shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 15 November 2016

WAYE SANADI? 58--66


[11/1, 9:10 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com karya kike kinaso ki karasa da imran koh? lah momy ai shi baice yana sona ba, kawai gaisuwa kawai muke kinga shi ba maye bane. oho miki dai wallahi ki iya kanki, zan iya momy amma ba yanzu ba. sadiya ce ta shigo yanzu muka hadu da imran zai fita nace har an gama soyayyar Allah sadiya bakya ganewa waya gaya miki soyayya muke? ana gobe abba zaizo bayan mun gama waya na mike na shiga toilet bayan na shirya na juyo ina kallon momy nace"momy zanje unguwa tayi saurin dago kai ina kika sani da zaki unguwa? kai momy me kika daukeni ina tare da oniya tana nunamin gurare kuma yau nidaya zan fita nayiwa hajiya tsaraba na bana abba ya kai mata. **** **** **** **** **** ** Rakiya!! Rakiya!! ta shiga kwala mata kira tayi saurin fitowa tana daura dankwali 'gani babah' gani nayi lokacin zuwanki asibiti yayi baki fito ba kin ta sana'ar taki" yanzu nake shirin fitowa ina gyara kayanmu dana wanke ne dana gama zan tafi. bara naje nayi barka kanki gama, tana maganar tana yafa mayafi bayan fitarta baifi minti biyu ba naji sallama na amsa tare da fitowa ina karasawa mukayi ido hudu dashi nayi saurin juyawa zan koma naji muryarsa babah tana nanne? a ciki na bashi amsa na shige cikin kallon fuskarsa babu abinda ya karan sai bakin ciki ina shiga daki na zauna wani irin hawaye ya zubomin wannan auren ba karamin ya karamin ba face bakin ciki tunda sanadin sa na rabu da farin cikin zuciyata, wayyo Allah na safiyya ina kika shiga kika barni da tunanin ki a raina bazan taba farin ciki ba muddin bakya tare dani, a wani hali kike shin tana raye tsahon wata uku ban sata a idona ba nayi saurin kauda tunani tana raye tabbas jikina yana ban safiyya tana raye ki dawo gareni na miki bayanin da zaki gamsu wallahi safiyyata ba shegiya bace kizo na gaya miki gaskiyar waccece ke, kuka yaci karfinta tafi minti biyar tana kuka jin muryar babah a waje tan gaisawa yasa tayi saurin tashi ta fada ban daki, wanka tayi ta fito babah zan tafi ta zaro kudi ta mika mata ki biya ta bakin asibiti ki siyomin kayanmiya. tana fitowa bakin titita samu mota ta shiga ta zauna kusa da wata yarinya wayartane tayi kara tayi saurin dagawa hello aunty na dawo can kuma tace a,a tun jiya na dawo na baro su lafiya. ta kara cewa aunty zaman lagos da dadi karatu yazo gangara sai dai innazo zaki sha labarin karatun safiyya umma tayi saurin dago kai tana kallon yarinyar, ita kuma ta cire wayar da ke kunnenta tana dariya nan take umm ta shiga tunanin tata safiiyan. hajiya ba a nan zaki sauka ba? tayi saurin kai dubanta kofar asibiti ake ta zaro kudi ta mika masa ta shige cikin asibiti. tafiya take amma ba sosai take ganin gabanta ba, babu abinda yake ranta sai tunanin safiyya har ta kusa karasawa dakin taji muryan asha mama sannu da zuwa nayi saurin juyowa ina murmushi, aysha antashi lafiya? lafiya klau mama. ina maman taki tana gida cewa tayi nazo na tafi dake gidanmu yau ba zata samu zuwa aiki ba, nama dade da zuwa harna fito saina hangeki. banyi musu ba na bita muka tafi dan na riga na saba da ita kusan yanayinsu daya da nanata illa wannan bata da taurin kan nan gata kuma da hakuri sabanin nana. babu wsni nisa tsakaninsu da asibitin muna tafiya tana jana da hira har muka karaso gidansu, wani falo ta kaini bai kyan tsari mama ki zauna bara na kira momy ina zama ta kwalawa yar aikinsu kira lami ki kawo ruwa anyi baki tana fadar hak ta hau bens wanda mattatakalarsu take cikin falon da nake zaune. tana hawa wata budurwa ta shigo hannunta dauke da tire an dora lemun kwali da ruwan roba sai wani kofi mai kyau............ 