shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 21 December 2016

waye Sanadi?? 83 & 84



WAYE SANADI?💘 8⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf *****TUNA Baya***** ta shigo dakin tare da sallama, ita daya ce a cikin bukar sai wani kyakkyawan yaro da ba zai haura shekara hudu ba, yana ganin shigowarta ya hau murna. Ba ta ko kalle shi ba ta karasa gaban Yayarta ta tsugunna suka gaisa. Ya taso da gudu ya hau cinyarta, tana kokarin ture shi suka hada ido ta dan daure ta bar shi, yana wasa da awarwariayen hannunta."Yaya za mu tafi fa, in kina da sako ki bayar na taho miki da shi."Duk kun hadu ne?" Ba ta yi magana ba sai kai da ta daga mata,"Ba ni da sako ga Sale nan ku tafi da shi, shi ma ya ga gari."Ta dan dago da saurinta suna hada ido ta mayar da kanta ta dan yi jim, sannan ta mike."Bara na tafi suna jirana."To ba ki ji abin da na ce ba ne, ga Sale zai bi ku shi ma ya ga gari.'To yaya na ji ya taso mu tafi.Cikin fushi ta dago kai tare da cewa, "Sofi ki kiyaye ni ki kama hannunsa ku tafi duk abin da zai same shi ya same ku tare, bana san sakarcin banza kamar ba ke ki ka haifi yaron nan ba, shi ma zai zo ya same...."Kan ta rufe baki ya shigo shi ma gabanta ya tsugunna kamar mai neman gafara. Suna gama gaisawa ta rufe shi da fada kamar za ta cinye shi, babu abin da yake sai hakuri yake ba ta. Ta dan sassauta murya ta ci gaba da cewa "Ba ka ganin dan uwanka neman haihuwar yake ido rufe amma ku Allah ya ba ku kuna wulakantawa, ku ne iyayensa ku za ku ja shi a jiki har ya gaya muku damuwarsa, to kuna baya da shi ba kwa jan sa a jiki, kuna nuna masa kauna to ya za a yi ya saki jikinsa da ku? In kiwo za ka ka ja danka ku tafi, haka in kasuwa za ki ki ja shi ku tafi, ba kya ganin yadda 'yan uwanki suke jan 'ya'yansu a jiki,Rashin kula shi da ku ke, shi ya ja 'yan uwansa suke dukansa. Yanzu, jiya da ba don na zo lokacin da suke fada da Jauro ba da sai dai a kashe shi a gabanki kina kallonsa. To daga yau bana san sakarcin banza, ku ja danku a jiki, ku nuna masa kauna da kulaw..."Kan ta karasa aka yi sallama aka shigo."Lafiya ku ke zaune muna tu fa man tsimayi?""Nina tsayar da su ina musu fada kan sakarcin da suke kan Sale. Yauwa Yaya ki yi musu har da duka sun cancanci haka."Tun da muka fito da Sale a hannuna mutan gidan suke kallona cikin mamaki, nan da nan kunya ta rufe ni bar ma da tsoron maganganun da za su biyo bayan hakan. Haka muka tafi kai nono cikin gari. Magajiya ta matso kusa da ni. Yau yana ganki da Sale?' Ta fada tana murmushi.Na dan sunkuyar da kaina."Hum, Yaya ce ta matsa sai mu tafi dashi."Ta yi daida..Daidai lokacin muka zo gifta wani katon shagon saida kayan yara muka karasa tare da yin talian nono da sauri mutanen da ke siyayya a shagon suka juyo suna kallonmu bar mai shagon ya bude baki xai yi magana wani hamshakin Alhaji ya ce."Ku kawo mu gani." Yana maganar yana kallon Sale. Muka karasa gabansa tare da sauke kwaryar da take kanmu. Karar waka ta cika dakin muka hau dube-dube, sai Alhajin yasa hannu ya dauko wata katuwar aba baka ya kara a kunnensa ya hau magana muka tsaya cikin mamaki muna kallonsa har ya gama. Sale ya tafi