shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 13 December 2016

waye sanadi?? 73--75[11/28, 9:46 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣3⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com 'Yar uwata Rukayya masoyi yata na san na yi miki laifi da dama wanda 'yar wannan takardar ta yi kadan na ba ki hakuri a cikinta, yanzu ma zan miki wanta sabon babban laifin Momy na riga na gama yanke wa kaina hukuncin barin gidanmu, in kuma na koma zuciyata zata iya hugawa na mutu. Ba zan iya rayuwa da Ummata ba, bayan taci amanata tabi ta hunyar da Ubangiji ya haramta, ki mikan godiya mara adadi ga Abbanki da kawunki sun nuna min kauna ta hakika, wanda hakan yake ragen radadin da yake damun zuciyata. Momy na san kun nuna min so da Sadiya wanda ba zan taba mancewa da shi ba. Momy zuciyata ta damu da ciwon son Imran, na san lokacin da ki ka karanta wasikar nan na yi nisa da barin birnin Ikko, ki bawa Imran hakurin rashina, ki kuma gaya masa sakona. Taki: Safiyya Mukhtar. Tana gama karantawa wasu zafafan hawaye suka zubo mata, ta durkushe a wajen tana kuka. Me yasa haka Saffiya? Ina ki ka shiga ki ka bar mu cikin kewarki, muna .sonki da yawa, kin samu cikin damuwa Kawu yana cikin tashin hankali, muna son ki da yawa, don Allah ki dawo gare.... Kuka ya ci karfinta ta kasa karasawa. "Haba Rukayya kina abu kamar ba Musulma ba, ki tashi ki roki Ubangiji Allah ya bayyana ta." Zuciyarta ta tunatar da ita, haka ta yi saurin mikewa ta fada toilet. Washe gari karfe goma ta fito ta dau sabuwar motarta da Kawunta ya sai mata, yau ne karon farko da ta hau motar. Gidansu Sadiya ta nufa wayarta tayi kara."Hello Imran, an ganta?" Muryarsa cike da tarin damuwa ya ce, "Rukayya babu irin nemanta da banyi ba, amma babu labari, don Allah RuRayya in kuna tare da Safiyya ki gayan ko hankalina ya kwanta in na rasa Safiyya ban san ya rayuwata za ta kasance...." Muryarsa ta hau rawa. 'Wallahi Imran ba mu tare da Safiyya, yau na ga Wasikarta a jakata kuma an kirani ana gaya min in bada miliyari biyar a sake ta." Don Allah ki ban number na kira wallahi ko sama da miliyan hamsin ne zan bayar, don Allah Rukayya ki taimaka wa rayuwata." 'Imran na fi ka shiga damuwa na rasa ina zan saka rayuwata, ban san haka muka shaku da Safiyya ba." "Uhum!" Ya sauke numfashi. 'Ki yi hakuri Rukayya na dade ina kaunar Safiyya tsakanina da Allah yanxu don Allah ki turon da number da ta aka kiraki fa ita." 'Uhm Imran, ka san abun takaicin?" ''Sai kin fada." Ya ce da sauri. 'Mutanen da suka yi kirana sun yi bidding number. "oh My God!" Ya furta cikin fushi. Ya ci gaba da cewa. "Rukayya ki turon number account dinki na turo miki da miliyan biyar don ki ajiye kuma nan da sati daya zan zo Kano nasa kakanmu ya taimaka mana da addu'a." 