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/2, 9:00 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 5⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com sannu da zuwa hajiya yauwa sannunki ta ajiye har ta juya ta dawo dan Allah hajiya na tambayeki abin ya ban mamaki amma na hadiye nace Allah yasa na sani. muryar a hanki kamar tana tsoro kar wani yaji abinda take san fada tace dan Allah kema irin mutanen nan ne da ake nunawa a talabijin naga kuna kama kum gashi kinsa hakori ance daman a garin ake sawa nace daman a wani gari ake ganinsu a talabijin? da sauri tace naji aunty aisha tana cewa makka abin ya ban dariya nace bi ba,a makka name ba na dai taba zuwa sau daya' ta hau dariya amma wallahi kuna kama babu abinda ya rabaku dasu keda alhajin kegos shima kamarku daya kan ta sake wata magana taji saukowa tayi saurin fita tana dariya. ta karaso fuskarta a cike da nishadi sannu da zuwa kina tare da lami tana miki shirme koh? bance komai ba illa murmushi muka gaisa kin ganni yau bana jin dadin jikina ba zan samu damar zuwa ba shine na tura aysha ta taho dake dan karkizo bana nan. nim de yau banzo da wuri ba, tace bari na shiga kitchen tunda ta tashi na fada tuniyar tunani har ta dawo ta hau kiran sunan. rukayya!! rukayya!! nayi saurin dago kaina kamar wadda ta tashi daga barci ta zauna kusa dani haba rukayya me kika rasa kikeso ki jawa kanki wata cutar, kullum kina cikin tunani ki tuna kina da ciki kullum in an auna miki jininki baya sauka sai kara hawa yake, ki cire tunanin komai a ranki. me yake damunki? duk wanda ya kalleki ba zai ga alamun damuwa a tare daka ba' tayi kasa kasa da murya wallahi rukayya in wata ta gaya miki halin da take ciki sai kinga ke a aljanna kike. na numfasa tare da goge fuskata likita matsalat ta zarce yanda kike zara lik....kan na karasa tayi saurin cewa sunana khadija dahie ta fadi hakan ne dan na daina gaya mata sunan danake kiranta dashi. murmushu nayi mata kawai sannan naci gaba da cewa Dan Allah in bazaki damuba ina so na miki wata tambaya tace Allah yasa na sani dan Allah aysha yarkice ta cikinki? karkiyi mamakin tambayan kokiji haushin amsar ki nake jira gaskiya aysha ba yata bace yar yayanace uwarmu daya ubanmu daya danayi aure na jima ban haihu ba dan haka ya barmin ita har kawo yanzu da nake haihuwa inada yaya hudu duk suna makarant to yanzu khadiya in aysha ta bata yaya zakiji a ranki? ta dafe kirji tare da zaro ido ai sai na kusa mutuwa Allah kada ma ya nunamin wannan ranar" khadiya yata ce ta bar gabana yau tsahon wata uku me yasa ban mutu ba? na tsaya ga yawaita tunani ta dago kai cikin tausayawa rukayya ya akayi tabar gabanki? kan wani dalili ne wanda ya zama sirrina khadiya ita daya na haifa sai wannan abinda yake cikina. gaskiya rukayya dole ki shiga cikin damuwa amma kiyi hakuri duk wsni tsanani yana tare da sauki, insha Allahu zata dawo gareki rukayya me yasa baku kai gidan radio ba kinga ba bata tayi ba ita ta tafi da kanta lokacin ya rage saura kwana daya ta tafi lagos karasa karatu au karatu take? tana karatu mana shekara uku tana zuwa jami,a to rukayya bakya tunanin koh tana can tana karasa karatun me zai hana kisa abbanta yaje can legos din ya dubo koh tana can, babanta ya mutu kuma wanda nake aure kan mu rab...." yanzu baki da aure? na daga mata kai yasa kawarta ta dubuta tunda sukaje take nemanta har wasu makarantu taje bata ganta ba nasan hakin safiyya tana da wani irin zuciya in dai ta fadi abu saita aikata nayi imani inda muka rabu tana cikin wannan halin zayyi wuya ta dawo gareni ko safiyya bata rantse ba indai tace ta bar abu to ko ta barshi har abada bare kuma ta rantse nariga nayi rashin safiyya babah da abba sun min SANADIN rabuwa da yata" bata san lokacin data furta haka ba cikin mamaki dr khadija tace suwaye? babah da Âbba 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/3, 8:43 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com