shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 13 December 2016

waye sanadi?? 76--80[12/8, 8:34 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣7⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf 'Ni dai gaskiya Yaya ban san shiga ka kira maigadi ya dauke shi." Cikin tsawa ya ce, "Baki da hankali za ki ce mai ya zo ya dauke shi." (Allah Sarki maigadi ba mutum ba!!!). Ta yi saurin fitowa ta dau Hassan wanda yake ta sharar barcinsa hankali kwance. Tana zuwa falon ta shi ta fito. Ya bi bayanta da kallo tare da murmushi.Tana zaune a kan sallaya yashigo, ba ta ko dago ta kalli mai shigowa ba tunda ta riga ta san babu mai shigowa sai BABBAN MAK1YINTA IMRAN. Ya karaso ya zauna a gabanta. "My wife ya gida? Bai damu da rashin ba shi amsa ba, ya ci gaba."Yau na zo baki mamaki maza taso ki ga kyawawan, kannenmu masu kama da ke Ummanki ta 'Haifa mana yau ga Ummanki a gidanmu ita da Daddy da auta sun zo nemanki, taso ki gansu."Yana maganar yana kokarin kama hannuna, ban san lokacin da na daga hannuna na zabga masa mari ba ya rike wajen cikin mamaki."Safiyya Imran ki ka mara?" Ya fada yana nuna kansa cikin tsawa. Na ce, "Na mara ka yi abin da za ka yi a…. Kan na karasa na ji kukan yaro a falo. Da gudu Imran ya fita ashe tsawar da na yi ce ta tada Hassan har ya fado daga kan kujera. Ya shigo da shi yana kuka 'Safiyya kin ga kin tashi Hassan, kalli ki ka ga wallahi kamar ku daya." Kuka Hassan yake sosai yana kuma mikon hannu don na dauke shi. Nan take na ji tausayin yaron tare da Kaunarsa sun cikan zuciya. Ina kuka nasa hannu na karbe shi, Swan na dauko na ba shi ya sha sosai, na hau jijjiga shi bar ya yi shiru. Bakin gadon na samu na zauna yana hannuna barci ya dauke shi. na ji maganar, Imran.Tabbas ba ni da matsala wajen raino, Safiyya ta za ta yi wa 'ya'yanmu raino mai kyau; barana dauko hussaini ki gan shi. Yau da na ga Umman Safiyya kamar ku daya daman Khadija Ce kamurmu daya kin ga nima ina kama da Umma." Ya fitaa ya dauko Hussuini.Na yi tunanin babu wani yaron, na dago kaina idona cike da ruwan hawaye. na ce, Ka gayan gaskiya wadannan yayan waye ko su ma debo su ka yi ka cucesu?"Yana dariya ya ce. "haba Safiyya duk shaidar zaluncin da ki ke min ba zan iya zaluntar yaran da nake so ba, nake kuma fatan ki haifar min irin...."Hararar da ya ga na wurgo masa ce ta hana shi karasawa."Allah ya tsare ni hada iri da kai. ina tambayarka ka gayan 'ya'yan wa ye?" "Na rantse miki da girman Allah Safiyya su Hassan Kannanki ne Ummanki ce ta haife su, a yanzu haka Ummanku tana gidanmu tare da Alhaji Nasiru sun zo nemanki sun ga jaridar da hotanki yake ana nemanki. Allah Sarki gidansu Momy suna sonki sosai, amma ke kina son jefa rayuwar ki cikin gagari." Na dago kaina da sauri ina kallonsa, kwarjininsa yasa na sunkuyar da kaina Kirjina yana bugawa wanda ban san dalilinta ba."Alhaji Nasiru yana shirin shigar da Karar RuKayya da Sadiya har ma da iyayensu za a fara shari'a a kan Batan ki na kuma tabbatar in har SU RUKAYYA suka je gaban alkali ba su da ta cewa, zaki sasu cikin tashin rigima da tashin hank...."Na katse shi c'ikin kuka, 'Ka cuce ni Imran ba zan taba yafe maka ba. in har aka yi wa su Rukayya wani hukunci ba su ji ba, ba su gani ba. Wallahi bazan taba yafe maka ba, bana kaunar ganinka k'a warga za min duk wani farin cikin rayuw...."Kan na karasa ya katse ni. "No Saf'iyya kar ki doran laifi ni din Imran taimakar ki na yi da na tsare ki. in da kin tafi ba ki san hannun da za ki fada ba. in har ki ka amince aka daura mana aure zan saka hannu na tattara miki duk wani farin cikinki da a baya ki ke fadan Imran ya warga za to zai dawo miki da shi. Ina sonki