shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 21 December 2016

waye Sanadi?? 83 & 84WAYE SANADI?💘 8⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf *****TUNA Baya***** ta shigo dakin tare da sallama, ita daya ce a cikin bukar sai wani kyakkyawan yaro da ba zai haura shekara hudu ba, yana ganin shigowarta ya hau murna. Ba ta ko kalle shi ba ta karasa gaban Yayarta ta tsugunna suka gaisa. Ya taso da gudu ya hau cinyarta, tana kokarin ture shi suka hada ido ta dan daure ta bar shi, yana wasa da awarwariayen hannunta."Yaya za mu tafi fa, in kina da sako ki bayar na taho miki da shi."Duk kun hadu ne?" Ba ta yi magana ba sai kai da ta daga mata,"Ba ni da sako ga Sale nan ku tafi da shi, shi ma ya ga gari."Ta dan dago da saurinta suna hada ido ta mayar da kanta ta dan yi jim, sannan ta mike."Bara na tafi suna jirana."To ba ki ji abin da na ce ba ne, ga Sale zai bi ku shi ma ya ga gari.'To yaya na ji ya taso mu tafi.Cikin fushi ta dago kai tare da cewa, "Sofi ki kiyaye ni ki kama hannunsa ku tafi duk abin da zai same shi ya same ku tare, bana san sakarcin banza kamar ba ke ki ka haifi yaron nan ba, shi ma zai zo ya same...."Kan ta rufe baki ya shigo shi ma gabanta ya tsugunna kamar mai neman gafara. Suna gama gaisawa ta rufe shi da fada kamar za ta cinye shi, babu abin da yake sai hakuri yake ba ta. Ta dan sassauta murya ta ci gaba da cewa "Ba ka ganin dan uwanka neman haihuwar yake ido rufe amma ku Allah ya ba ku kuna wulakantawa, ku ne iyayensa ku za ku ja shi a jiki har ya gaya muku damuwarsa, to kuna baya da shi ba kwa jan sa a jiki, kuna nuna masa kauna to ya za a yi ya saki jikinsa da ku? In kiwo za ka ka ja danka ku tafi, haka in kasuwa za ki ki ja shi ku tafi, ba kya ganin yadda 'yan uwanki suke jan 'ya'yansu a jiki,Rashin kula shi da ku ke, shi ya ja 'yan uwansa suke dukansa. Yanzu, jiya da ba don na zo lokacin da suke fada da Jauro ba da sai dai a kashe shi a gabanki kina kallonsa. To daga yau bana san sakarcin banza, ku ja danku a jiki, ku nuna masa kauna da kulaw..."Kan ta karasa aka yi sallama aka shigo."Lafiya ku ke zaune muna tu fa man tsimayi?""Nina tsayar da su ina musu fada kan sakarcin da suke kan Sale. Yauwa Yaya ki yi musu har da duka sun cancanci haka."Tun da muka fito da Sale a hannuna mutan gidan suke kallona cikin mamaki, nan da nan kunya ta rufe ni bar ma da tsoron maganganun da za su biyo bayan hakan. Haka muka tafi kai nono cikin gari. Magajiya ta matso kusa da ni. Yau yana ganki da Sale?' Ta fada tana murmushi.Na dan sunkuyar da kaina."Hum, Yaya ce ta matsa sai mu tafi dashi."Ta yi daida..Daidai lokacin muka zo gifta wani katon shagon saida kayan yara muka karasa tare da yin talian nono da sauri mutanen da ke siyayya a shagon suka juyo suna kallonmu bar mai shagon ya bude baki xai yi magana wani hamshakin Alhaji ya ce."Ku kawo mu gani." Yana maganar yana kallon Sale. Muka karasa gabansa tare da sauke kwaryar da take kanmu. Karar waka ta cika dakin muka hau dube-dube, sai Alhajin yasa hannu ya dauko wata katuwar aba baka ya kara a kunnensa ya hau magana muka tsaya cikin mamaki muna kallonsa har ya gama. Sale ya tafi wajensa da gudu.Baffa ba ni na gani," Ya dauke shi ya dora sa a cinyarsa yana murmushi.'Dan Baffa me za ka yi da waya?' Sale ya ce Wasa zan yi da ita, ban da kayan wasa, baba ba ta sai mun sai dai ta dinga dukana ba ta ma kula ni kullum tana ganin yara suna dukana ba ta hana kowa. kai ma ka yi mata fada kamar yadda su Yaya suke mata.Ya yi shiru yana kallonsu kanta yana sunkuye kunya duk ta baibaye ta.'Ka yi hakuri ni zan sai maka kayan Wasa har ma da na sawa."Sunnan ya juyo wajen umma fuskarsa a hade ya ce, "Me yasa ku ke takurawa karamin yaro? Kuna daya daga cikin azaluman iyaye masu wulakanta ya yansu ko?"cikin mamaki suka kalii juna ita da Magajiya, ganin yanda yake fada kamar dansa ya katse musu tunani da cewa, wasu suna neman °yaya ido a rufe Allah bai ba su ba. ku ya ba ku kuna wulaRanta su. Ya dan rage murya ya ci guba da cewa.Don Allah ku dinga tattalin 'ya'yanku kuna kula da su, in ba kwa jan su a jiki kuna nuna-musu kulawa sai su shiga wani hali.Na daga masa kai,"Ku zuban na dari uku-uku.Sunnun ya juyo wajen mai shagon."Malam hada masa kuyan wasa da na suwa."To Alhaji." Ya mike jikinsa na rawa ya shiga hada kayan.Ya juyo wajen mu ya ce, "Ina san na sari shanu a wajen akwai masu siyarwa? Sale ya yi saurin cewa, "Baffanmu yana da su da yawa ka zo mu je ya siyar ma ni kuma zan bar maka nawa Au kai ma kana da sa? Yaya sunanka?'Sale Ba ku ban amsu ba Mugajiya ta ce, "Ana siyarwa Ya dan numfasa, yana danna faskekiyar wayar da take hannunsa ya ce "To yunzu ya za a yi na siya, tunda ban san wajen ku ba? baffa ka bi mu mu tafi garinmu, sai ka siya mu tafi gidanka. Hakan ce ta faru har muka gama tallan nono yana yaune a shagon mutumin da muKa yi masa lallar, ya mike ya dan fito bakin shago.'Kun san tafiyarmu ba za ta zo daya da ku ba. in kuma za ku shiga motata mu lafi to Na girgiza kai na ce Ba za mu shiga motarka ba sai dai mu yi gaba ka bi mu a baya har mu je Sale ya hau kuka Ni dai babah ba zan tafi a kafa ba Baffa zai bi." Yana maganar yana rike hannunsa Magajiya ta jani gefe, mun dan jima muka dawo gabansa. Magajiya ta ce,Mu je mun yarda za mu shiga motar ka Wannan shi ne karanmu na farko shiga mota. Tafi-tafi har muka je garinmu yana ta mamakin mutanen da suke rayuwa cikin wannan surkukin dajin. Mamakinsa ya tsaya cak ganin mun bullo cikin gari duk inda muka wuce yara da manya kallonmu suke har muka karasa. Ya fito yana rike da Sale, Sale haka garin naku yake, gaskiya da wuyar zuwa, kuna shan tafiya. Amma kafarku tana ciwo kam Ya girgiza masa kai tare da cewa Don Allah in za ka tafi zan bika ka sani a makarantar boko Ai ba za su ba ni kai ba in da za su ba ni kai zan yi mutukar farin ciki a ce an bar min kai ka yi karatu mai..Bakinsa ya kasa karasa abin da yake san fada, sakamakon ganin wasu gungun shanu sun taho farare sol da su kai ka ce gaba dayan shanun garin ne suka hadu. Maza biyu ne ke jan tawagar shanun Suka karaso wajen fuskarsu dauke da mamakin ganin mota cikin garinsu. Alh. Dahiru ya matso ya mika masu hannu don su gaisa cikin dari-dari suka mika masa hannu, kan ya yi magana Sale ya ce Baffa wajenku ya zo zai sai shano a kasuwa muka taho da shi har ma ya sai min kayan wasa. Bara na dauko masa tabarma Ya zuru cikin gidan da gudu. Bai jima ba ya dawo da tabarma, sun jima suna tattaunawa da su Mado.Cikin gidan kuwa tunda su Magajiya suka bawa yayar mazajensu labrin bakon da suka taho da shi zai sai shanu har ma da siyayyar da ya yi wa Sale. Ta ko rufe su da ruwan fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har matan gidan taya ta suke haka suka shigo suka same ta, dakyar suka lallaba ta suka shiga cikin bukkarta. Ta dago tana hararar su dukansu kansu yana kasa.Haka kawai ku dauko mana mutum ba ku san wa ye ba mugu ne dan yankan kai ne muna zamanmu lafiya ki dauko mana bala'i, ni dai ban yarda da shi ba watakila ma irin barayin yara ne, ya gan ku da da yana so ya sace shi har da yi masa siyayya, to wallahi bara na gaya muku duk abin da ya sami Sale ku kuka da kan ku, kuma maza ku gaya masa shanunmu ba na siyarwa ba ne ya bar mana unguwanmu. Yanzu ina ma Salen yake? Bakin Mado na rawa ya ce, Yana wajensa Ta mike da sauri Maza ku taho da shi, kar ya gudu da shi Har matan gidan suka fito waje da gudu, babu mota babu Sale. Ta juyo tana kallon Sofi da Magajiya. Kun ga abin da kuka ja mana ko? To wallahi ba zan koma cikin gidan nan ba in za a shekara dubu sai kun je kun nemo sa, bar mazajen ku ku bar gidan nan ga shanun nan ku dibi naku ku tafi, wallahi duk wanda ya shigo gidan nan a cikinku ba tare da Sale ba sai na KASHE shiSANADIN zuwan su Mado cikin birni Kano kenan. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/20, 9:06 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf Bakina narawa nace, ‘Umma Kawun Rukayya, shi ne mahaifina?”na daga kai. Na ji wani irin jiri yana dibana nayi baya zan fadi, naji an tare ni kannakara sa suma a jikin wanda ya tare ni naji sautin muryar Alkali yana ba da umarnin kama Imran. Magana na dinga ji sama-sama tare da sautin kukan Rukayyar Momy na, muryar da baza ta taba bace min ba, nayi yunkurin bude idona wanda sukayi min nauyi sosai tare da azabar yaji kamar an zuban barkono, nabude su dakyar idona cikin fuskar Ummana kantana kasa tana sharer hawaye ta jimuryata.“Umma me ye kike kuka?”Ta yi saurin dago tana kallona damuwar da take fuskarta ta bace murmushi tayi Ni kaina, ban san lokacin da murmushin ya sauka a kan kyakkyawar fuskataba. Kan ta yi Magana Momy ta dago idonta duk sun kumbura, na bude baki dakyar nace.Momyki bar kuka gani na dawo.”Ina maganar inakokarin kama hannunta, ta yi saurin mikon hannunta, na rike ina mata murmushi ta ce.“Safiyya kukan farin ciki nake da Allah ya bayyana gaskiya cikin kankanin loakci, ban zaci haka daga Imra...”Kan ta karasa abin da yake bakinta aka turo kofar aka shigo. Kawun Momy ne ya shigo yana shigowa Hajiya Amina (mahaifiyar Imran) ta shigo, na yi saurin mike ido. Hajiya Amina ta karaso gabana ta dan dafa gefen gadon ta ce, “Sannu Safiyya.Kai kawai na daga mata, kan ta kara magana wayarta ta hau kara, ta zaro a jaka ta fita. Tana fita Umma ta bi bayanta Kawun Rukayya ya zauna a inda ta tashi.“Safiyya bude idonki don Allah.” Na ji muryarsa. Muryata a sarke na ce, “Kawu da gaske kai ne mahaifina?’“Ki daina kokwanton haka babu wani kokwanto ke ‘yata ceta jinina.” Cikin shashshekar kuka na ce, “Abba me yasa ka guje ni lokacin da nake bukatarka ka ki ka tallafi rayuwata lokacin da nake tsananin bukatar tallafinka? Sai wani wanda ba shi ya haife ni ba ya tsaya ya tallafi rayuwata, ya yi min taimakon da ba zan taba mancewa da shi ba. Na so a ce Alhaji Nasiru ne ya haife ni, na san ba zan yi nad....” Kuka ya ci karfina na kasa karasawa.Ya dago yana kallon Rukayya (Momy), suna hada ido ta tafi ya zama daga ni sai shi a dakin.“Safiyya bude idonki.”Ban yi musu ba na bude sai dai na kasa dagowa na kalle shi.“Ki yi shiru ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo.”Na ce, “Abba don Allah ka gayan gaskiya ta wace hanya ku ka haifi ni.”Kai tsaye yaban amsa da cewa ‘Safiyya ta hanyar aure muka same ki.” Na kara cewa, “To me yasa ka ki karBata a matsayin ‘yarka?”