nayi saurin dago kai dan kwata-kwata ban san na furta hakan ba khadija bari na tafi. a,a ki bari na gama abinci nayi zaton yini zaki yi. sai karfe uku na fito daga gidan khadija ina shiga na tadda babah tana shara ni magajiya, rakiya kin daga hankali baki taba dadewa haka ba nayi murmushi nace babah yau akwai mutane kuma malaman lafiyar bata zo da wuri ba shiya sa kikaga na dade na jawo kujera na zauna ban jima da zama ba jummai ta shigo harkin dawo rakiya? ehh hajiya na dawo. **** **** **** **** **** A hankali yake rukin motar cikin nishadi ya shigo cikin makarantar , kamar ance juyo bayanka ya hangi mata sanye da likaf tana nunawa wasu samari motarsa yana kokarin ya dawo baya wayarshi yayi kara ya duba cikin screen my Dady dan haka yayi saurin dagawa bayan ya gama wayar ya juyo yana kallon wajen da yaga an nuna motarsa amma babu kowa a wajen, kai kawai ya girgiza yayi gaba. yana karasowa ya tadda momy ta fito a,a aunty momy ina zuwa? bansani ba na gaya maka ka dinga kirana da rukayya in ba haka ba zamu samu damuwa yan dariya ya fito daga motarsa sanye yake da rantsatsiyar farar shadda ta kamfanin chetex kanshi babu hula sai lallausan bakin gashinsa da yasha gyara sajensa kwance luf a kyakkyawar fuskarsa, bakin ya riga ya saba amma zanyi kokarin gyarawa bari na kira maka safiyyar tana fadan haka ta juya ciki tare muka fito momy tace imran bari naje cikin makaranta wajensu sadiya minti uku. wai safiyy baki iya gaisuwa ba? ban iya ba kuma ba zan koya ba' kiyi hakuri kanwata ki mayar da wukar kar a yanka yaya imran, murmushi nayi ina kallonsa abin kamar a mafarki yau safiyya tayiwa imran murmushi insha Allah daga yau harara ta kare. kanwata mun wuni lafiya? ba gani ba wai ma me ya dawo da kai ina ba jiya kazo ba? dan kuma na baka dama shine kullum sai ka zo" kai kanwata abin harda kari jiya banzo ba ina zaton tun ranar da abbanmu yazo muka gaisa sai yau na dawo. waye abban naka? kan babba kana karya kiya saida kazo har naki zuwa mu gaisa saida momy kuka gaisa, yana dariya yace kinga aikin bawa kanki amsa dana zo naki fito mun gaisa ba sai da momy muka gaisa, har na zo mata da budurwata suka gaisa naso ki ganta kiga yayanki koh ya iya zabe" na dago kai ina hararansa wsi kai wacece kanwar taka?? safiyya ce kanwar imran Allah ya kiyaye na juya zan tafi naji muryarsa hab yar kanwata kiyi hakuri naci darajar umma nayi saurin juyowa ina kallonsa ji nayi hawaye yana taho min nayi saurin tsungunawa, ya karaso da sauri fuskarshi dauke da tashin hankali ya tsuguna safiyya lafiya kike hawaye? nan take nasa masa kuka ya shig tsananin tashin hankali meya same ki? wani abinne yake miki ciwo? ni na bata miki rai? dan Allah kiyi shiru ki gayamin kaina girgiza mass to me yasa ki kuka? imran ummata na tuna to kiyi hakuri gobe tunda weekend ne sai muje kano kiyi kwana daya na girgiza kai ina kuka ba zani ba!! bazani ba!! ina fadar haka na mike cikin hostel ya tsaya sororo cikin mamaki har momy ta dawo yan a ganka kai daya ina safiyyar? hum momy lamarin safiyya yana bani mamaki cikin rashin fahimta tace ban gane ba, imran meye yake faruwa? muna hira daga nace mata dan darajar umma shine ta samin kuka, na tambayeta tace ummar ta ta tuna daga nace gobe zamuje taga ummanta shine fah ta hau kuka tana bazata ba tayi saurin shigewa ciki. yayi saurin bude motarsa ya dauko mata jakar rubutun, momy ga rubutun zan kiraki an jima naji me yasa kuka." 