'To Imran, na gode zan turo maka." Ya katse wayar yana dariya ya juyo yana kallon Safiyya wadda take durkushe a gabansa tana sharman kuka. gaskiya baby kin yi sa'ar qawa, Ruakyya tana sonki da yawa bar ma iyayenta suna kaunarki, kin shiga family dinsu a nasara, Batan ki ya saka su cikin damuwa. Me zai hana ki amince a daura mana aure ki koma gare su? Kin zauna kullum kina cikin kuka, du bi yadda ki ka koma, ni kaina kin saka ni cikin damuwa kin rabani da iyayena da kannena gara ke da rukayya kawai na rabaku don daman kince baza ki koma wajen iyayen kiba kina ganin kin shirya wa kanki rayuwa mai amfani, ace mahaifiyarki mai kaunarki kike gud...." Kan ya karasa na katse shi cikin tsawa. "Bana kaunar jin mayaudaran kalamanka, me ye ruwanka da rayuwata da ta Ummata? Ba zan koma gidan ba, ina ga yanzu ba sato ni ka yi ba ka zo ka tsare ni ka aikata abin da ranka yake ba ka, kuma ban da wani sauran amfani a wajenka." "No Safiyya, kina da amfani a wajena sosai kusan zan iya cewa ke ce rayuwata, sonki da kaunarki shi ya hana ni na bar ki ki yi nisa da rayuwarta, ban san irin rayuwar da zan yi ba muddin ba ma tare." Ya sauko daga kan kujerar ya tsugunna a gabanta ya hade hannayensa tare da dora su a kan kirjinsa. 'Safiyya don Allah ki taimaki rayuwata ki amince min na aure ki, ina kaunarki da yawa Safiyya ban san wane hali zan shiga ba muddin ki ka guje ni, zuciyata tana gaf da mutuwa.Safiyya sonki ya zame min tamkar ruwa mahadin rayuwa babu yadda za ayi na daina sonki, in har zan daina sonki to zan daina shan ruwa, domin dorewar rayuwa daina shan ruwa ba karamin hadari bane ga rayuwa haka sonki ya zame min. Daina sonki a zuciyata daidai yake da daina numfashina, zan... Na katse shi cikin kuka."Bana sonka, bana kaunarka, ba zan kuma taba sonka ba har karshen rayuwata, ka cuce ni ka Batan rayuwa, dama za ka taimaki kanka ka cire ni a zuciyarka zai fiye maka sauki ba zan taba auran mugu azzalumi irinka ba, gara ma ka cirewa ranka tunanin rayuwa da ni, duk daran dadewa na fita daga nan sai mun hau kotu. Kullum ina kai kukana wajen Ubangiji ina rokar Sa ya gaggauta yi min sakayya akan ka mugu mai lalata yara."Ya yi saurin toshe kunnuwansa hade da rintse ido ya hau girgiza kai. "Ki bar gayan wannan zafafan kalaman da suke shirin tarwatsan kwakwalwata tunda nake ban taba bata diyar kowa ba, bana fatan na aikata haka a kan kowa,ke daya haka ta faru a tsakaninmu, kuma da ka ke ba kari na tsani mutumin da yake bata rayuwar yara.Hum! Safiyya baki san waye Imran ba, wallahi Safiyya tunda nake ban taba kula wata 'ya mace ba da sunan soyayya, ke daya ce macen da na taba soyayya da ita. Ki taima.... Kan ya karasa na mike na yi cikin dakin ina mai ci gaba da kukana. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [11/29, 10:32 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣4⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com *** **** **** ***** ******* *** "Rakiya! Rakiya!!" Baba ta hau kiran sunanta. Ta yi saurin fitowa tana goge ido ga dukkau alamu kuka ta yi har ta gaji. "Kina daki kina sana'ar taki Hassan har ya rarrafa ya fita zaure yana kuka "Baba, Hussaini nake lallabwa ,zai yi barci na zata hassan yana rumfa yana wasa 'Kalli yadda idonki ya yi, wallahi Rakiya ki taimakawa kanki ki cire tunani a ranki yarinyar da ta guje ki yau shekara har da wata uku, amma ba ki cire ta a ranki ba, ita da take neman albarka a wajenki ta guje ki ta tsallake ta bar gabanki ba ta taba tunanin ta zo wajenki ba, kina raye ba kya raye duk ba damuwarta ba ce, amma ki…….. Ni fa Baba ba tunanin Safiyya nake ba, na gaya miki Hussaini na ke lallabawa so nake ya yi barci kan Aysha ta zo daukar su." 