“Safiyya ki kaddara haka Ubangiji ya shirya, kuma ba mu isa mu wargaza shirin Ubangiji ba ya riga ya tsara haka za ta faru a gare mu in har kin yarda da lamuran Ubangiji to kar ki dau wannan kaddara ki mata mummunanar fassara, ki dau hakan wata jarrabawa ce da Ubangiji ya yi miki.”“To yanzu me ye matsayina a wajenka? ”Ya dan yi dariya, sannan ya ce, “Tun farkon ganinki a matsayin kawar Rukayya Allah ya zuban kaunarki a lokacin da ki ka bata na shiga tsantsar tashin hankali ni kaina wnai lokacin na kan tambayi kaina me ye yasa na damu da batan ki? Ashe ban sani ba ke ‘yata ce.”Na katse shi, ‘Abba ka yarda yanzu ka karbe ni a matsayin ‘yarka Baba ta daina yi min gori.”“Tunda na ganki zuciyata take gayan duk abin da Rukayya ta haifar min nawa ne sharrin makiyanmu ne ya raba mu, na yi neman Rukayya na rasa sai jiya Allah ya hada mu. Safiyya nayi matukar farin ciki da Allah ya ban ke, zan baki kulawar da duk wani uba yake bawa ‘yarsa. Na rasa in da zan saka zuciyata don murna abin da na fitar da ran samun sa yau ga shi Allah ya ban.”Da sauri na ce, “Abba kannena nawa?”“Safiyya ke daya Allah ya ban, k...”Kan ya karasa Alhaji Nasiru ya shigo, yana ganina a zaune fuskarsa ta fadada da murmushi ya karaso da sauri. ‘Sannu Safiyya kin tashi.”Na dan sunkuyar da kaina na ce, “Dady na tashi,ina Khalifa?”‘Khalifa yana gaishe ki, dazu ya zo kina barci, kuma lokacin zai wuce Bauchi kin san ya samu aiki a can Bauchin.”Na ce, “Allah ya sanya alkhairi Dady, ina su Hassan?”Cikin mamaki ya ce, “Wa ye ya gaya miki Umma ta haihu?”Na dan yi murmushi sannan na ce, “Imran ne ya gayan har ma ya kai min su na gani lokacin da ku ka je nemana can Lagos din.”‘Kai wannan yaron bai kyauta ba, a haka kamar na zai aikata haka ba.”Abba ya ce, “Daman shi mutum ai ba ka san in me ye yake zuciyarsa sai Allah, amma ni ina ganin bai kamata mu bar shi a hannun court ba, kawai a karbo shi mu yi abin mu cikin sirri ba sai an fantsamawa duniya ba, kuma ko don iyayensa sai a rabu da shi tunda Allah ya kubutar da ita.”Dady ya ce, “Ni kaina na so haka, amma mahaifiyarsa ta ce abar shi alkali ya yi masa hukuncin daidai da laifinsa, don dazu muka yi waya da mahaifinsa, shi ma haka ya ce a rabu da shi.”Ya dan juyo wajena, ‘Safiyya ya aka yi ya dau...” Da sauri na ce, “Abba bana san hirarsa don Allah ku bar fadan sunansa, Allah zan iya mutuwa.”Ina fadar haka na saka kuka.Daddy ya ce, “Ki yi hakuri Safiyya ba za mu kara hirarsa a gabanki ba, ki bar kukan nan kar su Hassan su zo su ga Antynsu tana kuka.”Yana fadar haka na yi shiru ya juya wajen Abbana yana murmushi, sannan ya ce, “Alhaji Mukhtar zan je gida ina tunanin kuma ba zan dawo asibitin nan na tadda ku ba, na ji yana anjima zai sallame mu tunda ta farka.”‘Haka ne Alhaji Nasiru na gode da kulawar da ka bawa Safiyya bakina ba zai iya fadar godiyar a wannan lokacin ina fatan zuwa har gida don....”Kan ya karasa ya katse shi. “Haba Alhaji Mukhtar me ye abin godiya ni na dau Safiyya kamar ‘yar da na haifa, duk abin da na yi mata na yi don Allah.” Sannan ya juyo wajena ya ce, “Safiyya gidan Ummanta ki za ki tafi ko gidan Abban naki za ki tafi?”Kan na yi magana Abba ya ce, “A’a gidana za mu tafi ta dan kwana biyu ko?”Na dago da sauri na ce, “Abba ina san ganin Ummata fa, ka bar ni in kwana daya sai mu tafi gidan naka.“Duk abin da kike ina so, bari li kita ya sallame mu sai na kai ki ” Na dan yi murmushi na ce, “Na gode Abbana.”Daddy ya ce, ‘Ni ba za ki zo ki kwanar min ba.”Ban yi magana ba sai kaina da na sunkuyar. Abba ya ce, “Kai ma za ta zo ta yi maka kwana biyu ko don Khalifa.”Tare suka fita. Suna fita Rukayya ta shigo.‘My Sister kuna ta hire da Abba kin manta da Rukayya?‘Lah Momy ban manta da ke ba, hasali ma babu abin da yake raina sai ke da Sadiyya.”‘Tana ina na ba ta hakuri? Na san na muku laifi. Momy a yi min afowa ba zan kar...”Kan na karasa ta katse ni da cewa, “Baby bana san tuna baya abu ya riga ya wuce komai sai labari. Sadiyya ta je gida wanka tun jiya muna nan muna kukan mun ga samu mun ga rashi ga baby ta dawo kuma za ta gudu ta bar mu.”Na dan yi murmushi, ‘Ga ni Momy insha Allahu muna tare.” Na dan yi shiru.“No baby, Doctor ya hana ki tunani.”‘Momy ba tunani nake ba, ai tunani ya kare na ga Abbana.” Na dan girgiza kaina.“Momy don haka muke kaunar juna tsakani da Allah ashe Momyta ‘yar uwata ce ta jini, Momyna kuma Antyna, Kawun Momyna da ya nunan kauna tun kan ya san wace ce ni yake nuna min kauna har ya yi min kyautar da bazan taba mancewa da ita ba.”Na sauke numfashi sannan na tambaye ta cewa “Ina Ummata?” “Ai tunda ki ka farka Umma ta tafi gida tare da Sadiyya, Abbana ya tafi ya kai su gida.”Kan na yi magana Abbana ya shigo tare da Doctor ya tambaye ni abin da yake damuna, na gaya masa babu abin da yake min ciwo sai idona da kaina da suke ciwo.”Magunguna ya rubutan sannan ya sallame mu. Muna kokarin shiga mota Abban Rukayya ya shigo, ya ganmu a tsaye tare da Momyna tana min hire sai kokarin sani dariya take. Ya karaso fuskarsa dauke da dariya.“Na ji dadin ganinki haka Safiyya, Hajiyata na ta dokin ganinki amma can za mu tafi ko?”ta ce, ‘Abba, tun da ta dawo nakc ta lallaba ta yarda mu je gidanmu wai ita sai gobe, yanzu wajen Umma za mu kai ta.”Ya ce, ‘‘Wai haka Safiyya?”Abba ka yi hakuri ina bukatar ganin Ummata.'’ Na juyo wajen Momy na ce, “Haba Momyna ki ban na ga Ummata kwana daya kawai zan yi musu na taho wajenki, shi kenan na dawo nan bar abada.” Ta juyo da sauri tana dariya.“Abba ka zama shaida Safiyaya za ta dawo gidanmu.”“To na zama shaida.”Sannan muka tafi har kofar gidanmu Abana ya kai ni (da yake Momy ta bi Abbanta). Ya yi parking. Har na ziro kafa ta zan fito na ji muryarsa.“Safiyya zan je nadawo mai ki keso na taho miki da shi?” Na girgiza kai.“A’a ki min magana bana san girgiza kai, in kuma wani abun ne yake damunki ki fadan yanzu mu koma asibit, bana san ganinki cikin damuwa.”Na dan yi dariya, sannan na ce, “Babu abin da yake damuna Abba, zuciyata cike take da tsantsan farin ciki, yau gani ga mahaifina farin ciki ne yake hana ni magana.”‘To in har kina farin ciki da kasancewa ta mahaifinki ki gayan abin da ki ke so na kawo miki anjima.” ' Da sauri na ce, “Abba ka kawo min kayan dadi.” tare muka fito daga cikin motar ya bude but ya firfito da manyan ledoji har guda hudu, daidai lokacin Kado ya fito daga cikin gidansu yana ganina ya saki baki cikin sanyin murya na ce Kado don Allah zo ka dibar min mu shiga. Ya dawo da saurinsa suka gaisa da Abbana ya dibi kayan ya shiga na juyo wajen Abba na ce.“Abba bara ka shiga ku gaisa da Baba.”“Hum Safiya ina jin nauyin abin da ya faru tsakanina da Baba, amma na san ke za ki zama SANADIN ganowar komai ki gaishe ta har Umma, anjima in na zo zan shiga mu gaisa. Yana fadar haka ya koma mota.Na shiga gidan tare da sallama, muka yi karo da Baba tana kokarin fitowa na dan yi murmushi. Ina kuma za ki gani na zo?” Ta sa dariya.“Ba zan iya zama ba sai na ganki, lallai da na yi wa gidansu yaji.”Na hango Hassan yana tafiya a jikin bango na karasa da sauri na daga shi.“My boy ina Ummanmu?”Kamar ya sani ya kama yi min dariya, na juyo wajen Baba wadda ta biyo baya na bakinta yaka sa rufuwa.‘Ga Hassan nan kamar ku daya babu abin da ya raba ku.”Da sauri na ce, ‘A’a Baba ni da Abbana nake kama babu abin da ya raba mu, Hassan ko da Umma yake kama.” Na shiga cikin dakin tana zaune tana ba wa Hussaini nono, na karasa gabanta na tsugunna, Baba ta yi saurin fita ba. “Bara na kawo wa bakuwa abinci mai jaki, sanna na zo mu gaisa.”Na dan yi dariya na ce, Umma an tashi lafiya.”‘Lafiya, ya jikin naki?”“Na ji sauki daman ciwon tunanin Ummata ne.”‘Inda kina tunani ba za ki tafi ki bar ni ba har tsawon shekara daya.”“No Umma ki yi hakuri ke daya zan bawa hakuri, Baba kora ta ta yi na san ba ta damu da rashina ba, ke daya ki ka shiga damuwa, ki yi min afuwa don Allah ki yafc mini.”“Daman na riga na yafe miki, kuma ma tafi yarki ta zama SANADIN na haduwarki da mahaifinki.”Na dan yi dariya, na zauna a kusa da ita, Ina zama su Baba Magajiya suka shigo.Sai wajen karke hudu gidan ya zama shim, sai ni da Umma, sai kuma su Hussaini da suke wasa. Na jawo ledojin da Abbana ya ban na hau duba dogayen riguna kala-kala, sai mayuka da kuma mayafai har ma da takalma masu matukar kyau Na nuna wa Umma.Ta ce, “To ki tashi ki yi wanka ki kara jin karfin jikinki.”‘Yanzu zan tashi bara na gama shiryawa su Hassan kaya,”Baba ta mi ke da saurinta, “Bara na kai muku ruwan.”Ina fitowa Momy ta yi sallama. Bayan sun gaisa da su Baba ta juyo wajena… 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Waye sanadi? 82WAYE SANADI? 8⃣2⃣ MUH'D*ABBA*GANA www.MuhdAbbagana.cf 'Dan albarka za ka fara halin naka koh, ya mutanen gidan da fatan kowa lafiya? "Duk lafiya sun a ma gaishe ka."'To madallah ya kumu yarinya da jiki?" 'Hum, malam ta ma ji sauki."To, mana godewa Allah. "Ya mike muka shiga ciki babu kowa sai tarin almajirai. Cikin dakinsa muka shiga cikin nutsuwa na Kara gaishe shi, ya amsa shiru ya biyo baya. Na daure na ce, "Malam an yi min aikin?"Ya dan sauke numfashi yana kallona, sannan ya fara magana. "Imran na dau tsawon kwana biyu ina maka aiki, kuma babu abin da nake gani sai tarin alkhairi mai yawan gaske, amma fa bayan an sha wuya tare da riginginmu komai zai zama tarihi."Yana murmushi ya ce, "Na gode Malam. Sannan ya gaya masa yadda suka yi da Safiyya. Ya jima kan ya yi magana ya sauke numfashi.'Imran kana ganin in aka daura maka aure ba tare da sanin Salisu ba, ba zai haifar maka da matsala ba?" Ya yi saurin cewa, Wallahi Malam babu wata matsala da za ta faru, ka ga shi Dady baya gari, kuma su iyayenta sun ce in har gobe ban turo waliyina ba za su bawa dan uwanta. Don Allah ka taimakan ina so da ya dawo sai ka gaya masa. "'Har yanzu kai yaro ne Imrana, ba ka san ya rayuwa take ba, ka je ka Iallaba iyayenta zuwa nan da kwana uku, ka ga kan sannan su "Dahiru sun zo sai mu je tare da su a daura maka auren."Ya kara tausasa murya ya ce, "Ni dai Kawu ka taimakan kar na rasa ta, kasan yaya Yusuf bai yi aure ba, sai ni kaninsa."Shi kenan gobe ka zo mu je sai a daura auren in ya so daga baya kwa yi bikin."Cikin murna na dago ina godiya na zaro dubu hamsin. 