wajensa da gudu.Baffa ba ni na gani," Ya dauke shi ya dora sa a cinyarsa yana murmushi.'Dan Baffa me za ka yi da waya?' Sale ya ce Wasa zan yi da ita, ban da kayan wasa, baba ba ta sai mun sai dai ta dinga dukana ba ta ma kula ni kullum tana ganin yara suna dukana ba ta hana kowa. kai ma ka yi mata fada kamar yadda su Yaya suke mata.Ya yi shiru yana kallonsu kanta yana sunkuye kunya duk ta baibaye ta.'Ka yi hakuri ni zan sai maka kayan Wasa har ma da na sawa."Sunnan ya juyo wajen umma fuskarsa a hade ya ce, "Me yasa ku ke takurawa karamin yaro? Kuna daya daga cikin azaluman iyaye masu wulakanta ya yansu ko?"cikin mamaki suka kalii juna ita da Magajiya, ganin yanda yake fada kamar dansa ya katse musu tunani da cewa, wasu suna neman °yaya ido a rufe Allah bai ba su ba. ku ya ba ku kuna wulaRanta su. Ya dan rage murya ya ci guba da cewa.Don Allah ku dinga tattalin 'ya'yanku kuna kula da su, in ba kwa jan su a jiki kuna nuna-musu kulawa sai su shiga wani hali.Na daga masa kai,"Ku zuban na dari uku-uku.Sunnun ya juyo wajen mai shagon."Malam hada masa kuyan wasa da na suwa."To Alhaji." Ya mike jikinsa na rawa ya shiga hada kayan.Ya juyo wajen mu ya ce, "Ina san na sari shanu a wajen akwai masu siyarwa? Sale ya yi saurin cewa, "Baffanmu yana da su da yawa ka zo mu je ya siyar ma ni kuma zan bar maka nawa Au kai ma kana da sa? Yaya sunanka?'Sale Ba ku ban amsu ba Mugajiya ta ce, "Ana siyarwa Ya dan numfasa, yana danna faskekiyar wayar da take hannunsa ya ce "To yunzu ya za a yi na siya, tunda ban san wajen ku ba? baffa ka bi mu mu tafi garinmu, sai ka siya mu tafi gidanka. Hakan ce ta faru har muka gama tallan nono yana yaune a shagon mutumin da muKa yi masa lallar, ya mike ya dan fito bakin shago.'Kun san tafiyarmu ba za ta zo daya da ku ba. in kuma za ku shiga motata mu lafi to Na girgiza kai na ce Ba za mu shiga motarka ba sai dai mu yi gaba ka bi mu a baya har mu je Sale ya hau kuka Ni dai babah ba zan tafi a kafa ba Baffa zai bi." Yana maganar yana rike hannunsa Magajiya ta jani gefe, mun dan jima muka dawo gabansa. Magajiya ta ce,Mu je mun yarda za mu shiga motar ka Wannan shi ne karanmu na farko shiga mota. Tafi-tafi har muka je garinmu yana ta mamakin mutanen da suke rayuwa cikin wannan surkukin dajin. Mamakinsa ya tsaya cak ganin mun bullo cikin gari duk inda muka wuce yara da manya kallonmu suke har muka karasa. Ya fito yana rike da Sale, Sale haka garin naku yake, gaskiya da wuyar zuwa, kuna shan tafiya. Amma kafarku tana ciwo kam Ya girgiza masa kai tare da cewa Don Allah in za ka tafi zan bika ka sani a makarantar boko Ai ba za su ba ni kai ba in da za su ba ni kai zan yi mutukar farin ciki a ce an bar min kai ka yi karatu mai..Bakinsa ya kasa karasa abin da yake san fada, sakamakon ganin wasu gungun shanu sun taho farare sol da su kai ka ce gaba dayan shanun garin ne suka hadu. Maza biyu ne ke jan tawagar shanun Suka karaso wajen fuskarsu dauke da mamakin ganin mota cikin garinsu. Alh. Dahiru ya matso ya mika masu hannu don su gaisa cikin dari-dari suka mika masa hannu, kan ya yi magana Sale ya ce Baffa wajenku ya zo zai sai shano a kasuwa muka taho da