Safiyya, Rukayya tana sonki. ki taimaka ki daure mu ci gaba da rayuwa."Ina kuka na ce, "Ba zan aure ka ba, Allah ya tsare ni da auranka, kuma wallahi ba zan ba ka yaran nan ba ko za su yi kukan jini sai ka fitar da ni daga gidan nan na gaji da zama da kai in kashe ni za ka yi gara ka kashe ni na huta da bakin cikin kallonka.""No my life, ba zan kashr ki ba illa zan bar ki a gidan nan mu ci guba da rayuwarmu." Wayar shi ta yi kara ya zaro. "Hello Khadija." Can bangarrn ta ce, "Yaya na dawo gani a bakin gate."Okey ina zuwa." Ya katse wayar ya juyo wajena. "Ba ni kannena mu tafi."Cikin kuka na ce, "Allah ba zan ba ka su ba sai ka fitar da ni daga gidan nan, "Hum Suffy tawa bara na zo na mayar da ke lazy, sai na kar be su ta ruwan sanyi, daman na yi kewarki tun ranar dana sha dadi! kina barci har yanzu ba a kara kula ni ba." Yana maganar yana kokarin cire riga,Cikin kuka na ce, "Ba zan hana ka aikata abin da ranka yake so ba, amma wallahi ka sani duk ranar da haka ta kuma faruwa a tsakaninmu sai na kashe kaina. Daga yau ba zan kara cewa ka fitar da ni daga gidan nan ba, mu zauna har karshen rayuwarmu, ni na san duk daran dadewa zan fita daga gidan nan, kuma wallahi Imran muddin na fita daga gidan nan sai na jefa rayuwarka cikin tashin hankali, wanda za ka yi dana sanin zuwa duniya har ka san wata Safiyya, mugu azzalurn...."Kuka ya ci karfina na kasa karasawa. Bai kara magana ba ya karBi su Hassan ya fita. Sai da su Umma suka yi kwana biyu a Lagos suna neman Safiyya duk wani asibiti da makaranta babu wanda ba su je ba, har da Hajiya Amina ake yawon, ga kuma uban tafiya Imran. Hankalin Umma ya yi mugun tashi.Yau karfe hudu Imran ya shigo gidan babu kowa sai Umma da Hajiya Amina wadda take cikakkiyar Barrister mai zaman kanta, babu abin da take sai bawa Umma hakuri tare da kwantar mata da hankali Bayan sun gaisa yace "U'mma ina ganin duk yadda aka yi kawayenta sun san inda take yana da kyau a mika su kotu lallai-lallai su fadi inda take.""Ni kaina abin da nake tunani kenan.Cewar Hajiya Amina."Rukayya na miki alkawarin tsaya muku har sai sun fadi inda suka kai ta, bara Alhaji Nasirun ya zo mu yi magana."Suna cikin maganar Khadija ta shigo tare da su Khalil da gudu kowa yana kokarin daukar su Hassan. Kwata-kwata ba su kula da Imran ba, sai tsa warsa sukaji."Ba ku da hankali sai ku shigo daki da gudu har kuna taka mutane."Tunda ya fara maganar Salim da Khali! suna kame a wajen. Salim ya dago muryarshi na rawa ya ce, Sorry brother."Ya kara matse gira, "Malamai ku fice a dakin."Khalil ya kai hannu zai dau Hussaini, Khadija ta ce, "Au kai ba ka ji maganar yaya ba, ba cewa ya yi ku fita ba.Tana maganar tana murmushi ya girgiza kai ya juya. Ta juyo wajen Imran. Brother yanzu muka yi waya da yaya yusuf yana nan zuwa weekend tare da yaya babba dukka tare zasu taho "Kai Sister ban san karya fa. Dazun munyi waya da big brother har ya ban muka gaisa da Anty Hafsa basu gayan za su zo ba.'Allah Brother ba da wasa nake baita ma bai gaya mata ba , kuma kira my lowly sister ka tambayeta ""Shi kenan sister in na fito ma yi Magana yanzu muna wata maganar. Su Hassan ta dauka ta fita Ya jima suna tausar Umma har alhaji nasir ya dawo. Nan Imran ya gaya masa abin da suka yanke "Nima haka na shirya kuma tun a kano mu ka yanke shawaran kai su kara, kuma na ji dadin wannan taimakon da Hajiya Amina za ta yi mana. "Ina ganin wata makarkashiya suka kullawa Safiyya dole su fito da ita duk inda suka kai ta gobe zamu wuce Kano, da na koma zan shigar da karansu court sai na kira na gaya maku ranar da za a fara zaman courtu."Shi kenan Abba ni kaina zan zo tare da Momy bara na je na yi wasu Hassan tsaraba." Ya mike yana kiran Khadija tare suka fita dasu Hassan.Khadija ce take tuka motar. Imran yace sister muje ki kaini gidan da kika kai ni rannan."Yaya mu da muke sauri.""Haba sister duka minti biyu zan yi "Allah ka wuce minti biyu sai na gudu na barka eh 'Nayarda sister. 