'Malam ga sadaki.""A'a ka bar abin ka ka yi wani abun ni zan bada sadaki a matsayin gudummawata."Yana fitowa daga gidan Malam kai tsaye cikin kasuwa ya nufa duk wani abu da ake zubawa a lefe sai da ya siya sai da ya cika akwati set shida nan take ya biya kudin aka zuba masa a but, ya taho zuciyarsa fal da faiin ciki.Ya shigo tare da sallama, na dago fuskata a hade, kallo daya na yi masa na maida kaina. Ya karaso kusa da ni."Safiyya zo mu je falo ki ga wani abu."Ban yi musu ba na biyo shi zuwa falon. Akwatuna na gani har guda shida.'Safiyya ga kayan lefe nan na yi miki."Na dago da sauri na ce, "Ban gane ka yi minkayan lefe ba, ni da da an daura mana aure za ka sake ni ko ka mance da haka?"Yana murmushi ya ce, Na san da haka wannan lefan na yi ne kawai don na faranta miki ko ba ky...."Kan ya karasa na katse shi da cewa, 'Bana bukatar kayan lefen ka burina gari ya waye a daura mana aure ka sake ni."Ina fadar haka na juya ciki ya biyo bayana da kallo fuskarshi dauke da murmushi. *****WASHE GARI***** Misalin karfe goma Imran ya shigo ya ci farar shadda har da babar riga fuskarshi sanye da farin gilas, wanda ya kara kawata fuskarshi. Na dago ina kallonsa har ya karaso ya tsaya a gabana yana murmushi.'Ya dai Safiyya na yi miki kyau ne ki ke kallona?"Na yi saurin dauke kaina, ya dan rankwafa, muryarshi a hankali ya ce, "Don Allah Safiyya ki yi wanka ki canja kayan nan. 'Babu ruwanka da canja kayana in ka je an daura to ka sake ni na tafi."Fuskarshi cike da murmushi ya ce, "Ba a daura ba yanzu zan je na dauko su ai a nan za a daura, ki daure ki canja kayan nan don Allah." Yana fadar haka ya fita.Bai fi rabin awa da fita ba na jiyo hayaniyar mutane a falon na yi saurin zuwa bakin kofar na leka ta kofar da ake zura makulli. Mutane ne su wajen goma dukkaninsu sun manyanta, ina kallo suka daura aurena da Imran. Wani tsoho mai zaman zabga addu'a yake suna amsawa da amin. Ni kuma ina amsawa da ba amin ba. Aka mikawa wani farin dattijo sadakina. Suna zaune aka dinga shigo rnusu da abinci, bayan sun gama suka fita na koma ina hawaye na zauna.Har wajen karfe goma ban ga Imran ba, duk hankalina a tashe yake ga zazzafan zazzabin da ya rufe ni, ya shigo yana waya har ya gama sannan na dago kaina muka hada ido ya sakar min murmushi."AMARYAkinshakamsh..."Kan ya karasa na katse shi da cewa, "Imran kai fa nake jira."Ya dan rage murmushin fuskarsa."Safiyya jiran me ki ke min haka?"Na Kara daure fuska na ce, 'Ina jiran ka zo ka sake ni, kan..."Dariyarshi ce ta dakatar da ni daga abin da nake son fada na tsaya cikin mamaki ina kallonsa.'Hum, Saffiya kina nufin ni Imran na sake ki da hannuna? Har abada ba zan taba iyawa ba. Safiyya ke naso, ke nake so kuma ke zan ci gaba da so har zuwa ranar da ban santa ba. Zan kasance jarumin da ka iya fito-na-fito da kowa in har akan sonki da kaunar...."Kan ya karasa na katse shi."Kana nufin ba za ka sake ni ba?"Kan ya ban amsa aka hau kwankwasa kofa, wata irin razana hade da firgicewa ne suka bayyana a kan fuskarsa. Ya mike jikinsa yana rawa ya leka, da sauri ya dawo da baya. Daidai lokacin aka kara buga Kofar karo na biyu ya karaso gabana fuskarshi ta jike da gumi, na ji muryarshi a hankali."Ki rufan asiri Safiyya ki shiga bandaki yayana ne ya zo da iyalensa don girman Allah ki rufan asiri." Ganin tsantsan tashin hankalin da ya shiga karan farko dana ji tausavinsa. Ban masa magana ba na shiga bandakin ya biyo ni ya kulle tare da ban umarnin nasa sakata, Ya dawo bakin kofa ya dan saisaita nutsuwarsa, sannan ya bude yana murza ido. Dr. Dahir ya kalle shi sama da kasa, sannan ya yi magana."Tun dazun muna bugawa ba ka bude ba me ka ke yi a daki ka kulle kanka?"Ya dan kararo muryarshin dole yana shafar kwantacciyar surnarsa ya ce, "Hum wallahi Brother barci ne ya dauke ni. Ina su Abdul-Jalal?"'Suna falo, ka zo ka kai mu gida saukar mu kenan." Ai bai tsaya rufo dakin ba ya fito suka tafi. Suna zuwa gida hira ta barki Hajiya Amina ta juyo tana kallon Imran."Ka san gobe Rarfe bakwai za mu tafi so nake sha biyu mun taho.'Ina sane Momy."Shiru-shiru Safiyya ta ji Imran ya bude ta ba ta ji ba, ga gidan shiru don haka ta zare sakatar komai zai Faru ya faru. Ganin babu kowa ga kuma kofar dakin a bude yasa ta dan zura kanta falon kamar a rnafarki ta hangi kofarsa a bude har ma tana hangen get din gidan, wanda shi ma kofarsa take a bade, har ma tana ganin motoci na wucewa. Da sauri na koma na dauko jakata, babhar rigar Imran na harde ni na yi saurin tsugunnawa na dauke na ji nauyi, na yi saurin zura hannu na a aljihunsa na zaro rafar 'yan dubu guda biyu (Dubu dan biyu) na zuba a jakata jikina na rawa kamar mazari na fita daga gidan. Court ta cika makil illa mutum daya da ake jira Alkali Abdurrahman ya shigo ana take masa baya. wannan lokacin duk wani Bangare biyu sun hadu, Alh Ibrahim, Sadiyya, Rukayya, sai kuma lauyansu Barr M- Shamsu, ilia Alh. Mukhtar da ake jira. Haka bangaren. Alhaji Nasir ga shi ga Umma wadda ta rufe fuskarta da nikaf ga lauyansu Barrister Amina Khalil da dan rakiyarta Imran, wanda ya ki bari su hada ido da su Rukayya. Bayan an gama karantawa Alkali shari'a ya dago ya kalli na kusa da shi suna hada ido ya yi saurin fita. Daidai wannan lokacin Alh. Mukhtar ya shigo, babu wanda ya ga shigowarsa sai Umma, ta yi wata irin zabura, Alh, Nasir ya ce, 'Lafiya?" Ta ma kasa magana sai kai da ta girgiza masa, kan ta dawo daga shoking ta ga abu kamar a cikin mafarki NANA SAFIYYA ta shigo,Ba ma Umma ba duk wanda ya san akan abin da za a fara shari'ar ya gigita da ganinta. Shi kuwa kanwa uwar hadin mutuwar zaune ya yi. Ta karasa ba tare da ta kalli kowa ba har gaban Alkali, da kansa AIhaji Abdurrahman yace.."Ke ce Safiyya?"Na ma kasa magana sai kai na daga masa."To ina ki ka shiga?"hannu na daga na nuna imran na ce, "Ga wanda ya sace ni."Can na ji muryar Umma ta kira sunana na yi saurin juyowa ina kallonta ta hau nuna Kawun rukayya, sannan tace, safiyya ga mahaifinki..... 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Tuesday 13 December 2016

waye sanadi?? 81💘WAYE SANADI?💘 8⃣1⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf "Alh. Nasiru nine mahaifin su Rukayya yaran da ka shigar court kana tuhumarsu kan Batan 'yarka Safiyya, mun zo ne muyi magana ta fahimtar juna sbaoda bai kamata a ce da kimarmu da mutuncinmu mun je gaban aikali kan wata matsalar da mu a gamnmu in mun zauna mun fiiskanci juna za mu iya maganinta. Don haka muka zo mu yi magana ta fahimtar juna za mu yi kokarin shawo kan matsalar ba saimu je ga zuwa court." Ya dan tsaya ya sauke numfashi. Alh. Ibrahim ya karBa, "Na san ba za ka rasa sanin fuskokinmu ba, kuma bai kamata da kimarmu a idon jama'a a ce mun je gaban court muna karar junanmu ba, gara mu hadu mu yi maganin matsalar da kanmu."Alh. Nasiru ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Duk abin da ku ka fada haka ne, to amma a inda matsalar take shi ne har yanzu ba ku fadi inda matsalar take ba, kuna ta maganar mu fuskanci juna. In har maganar fuskantar juna ce nima ina son haka, tunda tun farko ni na so mu fuskanci juna mu yimagana cikin mutunci, amma hakan bai samu ba, ranar da na ga hotunan Safiyya a jarida ana cigiyarta na tashi da kaina na je wajen 'yarka Rukayya ta yi min bayanin ya aka yi Safiyya ta Bata, amma kwata-kwata ta kasa yi min magana saboda borin kunya.'Yarku ta munafince ni, zuwana biyu Lagos nemanta, kuma wajensu nake zuwa ita da daya kawar ta Sadiya bayan zuwa kullum cikin waya nake na tambaye su sun ganta, ko sun ji labarinta. Amma sai su ce min suma kullum cikin nemanta suke rana tsaka kuma na ga suna cigiyarta abun ya yi min ciwo. Kuna ganin sun yi daidai? Ya yi shiru yana kallonsu."Gaskiya ba su yi daidai ba, kuma mu ka ga ba mu san an yi haka ba. Sai da muka ce ya kamata a zo gidansu Safiyya a gaya rnusu Batanta, sannan take gaya mana wai tun kafun su tafi Lagos ta bar gida ta ce kuma ba za ta taba komawa ba. Wallahi Alhaji Nasiru tana gaya mana haka muka hau ta da fadan me yasa mu ba ta gaya mana ba. Kan Alh. Nasiru ya yi saurin katse shi da cewa, 'Wannan duk ba maganar da za a dauka ba ce, ni din nan a yanzu cikin zargi nake a kan Batan Safiyya, mahaifiyarta ce take zargina da SANADIN Batan Safiyya, don haka ni yanzu ba zan iya ce muku komai ba."Alh. Mukhtar ya ce, "Mu ma ba so muke ka ce mana komai ba, ilia muna so ka janye karar da ka kai zuwa court bai kamata a ce mun hau court ba kan matsalar da ina ganin za mu iya maganinta ba tare da mun yi wa kan rnu tirere a gaban dumbin dubatar alumma ba."'Ni kaina zan so hakan, to amma ba nine matsalar ba mahaifiyar Safiyya ce matsala. Safiyya amana ce a gare ni, don haka ya zama dole na tsaya tsayin daka na taimake ta a kowanne hali take.""Mu kanmu za mu iya taimakon Safiyya, Rukayya tana son Safiyya na yi imanin ba za ta taba cutarta ba, har ma Sadiyya. Don haka muke so kai yi wa mahaifiyarta magana ta yarda a janye karar, sai mu fuskanci maganar nemanta ba wai mu zauna bata lokacinmu a court ba."Zan yi wa mahaifiyarta maganar da muka yi da ku in har ta amince a janye zan so hakan."Shi kenan Alhaji Nasiru mun gode da karbar da ka yi mana, kuma mun ji dadin sauraronmu da ka yi." Har bakin darareriyar motar su ya rakosu,Tana zaune a falon ta rafka uban tagumi ga Hassan a gabanta yana jan kayan jikinta, amma kwata-kwata hankalinta baya wajensa ya tafi ga tunanin NANA SAFIYYA ruwan ranta. Ya shigo tare da yin sallama har ya Karaso gabanta ya dau Hassan.Rukkayya! Rukkayya!!" Ya kira sunanta.Ta dago a firgice ta gan shi a tsaye, cikin tausayin halin da take ciki ya ce, "Don Allah Rukayya ki bar tunani kar wani ciwo ya kama ki, insha Allahu Safiyya ta kusa dawowa gare mu."Ta daure zuciyarta suka gaisa."Ina Hussaini ne?"A takaice ta ba shi amsa da cewa "Sun shiga gidan Malam tare da Baba."Bayan ya zauna yake gaya mata zuwan su Alhaji Mukhtar. Ta dago tana kallonsa idonta cike da ruwan hawaye ta ce, "Meyasa ba ka tambaye su cewar 'yar tasu ta gaya musu inda ta kai Safiyya. Hawayen da suke cikin idonta suka gangaro zuwa dakalin fuskarta."Ki bar kukan nan Rukayya.""Duk ranar da ka ga na daina hawayen nan to ranar da na ga Safiyya ne, ranar hawayen zai bar idona. In har kana son farin cikina to ka zama SANADIN dawowar Safiyya gare ni, bana so mu yi wani sulhu gara mu je gaban alkalin.""Shi kenan Rukayya yadda ki ke so xa a yi, ko da sun dawo ba zan Kara sauraran su ba, kawai ma hadu a court, sai yanzu ma na kula da rainin hankaiin da suka yi mana 'ya'yansu munafukai ne na karshe, zuwana na karshe can Lagos yaran nan suka hadu har kuka suke ya zama ni nake ba su baki ina lallashin su."Umma ta ce, "Ban yi tunanin haka daga wajen yaran ba, ina musu kallon masu hakali da nutsuwa, ina jin dadin haduwarsu."'Hum, daman ba ka yabon dan kuturu sai ya girma da yatsu."Ita Rukayya tana ganina ta rude kwata-kwala ta kasa magana."Haka Sadiyar ma har yanxu ban ganta ba, don ko lokaicin da na raka yaron alkali ya kai musu sammace babanta ne ya leKo tun farko na fi jin haushin Sadiyar Ha ce ranar da na je rnakarantarsu nemanta ta ce ba ta nan rabon da su hadu tun ranar Jumma'a, kuma alhalin suna tare wai amma yaran nan suka rainan hankali." "Ni kaina farkon ganina da yaran nan bana tunanin haka daga gare su a fuskarsu akwai alama ta nutsuwa har ma da hankali, ashe a zuciyarsu ba haka ba ne."Har Baba ta dawo yana gidan. BAYAN KWANA BIYU Su Alh. Mukhlar suka dawo gidan Alh. Nasiru don jin inda maganarsu ta kwana. Tunda suka tura kiran sa suka ga canji da ya jima bai fito ba, har sun fara tunanin Kara tura kiransa suka hango tahowarsa yana waya. Har ya karaso bai gama wayar ba, yana karasowa kai tsaye ya shiga falon saukar baki suka bi shi a baya.Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya na yan wasu sakanni. Alh. nasir ya katse shirun da cewa 'Kamar yanda na gaya muku cewar zan je na gayawa mahaifiyar Safiyya zuwanku da yadda muka yi da ku, to na je na kuma gaya mata." Ya dan yi shiru yana kallon Alh. ibrahim.Shirun da ya yi ne yasa Alh. Mukhtar dagowa shi ma yana kalonsa, shiru babu wanda ya yi magana. Alh. Ibrahim ya ce,."To ya ku ka yi da ita rnahaifiyar Safiyyar?"Ya dan yi jini yana saka abin da zai fada, ya dan sauke marayan numfashi tare da daga hannunsa ya (dora akansa yana shafa gashin kansa. Sannan ya fara magana."Gaskiya Alh. Ibrahim mahaifiyarta ta ki amincewa mu yi sulhu na yi duk iya yina taki yarda ita tana tunanin su suka batar da Safiyya, kuma ko ni kaina ina tunanin haka, ina ganin abin da zai fi ku je ku kara tambayar yaranku su fadi inda suka boye ta, ni zan yi d'awainiyar. zuwa taho da ita. Ina ganin haka zai fi zama alkhairi a gare mu, in har suka fadi inda suka bar ta, ni kuma na yi muku alkawarin gobe zan yi waya a janye karar."Alh. Mukhtar ya dago cikin fushi ya ce, "Na gane nufinka ka fito ka ce ba a janye karar'ya'yanmu daga court ba kana magana kamar ta yara, waye ya gaya maka su suka boye yar matarka? Idan kana da shaidar hakan ka fadan mu kuma in har ka ba mu cikakkiyar shaidar da ta nuna su suka boye 'yarka mun yarda ka kai kararmu kowacce court da ke duniya don yanke mana hukunci. Mun zo maka da sul...."Kan ya karasa ya katse shi da cewa, 'Tabbas ina da shaidar da zan tabbatar da haka, kuma ku kanku kun san 'ya'yanku ba su da gaskiya, don haka ku ke neman sulhu cikin gida ba tare da mun je gaban court ba. Bara na gaya muku gaskiya ko da babarta ta yarda a janyc kararku a court ni ba zan yarda ba."Alh. Ibrahim ya tari numfashinsa da cewa, 'Mu daman haka muke so mu ji daga wajenku, Allah yana bayan mai gaskiya." Ya mike. "Kawu taho mu tafi."Yana fadar haka ya fita daga falon. Alh. Mukhtar ya mike jikinsa a sanyaye har ya kai bakin kofa ya juyo yana kallon Alh. Nasiru ya dan yi murmushi sannan ya ce.'Alh. Nasiru ba mu yi tsammanin haka daga wajenka ba, amma babu komai."Yana fadar haka ya fita daga falon.Tunda suka sbiga mota babu wanda ya yi magana kowa da abin da yake sakawa a ransa, har suka karaso gida a gate Alh. Mukhtar ya sauke Alh. Ibrahim.Tana zaune a falo tana karatun Alkur'ani ya shigo."Abba sannu da zuwa."Bai amsa mata ba ya hau sama. Jikinta a sanyaye ta mike tana shiga daki ta ji kiransa ta fito da sauri. Yana zaune a falo har Hajiya, ta karasa gabansa ta zauna muryarta na rawa ta ce, "Ga ni Abba."Ya dago fuska a hade cikin tsawa ya ce, "Ki gayan gaskiya ina ki ka kai Safiyya?"Wata irin dagowa na yi ina kallonsa, ita kanta Hajiya dagowa tayi. "Abba ban gane nufin k aba yayi saurin katse ni da cewa, "Tun muna mu biyu da ke ki gayan gaskiya me ya faru da Safiyya?" 'Wallahi Dady ban san me ya faru da ita ba, mun fita da Sadiyya muka dawo ba mu ganta ba sai yanzu da na dawo na ga wasikar da ta yi min cikin Jakarta."Ina maganar ina kuka; Ya juyo wajen Hajiya Hassana ya ce, "Me ki ka sani dangane da Batan Safiyya ki gayan tsakaninki da Allah Cikin rnarnaki Hajiya ta ce, "Alhaji wani abun ne ya faru ka ke wannan tambayar?""Babu abin da ya faru ina so na san gaskiyar inda yarinyar mutane take, kar mu yi wahalar banza a court a zo a tsananta bincike a kama mu da laifi saboda na fuskanci iyayenta suna ganin kamar ku ku ka boye ta, ko ku ka batar da ita. Don haka nake so na ji gaskiyar abin da ya faru da ita."Na dago ina hawaye na ce, "Wallahi Abba iya gaskiyata na gaya maka, a ranar da za ta bata sai da muka yi fada muka shirya a lokacin kuma duk akan ta ce ba za ta koma Kano ba, muka yi fadan bayan mun shirya muka fita da sadiya shine dawowarmu muka tarar bata nan bayan na dawo ne na duba jakata shine na tarar da wasikanta da sauri yace yanzu ina wasikar? yana wajen hajiya ya juyo wajenta kan yayi magana ta mike bata fi min ti biyu ba ta dawo dauke da farar takarda mai dauke da rubutun nana safiyya bayan ya gama karantawa, ya dago kansa yana murmushi ko wanan takarda ta ishe mu shaida in ya ishe shida in yaso alhaji nasir yaje can ya nemo WAYE SANADIN batan yarsa kan ya karasa salim ya shigo bayan sun gaisa da abba ya ce ke kuma sarkin daukar magana me ya saki kuka ko kina tsoron haduwarku da manta sabo (alkali) ne? ya dan yi murmushi maganin kwashe-kwashen kawaye kenen kallo daya zakayi masa kasan yana cikin tsantsar farin ciki, ***** ***** ***** ***** ***** shi daya cikin mota sai faman murmushi yake ji yake kamar anyi masa bushara da gidan aljanna ya karya kan motarsa ya shigo layin gidan mallam kalil tun daga kofar gida ya hango manyan motoci ya karasa ya yi fakin. ya shigo tare da sallama malam kalil yana ganin shigowarsa ya hau murmushi ya karasa har kasa gabansa ya zube bayan ya gaishe shi ya juyo wajen mutanen da suke gaban kakansa tsoho mai ran karfe kaki ka mutu araba mana gado ko sai kaga jikokin imran naka ne? 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

waye sanadi?? 76--80[12/8, 8:34 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣7⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf 'Ni dai gaskiya Yaya ban san shiga ka kira maigadi ya dauke shi." Cikin tsawa ya ce, "Baki da hankali za ki ce mai ya zo ya dauke shi." (Allah Sarki maigadi ba mutum ba!!!). Ta yi saurin fitowa ta dau Hassan wanda yake ta sharar barcinsa hankali kwance. Tana zuwa falon ta shi ta fito. Ya bi bayanta da kallo tare da murmushi.Tana zaune a kan sallaya yashigo, ba ta ko dago ta kalli mai shigowa ba tunda ta riga ta san babu mai shigowa sai BABBAN MAK1YINTA IMRAN. Ya karaso ya zauna a gabanta. "My wife ya gida? Bai damu da rashin ba shi amsa ba, ya ci gaba."Yau na zo baki mamaki maza taso ki ga kyawawan, kannenmu masu kama da ke Ummanki ta 'Haifa mana yau ga Ummanki a gidanmu ita da Daddy da auta sun zo nemanki, taso ki gansu."Yana maganar yana kokarin kama hannuna, ban san lokacin da na daga hannuna na zabga masa mari ba ya rike wajen cikin mamaki."Safiyya Imran ki ka mara?" Ya fada yana nuna kansa cikin tsawa. Na ce, "Na mara ka yi abin da za ka yi a…. Kan na karasa na ji kukan yaro a falo. Da gudu Imran ya fita ashe tsawar da na yi ce ta tada Hassan har ya fado daga kan kujera. Ya shigo da shi yana kuka 'Safiyya kin ga kin tashi Hassan, kalli ki ka ga wallahi kamar ku daya." Kuka Hassan yake sosai yana kuma mikon hannu don na dauke shi. Nan take na ji tausayin yaron tare da Kaunarsa sun cikan zuciya. Ina kuka nasa hannu na karbe shi, Swan na dauko na ba shi ya sha sosai, na hau jijjiga shi bar ya yi shiru. Bakin gadon na samu na zauna yana hannuna barci ya dauke shi. na ji maganar, Imran.Tabbas ba ni da matsala wajen raino, Safiyya ta za ta yi wa 'ya'yanmu raino mai kyau; barana dauko hussaini ki gan shi. Yau da na ga Umman Safiyya kamar ku daya daman Khadija Ce kamurmu daya kin ga nima ina kama da Umma." Ya fitaa ya dauko Hussuini.Na yi tunanin babu wani yaron, na dago kaina idona cike da ruwan hawaye. na ce, Ka gayan gaskiya wadannan yayan waye ko su ma debo su ka yi ka cucesu?"Yana dariya ya ce. "haba Safiyya duk shaidar zaluncin da ki ke min ba zan iya zaluntar yaran da nake so ba, nake kuma fatan ki haifar min irin...."Hararar da ya ga na wurgo masa ce ta hana shi karasawa."Allah ya tsare ni hada iri da kai. ina tambayarka ka gayan 'ya'yan wa ye?" "Na rantse miki da girman Allah Safiyya su Hassan Kannanki ne Ummanki ce ta haife su, a yanzu haka Ummanku tana gidanmu tare da Alhaji Nasiru sun zo nemanki sun ga jaridar da hotanki yake ana nemanki. Allah Sarki gidansu Momy suna sonki sosai, amma ke kina son jefa rayuwar ki cikin gagari." Na dago kaina da sauri ina kallonsa, kwarjininsa yasa na sunkuyar da kaina Kirjina yana bugawa wanda ban san dalilinta ba."Alhaji Nasiru yana shirin shigar da Karar RuKayya da Sadiya har ma da iyayensu za a fara shari'a a kan Batan ki na kuma tabbatar in har SU RUKAYYA suka je gaban alkali ba su da ta cewa, zaki sasu cikin tashin rigima da tashin hank...."Na katse shi c'ikin kuka, 'Ka cuce ni Imran ba zan taba yafe maka ba. in har aka yi wa su Rukayya wani hukunci ba su ji ba, ba su gani ba. Wallahi bazan taba yafe maka ba, bana kaunar ganinka k'a warga za min duk wani farin cikin rayuw...."Kan na karasa ya katse ni. "No Saf'iyya kar ki doran laifi ni din Imran taimakar ki na yi da na tsare ki. in da kin tafi ba ki san hannun da za ki fada ba. in har ki ka amince aka daura mana aure zan saka hannu na tattara miki duk wani farin cikinki da a baya ki ke fadan Imran ya warga za to zai dawo miki da shi. Ina sonki Safiyya, Rukayya tana sonki. ki taimaka ki daure mu ci gaba da rayuwa."Ina kuka na ce, "Ba zan aure ka ba, Allah ya tsare ni da auranka, kuma