shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 26 November 2016

Waye sanadi? 67---70[11/14, 7:58 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣7⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com ga safiyya tana so ku gaisa "hello aunty' aunty kin manxe dani ba kya kirana a waya can barin safiyya tace kiyi hakuri kanwata ban cika kunna wayata ba shikenan aunty na hakura yaya ya gaya miki ummata ta haihu baki min barka ba, an min kanne har guda biyu aysha bai gaya min ba da har suna zanzo lah! aunty kizo daman gobe ne sunan tana dariya tace aysha kinga lokaci ya kure da sai nazo amma ki mata barka duk ranar da nazo zanzo naga kannenmu a,a ba zan yarda ba bara na baki kiyi wa umman barka to a bata inyi mata kada kanwata tayi fushi dani ta mikawa umma waya tana dariy umma ga kawata ku gaisa ta karbi wayar tare da yin sallama kirjin safiyy ya buga da sauri daidai lokacin network ya hau rawa muryar nana ta dauke umma ta mikowa aysha waya tare da gaya mata bata jin magana tayi saurin sawa a kunnent hello aunty hello aunty ba kyaji ne ta katse wayar, ina zaton network yana da matsala nasan zai kara kira sai ku gaisa salima tace umma wannan kamar su daya da khalil aysha tace ni kum nafi ganin kamar su da abdul, da yaya imran kalli irin giransu daya ita dai umma kallonsu take tana dariya daga suce suna kama da wane sai suce suna kama da wani. washe gari karfe takwas alhaji nazo gidan tare da khalifa sai kanin hajiyarsa khalifa ne ya shigo umma da matar malam mado suna aiki bayan sun gaisa ya shigo rumfar. fitowa ta kenan daga wanka sai aysha tana sawa hassan kaya hussaini kuma yana hannun salima suka gaisa ya karbi hussaini. ya juyo yana kallon aysha ina umman? kan tayi magana salima tace tana daki don Allah kanwata dauki tabarma ki kai zaure salima ta mike da saurinta tana fita umma ta fito aza khakifa ne nine umma an tashi lafiya? lafiya klau khalifa ya mutanen gida? duk suna lafiya tare muke da kawunmu daga adamawa yazo za a kai masa yaran ya gani" duk da ba wani taro akayi ba mutanen unguwar sun shigo sosai sai wahe garin suna su aysha da salima suka tafi. tun bayan suna wani waye wan gari sai alhaji nasir yazo sau biyu wajen yaransa in banda gaisuwa babu abinda yake hada mu tun babah tana yimin fasa har ta gaji ta hakura sai dai ita ta zauna suyi hira. haka aysha duk ranar asabar sai tazo wata ran har da Dr khadija ake zuwa, duk ranar da aka zo sai an kira yaya imran mun gaisa wata ran har mamansu sai da aka ban muka gaisa da su khalil. ranar danayi kwana arba'in gidansu aysha na fara zuwa tare da taimakon zuwaira yar autar malam mado ta goyi hassan muka tafi, murna wajensu aysha har ta rasa inda zata sa kanta haka mamansu Dr. khadija sai yamma Dr. khadija dasu aysha suka kawo mu gida. cikin wata uku inka gansu bazakace watansu uku ba sai kayi tunanin sun kai shekara, sunyi kiba sosai kamar ya'yan karabawa kayan wasa da kayan sawa har mamakin alhaji nasir nake kwata-kwat baya jin zafin kudin. har yar aiki ya kawo mana din kula dasu. **** **** **** **** **** cikin farin ciki ta shigo cikin dakin nasu, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin tsananin farin ciki sanye take cikin material light pink an masa diniki mai kyau na riga sa siket. siket din ya fito da shape din kugunta farin ciki kike haka tun dazun sai dinple sinki ne yake motsawa haka inda labari bani in sha momy ba wani labari bane kawai ina murnar gama karatune kamar yau safiyya ta shiga B.U.K wai yau safiyya ta gama abin da ya kai ta har tana shirin karbar matsayi gaskiya dole muyi murna ina sadiya ne? tana tare da oniya momy tace kizo ki fara hada kayanki ina tunanin gobe zamu bar nan gobe kuma momy? a,a to zamu cigaba da zamane bayan mun gama abinda ya kawo mu. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/15, 8:30 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com nayi saurin zama a katifa na dago fuskata wadda har ruwan hawaye sun fara sallama nace nikam momy bazam koma na bar kano har abada ta dago tana hararata wai ke meyasa baki da hankaki in baki kima ba ki gayan ina zaki koma da zama? zan shiga duniya har abada bana fatan na kara ganin ummata in da kin san zaki shiga duniya da tun farko baki batawa kanki lokaci ba tunzuwanmu kinyi abinda zuciyarki take gaya miki wallahi momy bazan koma wajem umma b gara ma ki rabu dani na riga ba gama yankewa kaina hukunci babu kaffara in har kika dau shawarar zuciyarki zakizo kiyi dana sani lokacin da bashi da amfani lokaci ya kure kuma a lokacin zaki san ni rukayya mai kaunarkice. wallahi safiyya daga yau har abada ba zan kara gaya miki gaskiy ba kije ji yi duk abinda zuciyarki ta gaya miki tana fadar haka ta mike ta fit nayi saurin mikewa na karssa wajen loka na bude duk wasu muhimman takardu na debo su na zuba cikin jakar hannuna na. na riga na gama sakarwa kaina mafita. ina cikin daki momy ta shigo na tsugunna na bara hakuri tana murmushi tace baby ya riga ya wuce daman kekike jan abinda zamuyi fada , ina gaya miki gaskiya ne ki bari muje kano ki saurari maganar umma ki kuma nemi gafararta don wallahi kin daga mata hankali shekara daya ba kasan inda yarka take ba. na daga mata kai sadiya suka shigo tare da oniya yanzu daman gobe zaku tafi baku gaya min ba? oniya ta fada tana share hawaye na matso kusa da ita ina murmushi kiyi hakuri yar uwata kwanan nan zamu dawo. karfe takwas imran yazo lokacin su momy da sadiya basu nan na mike tare da bude jakar momy na zura mata envelop ina hawaye nabi dakin da kallo nayi saurin goge idona na fita ta baya don karmu hadu dasu momy, na kirashi ta waya nake gaya masa ina bayan makaranta. banfi minti uku ba yazo ya fito daga mota fuskanshi dauke da murmushi kanwata unguwa zaki? na girgiza kai cikin sanyin murya nace imran yaufa zamu rabu ina fatan zaka yafemin a zamanmu in na saba maka cikin razana yace ban gane nufin kiba, ba gobe tare dani zamu tafi kano ba? na girgiza kai ni ba zan koma kano ba na bar kano har abada ina tunanin kamar ganin karshe kake min. haba safiyya ki bar fadan haka don Allah idan kika tafi ina zan saka rayuwata don Allah ki rufan asiri karki guje ni safiyya duk inda zaki tafi ba zai kai darajar gidan mahaifinki ba, na dago idona mai cike da hawaye nace imran kace dui inda zani ba kamar gidan mahaifina bako? ya ma kasa magana sai kai ya daga nace to imran ni banda mahafin da zanje gidansa kamar yaya baki da mahaifi dazaki wajensa mutuwa yayi? imran nima bansani ba, ya mutu ko yana raye Allah masani zaman da mukayi da kai ina jin zuciyata tana yi min babu dadi dazamu rabu me yuwa ne tana kewar sabon da mukayi na dago kaina ina kallonsa abindana gani cikin idonsa yasa nayi saurin sunkuyar da kaina . naji muryarsa cikim amwani irin yanayi mai wuyar fassarawa yace safiyya ki taimakawa rayuwata karki tafi ban san halin da zan shiga ba bana magana biyu zan tafi imran ya daga kansa sama yana neman mafita cikin dakika biyu ya samawa kamsa mafita imran Allah ya hada fuskokin...."kan na karasa naji kamar an buga hankici ya daki fuskata nan take hankalina ya gushe nayi baya zan fadi naji an tare ni ana kyalkyala dariya iya abinda zan iya tunawz kenan . A hankali na shiga yunkurin bude idona naji sun min nauyi sosai hannuna na daga na kai zuwa idona don su taimakan har nayi nasarar bude su. wata irin razana nayi na mike tsaye ina kallon jikina kan na gama tantance kayan jikina wata kofa ta bude ya fito daure da tawul daya kuma yana tsane kansa fuskarshi dauke da murmushi amarya kin tashi?..... 