shi har ma ya sai min kayan wasa. Bara na dauko masa tabarma Ya zuru cikin gidan da gudu. Bai jima ba ya dawo da tabarma, sun jima suna tattaunawa da su Mado.Cikin gidan kuwa tunda su Magajiya suka bawa yayar mazajensu labrin bakon da suka taho da shi zai sai shanu har ma da siyayyar da ya yi wa Sale. Ta ko rufe su da ruwan fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har matan gidan taya ta suke haka suka shigo suka same ta, dakyar suka lallaba ta suka shiga cikin bukkarta. Ta dago tana hararar su dukansu kansu yana kasa.Haka kawai ku dauko mana mutum ba ku san wa ye ba mugu ne dan yankan kai ne muna zamanmu lafiya ki dauko mana bala'i, ni dai ban yarda da shi ba watakila ma irin barayin yara ne, ya gan ku da da yana so ya sace shi har da yi masa siyayya, to wallahi bara na gaya muku duk abin da ya sami Sale ku kuka da kan ku, kuma maza ku gaya masa shanunmu ba na siyarwa ba ne ya bar mana unguwanmu. Yanzu ina ma Salen yake? Bakin Mado na rawa ya ce, Yana wajensa Ta mike da sauri Maza ku taho da shi, kar ya gudu da shi Har matan gidan suka fito waje da gudu, babu mota babu Sale. Ta juyo tana kallon Sofi da Magajiya. Kun ga abin da kuka ja mana ko? To wallahi ba zan koma cikin gidan nan ba in za a shekara dubu sai kun je kun nemo sa, bar mazajen ku ku bar gidan nan ga shanun nan ku dibi naku ku tafi, wallahi duk wanda ya shigo gidan nan a cikinku ba tare da Sale ba sai na KASHE shiSANADIN zuwan su Mado cikin birni Kano kenan. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/20, 9:06 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf Bakina narawa nace, ‘Umma Kawun Rukayya, shi ne mahaifina?”na daga kai. Na ji wani irin jiri yana dibana nayi baya zan fadi, naji an tare ni kannakara sa suma a jikin wanda ya tare ni naji sautin muryar Alkali yana ba da umarnin kama Imran. Magana na dinga ji sama-sama tare da sautin kukan Rukayyar Momy na, muryar da baza ta taba bace min ba, nayi yunkurin bude idona wanda sukayi min nauyi sosai tare da azabar yaji kamar an zuban barkono, nabude su dakyar idona cikin fuskar Ummana kantana kasa tana sharer hawaye ta jimuryata.“Umma me ye kike kuka?”Ta yi saurin dago tana kallona damuwar da take fuskarta ta bace murmushi tayi Ni kaina, ban san lokacin da murmushin ya sauka a kan kyakkyawar fuskataba. Kan ta yi Magana Momy ta dago idonta duk sun kumbura, na bude baki dakyar nace.Momyki bar kuka gani na dawo.”Ina maganar inakokarin kama hannunta, ta yi saurin mikon hannunta, na rike ina mata murmushi ta ce.“Safiyya kukan farin ciki nake da Allah ya bayyana gaskiya cikin kankanin loakci, ban zaci haka daga Imra...”Kan ta karasa abin da yake bakinta aka turo kofar aka shigo. Kawun Momy ne ya shigo yana shigowa Hajiya Amina (mahaifiyar Imran) ta shigo, na yi saurin mike ido. Hajiya Amina ta karaso gabana ta dan dafa gefen gadon ta ce, “Sannu Safiyya.Kai kawai na daga mata, kan ta kara magana wayarta ta hau kara, ta zaro a jaka ta fita. Tana fita Umma ta bi bayanta Kawun Rukayya ya zauna a inda ta tashi.“Safiyya bude idonki don Allah.” Na ji muryarsa. Muryata a sarke na ce, “Kawu da gaske kai ne mahaifina?’