wallahi ba zan ba ka yaran nan ba ko za su yi kukan jini sai ka fitar da ni daga gidan nan na gaji da zama da kai in kashe ni za ka yi gara ka kashe ni na huta da bakin cikin kallonka.""No my life, ba zan kashr ki ba illa zan bar ki a gidan nan mu ci guba da rayuwarmu." Wayar shi ta yi kara ya zaro. "Hello Khadija." Can bangarrn ta ce, "Yaya na dawo gani a bakin gate."Okey ina zuwa." Ya katse wayar ya juyo wajena. "Ba ni kannena mu tafi."Cikin kuka na ce, "Allah ba zan ba ka su ba sai ka fitar da ni daga gidan nan, "Hum Suffy tawa bara na zo na mayar da ke lazy, sai na kar be su ta ruwan sanyi, daman na yi kewarki tun ranar dana sha dadi! kina barci har yanzu ba a kara kula ni ba." Yana maganar yana kokarin cire riga,Cikin kuka na ce, "Ba zan hana ka aikata abin da ranka yake so ba, amma wallahi ka sani duk ranar da haka ta kuma faruwa a tsakaninmu sai na kashe kaina. Daga yau ba zan kara cewa ka fitar da ni daga gidan nan ba, mu zauna har karshen rayuwarmu, ni na san duk daran dadewa zan fita daga gidan nan, kuma wallahi Imran muddin na fita daga gidan nan sai na jefa rayuwarka cikin tashin hankali, wanda za ka yi dana sanin zuwa duniya har ka san wata Safiyya, mugu azzalurn...."Kuka ya ci karfina na kasa karasawa. Bai kara magana ba ya karBi su Hassan ya fita. Sai da su Umma suka yi kwana biyu a Lagos suna neman Safiyya duk wani asibiti da makaranta babu wanda ba su je ba, har da Hajiya Amina ake yawon, ga kuma uban tafiya Imran. Hankalin Umma ya yi mugun tashi.Yau karfe hudu Imran ya shigo gidan babu kowa sai Umma da Hajiya Amina wadda take cikakkiyar Barrister mai zaman kanta, babu abin da take sai bawa Umma hakuri tare da kwantar mata da hankali Bayan sun gaisa yace "U'mma ina ganin duk yadda aka yi kawayenta sun san inda take yana da kyau a mika su kotu lallai-lallai su fadi inda take.""Ni kaina abin da nake tunani kenan.Cewar Hajiya Amina."Rukayya na miki alkawarin tsaya muku har sai sun fadi inda suka kai ta, bara Alhaji Nasirun ya zo mu yi magana."Suna cikin maganar Khadija ta shigo tare da su Khalil da gudu kowa yana kokarin daukar su Hassan. Kwata-kwata ba su kula da Imran ba, sai tsa warsa sukaji."Ba ku da hankali sai ku shigo daki da gudu har kuna taka mutane."Tunda ya fara maganar Salim da Khali! suna kame a wajen. Salim ya dago muryarshi na rawa ya ce, Sorry brother."Ya kara matse gira, "Malamai ku fice a dakin."Khalil ya kai hannu zai dau Hussaini, Khadija ta ce, "Au kai ba ka ji maganar yaya ba, ba cewa ya yi ku fita ba.Tana maganar tana murmushi ya girgiza kai ya juya. Ta juyo wajen Imran. Brother yanzu muka yi waya da yaya yusuf yana nan zuwa weekend tare da yaya babba dukka tare zasu taho "Kai Sister ban san karya fa. Dazun munyi waya da big brother har ya ban muka gaisa da Anty Hafsa basu gayan za su zo ba.'Allah Brother ba da wasa nake baita ma bai gaya mata ba , kuma kira my lowly sister ka tambayeta ""Shi kenan sister in na fito ma yi Magana yanzu muna wata maganar. Su Hassan ta dauka ta fita Ya jima suna tausar Umma har alhaji nasir ya dawo. Nan Imran ya gaya masa abin da suka yanke "Nima haka na shirya kuma tun a kano mu ka yanke shawaran kai su kara, kuma na ji dadin wannan taimakon da Hajiya Amina za ta yi mana. "Ina ganin wata makarkashiya suka kullawa Safiyya dole su fito da ita duk inda suka kai ta gobe zamu wuce Kano, da na koma zan shigar da karansu court sai na kira na gaya maku ranar da za a fara zaman courtu."Shi kenan Abba ni kaina zan zo tare da Momy bara na je na yi wasu Hassan tsaraba." Ya mike yana kiran Khadija tare suka fita dasu Hassan.Khadija ce take tuka motar. Imran yace sister muje ki kaini gidan da kika kai ni rannan."Yaya mu da muke sauri.""Haba sister duka minti biyu zan yi "Allah ka wuce minti biyu sai na gudu na barka eh 'Nayarda sister. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/9, 7:50 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf Ya fito hannunsa rike da Hassan, tana can karshen gado zazzafan zazzabi ne ya rufe ta sai rawar dari take. Ya shigo dakin."Safiyya ga su Hassan za su yi niiki sallama gobe za su koma Kano."Yana maganar yana kwantar dashi ya fita. Tunda yake maganar ta dago kai da ta ji motsi a kusa da ita ta yi saurm janye bargon daga fuskarta. Tabbas Hassan Kaninta ne babu abin da ya raba su da ni. Jin da tayi ana taba mata fuska yasa ta tashi zaune tana daukarsa ta ji hawaye yana zubo mata ba ta san lokacin da bakinta ya furta."Hassan ina Ummata?" "Umma tana nan cikin kewarki da kin daure an daura mana aure, don Allah Hussaini kusa baki Antynku ta yarda ta aure ni." Yana maganar yana kalonta, wayarsa ta hau kara ya zaro cikin aljihunsa. Ya jima yana waya har ta gama daukarsa bai kula ba tana ganin zai juyo sai ta kau da wayar. Ya juyo yana kallonta,"Kalli yadda ki ka rame Safiyya kamar ba ke ba, don girman Allah ki canja kayan jikinki ba zan so ganinki a haka ba, please my wife..."Karar wayarsa ya hana shi karasa abin da yake son fada. Yana gama wayar ya dauke su Hassan suka fita."Kai yaya ka je ka yi zamanka da badon su Hassan ba da tuni na yi tafiya ta."'Sorry Sister ina shirin fitowa ki ka kira." Khadija ta dan juyo ta kallon imran ya daga mata gira ya dai kanwata ta numfasa"'Ni ko yaya ina ganin tsare Safiyya daka yi ba shi ne zai magance maka matsar ba .cikin razana ya dago alamun rashin gaskiya "Khadija wa ye ya gaya miki na tsare Safiyya? Hmm yaya duk cikin yan uwana babu wanda muka shaku sama da kai, ko Aysha da muke twins ba mu yi shakuwar da muka yi da kai ba. wanda haka ya sa babu halinka da ban sani ba. Kai ka Boye Safiyya tana wajenka cikin wannan gidan. kana ganin halin da iyayenta suka shiga, amma kwata-kwata ka nuna ba ka santa inda take ba. ba'ka tunan wata rana gaskiya zai bayyana Safiyya ta amince maka amma iyayenta su ki aminwa tunda ka riga ka boye musu gaskiya a baya i am sorry' in na bata maka rai ta karasa maganar cikin taushin murya. Yayi kusan minti uku yana tunani, can ya dago kai yana murnmshi."No Sister, baki bata min rai ba-shawara ki ka ba ni. kuma na gode; amma na yi mamaki ya akayi ki ka gano yayanki. Khadija na rasa ya zan yi da rayuwa, ni kaina ina tunanin haka. amma Khadija ina ganin haka shi ne magani don wallahi ina kaunar Safiyya bazan bari ta subuce min ba "To amma...." Ya yi saurin katse ta da cewa"Sister na yarda da ke ki riken amanata maganar safiyya ta zama daga ni saike in mun koma gida zan gaya miki me yake faruwa tsakanina da Safiyya kada kimin kyakkyawar fahimta." Da haka babu wanda ya Kara magana har suka shiga cikin kasuwa kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa **** **** **** ******* ******** Tana zaune a falon babu kowa sai ita daya. Gashi a zahiri kallo take, ita kam hankalinla yana ga tunanin suhibarta Safiyyah mai gadi ya shigo tare da yin sallama ta dago a gigice tana kallonsa. 'Ranki ya dade barka da hutawa."Fuskarta a hade ta amasa saboda yanayinsa na san wasu. "rakiya rikakkiyar kubewa ana hutawa ne?"Ta dago kai. ya hau dariya."Ni kam inda za a sakar..."Kafin ya karasa na katse shi cikin fushi na ce. "Mallam ka fara abin da ya kawoka,ka cikan kunne. wato sai ka ga su Hajiya ba sa nan ka ke zuwa ka dame ni da surutun banza na gaya maka bana son irin wannan banson surutun wallahi zan hada ka da Abba ko yaya Isah. Fadi abin da ya kawo ka ka fita."Allah ya huce zuciyar Hajiya sako ne na kawowa Alhaji tun jiya wasu mutane suka kawo a ba shi." To ba zan karba ba ka bari in ya dawo ka ba shi." Ina fadar hakan na mike. ban fi minti goma da shiga dakina ba wayata ta yi kara."Hello, Sadiya kina lafiya?" Ta amsa mata da lafiya, Rukayya don Allah in kina gida ki zo akwai matsala.Da sauri na ce, "Me ye yake faruwa?"Kar ki daga hankali wayata babu caji in kin zo kya ji." Kan nayi magana wayar ta katse.Key din motata na zare ina fitowa muka hadu da Hajiya.'Har kun dawo?"'Mun dawo, ke kuma ina zaki? ""Hajiya yanzu zan dawo."Ba wai yanzu za ki dawo nake tambayarki ba, ina tambayar in da za ki ne?''Hajiya gidansu Sadiya za ni fa.""Allah ya kiyaye hanya."'Amin Hajiya."Har Babansu Sadiya yana gida dukkansu sun yi jugum-jugum kamar an musu mutuwa. Na shiga tare da yin sallama, muka gaisa na juyo yana kallon Sadiya wadda take kuka, da sauri na ce"Sister me ye ya faru?"Ta dago fuska cikin kuka ta ce, "RuKayya dazu aka aikowa da Baba sammace a kotu."Ya yi saurin cewa, "Kar ki kara cewa aka aikon da sammace ke da ki ka daukowa kanki ke aka aikowa da summace, babu abin da zai kai ni kotu wallahi sai dai ke ki je in ma rike ki za su yi har sai kin fito musu da 'yarsu babu ruwan Adamu.""Baba don Allah ka yi hakuri Sadiya wa ye ya aiko?"Alhaji Nasiru kan Batan Saffiya ya ce ni na boye ta." What? Na fada tare da zaro ido. Na juya wajen babar su Sadiya wadda suke kira da Gwaggo ina neman Karin bayani kan ta yi magana wayata ta yi Kara na zaro da sauri. "Hello Abba."Can Barin ya ce, "RuKayya kina ina ne?" Na ce Abba na je gidansu Sadiya, gidansu Safiyya sun aikowa su Sadiya takarda daga court ana kararta wai Safiyya tana wajensu sun boye ta,"Yana dariya ya ce, "Mu ma nan sun aiko mana da ita, ki zo gida yanzu kawunki yana san ganinki, ki kuma gayawa Sadiyar ta kawar da hankalinta kar ta damu.""Shi kenan Abba bara na dawo. Sadiya kar ki damu yanzu Abba yake gayan nima an aikon mana daga court bara na je gida." Na juyo ina kalon baban na ce."Haba kar ka damu babu abin da zai same ku mu ma lawyer ne nan da wasu 'yan lokutan bara na je gida zan kiraki ta waya anjima." Ina fadar haka na mike.Suna zaune a falo na karasa gaban Kawu jikina a sanyaye kaina sai faman sarawa yake."a a yana gan ki kamar ba ki da lafiya?" Na girgiza masa kai na ce Kawu an yini lafiya? Ya amsa da lafiya lau. Na juyo wajen Abba na ce, "Abba yanzu mu ake zargin mun 6atar da Safiyya har aka kai mu court." Ina fadar haka hawaye ya zubo min. 