'To ki karbi Hassan don ki ba shi nono ya sha." Hannu tasa ta dauke shi tana juyawa, ta ji sallama ba ta tsaya ta juyo ba saboda ta riga ta san mai sallamar. Sun jima suna hira da Baba, sannan ta ce, "Ka shiga wajensu Hassan mana." Tana maganar tana mikewa don fita. Abun da yake bakantawa Umma rai duk ranar da ya zo sai ta fita ta bar su, wanda hakan ba karamin Batawa mata rai yake ba. Sallamarsa ce ta katse mata tunani a ciki ta amsa ya karaso cikin falon ta daure zuciyarta suka gaisa, daga haka ya sa hannu ya dau Hassan wanda yake babbaka masa dariya, ya jima yana masa wasa tare da tambayarsa dan uwansa Hussaini. A hannunsa Hassan ya yayi barci Ya katse shirun da cewa, "Rukayya daman kinsan inda Safiyya take ki ka Boyen nake ta wahala a banza?" Wata irin dagowa ta yi tana kalonsa. "Ban gane kan maganar taka ba?" "Tun shekaran jiya nake jin cigiyarta a rediyo Sai jiya na ga jarida har ma da hotanta ana cigiyarta a lagos Yasa hannu a aljihunsa ya zaro jaridar ya nuna mata Hannunta na rawa ta karba, tabbas hoton safiyya Muryarta na rawa ta ce. "Wallahi ban san inda take ba, yau wata goma sha hudu. To wai ma wa yake nemanta har da buga hotantan?""Ranar da na ga hoton nata na yi binciken wadanda suke nemanta gidansu wata kawarta ne mai suna Rukayya, da kaina na je har gidansu ita Rukayyan tana ganina ta shaida ni, bayan mun gaisa nake tambayarta daman suna tare da Safiyyan, amma har Lagos din naje ku ka boyen. Nan ta hau inda-inda ta ma rasa me zata ce min, don haka na dawo cikin kuka, Umma tace yanzu daman suna tare da Safiyya? To ya aka yi suka rabu? ta yi min bayani ki kwantar da hankali zan shigar da karansu sai sun gaya mana inda sukabaro ta, ko kuma su gaya mana me yasa suka Boye ta, fatana ki ban goyon baya yanzu yau zan koma na samu mahaifin yarinyar sannan na je wajen dayar kawar tata, kuma insha Allah Allahu jibi zan tafi can Lagos din tunda a can ubangidana yake" 'Zan so ka taimakan ka tafi da ni can Lagos din don Allah ka taimakan ina son Safiyya bana kaunar in ga wani abu ya samu rayuwarta zan iya rantse maka cewar tun ranar da Safiyya ta tafi ta barni kullum zuciyata tana cikin kunci, babu wani minti da zai wuce ba tare da na tuna ta cikin zuciyata ba. Ta zama min tamkar kankara a cikin kwalba babu yadda za a cire kankarar nan a cikin kwalbar." "Ni kaina ina kaunar Safiyya kuma na yi miki alkawarin insha Allahu sai na nemo miki Safiyya duk inda take, ko don na fita daga zargin da ake min na SANADIN Batan Safiyya don Alfamar Manzon Allah (S.A.W.) sai na zama SANADIN dawowar Safiyya. Maganar zuwanki Lagos in har su Baba za su bari babu abin da zai hana mu tafi." Kan ma ta ba shi amsa ta shigo, "Kina sana'ar taki ne kin zauna kina kukan da ba shi da amfani, kin...." Kafin ta karasa na katse ta, ina ci gaba da kukana. "Baba kin ga hoton Safiyya na gani an buga ana nemanta za a bada kudi." Tana ganin hoton ta hau sallallami wajen Alhaji. "Su wa ye suke nemanta wani abun ta yi?" 