“Ki daina kokwanton haka babu wani kokwanto ke ‘yata ceta jinina.” Cikin shashshekar kuka na ce, “Abba me yasa ka guje ni lokacin da nake bukatarka ka ki ka tallafi rayuwata lokacin da nake tsananin bukatar tallafinka? Sai wani wanda ba shi ya haife ni ba ya tsaya ya tallafi rayuwata, ya yi min taimakon da ba zan taba mancewa da shi ba. Na so a ce Alhaji Nasiru ne ya haife ni, na san ba zan yi nad....” Kuka ya ci karfina na kasa karasawa.Ya dago yana kallon Rukayya (Momy), suna hada ido ta tafi ya zama daga ni sai shi a dakin.“Safiyya bude idonki.”Ban yi musu ba na bude sai dai na kasa dagowa na kalle shi.“Ki yi shiru ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo.”Na ce, “Abba don Allah ka gayan gaskiya ta wace hanya ku ka haifi ni.”Kai tsaye yaban amsa da cewa ‘Safiyya ta hanyar aure muka same ki.” Na kara cewa, “To me yasa ka ki karBata a matsayin ‘yarka?”“Safiyya ki kaddara haka Ubangiji ya shirya, kuma ba mu isa mu wargaza shirin Ubangiji ba ya riga ya tsara haka za ta faru a gare mu in har kin yarda da lamuran Ubangiji to kar ki dau wannan kaddara ki mata mummunanar fassara, ki dau hakan wata jarrabawa ce da Ubangiji ya yi miki.”“To yanzu me ye matsayina a wajenka? ”Ya dan yi dariya, sannan ya ce, “Tun farkon ganinki a matsayin kawar Rukayya Allah ya zuban kaunarki a lokacin da ki ka bata na shiga tsantsar tashin hankali ni kaina wnai lokacin na kan tambayi kaina me ye yasa na damu da batan ki? Ashe ban sani ba ke ‘yata ce.”Na katse shi, ‘Abba ka yarda yanzu ka karbe ni a matsayin ‘yarka Baba ta daina yi min gori.”“Tunda na ganki zuciyata take gayan duk abin da Rukayya ta haifar min nawa ne sharrin makiyanmu ne ya raba mu, na yi neman Rukayya na rasa sai jiya Allah ya hada mu. Safiyya nayi matukar farin ciki da Allah ya ban ke, zan baki kulawar da duk wani uba yake bawa ‘yarsa. Na rasa in da zan saka zuciyata don murna abin da na fitar da ran samun sa yau ga shi Allah ya ban.”Da sauri na ce, “Abba kannena nawa?”“Safiyya ke daya Allah ya ban, k...”Kan ya karasa Alhaji Nasiru ya shigo, yana ganina a zaune fuskarsa ta fadada da murmushi ya karaso da sauri. ‘Sannu Safiyya kin tashi.”Na dan sunkuyar da kaina na ce, “Dady na tashi,ina Khalifa?”‘Khalifa yana gaishe ki, dazu ya zo kina barci, kuma lokacin zai wuce Bauchi kin san ya samu aiki a can Bauchin.”Na ce, “Allah ya sanya alkhairi Dady, ina su Hassan?”Cikin mamaki ya ce, “Wa ye ya gaya miki Umma ta haihu?”Na dan yi murmushi sannan na ce, “Imran ne ya gayan har ma ya kai min su na gani lokacin da ku ka je nemana can Lagos din.”‘Kai wannan yaron bai kyauta ba, a haka kamar na zai aikata haka ba.”Abba ya ce, “Daman shi mutum ai ba ka san in me ye yake zuciyarsa sai Allah, amma ni ina ganin bai kamata mu bar shi a hannun court ba, kawai a karbo shi mu yi abin mu cikin sirri ba sai an fantsamawa duniya ba, kuma ko don iyayensa sai a rabu da shi tunda Allah ya kubutar da ita.”Dady ya ce, “Ni kaina na so haka, amma mahaifiyarsa ta ce abar shi alkali ya yi masa hukuncin daidai da laifinsa, don dazu muka yi waya da mahaifinsa, shi ma haka ya ce a rabu da shi.”Ya dan juyo wajena, ‘Safiyya ya aka yi ya dau...” Da sauri na ce, “Abba bana san hirarsa don Allah ku bar fadan sunansa, Allah zan iya mutuwa.”Ina fadar haka na saka kuka.Daddy ya ce, “Ki yi hakuri Safiyya ba za mu kara hirarsa a gabanki ba, ki bar kukan nan kar su Hassan su zo su ga Antynsu tana kuka.”Yana fadar haka na yi shiru ya juya wajen Abbana yana murmushi, sannan ya ce, “Alhaji Mukhtar zan je gida ina tunanin kuma ba zan dawo asibitin nan na tadda ku ba, na ji yana anjima zai sallame mu tunda ta farka.”