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/4, 8:32 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣1⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com karka damu imran lamarin safiyya sai addu'a momy hankalina ya tashi sosai bana so naga tashin hankalin safiyya please rukayya ki lallasheta kar kanta yayi ciwo yana fada fuskarshi cike da damuwa. ta shigo dakin ta samen na hada kai da gwiwa ina kuka ta karaso da sauri ta dago kaina safiyya me haka? ta fada cikin rudewa cikin dashewar murya nace momy umman ' to ba imran yace zai kaiki ba kince bakya so me kuma za,a miki? cikin kuka nace momy bana iya barci kullum ina cikin kewar umma amma bana fatan na kara ganinta, momy ya zanyi? hmm safiyya wallahi kiji tsoron Allah mahaifiyarki kike cewa bakya fatan ki kara ganint kan wani banzan tunanin ki da bashi da amfani. na dago ido duk sun canza kala saboda kukan dana sha yanzu momy bakya tausayin halin da nake ciki, ya zanyi da rayuwata, momy banda jigon rayuwata, banda mahaifi dan Allah ki gayan momy ya zanyi da rayuwata gashi bana fatan na kara ganin umma duk wani bakin ciki da nake ciki itace SANADI, me yass tabi hanyar da Allah ya haramta ta haifeni ki gaya min ina zansa rayuwata? nasha gaya miki in har zaki daka ta zuciya wallahi zata kaiki ta baroki, na gaya miki baki da shaidar da zaki tabbatarwa kanki ke shegiya ce in kuma kina da ita ki gayamin, momy kakatace ta gayamin to kakarkice ta haifeki?? na girgiza kai meyass baki saurari ummanki ba ? momy in na tsaya zuciyata zata iya bugawa kinga babban kuskure da kikayi kinga safiyya mu tafi a baki da uba kin isa ki canzawa kanki kaddara?? na girgiza kai to tunda kinsan da hake me yasa kika kasa cinye jarrabawar da ubangiji yayi miki kina abu kamar ba musulma ba, ko me umma tayi miki baki da abinda zaki saka mata, safiyya kiyi hakuri ki barwa Allah komai zakiga komai yazo miki da sauki. to momy ya zanyi? wa zai aureni banida uba? baki da shaidar da zaki tabbatarwa kanki baki da uba ki bari mu koma kano kiji bayanin da umma zatayi miki in har baki gamsu ba sai ki dau matakin da zaki dauka. kaina naji ya sara nayi saurin dafe shi tare da kiran sunan Allah cikin sarkewar murya nace' momy kaina zai cire ki taimakamin ta maso kusa dani tare da cire hannuna daga kaina sannu kiyi hakuri bara na kama miki a hankali naji rage zafi, barci ya soma daukana ta mike ta tsiyayo ruwan rubutun da imran ya kawo mata, ta shafa a fuskanta sai lokacin ta tuna da katin wayar data siyo ta dago tare da sawa daman abbanta zata kira taji yaje gida kira daya tayi aka daga hello abba' muryar hajiya taji bayan sun gaisa tace hajiya ina abba? kanta bata amsa taji ana cewa ya jikin Alhaji usman din "hajiya abbane bashi da lafiya? waye ya gaya miki? hajiya yanzu naji ance miki ya mai jiki kigayan me yasamu abba? ganin ta daga hankalinta tace karki rada hankalinki ranar daya je wajenku hanyar dawowa shida direbansa sukayi hatsari amma basu ji wani ciwo ba yanzu ma dan yana barci ne da saina bashi ku gaisa. cikin kuka tace hajiya ya za ayi ace sunyi hatsari baiji ciwo ba? gobe zanzo naga jikin abba haba rukayya na gaya miki baiji ciwo ba kiyi zamanki. Allah hajiya sainazo tana fadar haka ta katse wayar kukantane ya tasheni momy lafiya kike kuka? ta juyo wajena sadiyy abba sunyi hatsari wani irin zabura nan take na mance da ciwon kaina na hau kuka mundi rabin awa muna kuka babu mai bawa wani hakuri muna jin wayoyinmu suna kara bamu ko kallesu ba. sadiya ta shigo da gudunta tana sariya ganin halin da muke ciki yasa tayi saurin tsayawa sisters lafiya kuke kuka? cikin sanyi jiki ta karaso gaban momy aunty rukayya lafiya kuke kuka keda kike babba a cikinmu mune zamuyi haka kiyi hakuri dan Allah kiyi shiru kun dagan hankali dakyar ta iya bude baki tace sadiya abba nane yayi hatsari what? ta durta tare da mikewa daga tsugunen da tayi aunty rukayya yanzu yana ina? yana kano kuyi hakuri momy gobe saimu tafi muga jikin nasa, tafi minti biyar tana lallashinmu sannan mukayi shiru. