ni na fito sai na tsaya kusa da kanwata. da sauri nace wacece kanwar taka?? safiyya man koba kanwata bace? gaskiya ni ba kanwarka bace saboda me kika ce ha? ni daya ummana ta haifa banda yaya bare kanne to aii ummance ta haifen kinga na zama yayanki ko babu kara, kan na bashi amsa wayarsa tayi kara yayi saurin zarota daga aljihunsa hello khadija ya akayi? sun jima suna hira sannan sukayi sallama ya juyo wajena yace wata kanwatace yae rigima wai na dawo gida bata gaji da ganina ba. nace to ka koma mana nima na gaya maka aiki nake, in gaisuwane kazo yi mun gaisa bari na tafi ina san ganin momy zan zauna na jirata ki tsaya muyi dan hira kafin tazo. nafa gayamak aiki nake ka rabu dani in kanaso muci gaba da gaisawa to duk abinda na gaya maka karkace zaka gyaran koka takuramin ina fadar haka najuya na tafi. yana tsaye cikin mamaki yaji sallamar momy imran yanzu kazo? yayi saurin juyowa yana kallonta aunty momy na juma ke nake jira harm safiyya tazo mun gaisa, aunty momy naje wajen mallami nayi masa bayani to shine yace nazo da ita.... momy ta dago kai da sauri hmm imran kasan inzamu to safiyya bazata taba yarda muje ba "ai aunty momy baki tsaya na gama gaya miki ba, yana gayan haka nace mallam baza ta taba zuwa ba. wani rubutu ne ya bani nakai mata in ya kare sai na dawo 'imran bansan wani irin godiya zan maka ba nasan kanason safiyya tsakani da Allah ina maka fatan Allah ya baka safiyya amin aunty kasan wani abu imran? ya girgiza kai tunanin yadda zann mata ta dinga shan rubutun nake nima nayi tunanin haka dan na hango taurin kan safiyy za a sha wahala kan ta amince. momy ta hau dariya karka samu damuwa imran yanzu zanwa abba waya nayi masa bayani. kai naji dadi kin iya kawo shawara bari naje gidan kanwarmu ta damu na dawo kisan nima dan gatane kamar safiyya na au har ta zama taka? momy ba kekika bani ita ba. ina kwance ta shigo hannunt dauke da jakar rubutu kan nayi mata magana tace yanzu muka gawa waya da abba, amma koki kawo da gudu mugaisa ke nima ba hira mukayi ba turo abonkisa yayi ya kawo mana rubutu. cikin mamaki nace rubutu kuma? ta daga kanta tare da nunamin jakar hannunta. to ce mai kikayi bamu da lafiya? kewa yayi na tsari ne saboda mutane kuma bamu san zuciyarsu ba na hau dariy gaskiya abba yana sonmu da yawa, gara ana taimakawa da rubutu saboda mayu irinsu saifu da .....sai kuma nayi shiru ta dago kai ta harareni da kuma wa?? momy ba wani abu zance bafa. 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).