‘Haka ne Alhaji Nasiru na gode da kulawar da ka bawa Safiyya bakina ba zai iya fadar godiyar a wannan lokacin ina fatan zuwa har gida don....”Kan ya karasa ya katse shi. “Haba Alhaji Mukhtar me ye abin godiya ni na dau Safiyya kamar ‘yar da na haifa, duk abin da na yi mata na yi don Allah.” Sannan ya juyo wajena ya ce, “Safiyya gidan Ummanta ki za ki tafi ko gidan Abban naki za ki tafi?”Kan na yi magana Abba ya ce, “A’a gidana za mu tafi ta dan kwana biyu ko?”Na dago da sauri na ce, “Abba ina san ganin Ummata fa, ka bar ni in kwana daya sai mu tafi gidan naka.“Duk abin da kike ina so, bari li kita ya sallame mu sai na kai ki ” Na dan yi murmushi na ce, “Na gode Abbana.”Daddy ya ce, ‘Ni ba za ki zo ki kwanar min ba.”Ban yi magana ba sai kaina da na sunkuyar. Abba ya ce, “Kai ma za ta zo ta yi maka kwana biyu ko don Khalifa.”Tare suka fita. Suna fita Rukayya ta shigo.‘My Sister kuna ta hire da Abba kin manta da Rukayya?‘Lah Momy ban manta da ke ba, hasali ma babu abin da yake raina sai ke da Sadiyya.”‘Tana ina na ba ta hakuri? Na san na muku laifi. Momy a yi min afowa ba zan kar...”Kan na karasa ta katse ni da cewa, “Baby bana san tuna baya abu ya riga ya wuce komai sai labari. Sadiyya ta je gida wanka tun jiya muna nan muna kukan mun ga samu mun ga rashi ga baby ta dawo kuma za ta gudu ta bar mu.”Na dan yi murmushi, ‘Ga ni Momy insha Allahu muna tare.” Na dan yi shiru.“No baby, Doctor ya hana ki tunani.”‘Momy ba tunani nake ba, ai tunani ya kare na ga Abbana.” Na dan girgiza kaina.“Momy don haka muke kaunar juna tsakani da Allah ashe Momyta ‘yar uwata ce ta jini, Momyna kuma Antyna, Kawun Momyna da ya nunan kauna tun kan ya san wace ce ni yake nuna min kauna har ya yi min kyautar da bazan taba mancewa da ita ba.”Na sauke numfashi sannan na tambaye ta cewa “Ina Ummata?” “Ai tunda ki ka farka Umma ta tafi gida tare da Sadiyya, Abbana ya tafi ya kai su gida.”Kan na yi magana Abbana ya shigo tare da Doctor ya tambaye ni abin da yake damuna, na gaya masa babu abin da yake min ciwo sai idona da kaina da suke ciwo.”Magunguna ya rubutan sannan ya sallame mu. Muna kokarin shiga mota Abban Rukayya ya shigo, ya ganmu a tsaye tare da Momyna tana min hire sai kokarin sani dariya take. Ya karaso fuskarsa dauke da dariya.“Na ji dadin ganinki haka Safiyya, Hajiyata na ta dokin ganinki amma can za mu tafi ko?”ta ce, ‘Abba, tun da ta dawo nakc ta lallaba ta yarda mu je gidanmu wai ita sai gobe, yanzu wajen Umma za mu kai ta.”Ya ce, ‘‘Wai haka Safiyya?”Abba ka yi hakuri ina bukatar ganin Ummata.'’ Na juyo wajen Momy na ce, “Haba Momyna ki ban na ga Ummata kwana daya kawai zan yi musu na taho wajenki, shi kenan na dawo nan bar abada.” Ta juyo da sauri tana dariya.