'Babu abin da tayi." Nan ya kwashe duk yadda aka yi ya gaya mata. "Amma wadannan kawayen sun cika munafukai, wallahi na ba ka goyan baya dubu bisa dubu duk ka kama su har iyayensu, sai sun gaya mana gaskiyar ya aka yi ta bata har suka saka hotonta duniya take ganinta kuma na yarda ku je da Rakiya ko don hankalinta ya kwanta." Ta mike da sauri. "Bara na je na nunawa Malam." Ba ta yi mint! uku da fita ba suka shigo gaba dayansu kowa yana fidan albarkarkacin bakinsa. Nan dai Malam ya ce gobe da umma da kuma auta yarsa za mu je mu yi kwana kadan. Washe gari karfe tara muka bi jirgi zuwa Lagos. Alhaji Nasiru ya juyo yana kallona. "Na yi wa ubangidana waya na gaya masa za mu zo, shi din baya gari, amma babu matsala tunda iyalinsa suna gidan, har ma ya yi musu waya kuma na riga na san gidan tunda daman na yi zaman gidan." Umma ta ce, "Mu da ba dadewa za mu yi ba duka gobc za mu juyo." Muna sauka aka kira wayarsa, bayan ya gama ya juyo. Ga motar can ku zo mu je." Ya karbi Hassan wanda yake hannun auta. tsaye take jikin mota fuskarta dauke da murmushi muka karasa ta ce, "Sannunku da zuwa." Tana maganar tana karbar Hussaini. "Khadija kin girma, in a hanya muka hadu ba zan gane ki ba, Abba duk na rame karatu ya dau zafi ranar da Daddy ya dawo daga Malesiya cewa ya yi bai gane ni ba, kai ma Abba don ka daina zuwa ne. Ina Maryam da Khalifa?" "Duk suna lafiya suna gaishe ki." 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/1, 9:13 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣5⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.muhdabbagana.cf Ta bude motar muka shiga ni dai kallonta kawai nake kusan komai nata irin na Safiyya ne, musamman wajen 'Kama suna kama sosai. Wani tafkeken gida muka shiga wanda iya tsaruwa ya tsaru. Ta yi fakin muka fito. Tunda muka shiga falon Da murmarta ta sauko ta tare mu."Sannunku da zuwa, kun sha hanya Bayan mun gaisa ta juyo wajen Alhaji Nasiru, "Alhaji Nasir ba ka zumunci ka buya a duniya, yanzu ma zuwanka, da dalili. Wallahi jiya muke hirarka da Khadija take cewa ba za ka gane ta ba. Na ce Aysha ce ba zai gane ba ita da take Kano, yaushe rabon da ka ganta, ina tunanin an fi shekara goma rabonka da garin..."Kan ta karasa aka yi sallama ya shigo sanye yake cikin farar shadda sai daukan ido take. Fuskar Alhaji Nasir dauke da mamaki ya ce."Ba dai Imran ne ya zama haka ba?" Hajiya Amina ta juyar da fuskarta tana kallon Umma ta ce, "Rukayya taso mu shiga ciki."Imran ya tsugunna yana gaida Umma tare da kar bar Hassan."Kai boy yaya sunanka?" Hassan ya hau dariya. Ya juya wajen Alhaji Nasiru suka gaisa tare da tambayarsa su Abba., "Duk suna lafiya, Maryam ta ce a gaishe ka.""Ina ansawa." Auta ta gaishe shi.Ya juya wajcn Hajiya Amina, 'Momy an tashi lafiya?" Cikin fushi ta ce, "Lafiya kalau, ka tafi haka zalika lafiya (kalau ka dawo ka same mu."Kan ya yi magana suka shiga ciki tare da Umma,Alhaji Nasiru ya ce, "Laifi kai wa Momy, ni da na san Imran dan gatan Momy yau na ga Momy tana fushi da shi."Ya sunkuyar da kansa yana murmushi, "Abba tafiya na yi ban sanar dasu ba shine Momy take fushi da ni, yanzu ma Daddy ne ya yi rnin waya ka zo kana neman wata yarinya, ya