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/8, 8:01 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣2⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com waya tayi kara a fusace na daga mallsm ka rabu dani ina fadar hama na katse, naci gaba da kukana sadiya ta mike bari na gawaya farida bayan fitar ta momy ta kalleni ki bar kuka dazu kika gama kukan ciwon kai, cikin dasj hewar murya nace momy kizo mu tafi yau ta girgiza kai yamma tayi ki bari gobe mu tadi shigowar sadiya ce ta katse maganar aunty ruky kizo inji imran" momy tace ki goge fuskarki muje koh. yana tsaye jikin motarsa sanye da bakar jallabiya kanshi babu hula muka karasa cikin rudewa ya tare mu rukayya yaushe abban yayi haysari? cikin saekewar murya tace wallahi imran ban sani ba tun ranan daya tafi bamu kara waya ba sai yau na kira wayarshi naji hajiya ta daga shine take gayamin ta karasa maganan cikin kuka. kiyi hakuri ya dago fuska cikin damuwa kuyi hakuri kukan bashi da amfani gobe sai muje a ga jikin nasa yanzu bari naje airport nayi mana bukin momy tace na gode imran bari na dauko kudi muje ta juyo tana kallon sadiya kan tayi magana imran yace 'wane kudi zaki dauko rukayya gani kawai ku shiga mota muje ita dayan yar uwanku ba zata bane? duk na duba ban ganta ba muje kawai, har mukaje muka dawo ina kuka fakin daya yi yasa na dago kaina duk sun fita saini daya ina kokarin fita naji muryarsa ya kira sunana cikin kasalalliyar murya safiyya!! na dago kai ina kallonsa kiyi hakuri ki bar kukan nan karki jawa kanki wani ciwon don Allah kinfi awa kina kuka kiyi hakuri kinga gobe zamuje ki ganshi, hankali na tashi in naga kanwata cikin damuwa bare kuma naga tana kuka sai naji kamar zan mutu kiyi hakuri kanwata ki bar kukan nan yana taban zuciya. ya jima yana lallashina sannan ya samu nayi shiru na zaro kafata zan fita naji muryarsa safiyya ki min alkawarin ba zaki kara kukan nan ba , na daga masa kai haba yar kanwata kimun magana naji dadi muryata a dashe nace zan tafi na kwanta. yanzu zakiyi barci? kaina ciwo yake kinga gobe in munje kuka ya kare kiga Abba da umma nayi saurin dago kai bana son kana kiran ummata kana sa zuciyata tana bugawa ka kiyaye ina fadar haka na fita daga motar. farida na hanga tana ganin na fito tayi saurin shigewa na karasa dakin na jiyo masifar farida. har na karasa taba fada ko kallonta ban ba na karasa kan katifa na kwanta bayan ta fita na juyo ina kallon sadiya me kukayi wa farida take fada? rabu da farida rashin mutunci takeji dan Allah ba a gabanku na fita nemanta na gaya mata abban ruky yayi hatsari ba har zuwan imran ban ganta ba duk cikin makarantan nan na duba ban ganta shine tazo tana fada rashin mutunci take ji wallahi dan bana biye mata da sai munyi fada. sadiya ta mike bari naje daki na dauko kayana danni wallahi ba zan kwana a dakin ba, nasan yanzu kwana zatayi tana mita. washe gari karfe takwas mun gama shiri imran kawai muke jira momy tace wai yau bara muyi break bane? watace tayi kara sadiya ta mikon na daga kanwata an tashi lafiya na amsa da lafiya klau da fatan kun shirya tun dazun muka shirya kai muje jira okey ku fito mu tafi najuyo ina kallon sadiya yazo. yana zaune a gaban mota ya zuro fuskarsa har muka karaso idonsa yana kanmu fuskarsa dauke da murmushi da suka dada masa kyau hada da kwarjini aunty an tashi lafiya? gani mukayi an bude murfin motar wata kyakkyawar budurwa ta fito fuskarta dauke da murmushi sannun ku ta furta tana kallon imran. tunda muka shiga mota take hira dan naji kaunar yarinyar a raina. sai dataga jirginmu ya tashi sannan taja motar ta tafi. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/10, 8:12 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com karfe sha biyu mua sauka a kano momy ta kunna wayarta zata yi kira ya juyo rukayya wa zaki kira? zan kira hajiyane ta turo a daukemu tun kan mu taho nayi way gidan mamam miji...kanya karass wayarsa tayi kara ya zaro ya daga bayan ya gama magana kuzo mu karasa ga motar can mijin mama nane. yana maganar yana nunam mana wata farar honda. mufa asibiti zamu fara zuwa momy ki kira ki tambayi wani asibiti ne ku bari muje gida in mun huta in yaso sai mu tafi. sadiya tacs gaskiya mu fara zuwa can asibitin koya kika gani aunty ruky, ni dai a ganina mu fara zuwa mu hadu tunda dai munzo kano din zuwa can ba zai bada wuya ba. muka karasa wajen motar dureban motan ya fito da sauri ya bude mana sannunku da zuwa gaba imran ya shiga mu kuma muka shiga baya wayar momy tayi kara hello hajiya nazo kano a wani asibiti kuke to shikenan wai suna nassarawa yayi saurin juyowa muma nassarawar zamu kunga babu nisa. har muka karasa babu wanda ya kara magana muna yin parking yara suka fito da saurinsu su hudu oyoyo yaya ya bude mota ya fita yana dariya hi babies ina momy? mai wayo daga cikin su tace taje aiki to ina ayshata? tana ciki wai fushi take bakazo da wuri ba. aunty ku fiti mu shiga suna gaba muna bayansu yaran sai surutu suke masa tana zaune ta rufe idonta ya karasa gabanta yana dariya am sorry lovely sister nasan nayi laifi cikin shagwaba tace bazan bude idona ba sai ka goyeni lala sister kinyi girma yanxu bakya ganin inda kika koma ai sai ki karyani ta kara rintse murya Allah bazan hakura ba saika goye ni ko na kira abban salima nace kazo kana dukana karki min sharri hau na goyeki tayi saurin dane bayansa tana dariya ya mike yana zagaya falon to bude idonki, tana bude kamar a mafarki taga yan mata a zaune suna murmushi wata irin wuntsulowa tayi daga bayansa yaran suka hau dariya. Allah yaya ba zan yarda ba sai na gayawa momy shine baka gayamin kuna tare da baki ba sannunku da zuwa momy tace yauwa yar gatan imran kinsha goyo kai aunty Allah naji kunya bari na kawo muku ruwa ta mike tana kiran lami. cikin mintina biyu suka cika gabanmu da kayan marmari har kasa suda yaran suka tsunguna suna gaushemu ta juyo wajensa. yaya baka gaya min sunan su ba yana murmushi yace ki gaya musu sunanki dana kannanki suma su gaya miki nasu. ta juyo sunana aysha ta nuna wata yarinya wannan kuma salima ga salim toh ni sunana safiyya wannan kuma sadiya sai kuma aunty mu rukayya. lah yaya kusan irin muryarku daya . saida mukayi sallah muka tafi har wannan lokacin mamansu bata dawo ba muna gidan ta bugo waya tayi mana sannu da zuwa. babu wani nisa tsakanin gidan da asibiti muna shiga momy takira hajiya tana ganinmu ta hau murna na gaya muku ba wani ciwo yaji ba kun bi kun daga hankalinku. sadiya tace hajiya dole mu daga hankalinmu abba shi kadai yake zuwa mana yayi hatsari mu kasa zuwa ta juya tana kallon imran yayi saurin zubewa yana gaisheta, momy tace hajiya surinkine saurayin safiyy ne sunansa imran shi ya biya mana mukazo hajiya karya take saurayintane tana murmushi tace an gode, hajiya ba komai . tana gaba muka shiga dakin tare da yin sallama su biyune a dakin yana zaune a kan gado ba wani ciwo yaji ba illa hannunsa daya da aka dora. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/10, 9:26 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com sannu abba ina maganar ina hawaye yayi saurin rike hannuna meye abin kuka safiyya kinga naji sauki, su momy suka karaso su da imran da sadiya suka gaishe shi, momy ta tashi da sauri ta karasa wajen daya mutumin da yake zaune kawu ya jiki maganar datayine ya sa ya dago idonsa muna hada ido naji zuciyata ta buga nayi saurin sauke idona kasa na tsuguna ina gaisheki hannu yasa ya dagonu sannu yata kunzo lafiya? cikin sanyin murya nace lafiya klau abba ya mai jiki? momy ta jawo kujera muka zauna. babu abinda yazo a raina sai tunanin ima nima ina da uba wata irin soyayya ce baran nuna masa ba amma umma tabi ta hanyar da ubangiji ya haramta ta sameni ban san lokacin da hawaye ya dinga zubomin ba, hajiya ta matso kusa dani meya saki kuka