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/9, 7:50 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣8⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf Ya fito hannunsa rike da Hassan, tana can karshen gado zazzafan zazzabi ne ya rufe ta sai rawar dari take. Ya shigo dakin."Safiyya ga su Hassan za su yi niiki sallama gobe za su koma Kano."Yana maganar yana kwantar dashi ya fita. Tunda yake maganar ta dago kai da ta ji motsi a kusa da ita ta yi saurm janye bargon daga fuskarta. Tabbas Hassan Kaninta ne babu abin da ya raba su da ni. Jin da tayi ana taba mata fuska yasa ta tashi zaune tana daukarsa ta ji hawaye yana zubo mata ba ta san lokacin da bakinta ya furta."Hassan ina Ummata?" "Umma tana nan cikin kewarki da kin daure an daura mana aure, don Allah Hussaini kusa baki Antynku ta yarda ta aure ni." Yana maganar yana kalonta, wayarsa ta hau kara ya zaro cikin aljihunsa. Ya jima yana waya har ta gama daukarsa bai kula ba tana ganin zai juyo sai ta kau da wayar. Ya juyo yana kallonta,"Kalli yadda ki ka rame Safiyya kamar ba ke ba, don girman Allah ki canja kayan jikinki ba zan so ganinki a haka ba, please my wife..."Karar wayarsa ya hana shi karasa abin da yake son fada. Yana gama wayar ya dauke su Hassan suka fita."Kai yaya ka je ka yi zamanka da badon su Hassan ba da tuni na yi tafiya ta."'Sorry Sister ina shirin fitowa ki ka kira." Khadija ta dan juyo ta kallon imran ya daga mata gira ya dai kanwata ta numfasa"'Ni ko yaya ina ganin tsare Safiyya daka yi ba shi ne zai magance maka matsar ba .cikin razana ya dago alamun rashin gaskiya "Khadija wa ye ya gaya miki na tsare Safiyya? Hmm yaya duk cikin yan uwana babu wanda muka shaku sama da kai, ko Aysha da muke twins ba mu yi shakuwar da muka yi da kai ba. wanda haka ya sa babu halinka da ban sani ba. Kai ka Boye Safiyya tana wajenka cikin wannan gidan. kana ganin halin da iyayenta suka shiga, amma kwata-kwata ka nuna ba ka santa inda take ba. ba'ka tunan wata rana gaskiya zai bayyana Safiyya ta amince maka amma iyayenta su ki aminwa tunda ka riga ka boye musu gaskiya a baya i am sorry' in na bata maka rai ta karasa maganar cikin taushin murya. Yayi kusan minti uku yana tunani, can ya dago kai yana murnmshi."No Sister, baki bata min rai ba-shawara ki ka ba ni. kuma na gode; amma na yi mamaki ya akayi ki ka gano yayanki. Khadija na rasa ya zan yi da rayuwa, ni kaina ina tunanin haka. amma Khadija ina ganin haka shi ne magani don wallahi ina kaunar Safiyya bazan bari ta subuce min ba "To amma...." Ya yi saurin katse ta da cewa"Sister na yarda da ke ki riken amanata maganar safiyya ta zama daga ni saike in mun koma gida zan gaya miki me yake faruwa tsakanina da Safiyya kada kimin kyakkyawar fahimta." Da haka babu wanda ya Kara magana har suka shiga cikin kasuwa kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa **** **** **** ******* ******** Tana zaune a falon babu kowa sai ita daya. Gashi a zahiri kallo take, ita kam hankalinla yana ga tunanin suhibarta Safiyyah mai gadi ya shigo tare da yin sallama ta dago a gigice tana kallonsa. 