WAYE SANADI?
8⃣2⃣
MUH'D*ABBA*GANA
www.MuhdAbbagana.cf
'Dan albarka za ka fara halin naka koh, ya mutanen gidan da fatan kowa lafiya? "Duk lafiya sun a ma gaishe ka."'To madallah ya kumu yarinya da jiki?" 'Hum, malam ta ma ji sauki."To, mana godewa Allah.
"Ya mike muka shiga ciki babu kowa sai tarin almajirai. Cikin dakinsa muka shiga cikin nutsuwa na Kara gaishe shi, ya amsa shiru ya biyo baya. Na daure na ce, "Malam an yi min aikin?"Ya dan sauke numfashi yana kallona, sannan ya fara magana. "Imran na dau tsawon kwana biyu ina maka aiki, kuma babu abin da nake gani sai tarin
alkhairi mai yawan gaske, amma fa bayan an sha wuya tare da riginginmu komai
zai zama tarihi."Yana murmushi ya ce, "Na gode Malam. Sannan ya gaya masa yadda
suka yi da Safiyya. Ya jima kan ya yi magana ya sauke numfashi.'Imran kana ganin in aka daura maka aure ba tare da sanin Salisu ba, ba zai haifar maka da matsala ba?" Ya yi saurin cewa, Wallahi Malam babu wata matsala da za ta faru, ka ga shi Dady baya gari, kuma su iyayenta sun ce in har gobe ban turo waliyina ba za su
bawa dan uwanta. Don Allah ka taimakan ina so da ya dawo sai ka gaya masa. "'Har yanzu kai yaro ne Imrana, ba ka san ya rayuwa take ba, ka je ka Iallaba iyayenta zuwa nan da kwana uku, ka ga kan sannan su "Dahiru sun zo sai mu je tare da su a daura maka auren."Ya kara tausasa murya ya ce, "Ni dai Kawu ka
taimakan kar na rasa ta, kasan yaya Yusuf bai yi aure ba, sai ni kaninsa."Shi kenan gobe ka zo mu je sai a daura auren in ya
so daga baya kwa yi bikin."Cikin murna na dago ina godiya na zaro dubu hamsin.
'Malam ga sadaki.""A'a ka bar abin ka ka yi wani abun ni zan bada sadaki a matsayin gudummawata."Yana fitowa daga gidan Malam kai tsaye cikin kasuwa ya nufa duk wani abu da ake zubawa a lefe sai da ya siya sai da ya cika akwati set shida nan take ya biya kudin aka zuba masa a but, ya taho zuciyarsa fal da faiin ciki.Ya shigo
tare da sallama, na dago fuskata a hade, kallo daya na yi masa na maida kaina. Ya karaso kusa da ni."Safiyya zo mu je falo ki ga wani abu."Ban yi musu ba na biyo shi zuwa falon. Akwatuna na gani har guda shida.'Safiyya ga kayan lefe nan na yi miki."Na dago da sauri na ce, "Ban gane ka yi minkayan lefe ba, ni da da an daura mana aure
za ka sake ni ko ka mance da haka?"Yana murmushi ya ce, Na san da haka wannan lefan na yi ne kawai don na faranta miki ko ba ky...."Kan ya karasa na katse shi da cewa, 'Bana bukatar kayan lefen ka burina gari ya waye a daura mana aure ka sake ni."Ina fadar haka na juya ciki ya biyo bayana da kallo fuskarshi dauke da murmushi.
*****WASHE GARI*****
Misalin karfe goma Imran ya shigo ya ci farar shadda har da babar riga fuskarshi sanye da farin gilas,
wanda ya kara kawata fuskarshi. Na dago ina kallonsa har ya karaso ya tsaya a gabana yana murmushi.'Ya dai Safiyya na yi miki kyau ne ki ke kallona?"Na yi saurin dauke kaina, ya
dan rankwafa, muryarshi a hankali ya ce, "Don Allah Safiyya ki yi wanka ki canja kayan nan. 'Babu ruwanka da canja kayana in ka je an daura to ka sake ni na tafi."Fuskarshi cike da
murmushi ya ce, "Ba a daura ba yanzu zan je na dauko su ai a nan za a daura, ki daure ki
canja kayan nan don Allah." Yana fadar haka ya fita.Bai fi rabin awa da fita ba na jiyo
hayaniyar mutane a falon na yi saurin zuwa bakin kofar na leka ta kofar da ake zura makulli. Mutane ne su wajen goma dukkaninsu sun manyanta, ina kallo suka daura aurena da Imran. Wani tsoho mai zaman zabga addu'a yake suna amsawa da amin. Ni kuma ina amsawa da ba amin ba. Aka mikawa wani farin dattijo sadakina. Suna zaune aka dinga shigo rnusu da abinci, bayan sun gama suka fita na koma ina hawaye na zauna.Har wajen karfe goma ban ga Imran ba, duk hankalina a tashe yake ga zazzafan zazzabin da ya rufe ni, ya shigo yana waya har ya gama sannan na dago kaina muka hada ido ya sakar min murmushi."AMARYAkinshakamsh..."Kan ya karasa na katse shi da cewa, "Imran kai fa nake jira."Ya dan rage murmushin fuskarsa."Safiyya jiran me ki ke min haka?"Na Kara daure fuska na ce, 'Ina jiran ka zo ka sake ni, kan..."Dariyarshi ce ta dakatar da ni daga abin da nake son fada na tsaya cikin mamaki ina kallonsa.'Hum, Saffiya kina nufin ni