safiyya? tana fadar haka kamar ta turani na hau kuka abba yace safiyya meye ya saki kuka ko baki da lafiyane? na girgiza kai sadiya tace wai ke meyasa kike haka kin fi son kullum ki daga mana hankali. shi ko imran yama kasa motsi ya mike jikinsa a sanyaye ya fita dan zuciyarsa zatq iya bugawa in har ya ci gaba da sauraron kukanta waje yayi ya samu waje ya zauna ya rafka tagumi ya fada duniyar tunani meyeke damun rayuwar safiyya?? ita ina nata iyayen? me yasa bata so ayi mata maganar ummanta? meye dangantakarsu da rukayya da sadiy meyasa kullum cikin damuwa da kuka take? tambayoyin da ya kasa bawa kansa amsa kenan koma mene in Allah ya yarda safiyya sain zama SANADIN sanyaki cikin farin ciki nazama SANADIN kawai miki da duk wata damuwarki, nayi SANADIN gyara tsakaninki da mahaifarki, koma meye sai na zama SANADIN gyaruwar rayuwarki ina sonki safiyya son tsakani da Allah tun kan na ganki na kamu da sonki zan soki ko a wani haki kike, ko wacece ke zan aureki na zauna daje insha Allahu safiyya sai mafarkina ya tabbata a kan.... maganar rukayya ce ta katse masa tunani ya dago imran ya ka fito ka zauna anan? rukayya bazan iya zama ina sauraron sautin kukan safiyya ba please rukayya ki gayan meye yake damun rayuwar safiyya, na fuskanci rayuwar safiyya tana tattare da matsla kuma momy nasan kinasane da matsalar kuma kinsan abinda yake damunta ki gayamin dan Allah waje ta samu ta zauna gaskiya imran bazan iya gaya maka damuwar safiyya ba damuwarta ta bani amana kaga in har na gaya maka naci amana kayi hakuri imran bazan iya gaya maka ba amma karka fidda rai ita safiyyar zata gaya maka damuwarta da kanta na fuskanxu imran kana da sa,a cikin mamaki yace rukayya saboda me kikace haka? imran rayuwar safiyya babu abinda ta tsana sama da tsaya tana magana namiji amma gashi rana tsaka kazo ka karya wannan kiyayyarar har ku tsaya kuna hira wani abin ita daya in tana kwance zakaga tana murmushi in na tambayeta dalili sai tace in ta tuna kiranta da kake kanwarka shine yake bata dariy na tabbata gaba kadan zaku shaku da safiyya zata iya gaya maka damuwarta. to yanzu ta daina kuka? tun yaushe tayi shiru yanzu haka ma dariya take kawauna yana bata labari ya saki murmushi momy bara na shiga muyi sallama da abba naje gidan mamana anjima zan dawo tare suka shigo yana fita yaya isha ya shigo (yayan rukayyane) ga dukkan alamu bashi wasa yaje gaban mahaifinsa sun jima suna hira sannan yatafi karfe takwas imran ya dawo hannunsa rike da babban flask bayansa aysha tare da mahaifiyarta lokacin da suka shigo muna waje muna sallah sun jima sannan ta fito aysha tace yay inaso aunty rukayya ya hango sadiya yayi saurin karasaws wajent har kasa ta tsugunna ta gaishesu yace sadiya ina su rukayya? imran yanzu suka fita su da yaya salim aysha tace naso momy kiga me kama dani murmushi tayi tace wata rana zan ganta. basufi minti goma da tafiya ba muka dawo hajiya ta fito kuzo mu tafi tunda ga me kwannan yazo hajiya bari nayi wa abba sallama na shiga tare da yin sallama ya amsa fuskarshi cike da murmushi har kun dawo safiyya? na daga masa kai. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/14, 7:24 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣5⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Na daga masa kai har na juyo zan fita abba kawun ya tafine? kwata kwata ban san lokacin da bakina yayi tambayar ba yaje gida tundazun yake jiran dawowarku amma yace gobe kanku tafi zaizo kuyi sallama nace Allah ya kaimu muma zamu tafi yace to saoda safe zakuje can gidan kune? na girgiza masa kai ban san lokacin da hawaye ya taho min ba nayi saurin fita ya tsaya yama kallon ikon Allah meye yake damun safiyya ya tambayi kansa ko rukayyace take bata mata rai Allah ya kaimu gobe zan tambayeta. ina fitowa na tarar da imran ya dawo nayi saurin