'Ranki ya dade barka da hutawa."Fuskarta a hade ta amasa saboda yanayinsa na san wasu. "rakiya rikakkiyar kubewa ana hutawa ne?"Ta dago kai. ya hau dariya."Ni kam inda za a sakar..."Kafin ya karasa na katse shi cikin fushi na ce. "Mallam ka fara abin da ya kawoka,ka cikan kunne. wato sai ka ga su Hajiya ba sa nan ka ke zuwa ka dame ni da surutun banza na gaya maka bana son irin wannan banson surutun wallahi zan hada ka da Abba ko yaya Isah. Fadi abin da ya kawo ka ka fita."Allah ya huce zuciyar Hajiya sako ne na kawowa Alhaji tun jiya wasu mutane suka kawo a ba shi." To ba zan karba ba ka bari in ya dawo ka ba shi." Ina fadar hakan na mike. ban fi minti goma da shiga dakina ba wayata ta yi kara."Hello, Sadiya kina lafiya?" Ta amsa mata da lafiya, Rukayya don Allah in kina gida ki zo akwai matsala.Da sauri na ce, "Me ye yake faruwa?"Kar ki daga hankali wayata babu caji in kin zo kya ji." Kan nayi magana wayar ta katse.Key din motata na zare ina fitowa muka hadu da Hajiya.'Har kun dawo?"'Mun dawo, ke kuma ina zaki? ""Hajiya yanzu zan dawo."Ba wai yanzu za ki dawo nake tambayarki ba, ina tambayar in da za ki ne?''Hajiya gidansu Sadiya za ni fa.""Allah ya kiyaye hanya."'Amin Hajiya."Har Babansu Sadiya yana gida dukkansu sun yi jugum-jugum kamar an musu mutuwa. Na shiga tare da yin sallama, muka gaisa na juyo yana kallon Sadiya wadda take kuka, da sauri na ce"Sister me ye ya faru?"Ta dago fuska cikin kuka ta ce, "RuKayya dazu aka aikowa da Baba sammace a kotu."Ya yi saurin cewa, "Kar ki kara cewa aka aikon da sammace ke da ki ka daukowa kanki ke aka aikowa da summace, babu abin da zai kai ni kotu wallahi sai dai ke ki je in ma rike ki za su yi har sai kin fito musu da 'yarsu babu ruwan Adamu.""Baba don Allah ka yi hakuri Sadiya wa ye ya aiko?"Alhaji Nasiru kan Batan Saffiya ya ce ni na boye ta." What? Na fada tare da zaro ido. Na juya wajen babar su Sadiya wadda suke kira da Gwaggo ina neman Karin bayani kan ta yi magana wayata ta yi Kara na zaro da sauri. "Hello Abba."Can Barin ya ce, "RuKayya kina ina ne?" Na ce Abba na je gidansu Sadiya, gidansu Safiyya sun aikowa su Sadiya takarda daga court ana kararta wai Safiyya tana wajensu sun boye ta,"Yana dariya ya ce, "Mu ma nan sun aiko mana da ita, ki zo gida yanzu kawunki yana san ganinki, ki kuma gayawa Sadiyar ta kawar da hankalinta kar ta damu.""Shi kenan Abba bara na dawo. Sadiya kar ki damu yanzu Abba yake gayan nima an aikon mana daga court bara na je gida." Na juyo ina kalon baban na ce."Haba kar ka damu babu abin da zai same ku mu ma lawyer ne nan da wasu 'yan lokutan bara na je gida zan kiraki ta waya anjima." Ina fadar haka na mike.Suna zaune a falo na karasa gaban Kawu jikina a sanyaye kaina sai faman sarawa yake."a a yana gan ki kamar ba ki da lafiya?" Na girgiza masa kai na ce Kawu an yini lafiya? Ya amsa da lafiya lau. Na juyo wajen Abba na ce, "Abba yanzu mu ake zargin mun 6atar da Safiyya har aka kai mu court." Ina fadar haka hawaye ya zubo min. 'Me ye abin kuka Kar ki dami kan ki har abada TAIMAKO ba zai taba zama CUTA ba, na san in da ki ke kaunar Safiyya bazaki taba cutar da ita ba. Daman na yi tunanin haka za zata faru, "Kawu ni kuma ina tunanin ba mu da mafita a kan 6atan Safiyya mu da Sadiya mun yi wauta sau biyu Daddynta yana zuwa Lagos nemanta muna 6oye ta, ni ban so aka yi cigiyarta a mujalla ba."Abba ya ce, "Hajiya ta gayan labarin da ki ka ba ta akan Safiyya, ni kaina na ga wautar ku, amma tunda abu ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba.Kawu ya ce, "Ina, ganin kan a yi zaman court ya kamata mu je wajen shi Alhaji Nasiru mu yi magana ta fahimtar juna da shi, mu din ba yara ba ne dukkanmu manyan mutane ne, in ta kama mu yi sulhu sai mun yi babu mutunci mu je gaban court."ta mike jikina a sanyaye ina shiga daki na yi kiran wayar, tana shiga ya daga."Assalamu Alaikum, Anty Rukayya kina lafiya." "Lafiya kalau Imran, ya gari?" Duk lafiya Rukayya bar yanzu ba su Kara kira ba?" 