“Abba ka zama shaida Safiyaya za ta dawo gidanmu.”“To na zama shaida.”Sannan muka tafi har kofar gidanmu Abana ya kai ni (da yake Momy ta bi Abbanta). Ya yi parking. Har na ziro kafa ta zan fito na ji muryarsa.“Safiyya zan je nadawo mai ki keso na taho miki da shi?” Na girgiza kai.“A’a ki min magana bana san girgiza kai, in kuma wani abun ne yake damunki ki fadan yanzu mu koma asibit, bana san ganinki cikin damuwa.”Na dan yi dariya, sannan na ce, “Babu abin da yake damuna Abba, zuciyata cike take da tsantsan farin ciki, yau gani ga mahaifina farin ciki ne yake hana ni magana.”‘To in har kina farin ciki da kasancewa ta mahaifinki ki gayan abin da ki ke so na kawo miki anjima.” ' Da sauri na ce, “Abba ka kawo min kayan dadi.” tare muka fito daga cikin motar ya bude but ya firfito da manyan ledoji har guda hudu, daidai lokacin Kado ya fito daga cikin gidansu yana ganina ya saki baki cikin sanyin murya na ce Kado don Allah zo ka dibar min mu shiga. Ya dawo da saurinsa suka gaisa da Abbana ya dibi kayan ya shiga na juyo wajen Abba na ce.“Abba bara ka shiga ku gaisa da Baba.”“Hum Safiya ina jin nauyin abin da ya faru tsakanina da Baba, amma na san ke za ki zama SANADIN ganowar komai ki gaishe ta har Umma, anjima in na zo zan shiga mu gaisa. Yana fadar haka ya koma mota.Na shiga gidan tare da sallama, muka yi karo da Baba tana kokarin fitowa na dan yi murmushi. Ina kuma za ki gani na zo?” Ta sa dariya.“Ba zan iya zama ba sai na ganki, lallai da na yi wa gidansu yaji.”Na hango Hassan yana tafiya a jikin bango na karasa da sauri na daga shi.“My boy ina Ummanmu?”Kamar ya sani ya kama yi min dariya, na juyo wajen Baba wadda ta biyo baya na bakinta yaka sa rufuwa.‘Ga Hassan nan kamar ku daya babu abin da ya raba ku.”Da sauri na ce, ‘A’a Baba ni da Abbana nake kama babu abin da ya raba mu, Hassan ko da Umma yake kama.” Na shiga cikin dakin tana zaune tana ba wa Hussaini nono, na karasa gabanta na tsugunna, Baba ta yi saurin fita ba. “Bara na kawo wa bakuwa abinci mai jaki, sanna na zo mu gaisa.”Na dan yi dariya na ce, Umma an tashi lafiya.”‘Lafiya, ya jikin naki?”“Na ji sauki daman ciwon tunanin Ummata ne.”‘Inda kina tunani ba za ki tafi ki bar ni ba har tsawon shekara daya.”“No Umma ki yi hakuri ke daya zan bawa hakuri, Baba kora ta ta yi na san ba ta damu da rashina ba, ke daya ki ka shiga damuwa, ki yi min afuwa don Allah ki yafc mini.”“Daman na riga na yafe miki, kuma ma tafi yarki ta zama SANADIN na haduwarki da mahaifinki.”Na dan yi dariya, na zauna a kusa da ita, Ina zama su Baba Magajiya suka shigo.Sai wajen karke hudu gidan ya zama shim, sai ni da Umma, sai kuma su Hussaini da suke wasa. Na jawo ledojin da Abbana ya ban na hau duba dogayen riguna kala-kala, sai mayuka da kuma mayafai har ma da takalma masu matukar kyau Na nuna wa Umma.Ta ce, “To ki tashi ki yi wanka ki kara jin karfin jikinki.”‘Yanzu zan tashi bara na gama shiryawa su Hassan kaya,”Baba ta mi ke da saurinta, “Bara na kai muku ruwan.”Ina fitowa Momy ta yi sallama. Bayan sun gaisa da su Baba ta juyo wajena… 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).