'Me ye abin kuka Kar ki dami kan ki har abada TAIMAKO ba zai taba zama CUTA ba, na san in da ki ke kaunar Safiyya bazaki taba cutar da ita ba. Daman na yi tunanin haka za zata faru, "Kawu ni kuma ina tunanin ba mu da mafita a kan 6atan Safiyya mu da Sadiya mun yi wauta sau biyu Daddynta yana zuwa Lagos nemanta muna 6oye ta, ni ban so aka yi cigiyarta a mujalla ba."Abba ya ce, "Hajiya ta gayan labarin da ki ka ba ta akan Safiyya, ni kaina na ga wautar ku, amma tunda abu ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba.Kawu ya ce, "Ina, ganin kan a yi zaman court ya kamata mu je wajen shi Alhaji Nasiru mu yi magana ta fahimtar juna da shi, mu din ba yara ba ne dukkanmu manyan mutane ne, in ta kama mu yi sulhu sai mun yi babu mutunci mu je gaban court."ta mike jikina a sanyaye ina shiga daki na yi kiran wayar, tana shiga ya daga."Assalamu Alaikum, Anty Rukayya kina lafiya." "Lafiya kalau Imran, ya gari?" Duk lafiya Rukayya bar yanzu ba su Kara kira ba?" 'Wallahi Imran har yanzu shiru sai kuma wata rigimar da ta taso mana." 'Ban gane ba.""Imran an kai kararmu court mu da Sadiya ana tuhumar mu da 6atar Safiyya."Cikin mamaki ya ce, "Wa ye ya kai ku court?" 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/10, 7:49 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf "Mijin Umman Safiyya, Alhaji Nasiru ne ya kai mu, kan.." Ya yi saurin katse ni. "Ita Safiyyan ina mahaifinta?"in zan baka labarin safiyya zamu dade har kudin wayarka ya kare Ya yi saurin cewa,karki damu rukayya waya ta da kudi Ba tare da wata damuwa ba ta ba shi labarin da Safiyya ta ba ta, Ya fi miniti uku baiyi magana ba. Na ce, "Imran ka yi shiru ko ba ka jina?"Ya sauka wata nannauyar ajiyar zuciya.'Rukayya ni kaina ina cikin matsala."cikin rashin fahimta nace Imran ban gane kana cikin matsala ba "Rukayya na san Alhaji Nasiru har ma Abban duk 'yan gidan na san su abokin Daddyna ne abun da baki sani ha, yau kwana uku da dawowar Alhaji Nasiru bar ma da Umman Safiyya daga gidanmu sun je neman Safiyya, kuma Momynta ita tasa a shigar da ku kara, ita Alhaji Nasiru ya dauka a matsayin lauyarsa duk ranar da aka fara zama a court ni kaina sai an neme ni, kin ga ni kaina ina cikin matsala," Ya karasa maganar cikin murya mai cike da tashin hankali.Muryata cike da tausayinsa tace, "Kar ka damu zan yi wa Abbana magana ba za a saka ka a shari’ar ba. Kai dai ka ci gaba da dubanta a can din.""Hum, Rukayya ba ki san halin da nake ciki ba kullum ina hanyar neman ta, kuma Rukayya ba ki san wani abu ba. "Sai ka fada." Na ce da shi.Ya kara saukc ajiyar zuciya karo na biyu."Momyna ta ce tana so na rako ta, kuma na san in har muka hadu da su Abba za su gane ni, har ma suyi min magana."'A'a Imran ban gane nufin ka ba, kana nufin kwata-kwata ba mu san ka ba?"Kai saye ya ce, "Inda dama ina san hakan.""gaskiya hakan ba za ta samu ba, don kun gaisa da su Abbana sai a tuhume ka.""Shi kenan Rukayya na gode, kin ga kudin ko na turo miki ta account dinki?"Na ce, "Na gani Imran tunani nake ma zan dawo maka da kudin tunda har yanzu ba su kara kira ba.""No Rukayya, ki bar su na san wata ran za su kira kullum ina addu'ar Allah yasa su kara kira a ba su su dawo mana da ita.""Amin don girman Allah."Khadija ta zama kamar mutum-mutumi a gaban yaya Imran tun bayan da ya gama gaya mata abin da ya faru tsakaninsa da Safiyya.Ta sauke wani gwauron numfashi, sannan tasa hannu ta goge gumin da ya yi wa fuskarta kawanya, kwata-kwata tunaninta ya gudu duk yadda Khadija ta shahara wajen warware matsala yau ta gaza nemar wa yayanta gagarumar matsalar da ya dauko, ta ma rasa ta inda za ta fara magana.Yana murmushi ya ce, "Sister kin yi shiru, ina alfahari da kasancewarki kanwa a gare ni Khadija wajen ba ni shawara mai amfani da kuma samar mani mafila, yanxu ma gani gabanki ina neman mafita da shawara da fatan ba za ki zuban kasa a ido ba."Hum, Brother na, rasa ina mafita gaskiya, ka yi ganganci haka da ka dauke safiyya bashi ne mafita ba. Ina ganin hakan da ka yi shi ya kara dasa tsanarka a zuciyarta. Shawara daya zan ba ka Brother ka fadawa Safiyya gaskiya in har ba ta yarda ba shi kenan Brother sai ka hakura da ita. Ina ganin ba ita daya ce mace ba, babu yarinyar da za ka ce kana so ta ce ba ta sonka,kawai ka hakura da ita ka cire ta a ranka."Ya hau girgiza kai, "Khadija ba zan taba iya cire Safiyya daga raina ba, ba zan iya ba! Ba zan iya ba!!" Yana maganar yana girgiza kai. 'Har abada ba zan iya cire kaunar Safiyya daga raina ba. Daina son Safiyya kamar daina numfashina ne wanda haka yana nufin mutuwa. Please Sister ki taimakan ina son Safiyya sosai in na rasa ta na yi imanin sai kun rasa ni."'In Allah ya yarda ma ba za ka rasa ta ba, balle har mu zo mu rasa ka. Ka fara gwada wannan shawarar in ba ta yi ba sai mu nemi wata, zan taimaka da addu'a Allah ya saka mata kaunarka a ranta har ta rasa ina za ta ajiye kaunarka a ranta."Yana murmushi ya ce, "Ameen kanwata ina fatan ki rike min sirrina ya zama daga ni sai ke, kar wani ya ji sirrinmu, zan je na gwada shawararki."Tare suka fito ya shiga cikin dakin Hajiya Amina. "Momy sannu da hutawa." Au kana dakin Khadija na yi tunanin ka tafi." Yana murmuslii ya ce, "Ina ciki rnuna shawara." 'Kuna shirme dai.""Yauwa Momy wai yaushe Dady zai dawo?" "jiya ina sallah ya kira ban daga ba, to yau kuma sai kira nake ta ki shiga. Ina tunanin saura sati biyu ya dawo. Kana sa ne da tafiyarmu Kano rana ita yau?" "Au Momy ranar Monday za a fara shari'ar?" "Ranar Monday za mu fara, har Khadija ta gayawa Aysha za mu zo Kano da kai dazu muka yi waya da Hajiyar sabon gida sun fara damuna yaushe za mu taho." Yana dariya ya ce, "Nima shckaran jiya na kira nake tambayarta ina tsohon mijinta na ce ta gaya masa in dai na zo Kano sai na karasa shi, tunda ya ki ya mutu mu ci gado.""Hum maza Abbanku ya ji kuna fadar haka, shi bazai so ya mutu ba."'Allah Momy ya dade shi da Malam."'Ai ka dawo kaina, to tashi ka fita. Kai da yan uwanka kuncinye uwata, shi ma malam din cinye shi za kuyi Ya mike yana dariya."Momy sun sha miya gara su mutu."Kan ta yi magana ya fita da sauri.Babu abin da ka ke ji cikin dakin sai sautin kukana, ina can a karshen gado. Yau kusan .kwana biyu ban ga Imran ba. Duk wata dabara da zanyi don na bar gidan nan na yi, amma ban yi nasara ba. Tun jiya nake fama da zazzafan zazza6i ban da karkarwa babu abin da jikina yake sai kuma sautin kukana da yake tashi.Ya turo kofar tare da yin sallamaduk tsananin kiyayyar da nake wa muryarsa a duk lokaci. da ya yi sallama saina amsa masa a zuciyata. Ya karaso gefen gadon ya zauna. Hannu yasa ya janye bargon ganin fuskata sharkaf da ruwan hawaye cikin kidimewa ya ce."Safiyya me ye ya sa ki kuka?"Ban iya bude baki na yi magana ba saboda azabar da kaina yake. Hannu yasa ya dago ni da nufin na zauna, kwata-kwata babu karfi a jikina ganin ina kokarin komawa na kwata yasa ya yi saurin kwantar da ni ya kai hannunsa zuwa kaina cikin tashin hankali ya furta."Ya Salam! Sannu Safiyya."Ya yi saurin mikewa ya fita, na bi shi da kallo ido cike da hawaye. Bai fi minti biyu ba ya dawo."Daure ki sha magani za mu yi Magana mai muhimmanci Ban yi musu ba na kar6a na sha. Flask din da ya shigo da shi ya jawo ya dau plate. Tuwon shikafa ya zubo ya miko min. Nan ma ban yi musu ba na kar6a, rabona da wani abu mai nauyi tun ranar da ya tafi. Ina gamawa na ji wani nannauyan barci ya kawon ziyara.Kamar a mafarki na dinga jin muryarsa yana karatun Alkur'ani, na bude idona a hankali na hange shi kan sallaya kan-shi a sunkuyc yana kallon Alkur'ani cikin zazzakar muryarsa yake karanta suratul Nisa'i. Na yi yunkurin tashi don shiga toilet ya dago yana kallona, muna hada ido na zabga masa harara na shiga toilet.Wanka na yi na dauro alwala, yana ganm fitowa ta ya mike daga kan sallayar, ina idarwa ya juyo wajena. Cikin taushin murya ya ce."Safiyya ki sauraran don Allah za mu yi magana, ina fatan za ki nutsu ki saurari abin da zan gaya miki."Yana magana yana kallona, na yi saurin dauke kaina gefe. Ya ci gaba da cewa."Ina fatan abin da zan gaya miki za ki yarda da shi, kuma ni a zuciyata zan gaya miki gaskiya ne, har ga Allah in kuma na miki karya ina fatan Alltah ya miki sakayya a yanzu-yanzu ga kuma Alkur'ani mai tsarki zan dafa. Kin san dai hukuncin wanda ya yi rantsuwa da Alkur'ani har ya dafa shi.""Kai!" Na yi saurin katse shi cikin tsawa na ce."Ka cikan kunne fa ka fadi tatsuniyar ka ka tafi, ga shi dai a fuska kamar ba azzalumi ba.""Ki bar kirana da azzalumi har a zuciyata haka nake babu zaluncin kowa a raina. Bana zaluntar ,kowa ba kuma na kaunar na zalunci kowa. Ke ma a yau nake zaton na wanke kaina daga zargin da ki ke min na Azzalumi."Murmushin da ke kan fuskarsa ya bace, ya sauke numfashi kamar wanda ya tashi daga barci. Ya fi minti uku bai yi magana ba, can ya Kara sauke numfashi karo na biyu ya ce."Safiyya na rantse miki da girman Zatin Allah ban aikata abin da ki ke zargin na yi miki ba."Da sauri na dago kai cikin sarkewar murya na ce, "Ban gane abin da ka ke nufl ba, kana nufin ka ce ba ka yi min fyade ba?'Ya dagan kai cikin dakiyar zuciya ya ce, "Ban miki komai ba Safiyya, wallal ban aikata abin da kike zargina da shi ba. Abun da ki ka ga ya faru lokacin da kika farka na yi haka ne don a tunanina za ki yarda ki aure ni sai na ga hakan bai sa kin amince za ki aurc ni ba,don haka na gaya miki gaskiya in "Kan ya Rarasa abun da yake san fada na katsc shi da cewa.Imran wa za ka mayar mara hankali."Na yi murmushin da ya fi kuka ciwo.Kar ka mata imran ba da 'yar shekara sha uku kake magana ba, da 'yar shekara ashirin da biyu ka ke magana. Na taka matakin jami'a har na yi gogayya da irinku, dadin bakinka ba zai maka wani amfani ba gara ka hakura na riga na barka da Allah, ina fatan ya yi min sakayya da gaggawa ka"Na san ba za ki yarda ba, bara na yi miki rantsuwa ta karshe."Hannunsa ya daga ya dora a kan Alkur'anin da yake gabansa, sannan ya ce, "Na rantse da girman Zatin Allah Safiyya ban miki fyade ba, idan kuma na yi miki Allah Ka gaggauta saka miki don girman Ka."Yana fadar haka ya dauke hannunsa daga kan Alkur'anin ya ci gaba da cewa, "Ki yi tunani Ssafiya ya za a yi a cc na kusancc ki ba ki ji wani canji a jikinki ba?" Ya mike tsaye. "Ki zauna ki nutsu ki yi tunani babu wata 'ya mace in dai kamilalliyar yarinya ce da namiji zai kusance ta ba ta ji wani canji a jikinta ba, in kuma za ki yi tunani na kusancc ki ba kya cikin hankalinki, amma kin san in har kin tashi za ki ga alama. Ki gayan tsakaninki da Allah in kin ji wani canji ko wata alama ta hakan ya faru, ni kuma na yarda ki min duk hukuncin da ki ka ga ya dace da ni. Zan karBa zan kuma amsa laifina a yi min duk hukuncin da ya dace da ni."Yana fadar haka ya fita ya bar ni cikin sanyin jiki da fadawa cikin zuzurfan tunani. Me yasa ban yi tunanin haka ba? Ya aka yi Imran ya fi ni hangen nesa? Me yasa kwata-kwata ban yi tunanin haka ba? Tabbas abin da Imran ya fada gaskiya ne babu yarinayr da za a kusanta ba ta ji wata alama ba, kuma ni kaina na san haka. Me yasa ban yi tunanin ba? Kai tsaye na bawa kaina amsa da cewa tashin hankali ne ya hana ni tsinkayar hakan babu wani canji ko alama da na gani a jikina. Akwai lokacin da na yi tunanin haka, arnma zuciyata ba ta ba ni goyan baya ba, don haka na cire tunanin bincikar wani yanayi a jikina ba. To me ye manufan sa na nunan ya kusance ni? Me hakan yake nufi? Me ye dalilinsa na tsare ni a nan gidan? "Tabbas Imran bai kusance ni ba."Na furta a fili tare da sakin wata siririyar dariya wadda ni kaina ban san ta fito ba. Allah na gode maka da…..to be continue soon!!! 