'Wallahi Imran har yanzu shiru sai kuma wata rigimar da ta taso mana." 'Ban gane ba.""Imran an kai kararmu court mu da Sadiya ana tuhumar mu da 6atar Safiyya."Cikin mamaki ya ce, "Wa ye ya kai ku court?" 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/10, 7:49 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 7⃣9⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf "Mijin Umman Safiyya, Alhaji Nasiru ne ya kai mu, kan.." Ya yi saurin katse ni. "Ita Safiyyan ina mahaifinta?"in zan baka labarin safiyya zamu dade har kudin wayarka ya kare Ya yi saurin cewa,karki damu rukayya waya ta da kudi Ba tare da wata damuwa ba ta ba shi labarin da Safiyya ta ba ta, Ya fi miniti uku baiyi magana ba. Na ce, "Imran ka yi shiru ko ba ka jina?"Ya sauka wata nannauyar ajiyar zuciya.'Rukayya ni kaina ina cikin matsala."cikin rashin fahimta nace Imran ban gane kana cikin matsala ba "Rukayya na san Alhaji Nasiru har ma Abban duk 'yan gidan na san su abokin Daddyna ne abun da baki sani ha, yau kwana uku da dawowar Alhaji Nasiru bar ma da Umman Safiyya daga gidanmu sun je neman Safiyya, kuma Momynta ita tasa a shigar da ku kara, ita Alhaji Nasiru ya dauka a matsayin lauyarsa duk ranar da aka fara zama a court ni kaina sai an neme ni, kin ga ni kaina ina cikin matsala," Ya karasa maganar cikin murya mai cike da tashin hankali.Muryata cike da tausayinsa tace, "Kar ka damu zan yi wa Abbana magana ba za a saka ka a shari’ar ba. Kai dai ka ci gaba da dubanta a can din.""Hum, Rukayya ba ki san halin da nake ciki ba kullum ina hanyar neman ta, kuma Rukayya ba ki san wani abu ba. "Sai ka fada." Na ce da shi.Ya kara saukc ajiyar zuciya karo na biyu."Momyna ta ce tana so na rako ta, kuma na san in har muka hadu da su Abba za su gane ni, har ma suyi min magana."'A'a Imran ban gane nufin ka ba, kana nufin kwata-kwata ba mu san ka ba?"Kai saye ya ce, "Inda dama ina san hakan.""gaskiya hakan ba za ta samu ba, don kun gaisa da su Abbana sai a tuhume ka.""Shi kenan Rukayya na gode, kin ga kudin ko na turo miki ta account dinki?"Na ce, "Na gani Imran tunani nake ma zan dawo maka da kudin tunda har yanzu ba su kara kira ba.""No Rukayya, ki bar su na san wata ran za su kira kullum ina addu'ar Allah yasa su kara kira a ba su su dawo mana da ita.""Amin don girman Allah."Khadija ta zama kamar mutum-mutumi a gaban yaya Imran tun bayan da ya gama gaya mata abin da ya faru tsakaninsa da Safiyya.Ta sauke wani gwauron numfashi, sannan tasa hannu ta goge gumin da ya yi wa fuskarta kawanya, kwata-kwata tunaninta ya gudu duk yadda Khadija ta shahara wajen warware matsala yau ta gaza nemar wa yayanta gagarumar matsalar da ya dauko, ta ma rasa ta inda za ta fara magana.Yana murmushi ya ce, "Sister kin yi shiru, ina alfahari da kasancewarki kanwa a gare ni Khadija wajen ba ni shawara mai amfani da kuma samar mani mafila, yanxu ma gani gabanki ina neman mafita da shawara da fatan ba za ki zuban kasa a ido ba."Hum, Brother na, rasa ina mafita gaskiya, ka yi ganganci haka da ka dauke safiyya bashi ne mafita ba. Ina ganin hakan da ka yi shi ya kara dasa tsanarka a zuciyarta. Shawara daya zan ba ka Brother ka fadawa Safiyya gaskiya in har ba ta yarda ba shi kenan Brother sai ka hakura da ita. Ina ganin ba ita daya ce mace ba, babu yarinyar da za ka ce kana so ta ce ba ta sonka,kawai ka hakura da ita ka cire ta a ranka."Ya hau girgiza kai, "Khadija ba zan taba iya cire Safiyya daga raina ba, ba zan iya ba! Ba zan iya ba!!" Yana maganar yana girgiza kai. 