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/16, 8:36 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 6⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com yana maganar yana mikon riga ta nayi saurin kallon jikina wata razananniyar kara na saka lau tayi zata fadi yayi saurin taro ta nan take ta sume a hannunsa. yayi saurin shimfide ta a gadon da sauri ya zura doguwar jallabiya ya fita ya nufi cikin mota. kayan jikinsa ya debo duk taimakon daya dace yayi mata ya fita yana murmushi har ya dawo tana barci ganin bata farka ba yasa hankalinsa ya dan tashi jikinsa a sanyaye ya karasa gefen tafkeken gadon ya zauna tare da dire ledan da take hannunsa. wayarshi ta hau kara ya zaro tare da jan tsaki ya daga ba tare da yayi magana ba cikin shagwaba tace hello yaya imran kana ina tun dazun dady yake nemanka ka daga mana hankali. cikin tsawa yace haba khadija na gaya muku ina lafiya akwai aikin da nake shiyasa ban kwana a gida ba yana fadar haka ya katse wayar. tsawarsa ne ya farkar da nana daga suman datayi, jin kukanta yasa imran juyiwa da sauri duk wani karfinta ta tattaro ta mike tsaye hannunta ta kalla tayi saurin fincike karin ruwan hawaye babu abinda yake zuwa a idanunta, kanta kamar zai fashe haka takeji ga wani irin zazzafan zazzabi da yayi mata sallama. karo na biyu ya kara miko mata rigarta yana murmushi. sai lokacin ta kalli jikinta tayi sarin rarumar bargo ta kare kirjinta ta dafo idonta tana kallonsa babu abinda ya hanga cikin kwayar idonta sai tsantsar kiyayyarsa bakinta take motsawa tana san magana amma ta gaza durkushewa tayi a wajen tana wani irin kuka. meye abin kuka safiyya? ina son kidayawa shi yasa na nuna miki kaunata farin ciki zaki imran ya hada jiki da keh, kin zauna kina kukan da bashi da amfani cikin wata irin murya na shiga magan ka cuceni imran kaci amanata ka wargaza duk wani farin cikina ta keta martabata ka tarwatsa duk wani burin rayuwata nayi bakin cikin tashina naso ace kana gama cika burinka ka kashe ni na huta da ciwon zuciya. imran ka gama da rayuwata, don Allah ka taimakan ka kasheni na huta ka taimaka ka kashe ni ba zan taba yafe maka ba, na tsane ka bana kaunar na ganka ka tashi a gabana" safiyya abinda kike so nayi miki kina maganar zaki shiga duniya nasan kuma in kin shiga duniya abinda zakiyi kenan don haka nace gara nina fara aikatawa nasan kuma zaki fadi haka, nikam ba zan kashe kiba ina sonki cikin tsawa nace baka son baka kaunata! har abada ba zan taba kaunarka ba kayi min tabun da har abada ba zai taba gogewa daga zuciyata ba, kaje Allah yayi min sakayya da gaggawa. ina fadar haka na fincike riga ta jiri na dibana kamar zan fadi nayi saurin dafe garon dakin. haka nabi bango har na kai kaina toilet na zura riga ta har na fito yana tsugunne inda na barsa naje kofar dakin don na bude na fita iya karfina na hau jan kofar amma na kasa na juyo ina kallonsa muryata a dashe nace kazo ka bude min zan fita yana wata irin dariyar mugunta yace safiyya kin shigo dakin nan kenan bazaki fita ba har sai kin amince zaki auren muyi rayuwa mai kyau da... kan ya karasa na katse shi wallahi imran dana aure ka gara na auri bakin maciji wanda kullum zai sare ni sau dubu zan zauna dashi da dai na zauna da kai. ina fadar haka na tsugunna a bakin kofar naci gaba da kukana ledar da ya shigo da ita ya ajiyen a gabana. ga abinci nan kar yunwa tayi miki illa' yana fadar haka ya tafi gado ya kwanta. a wajen na kwana ina kuka har gari ya waye kin yarda da imran gashi ya cuce ni yayiwa rayuwata karan tsaye. na mike jiri na diban na shiga toilet na dauro alwala, lokacin dana fito har lokacin yana barcinsa hankali kwance na karasa inda naga an shimfisa sallaya na juyo mayafi na tadda sallah bayan an idar naji wata azababbiyar yunwa wadda take shirin illata cikinta yayi wata irin murdawa ban san lokacin dana saki kara ba ya farka a gigice lafiya? ya fada yana murza ido ko muryarsa bana kaunar naji sautunta. nayi saurin toshe kunnuwana naci gaba da kukana babu magiyar da baiyi min ba don na gaya masa me yake damuna karshe ma sai na rufe fuskata naci gaba da kukana. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/18, 8:41 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com ya mike ya shiga toilet wanka yayi ya fita baifi minti goma ba ya dawo dauke da flask din shayi. zama yayi y hadan sannan ya mikomin kisha mu tafi na juyo ina kallonsa don gaskata abinda ya fada ya kara dagan kai ki sha mu tafi na maida ke na karba ina gama sha naji cikina yana hargitsewa amaine ya tason nayi saurin mikewa don na shiga toilet ina mikewa jiri ya debe ni na dawo zan fadi yayi saurin tare ni nayi yunkurin kwace kaina daga rikon da yayi min amma ya rike ni kam ga amai ya cikan baki, ki zauna karki fadi ganin ba zai sake ni ba yasa na sakar masa ama a fuska har na gama bai sakeni ba sai faman sannu yakemin ji nake kamar wuta yake zuban idan yayi min magana. gaba daya jikinsa ya baci da aman shayin danayi iya karfina na yunkur na hankadashi yayo baya kansa ya bugu, wata yar karamar kara ya saka ya kai hannunsa inda ya buge yana dubuwa yaga jini. safiyya kinga kin fasan kai koh? wallahi imran inda zan iya kashe kada sai na kashe ka dana ji muryarka gara kunnuwana su daina ji har abada. toilet ya shiga ya dauraye jikinsa da wajenda yaji ciwo da kansa ya zauna yayi gyaran waken ya juyo wajena. ga magani kisha karki wahala yana maganar yana mikon ban ko kalleshi ba nace ina jakata? mikon yayo na karba nayi saurin zazzagawa wayata ta fado nayi saurin dauka na kunna naji muryarshi karki sha wahala kinga layin wayarki dago kai na ganshi a hannunsa gabana ya karya shi ya kuma watsar. ga kayan break nan zan fita nemo kayan auran safiyya yana fadar haka ya mike nima nayi saurin mikewa ina zaki? yana bude kofar naga mun fito wani tafkeken falo ya sha kujeru ya karasa ya zauna yana dariya. zarcewa nayi wata kofa zuciyata cike da farin cikin ganinta a bude kan na karasa naga tana rufewa ba tare da an taba ta ba, abin ya ban mamaki na juyo ina kallonsa hannunsa dauke da dan remote. na gaya miki ba zaki taba barin gidan nan ba har sai kin amince zaki aure ni na kira malamai su daura mana aure. na dafo kai idona cike da hawaye imran dana aure ka gara na kare rayuwata cikin gidannan har na mutu, kasa hannu ka yanke duk wata alaka da ta fara ginuwa a tsakaninmu nafi son Allah ya sa na mutu na huta. ban so ka! bana kaunarka!! ko baya na gaya maka bazak taba samun soyayyata ba ballantan yanzu daka shayar dani tsantsar kiyayyark. ina rokon ubangiji yayi gaggawar yi min sakayya, banyi tunanin haka daga wajenka ba, ina tun farkon zuwanka me ka gaya min kan na karasa ya katseni cikin tsawa karki kara magana kunnuwana bazasu iya juran munannan kalamunki ba nayi tunanin haka kike so kiyi in kin shiga duniya to don imran ya fara meye abin damuwa? ina in na aure ki na taimake ki duk wanda zai aure ki zai goranta miki duk daran dadewa ni daya ne ballantan bazan goranta miki ba" bana kaunar taimakonka wallahi har abada ba zan taba auranka ba da na aure ka gara na auri kasurgumin kafiri bashi da addini, na san ba zai iya aikata wannan muguntar ba, wallahi gara na mutu banyi aure ba"' shikenan safiyya mu zauna a haka har karshen duniya yana fadar haka ya mike yayi cikin dakin da muka fito. a wajen na zauna naci gaba da kukana har barci ya dauke ni karfe sha biyu na fark naganni kwance a kan doguwar kujera, kwata-kwata banyi tunanin waye ya dora ni a kan kujerar ba da kuma yar guntuwar takardar data fado daga jikina ba, na mike jikina yana rawa sakamakon kyakkyawar yunwar da nakeji. nayi cikin dakin na debo kayan shayen daya kawo min na dawo falon na hada ina gama sha na lura da yar guntuwar takatdar na dauka naga rubutu kamar haka:" NANA SAFIYYA NA FITA NEMO KAYAN AUREN KI DA FATAN BAZAKIYI KEWATA BA GA KAYAN KALLO NAN KI KALLI INDIYA KI KOYI SOYAYYA DAZAMU SHIMFIDA IN MUNYI AURE KI KUMA KALLI MASU KAMA DAKE. NA KI A KULLUM A KODA YAUSHE ""IMRAN SALIS"". 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).