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/11, 8:27 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf Ka tsare ni a hannun wannan azzulumin na mike da sauri na shiga toilet. Sai bayan sallar Magriba ya dawo ina zaune ina karatun wani littafi tun na Momy ne. Zama ya yi a kasa, kwata-kwata ban dago kai na kalle shi ba. Hannu yasa ya karBi littafin ba tare da na ga tahowar hannun sa ba."NI NA YI kaina?" ya furta a hankali bayan ya kalli bangon littafin."Shi kuma haka sunansa yake, ba ni labari me littafin ya kunsa kinji kanwata Na dago fuskata cike da murmushi, abin da imran bai taba gani ba gani yake kamar a mafarki ya yi saurin rufe ido tare da budewa. Kan ya dawo daga duniyar mamaki ya ji maganata cikin taushin murya na ce.'Imran na yarda da abin da ka fada ka yi hakuri zargin da na yi ma don Allah."Saboda tsabar mamaki ya ma rasa bakin magana. Na kara cewa, "Ka yafe min Imran." Kur! Ya zuban ido ya ma kasa magana. nan da nan raina ya baci na yi kamar na tashi na shake shi don tsananin kiyayyar da nake masa na dai daure zuciyata don cinma burina."Ka yi min magana ka yafe min don Allah."Cikin sarkewar murya ya ce, "Sa...fi...yya.. da gaske ki ke kin yarda da abin da na fada miki, kin daina zargina?"Na daga masa kai."Na gode, na gode Safiyyata."Na mike tsaye, "Ka bude min na tafi."a daura mana aure don cika burin zuciyata, na yi miki alkawari da an daura mana aure zan sake ki. Kin ga na cika burin zuciyata ana daura mana zan sake ki, ki koma gida.Kin ga rana ita yau za a fara shari'a, ki yi wa Momy sakamakon alkhairi ki yarda na aure ki kin san in har aka aka fara zaman court za a yankewa su Rukayya hukunci ba akan hakkinsu ba, ki dubu soyayyar da Rukayya da Sadiya suka nuna miki har ma da iyayensu, ki yi musu halarci, ki yarda a daura mana aure, ki je ki ce su daga fushin kuliya, ki yi tunani na gaya miki da an daura mana aure zan sake ki ki tafi Kano. Na baki kwana biyu ki yi tunani."Yana fatfar haka ya kwanta a wajen da nake tsaye na tsugunna ina kuka.Me yasa Imran ya yi min haka? Yaya zan yi da raina? Ba zan iya auran Imran ba da na aure shi gara na zauna ban yi aure ba, in kuma har ban auri Imran ba za a yankewa Momy hukunci ba a kan laifinsu ba? To yaya zan yi? Ba ni da wani zabi da ya wuce na yarda a daura mana aure da Imran tunda ya yi min alkawarin da an daura mana aure zai sake ni.Na dago ina kailon Imran idona cike da hawaye na ce, "Ka rantse min da girman Allah da an daura mana aure za ka sake ni?"Ya yi saurin dago kansa."Na yi miki alkawarin da an daura mana aure zan sake ki, abin da ya sa ma na nace sai an daura mana aure kin ga ina yawan rantsewa akan sai na aure ki, to in kuma ban aure ki ba zan zo na yi kaffara, amma kin ga da an daura mana ban da kaffara sai na sake ki ki je ki auri SAIFULLAHI tunda shi kike so ba IMRAN ba. So..."Kan ya karasa na katse shi."Duk ba wannan maganar ce a gabana ba, tun farkon hadu warmu na gaya maka bana sonka, bana kaunarka, . ka hakura ka cire ni a ranka.""Hum Safiyya tun yaushe na cire ki a raina ki ban amsa kin amince a daura mana aure?"Na daga masa kai, daga kan nawa ya yi daidai da zubar zafafan hawaye daga idona. Ya mike zumbur kamar an tsira masa allura yana dariya."Gaskiya na yarda da kaunar da ke tsakaninku da Rukayya, insha Allahu gobe za a daura mana aure."Na yi saurin cewa, "Kuma goben za ka sake ni?" Ya dagan kai. **** **** **** **** **** ** Suna zaune a falon saukar baki suna jiran fitowar Alhaji Nasiru wanda Sadiya ce ta shaida masa zuwansu Alhaji Mukhtar da Alhaji Ibrahim, wanda suka zo yin sulhu tun kafin a je gaban kuri'a kan wata 'yar karamar matsala (amma fa a ganinsu. Batan jarumata Safiyya ne karamar matsala?). Ya shigo falon tare da sallama fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya, kowa da abin da yake sakawa cikin zuciyarsa. Alh.Mukhtar ya katse shirun da cewa.............. 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

waye sanadi?? 73--75[11/28, 9:46 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com 'Yar uwata Rukayya masoyi yata na san na yi miki laifi da dama wanda 'yar wannan takardar ta yi kadan na ba ki hakuri a cikinta, yanzu ma zan miki wanta sabon babban laifin Momy na riga na gama yanke wa kaina hukuncin barin gidanmu, in kuma na koma zuciyata zata iya hugawa na mutu. Ba zan iya rayuwa da Ummata ba, bayan taci amanata tabi ta hunyar da Ubangiji ya haramta, ki mikan godiya mara adadi ga Abbanki da kawunki sun nuna min kauna ta hakika, wanda hakan yake ragen radadin da yake damun zuciyata. Momy na san kun nuna min so da Sadiya wanda ba zan taba mancewa da shi ba. Momy zuciyata ta damu da ciwon son Imran, na san lokacin da ki ka karanta wasikar nan na yi nisa da barin birnin Ikko, ki bawa Imran hakurin rashina, ki kuma gaya masa sakona. Taki: Safiyya Mukhtar. Tana gama karantawa wasu zafafan hawaye suka zubo mata, ta durkushe a wajen tana kuka. Me yasa haka Saffiya? Ina ki ka shiga ki ka bar mu cikin kewarki, muna .sonki da yawa, kin samu cikin damuwa Kawu yana cikin tashin hankali, muna son ki da yawa, don Allah ki dawo gare.... Kuka ya ci karfinta ta kasa karasawa. "Haba Rukayya kina abu kamar ba Musulma ba, ki tashi ki roki Ubangiji Allah ya bayyana ta." Zuciyarta ta tunatar da ita, haka ta yi saurin mikewa ta fada toilet. Washe gari karfe goma ta fito ta dau sabuwar motarta da Kawunta ya sai mata, yau ne karon farko da ta hau motar. Gidansu Sadiya ta nufa wayarta tayi kara."Hello Imran, an ganta?" Muryarsa cike da tarin damuwa ya ce, "Rukayya babu irin nemanta da banyi ba, amma babu labari, don Allah RuRayya in kuna tare da Safiyya ki gayan ko hankalina ya kwanta in na rasa Safiyya ban san ya rayuwata za ta kasance...." Muryarsa ta hau rawa. 'Wallahi Imran ba mu tare da Safiyya, yau na ga Wasikarta a jakata kuma an kirani ana gaya min in bada miliyari biyar a sake ta." Don Allah ki ban number na kira wallahi ko sama da miliyan hamsin ne zan bayar, don Allah Rukayya ki taimaka wa rayuwata." 'Imran na fi ka shiga damuwa na rasa ina zan saka rayuwata, ban san haka muka shaku da Safiyya ba." "Uhum!" Ya sauke numfashi. 'Ki yi hakuri Rukayya na dade ina kaunar Safiyya tsakanina da Allah yanxu don Allah ki turon da number da ta aka kiraki fa ita." 'Uhm Imran, ka san abun takaicin?" ''Sai kin fada." Ya ce da sauri. 'Mutanen da suka yi kirana sun yi bidding number. "oh My God!" Ya furta cikin fushi. Ya ci gaba da cewa. "Rukayya ki turon number account dinki na turo miki da miliyan biyar don ki ajiye kuma nan da sati daya zan zo Kano nasa kakanmu ya taimaka mana da addu'a." 'To Imran, na gode zan turo maka." Ya katse wayar yana dariya ya juyo yana kallon Safiyya wadda take durkushe a gabansa tana sharman kuka. gaskiya baby kin yi sa'ar qawa, Ruakyya tana sonki da yawa bar ma iyayenta suna kaunarki, kin shiga family dinsu a nasara, Batan ki ya saka su cikin damuwa. Me zai hana ki amince a daura mana aure ki koma gare su? Kin zauna kullum kina cikin kuka, du bi yadda ki ka koma, ni kaina kin saka ni cikin damuwa kin rabani da iyayena da kannena gara ke da rukayya kawai na rabaku don daman kince baza ki koma wajen iyayen kiba kina ganin kin shirya wa kanki rayuwa mai amfani, ace mahaifiyarki mai kaunarki kike gud...." Kan ya karasa na katse shi cikin tsawa. "Bana kaunar jin mayaudaran kalamanka, me ye ruwanka da rayuwata da ta Ummata? Ba zan koma gidan ba, ina ga yanzu ba sato ni ka yi ba ka zo ka tsare ni ka aikata abin da ranka yake ba ka, kuma ban da wani sauran amfani a wajenka." "No Safiyya, kina da amfani a wajena sosai kusan zan iya cewa ke ce rayuwata, sonki da kaunarki shi ya hana ni na bar ki ki yi nisa da rayuwarta, ban san irin rayuwar da zan yi ba muddin ba ma tare." Ya sauko daga kan kujerar ya tsugunna a gabanta ya hade hannayensa tare da dora su a kan kirjinsa. 'Safiyya don Allah ki taimaki rayuwata ki amince min na aure ki, ina kaunarki da yawa Safiyya ban san wane hali zan shiga ba muddin ki ka guje ni, zuciyata tana gaf da mutuwa.Safiyya sonki ya zame min tamkar ruwa mahadin rayuwa babu yadda za ayi na daina sonki, in har zan daina sonki to zan daina shan ruwa, domin dorewar rayuwa daina shan ruwa ba karamin hadari bane ga rayuwa haka sonki ya zame min. Daina sonki a zuciyata daidai yake da daina numfashina, zan... Na katse shi cikin kuka."Bana sonka, bana kaunarka, ba zan kuma taba sonka ba har karshen rayuwata, ka cuce ni ka Batan rayuwa, dama za ka taimaki kanka ka cire ni a zuciyarka zai fiye maka sauki ba zan taba auran mugu azzalumi irinka ba, gara ma ka cirewa ranka tunanin rayuwa da ni, duk daran dadewa na fita daga nan sai mun hau kotu. Kullum ina kai kukana wajen Ubangiji ina rokar Sa ya gaggauta yi min sakayya akan ka mugu mai lalata yara."Ya yi saurin toshe kunnuwansa hade da rintse ido ya hau girgiza kai. "Ki bar gayan wannan zafafan kalaman da suke shirin tarwatsan kwakwalwata tunda nake ban taba bata diyar kowa ba, bana fatan na aikata haka a kan kowa,ke daya haka ta faru a tsakaninmu, kuma da ka ke ba kari na tsani mutumin da yake bata rayuwar yara.Hum! Safiyya baki san waye Imran ba, wallahi Safiyya tunda nake ban taba kula wata 'ya mace ba da sunan soyayya, ke daya ce macen da na taba soyayya da ita. Ki taima.... Kan ya karasa na mike na yi cikin dakin ina mai ci gaba da kukana. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/29, 10:32 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com *** **** **** ***** ******* *** "Rakiya! Rakiya!!" Baba ta hau kiran sunanta. Ta yi saurin fitowa tana goge ido ga dukkau alamu kuka ta yi har ta gaji. "Kina daki kina sana'ar taki Hassan har ya rarrafa ya fita zaure yana kuka "Baba, Hussaini nake lallabwa ,zai yi barci na zata hassan yana rumfa yana wasa 'Kalli yadda idonki ya yi, wallahi Rakiya ki taimakawa kanki ki cire tunani a ranki yarinyar da ta guje ki yau shekara har da wata uku, amma ba ki cire ta a ranki ba, ita da take neman albarka a wajenki ta guje ki ta tsallake ta bar gabanki ba ta taba tunanin ta zo wajenki ba, kina raye ba kya raye duk ba damuwarta ba ce, amma ki…….. Ni fa Baba ba tunanin Safiyya nake ba, na gaya miki Hussaini na ke lallabawa so nake ya yi barci kan Aysha ta zo daukar su." 'To ki karbi Hassan don ki ba shi nono ya sha." Hannu tasa ta dauke shi tana juyawa, ta ji sallama ba ta tsaya ta juyo ba saboda ta riga ta san mai sallamar. Sun jima suna hira da Baba, sannan ta ce, "Ka shiga wajensu Hassan mana." Tana maganar tana mikewa don fita. Abun da yake bakantawa Umma rai duk ranar da ya zo sai ta fita ta bar su, wanda hakan ba karamin Batawa mata rai yake ba. Sallamarsa ce ta katse mata tunani a ciki ta amsa ya karaso cikin falon ta daure zuciyarta suka gaisa, daga haka ya sa hannu ya dau Hassan wanda yake babbaka masa dariya, ya jima yana masa wasa tare da tambayarsa dan uwansa Hussaini. A hannunsa Hassan ya yayi barci Ya katse shirun da cewa, "Rukayya daman kinsan inda Safiyya take ki ka Boyen nake ta wahala a banza?" Wata irin dagowa ta yi tana kalonsa. "Ban gane kan maganar taka ba?" "Tun shekaran jiya nake jin cigiyarta a rediyo Sai jiya na ga jarida har ma da hotanta ana cigiyarta a lagos Yasa hannu a aljihunsa ya zaro jaridar ya nuna mata Hannunta na rawa ta karba, tabbas hoton safiyya Muryarta na rawa ta ce. "Wallahi ban san inda take ba, yau wata goma sha hudu. To wai ma wa yake nemanta har da buga hotantan?""Ranar da na ga hoton nata na yi binciken wadanda suke nemanta gidansu wata kawarta ne mai suna Rukayya, da kaina na je har gidansu ita Rukayyan tana ganina ta shaida ni, bayan mun gaisa nake tambayarta daman suna tare da Safiyyan, amma har Lagos din naje ku ka boyen. Nan ta hau inda-inda ta ma rasa me zata ce min, don haka na dawo cikin kuka, Umma tace yanzu daman suna tare da Safiyya? To ya aka yi suka rabu? ta yi min bayani ki kwantar da hankali zan shigar da karansu sai sun gaya mana inda sukabaro ta, ko kuma su gaya mana me yasa suka Boye ta, fatana ki ban goyon baya yanzu yau zan koma na samu mahaifin yarinyar sannan na je wajen dayar kawar tata, kuma insha Allah Allahu jibi zan tafi can Lagos din tunda a can ubangidana yake" 'Zan so ka taimakan ka tafi da ni can Lagos din don Allah ka taimakan ina son Safiyya bana kaunar in ga wani abu ya samu rayuwarta zan iya rantse maka cewar tun ranar da Safiyya ta tafi ta barni kullum zuciyata tana cikin kunci, babu wani minti da zai wuce ba tare da na tuna ta cikin zuciyata ba. Ta zama min tamkar kankara a cikin kwalba babu yadda za a cire kankarar nan a cikin kwalbar." "Ni kaina ina kaunar Safiyya kuma na yi miki alkawarin insha Allahu sai na nemo miki Safiyya duk inda take, ko don na fita daga zargin da ake min na SANADIN Batan Safiyya don Alfamar Manzon Allah (S.A.W.) sai na zama SANADIN dawowar Safiyya. Maganar zuwanki Lagos in har su Baba za su bari babu abin da zai hana mu tafi." Kan ma ta ba shi amsa ta shigo, "Kina sana'ar taki ne kin zauna kina kukan da ba shi da amfani, kin...." Kafin ta karasa na katse ta, ina ci gaba da kukana. "Baba kin ga hoton Safiyya na gani an buga ana nemanta za a bada kudi." Tana ganin hoton ta hau sallallami wajen Alhaji. "Su wa ye suke nemanta wani abun ta yi?" 'Babu abin da tayi." Nan ya kwashe duk yadda aka yi ya gaya mata. "Amma wadannan kawayen sun cika munafukai, wallahi na ba ka goyan baya dubu bisa dubu duk ka kama su har iyayensu, sai sun gaya mana gaskiyar ya aka yi ta bata har suka saka hotonta duniya take ganinta kuma na yarda ku je da Rakiya ko don hankalinta ya kwanta." Ta mike da sauri. "Bara na je na nunawa Malam." Ba ta yi mint! uku da fita ba suka shigo gaba dayansu kowa yana fidan albarkarkacin bakinsa. Nan dai Malam ya ce gobe da umma da kuma auta yarsa za mu je mu yi kwana kadan. Washe gari karfe tara muka bi jirgi zuwa Lagos. Alhaji Nasiru ya juyo yana kallona. "Na yi wa ubangidana waya na gaya masa za mu zo, shi din baya gari, amma babu matsala tunda iyalinsa suna gidan, har ma ya yi musu waya kuma na riga na san gidan tunda daman na yi zaman gidan." Umma ta ce, "Mu da ba dadewa za mu yi ba duka gobc za mu juyo." Muna sauka aka kira wayarsa, bayan ya gama ya juyo. Ga motar can ku zo mu je." Ya karbi Hassan wanda yake hannun auta. tsaye take jikin mota fuskarta dauke da murmushi muka karasa ta ce, "Sannunku da zuwa." Tana maganar tana karbar Hussaini. "Khadija kin girma, in a hanya muka hadu ba zan gane ki ba, Abba duk na rame karatu ya dau zafi ranar da Daddy ya dawo daga Malesiya cewa ya yi bai gane ni ba, kai ma Abba don ka daina zuwa ne. Ina Maryam da Khalifa?" "Duk suna lafiya suna gaishe ki." 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/1, 9:13 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣5⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.muhdabbagana.cf Ta bude motar muka shiga ni dai kallonta kawai nake kusan komai nata irin na Safiyya ne, musamman wajen 'Kama suna kama sosai. Wani tafkeken gida muka shiga wanda iya tsaruwa ya tsaru. Ta yi fakin muka fito. Tunda muka shiga falon Da murmarta ta sauko ta tare mu."Sannunku da zuwa, kun sha hanya Bayan mun gaisa ta juyo wajen Alhaji Nasiru, "Alhaji Nasir ba ka zumunci ka buya a duniya, yanzu ma zuwanka, da dalili. Wallahi jiya muke hirarka da Khadija take cewa ba za ka gane ta ba. Na ce Aysha ce ba zai gane ba ita da take Kano, yaushe rabon da ka ganta, ina tunanin an fi shekara goma rabonka da garin..."Kan ta karasa aka yi sallama ya shigo sanye yake cikin farar shadda sai daukan ido take. Fuskar Alhaji Nasir dauke da mamaki ya ce."Ba dai Imran ne ya zama haka ba?" Hajiya Amina ta juyar da fuskarta tana kallon Umma ta ce, "Rukayya taso mu shiga ciki."Imran ya tsugunna yana gaida Umma tare da kar bar Hassan."Kai boy yaya sunanka?" Hassan ya hau dariya. Ya juya wajen Alhaji Nasiru suka gaisa tare da tambayarsa su Abba., "Duk suna lafiya, Maryam ta ce a gaishe ka.""Ina ansawa." Auta ta gaishe shi.Ya juya wajcn Hajiya Amina, 'Momy an tashi lafiya?" Cikin fushi ta ce, "Lafiya kalau, ka tafi haka zalika lafiya (kalau ka dawo ka same mu."Kan ya yi magana suka shiga ciki tare da Umma,Alhaji Nasiru ya ce, "Laifi kai wa Momy, ni da na san Imran dan gatan Momy yau na ga Momy tana fushi da shi."Ya sunkuyar da kansa yana murmushi, "Abba tafiya na yi ban sanar dasu ba shine Momy take fushi da ni, yanzu ma Daddy ne ya yi rnin waya ka zo kana neman wata yarinya, ya ce na zo na taimaka maka tunda kai ka mance garin, "Haka ne Imran, 'yata ce ta zo karatu ta bata ina zaton yau wata biyu amma a maganar gaskiya kuma mu a tunaninmu shekararta daya har da wata biyu da bata sai shekaran jiya na ga mujalla ana nemanta. To da na yi bincike wasu kawa yen tane suke nemanta wai ashe mu duk neman da muka yi a Kano, suna tare da ita suka boye mana sai da suka gama karatun. To ban san ya aka yi ta bata ba don haka nazo da kaina. "Imran ya sauke dogon numfashi, "Abba daman kana da wata 'yar bayan Maryam?" "Uhm Imran yarinyar da ta bata 'yar matata ce ga mahaifiyarta nan take aure." Ya zaro jaridar ya mika masa."Ka ganta." Ya karba yana kallon fuskar Safiyyansa tana masa murmushi.Sun jima suna tattaunawa, kukan da Hassan ya fara ne ya tashi Imran ya shiga dakin mahaifiyarsa suna tare da Umma kamar sun wayi juna. Ya karasa wajen Hajiya Amina tare da kama hannunta."Don Allah Momy ki min afuwa na san na yi laifi ba zan Kara ba." Ya juyo yana kallon Umma."Umma don Allah ke ma ki sa baki ta yi hakuri ta daina fushi da ni." 'Ai ta hakura kai dai kar ka kara tafiya mai nisa haka ba tare da ka gaya musu ba, kayi girman da in ba a ganka ba hankali zai tashi. "Shi kenan Umma insha Allahu ba zan kuma ba, na ga yar kanwata fiishi take da ni."Hajiya Amina ta ce, "Rukayya ki karbi Hassan ya sha Mama."Ta ce, "Kawai rigima yake ba sha zai yi ba, su da shan Mama sai za su yi barci." Khadija ta shigo tare da Hussaini."Umma ya gama shan madarar kawo Hassan na ba shi na yi musu wanka mu yi barci."Har yanzu ba ta kalli inda Imran yake ba, ta dai tura hannu don ya ba ta Hassan ya kama hannunta yana dariya."Na san Momy ki ke taya fushi, to ita ma ta sauko Umman Hassan ta shirya mu ke ma yar kanwata ki sauko kar ki sa zuciyar Yaya Imran ta yi bindiga na gaya miki damuwata fa ba za ki tausayan ba.” Ya karasa maganar cikin muryar mai cike da tarin damuwa. Ta hau murmushi.'Sorry my brother na sauko.” Yauwa my lovely sister maza ba wa Hassan madara ki musu wanka mu je unguwa."Momy ta cc, "Ba ku da hankali za ku debi yara da ba’a ko yaye su ba." Umma ta ce, "Ki rabu da su su fita ko a can in dai na ba su da safe shi kenan don karfe goma Antynsu take di barsu su tafi sai biyar na yamma suke dawo." Khadija ta hau tsalle 'Thank you Umma. " "To Umma ki ba wa Hussain mama ya fara sha kan na shirya Hassan, in ya so da na ba wa Hassan ya sha shi ma sai na kawo shi ya Kara sha, kan nan ni kuma na shirya," Ta juya tana kalton auta."Sister taso mu je cikin dakina ki huta kan su Amal su dawo ki yi kawaye. "Tsaf suka shirya suka fita, motar Imran suka dauka. Babu abin da su Hassan suke sai barci.Khadija ta juyo wajen Imran, "Yaya don Allah za mu biya gidan su hanna "Gaskiya ba zan sarnu dama ba, amma da mun je ko baki shiga ba sai ki jc gidan nasu kan na gama abin da nake." Cikin murna ta cc, "Yaya na gode amma fa da su Hassan zan tafi.'Ke daya za ki tafi ki bar ni da su." "Ammm...."Ya yi saurin katse ta, "Kar ki ce komai in ba haka ba zan han zuwa gidansu kawar."Suna zuwa kofar gidan ya ce. 'Sister fito ki raka ni da daya." 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).