'Har abada ba zan iya cire kaunar Safiyya daga raina ba. Daina son Safiyya kamar daina numfashina ne wanda haka yana nufin mutuwa. Please Sister ki taimakan ina son Safiyya sosai in na rasa ta na yi imanin sai kun rasa ni."'In Allah ya yarda ma ba za ka rasa ta ba, balle har mu zo mu rasa ka. Ka fara gwada wannan shawarar in ba ta yi ba sai mu nemi wata, zan taimaka da addu'a Allah ya saka mata kaunarka a ranta har ta rasa ina za ta ajiye kaunarka a ranta."Yana murmushi ya ce, "Ameen kanwata ina fatan ki rike min sirrina ya zama daga ni sai ke, kar wani ya ji sirrinmu, zan je na gwada shawararki."Tare suka fito ya shiga cikin dakin Hajiya Amina. "Momy sannu da hutawa." Au kana dakin Khadija na yi tunanin ka tafi." Yana murmuslii ya ce, "Ina ciki rnuna shawara." 'Kuna shirme dai.""Yauwa Momy wai yaushe Dady zai dawo?" "jiya ina sallah ya kira ban daga ba, to yau kuma sai kira nake ta ki shiga. Ina tunanin saura sati biyu ya dawo. Kana sa ne da tafiyarmu Kano rana ita yau?" "Au Momy ranar Monday za a fara shari'ar?" "Ranar Monday za mu fara, har Khadija ta gayawa Aysha za mu zo Kano da kai dazu muka yi waya da Hajiyar sabon gida sun fara damuna yaushe za mu taho." Yana dariya ya ce, "Nima shckaran jiya na kira nake tambayarta ina tsohon mijinta na ce ta gaya masa in dai na zo Kano sai na karasa shi, tunda ya ki ya mutu mu ci gado.""Hum maza Abbanku ya ji kuna fadar haka, shi bazai so ya mutu ba."'Allah Momy ya dade shi da Malam."'Ai ka dawo kaina, to tashi ka fita. Kai da yan uwanka kuncinye uwata, shi ma malam din cinye shi za kuyi Ya mike yana dariya."Momy sun sha miya gara su mutu."Kan ta yi magana ya fita da sauri.Babu abin da ka ke ji cikin dakin sai sautin kukana, ina can a karshen gado. Yau kusan .kwana biyu ban ga Imran ba. Duk wata dabara da zanyi don na bar gidan nan na yi, amma ban yi nasara ba. Tun jiya nake fama da zazzafan zazza6i ban da karkarwa babu abin da jikina yake sai kuma sautin kukana da yake tashi.Ya turo kofar tare da yin sallamaduk tsananin kiyayyar da nake wa muryarsa a duk lokaci. da ya yi sallama saina amsa masa a zuciyata. Ya karaso gefen gadon ya zauna. Hannu yasa ya janye bargon ganin fuskata sharkaf da ruwan hawaye cikin kidimewa ya ce."Safiyya me ye ya sa ki kuka?"Ban iya bude baki na yi magana ba saboda azabar da kaina yake. Hannu yasa ya dago ni da nufin na zauna, kwata-kwata babu karfi a jikina ganin ina kokarin komawa na kwata yasa ya yi saurin kwantar da ni ya kai hannunsa zuwa kaina cikin tashin hankali ya furta."Ya Salam! Sannu Safiyya."Ya yi saurin mikewa ya fita, na bi shi da kallo ido cike da hawaye. Bai fi minti biyu ba ya dawo."Daure ki sha magani za mu yi Magana mai muhimmanci Ban yi musu ba na kar6a na sha. Flask din da ya shigo da shi ya jawo ya dau plate. Tuwon shikafa ya zubo ya miko min. Nan ma ban yi musu ba na kar6a, rabona da wani abu mai nauyi tun ranar da ya tafi. Ina gamawa na ji wani nannauyan barci ya kawon ziyara.Kamar a mafarki na dinga jin muryarsa yana karatun Alkur'ani, na bude idona a hankali na hange shi kan sallaya kan-shi a sunkuyc yana kallon Alkur'ani cikin zazzakar muryarsa yake karanta suratul Nisa'i. Na yi yunkurin tashi don shiga toilet ya dago yana kallona, muna hada ido na zabga masa harara na shiga toilet.Wanka na yi na dauro alwala, yana ganm fitowa ta ya mike daga kan sallayar, ina idarwa ya juyo wajena. Cikin taushin murya ya ce."Safiyya ki sauraran don Allah za mu yi magana, ina fatan za ki nutsu ki saurari abin da zan gaya miki."Yana magana yana kallona, na yi saurin dauke kaina gefe. Ya ci gaba da cewa."Ina fatan abin da zan gaya miki za ki yarda da shi, kuma ni a zuciyata zan gaya miki gaskiya ne, har ga Allah in kuma na miki karya ina fatan Alltah ya miki sakayya a yanzu-yanzu ga kuma Alkur'ani mai tsarki zan dafa. Kin