Imran na sake ki da hannuna? Har abada ba zan taba iyawa ba. Safiyya ke naso, ke nake so kuma ke zan ci gaba da so har zuwa ranar da ban santa ba. Zan kasance jarumin da ka iya fito-na-fito da kowa in har akan sonki da kaunar...."Kan ya karasa na katse shi."Kana nufin ba za ka sake ni ba?"Kan ya ban amsa aka hau kwankwasa kofa, wata irin razana hade da firgicewa ne suka bayyana a kan
fuskarsa. Ya mike jikinsa yana rawa ya leka, da sauri ya dawo da baya. Daidai lokacin aka kara buga Kofar karo na biyu ya karaso gabana fuskarshi ta jike da gumi, na ji muryarshi a hankali."Ki rufan asiri Safiyya ki shiga bandaki yayana ne ya zo da iyalensa don girman Allah ki rufan asiri." Ganin tsantsan tashin hankalin da ya shiga karan farko dana ji tausavinsa. Ban masa magana ba na
shiga bandakin ya biyo ni ya kulle tare da ban umarnin nasa sakata, Ya dawo bakin kofa ya dan saisaita nutsuwarsa, sannan ya bude yana murza ido. Dr. Dahir ya kalle shi sama da kasa, sannan
ya yi magana."Tun dazun muna bugawa ba ka bude ba me ka ke yi a daki ka kulle kanka?"Ya dan kararo muryarshin dole yana shafar kwantacciyar surnarsa ya ce, "Hum wallahi Brother barci ne ya dauke ni. Ina su Abdul-Jalal?"'Suna falo, ka zo ka kai mu gida saukar mu kenan." Ai bai tsaya rufo dakin ba ya fito suka tafi. Suna zuwa gida hira ta barki Hajiya Amina ta
juyo tana kallon Imran."Ka san gobe Rarfe bakwai za mu tafi so nake sha biyu mun taho.'Ina sane Momy."Shiru-shiru Safiyya ta ji Imran ya bude ta ba ta ji ba, ga gidan shiru don haka ta zare sakatar komai zai Faru ya faru. Ganin babu kowa ga kuma kofar dakin a bude yasa ta dan zura kanta falon kamar a rnafarki ta hangi kofarsa a bude har ma tana hangen get din gidan, wanda shi ma kofarsa
take a bade, har ma tana ganin motoci na wucewa. Da sauri na koma na dauko jakata, babhar rigar Imran
na harde ni na yi saurin tsugunnawa na dauke na ji nauyi, na yi saurin zura hannu na a aljihunsa na zaro rafar 'yan dubu guda biyu (Dubu dan biyu) na zuba a jakata jikina na rawa kamar mazari na fita daga gidan. Court ta cika makil illa mutum daya da ake jira Alkali Abdurrahman ya shigo ana take masa baya. wannan lokacin duk wani Bangare biyu sun hadu, Alh Ibrahim, Sadiyya, Rukayya, sai kuma lauyansu Barr M- Shamsu, ilia Alh. Mukhtar da ake jira. Haka bangaren. Alhaji Nasir ga shi ga Umma wadda ta rufe fuskarta da nikaf ga lauyansu Barrister Amina Khalil da dan rakiyarta Imran, wanda ya ki bari su hada ido da su Rukayya. Bayan an gama karantawa Alkali shari'a ya dago ya kalli na kusa da shi suna hada ido ya yi saurin fita. Daidai wannan lokacin Alh. Mukhtar ya shigo, babu wanda ya ga shigowarsa sai Umma, ta yi wata irin zabura, Alh, Nasir ya ce, 'Lafiya?" Ta ma kasa magana sai kai da ta girgiza masa, kan ta dawo daga shoking ta ga abu kamar a cikin mafarki NANA SAFIYYA ta shigo,Ba ma Umma ba duk wanda ya san akan abin da za a fara shari'ar ya gigita da ganinta. Shi kuwa kanwa uwar hadin mutuwar zaune ya yi. Ta karasa ba tare da ta kalli kowa ba har
gaban Alkali, da kansa AIhaji Abdurrahman yace.."Ke ce Safiyya?"Na ma kasa magana sai kai na daga masa."To ina ki ka shiga?"hannu na daga na nuna imran na ce, "Ga wanda ya sace ni."Can na ji muryar
Umma ta kira sunana na yi saurin juyowa ina kallonta ta hau nuna Kawun rukayya, sannan tace, safiyya ga mahaifinki.....
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Waye sanadi? 82
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.