ce na zo na taimaka maka tunda kai ka mance garin, "Haka ne Imran, 'yata ce ta zo karatu ta bata ina zaton yau wata biyu amma a maganar gaskiya kuma mu a tunaninmu shekararta daya har da wata biyu da bata sai shekaran jiya na ga mujalla ana nemanta. To da na yi bincike wasu kawa yen tane suke nemanta wai ashe mu duk neman da muka yi a Kano, suna tare da ita suka boye mana sai da suka gama karatun. To ban san ya aka yi ta bata ba don haka nazo da kaina. "Imran ya sauke dogon numfashi, "Abba daman kana da wata 'yar bayan Maryam?" "Uhm Imran yarinyar da ta bata 'yar matata ce ga mahaifiyarta nan take aure." Ya zaro jaridar ya mika masa."Ka ganta." Ya karba yana kallon fuskar Safiyyansa tana masa murmushi.Sun jima suna tattaunawa, kukan da Hassan ya fara ne ya tashi Imran ya shiga dakin mahaifiyarsa suna tare da Umma kamar sun wayi juna. Ya karasa wajen Hajiya Amina tare da kama hannunta."Don Allah Momy ki min afuwa na san na yi laifi ba zan Kara ba." Ya juyo yana kallon Umma."Umma don Allah ke ma ki sa baki ta yi hakuri ta daina fushi da ni." 'Ai ta hakura kai dai kar ka kara tafiya mai nisa haka ba tare da ka gaya musu ba, kayi girman da in ba a ganka ba hankali zai tashi. "Shi kenan Umma insha Allahu ba zan kuma ba, na ga yar kanwata fiishi take da ni."Hajiya Amina ta ce, "Rukayya ki karbi Hassan ya sha Mama."Ta ce, "Kawai rigima yake ba sha zai yi ba, su da shan Mama sai za su yi barci." Khadija ta shigo tare da Hussaini."Umma ya gama shan madarar kawo Hassan na ba shi na yi musu wanka mu yi barci."Har yanzu ba ta kalli inda Imran yake ba, ta dai tura hannu don ya ba ta Hassan ya kama hannunta yana dariya."Na san Momy ki ke taya fushi, to ita ma ta sauko Umman Hassan ta shirya mu ke ma yar kanwata ki sauko kar ki sa zuciyar Yaya Imran ta yi bindiga na gaya miki damuwata fa ba za ki tausayan ba.” Ya karasa maganar cikin muryar mai cike da tarin damuwa. Ta hau murmushi.'Sorry my brother na sauko.” Yauwa my lovely sister maza ba wa Hassan madara ki musu wanka mu je unguwa."Momy ta cc, "Ba ku da hankali za ku debi yara da ba’a ko yaye su ba." Umma ta ce, "Ki rabu da su su fita ko a can in dai na ba su da safe shi kenan don karfe goma Antynsu take di barsu su tafi sai biyar na yamma suke dawo." Khadija ta hau tsalle 'Thank you Umma. " "To Umma ki ba wa Hussain mama ya fara sha kan na shirya Hassan, in ya so da na ba wa Hassan ya sha shi ma sai na kawo shi ya Kara sha, kan nan ni kuma na shirya," Ta juya tana kalton auta."Sister taso mu je cikin dakina ki huta kan su Amal su dawo ki yi kawaye. "Tsaf suka shirya suka fita, motar Imran suka dauka. Babu abin da su Hassan suke sai barci.Khadija ta juyo wajen Imran, "Yaya don Allah za mu biya gidan su hanna "Gaskiya ba zan sarnu dama ba, amma da mun je ko baki shiga ba sai ki jc gidan nasu kan na gama abin da nake." Cikin murna ta cc, "Yaya na gode amma fa da su Hassan zan tafi.'Ke daya za ki tafi ki bar ni da su." "Ammm...."Ya yi saurin katse ta, "Kar ki ce komai in ba haka ba zan han zuwa gidansu kawar."Suna zuwa kofar gidan ya ce. 'Sister fito ki raka ni da daya." 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).