san dai hukuncin wanda ya yi rantsuwa da Alkur'ani har ya dafa shi.""Kai!" Na yi saurin katse shi cikin tsawa na ce."Ka cikan kunne fa ka fadi tatsuniyar ka ka tafi, ga shi dai a fuska kamar ba azzalumi ba.""Ki bar kirana da azzalumi har a zuciyata haka nake babu zaluncin kowa a raina. Bana zaluntar ,kowa ba kuma na kaunar na zalunci kowa. Ke ma a yau nake zaton na wanke kaina daga zargin da ki ke min na Azzalumi."Murmushin da ke kan fuskarsa ya bace, ya sauke numfashi kamar wanda ya tashi daga barci. Ya fi minti uku bai yi magana ba, can ya Kara sauke numfashi karo na biyu ya ce."Safiyya na rantse miki da girman Zatin Allah ban aikata abin da ki ke zargin na yi miki ba."Da sauri na dago kai cikin sarkewar murya na ce, "Ban gane abin da ka ke nufl ba, kana nufin ka ce ba ka yi min fyade ba?'Ya dagan kai cikin dakiyar zuciya ya ce, "Ban miki komai ba Safiyya, wallal ban aikata abin da kike zargina da shi ba. Abun da ki ka ga ya faru lokacin da kika farka na yi haka ne don a tunanina za ki yarda ki aure ni sai na ga hakan bai sa kin amince za ki aurc ni ba,don haka na gaya miki gaskiya in "Kan ya Rarasa abun da yake san fada na katsc shi da cewa.Imran wa za ka mayar mara hankali."Na yi murmushin da ya fi kuka ciwo.Kar ka mata imran ba da 'yar shekara sha uku kake magana ba, da 'yar shekara ashirin da biyu ka ke magana. Na taka matakin jami'a har na yi gogayya da irinku, dadin bakinka ba zai maka wani amfani ba gara ka hakura na riga na barka da Allah, ina fatan ya yi min sakayya da gaggawa ka"Na san ba za ki yarda ba, bara na yi miki rantsuwa ta karshe."Hannunsa ya daga ya dora a kan Alkur'anin da yake gabansa, sannan ya ce, "Na rantse da girman Zatin Allah Safiyya ban miki fyade ba, idan kuma na yi miki Allah Ka gaggauta saka miki don girman Ka."Yana fadar haka ya dauke hannunsa daga kan Alkur'anin ya ci gaba da cewa, "Ki yi tunani Ssafiya ya za a yi a cc na kusancc ki ba ki ji wani canji a jikinki ba?" Ya mike tsaye. "Ki zauna ki nutsu ki yi tunani babu wata 'ya mace in dai kamilalliyar yarinya ce da namiji zai kusance ta ba ta ji wani canji a jikinta ba, in kuma za ki yi tunani na kusancc ki ba kya cikin hankalinki, amma kin san in har kin tashi za ki ga alama. Ki gayan tsakaninki da Allah in kin ji wani canji ko wata alama ta hakan ya faru, ni kuma na yarda ki min duk hukuncin da ki ka ga ya dace da ni. Zan karBa zan kuma amsa laifina a yi min duk hukuncin da ya dace da ni."Yana fadar haka ya fita ya bar ni cikin sanyin jiki da fadawa cikin zuzurfan tunani. Me yasa ban yi tunanin haka ba? Ya aka yi Imran ya fi ni hangen nesa? Me yasa kwata-kwata ban yi tunanin haka ba? Tabbas abin da Imran ya fada gaskiya ne babu yarinayr da za a kusanta ba ta ji wata alama ba, kuma ni kaina na san haka. Me yasa ban yi tunanin ba? Kai tsaye na bawa kaina amsa da cewa tashin hankali ne ya hana ni tsinkayar hakan babu wani canji ko alama da na gani a jikina. Akwai lokacin da na yi tunanin haka, arnma zuciyata ba ta ba ni goyan baya ba, don haka na cire tunanin bincikar wani yanayi a jikina ba. To me ye manufan sa na nunan ya kusance ni? Me hakan yake nufi? Me ye dalilinsa na tsare ni a nan gidan? "Tabbas Imran bai kusance ni ba."Na furta a fili tare da sakin wata siririyar dariya wadda ni kaina ban san ta fito ba. Allah na gode maka da…..to be continue soon!!! 