goge hawayen fuskata imran yace hajiy ku taho mu tafi, tunda muka shiga mota babu wanda yayiwa wani magana har muka karasa bayan sun fita naji kiran imran sai da hajiya tasa baki sannan na fita yana jingine jikin motar da mukazo sanye yake da kananan kaya wanda sukayi matukar dacewa da kalarsa kanwaya ba muyi sallama ba, to dole ne sai munyi sallama na fada cikim fushi Allah ya bawa kanwata hakuri kana cin darajar alkawarin da nayi maka amma naga kana son wuce gona da iri kana neman takurawa rayuwata tun farko na gaya maka bazan taba sonka ba babu soyayy a tsarin rayuwata tun kan lokacinka ya kure ka kama gabanka kaje ka nemi me sonka bari na fada maka wani magana wallahi imran bazan taba sonka ba daga yau ma mun daina gaisawa na juya zan shiga gida naji muryarsa kiyi hakuri safiyya ban juyo ba ya karasa gabana ya tsunguna dan Allah safiyya kiyi hakuri ki bari muci gaba da gaisawa a maysayinki na kanwata shikenan zamu cigaba da gaisawaa amma wallahi ka kara takuramin har abada ba zamu kara gaisawa ba ina fadar haka na shige ciki. washe gari karfe sha biyu muka tafi kawun momy da salim ne suka kaimu airport, saida sukaga tashin jirginmu sannan suka tafi. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. 💘WAYE SANADI?💘 6⃣6⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com **** **** **** **** **** cikin ikon Allah yau kwanan umma uku da haihuwa. ta sauka lafiya Allah yayi mata kyautar kyawawan yayanta guda biyu duk maza kullum alhaji nasir yana gidan farin ciki har ya rasa inda zaisa kansa har mahaifiyarsa sai da khalifa ya kawo ta ga yara tayi murna sosai. da yake haihuwar gida tayi. Dr khadija da aysha zuka zo wa umma barka, lokacin alhaji nasir yana gidan yana ganin aysha ya dago kai tare da saurin mikewa yana fadin safiyya! safiyya! babah tayi saurin fitowa daga kicin tana kallon ikon Allah ya kara cewa safiyya! aysha tace ba ita bace ni sunana ayaha ta tsunguna tana gaishehi cikin mamaki uace sunanki aysha kuma? khadija tace wajen rukayya mukazo babah tace ku shiga tana ciki suna shiga umma ta hau murmushi sannunku da zuwa aysha har dake kan tayi magana babah ta shigo rakiya kinga wani ikon Allah yanzu don Allah me ya raba yarinyar nan da safiyya wallahi sai da tayi murmushi naga bata da hushirya sai kuma safiyya dana lura tafita tsayai umma tace itace likutan dana gaya miki ina zuwa awo wajenta, suka kara gaisawa da babah ta fita fita dan kawo musu ruwa aysha tace umma karmarku day da wannan ta nun daya daga cikin yaran wanda yake hannun mamanta ta dago kai tana murmushi ta hau dariya mama don Allah bani wayarki na kira yaya imran na gaya masa ta zaro wayar ta mika mata kyaji da shirmemki . yini sukayi a gidan aysha ta bawa umma imran suka gaisa yayi mata barka, da daddare alhaji nasir yazo bayan sun gaisa sa babah ya shigo dakin tare da sallama na amsa kaina yana kasa ina bawa hyssaini nono ya zauna tare da daukar hassan rukayya ya kira sunana a ciki na amsa don kwata-kwata bana kaunar yayi min magana sai wani rawan kai yake akan yayansa ni yayi SANADIN rabani da tawa yar. maganarshine ta katse tunanin da nake nayi niyyar canzawa su hassan suna ki gayan wane suka kike so ni dai na sawa hussaini "salisu" sunan ubangidana ke kuma ki gayan wane suna kike so a sawa hassan a sa masa sunan baffana "yusuf" ya mikon manyan ledoji guda bity ga kayan nan nasa aka dinko miki yana maganar yana mikewa. ana gobe suna da daddare dr khadija ta kawo aysha har ma da salima duk zasu kwana da kuma kayan barkansu umma tayi murna sosai zuwan aysha ko ba komai in suna tare da aysha tana debe mata kewar safiyya, wanda bata wuce minti biyar ba tare da tunaninta ba. wayar aysha ce tayi kara tayi saurin dagawa hello yaya imran kana lafiya? lafiya klau yar uwa. Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).