🅰bbagana hausa novels @ facebook. [12/11, 8:27 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘 8⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf Ka tsare ni a hannun wannan azzulumin na mike da sauri na shiga toilet. Sai bayan sallar Magriba ya dawo ina zaune ina karatun wani littafi tun na Momy ne. Zama ya yi a kasa, kwata-kwata ban dago kai na kalle shi ba. Hannu yasa ya karBi littafin ba tare da na ga tahowar hannun sa ba."NI NA YI kaina?" ya furta a hankali bayan ya kalli bangon littafin."Shi kuma haka sunansa yake, ba ni labari me littafin ya kunsa kinji kanwata Na dago fuskata cike da murmushi, abin da imran bai taba gani ba gani yake kamar a mafarki ya yi saurin rufe ido tare da budewa. Kan ya dawo daga duniyar mamaki ya ji maganata cikin taushin murya na ce.'Imran na yarda da abin da ka fada ka yi hakuri zargin da na yi ma don Allah."Saboda tsabar mamaki ya ma rasa bakin magana. Na kara cewa, "Ka yafe min Imran." Kur! Ya zuban ido ya ma kasa magana. nan da nan raina ya baci na yi kamar na tashi na shake shi don tsananin kiyayyar da nake masa na dai daure zuciyata don cinma burina."Ka yi min magana ka yafe min don Allah."Cikin sarkewar murya ya ce, "Sa...fi...yya.. da gaske ki ke kin yarda da abin da na fada miki, kin daina zargina?"Na daga masa kai."Na gode, na gode Safiyyata."Na mike tsaye, "Ka bude min na tafi."a daura mana aure don cika burin zuciyata, na yi miki alkawari da an daura mana aure zan sake ki. Kin ga na cika burin zuciyata ana daura mana zan sake ki, ki koma gida.Kin ga rana ita yau za a fara shari'a, ki yi wa Momy sakamakon alkhairi ki yarda na aure ki kin san in har aka aka fara zaman court za a yankewa su Rukayya hukunci ba akan hakkinsu ba, ki dubu soyayyar da Rukayya da Sadiya suka nuna miki har ma da iyayensu, ki yi musu halarci, ki yarda a daura mana aure, ki je ki ce su daga fushin kuliya, ki yi tunani na gaya miki da an daura mana aure zan sake ki ki tafi Kano. Na baki kwana biyu ki yi tunani."Yana fatfar haka ya kwanta a wajen da nake tsaye na tsugunna ina kuka.Me yasa Imran ya yi min haka? Yaya zan yi da raina? Ba zan iya auran Imran ba da na aure shi gara na zauna ban yi aure ba, in kuma har ban auri Imran ba za a yankewa Momy hukunci ba a kan laifinsu ba? To yaya zan yi? Ba ni da wani zabi da ya wuce na yarda a daura mana aure da Imran tunda ya yi min alkawarin da an daura mana aure zai sake ni.Na dago ina kailon Imran idona cike da hawaye na ce, "Ka rantse min da girman Allah da an daura mana aure za ka sake ni?"Ya yi saurin dago kansa."Na yi miki alkawarin da an daura mana aure zan sake ki, abin da ya sa ma na nace sai an daura mana aure kin ga ina yawan rantsewa akan sai na aure ki, to in kuma ban aure ki ba zan zo na yi kaffara, amma kin ga da an daura mana ban da kaffara sai na sake ki ki je ki auri SAIFULLAHI tunda shi kike so ba IMRAN ba. So..."Kan ya karasa na katse shi."Duk ba wannan maganar ce a gabana ba, tun farkon hadu warmu na gaya maka bana sonka, bana kaunarka, . ka hakura ka cire ni a ranka.""Hum Safiyya tun yaushe na cire ki a raina ki ban amsa kin amince a daura mana aure?"Na daga masa kai, daga kan nawa ya yi daidai da zubar zafafan hawaye daga idona. Ya mike zumbur kamar an tsira masa allura yana dariya."Gaskiya na yarda da kaunar da ke tsakaninku da Rukayya, insha Allahu gobe za a daura mana aure."Na yi saurin cewa, "Kuma goben za ka sake ni?" Ya dagan kai. **** **** **** **** **** ** Suna zaune a falon saukar baki suna jiran fitowar Alhaji Nasiru wanda Sadiya ce ta shaida masa zuwansu Alhaji Mukhtar da Alhaji Ibrahim, wanda suka zo yin sulhu tun kafin a je gaban kuri'a kan wata 'yar karamar matsala (amma fa a ganinsu. Batan jarumata Safiyya ne karamar matsala?). Ya shigo falon tare da sallama fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya, kowa da abin da yake sakawa cikin zuciyarsa. Alh.Mukhtar ya katse shirun da cewa.............. 🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).