shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 28 March 2017

Kukan kurciya 27&28 (END)




hausa novels https://mrsbilkisa.blogspot.com 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul)

 Kuyi ha'kuri da jinkirinmu wasu 'yan dalilaine suka kawo haka 🔚 Page2⃣7⃣&2⃣8⃣ ........Arikice Ameeda da ya Muzzaffar suke kallonsa, bindigarsa ya saita sosai akan ya Muzzaffar da Ameeda, hazbinallahu wani'imal wakil kawai suke ambata a zuciyarsu, ya Muzzaffar yay 'karfin halin faďin Sayeed mimuka yimaka? Yaushema kadawo 'kasar??. Cikin sanďa daddy yabiyo ta bayansa ya daki bindigar ta faďi (karku manta daddy babban ďan sandane) mari ya wankama sayeed ya'kara wanka masa wani, tuni sayeed yazube awajen saboda zafin mari, da'kyar momy da Ya Muzzaffar suka ri'keshi saboda sai kaima Sayeed duka yake tako ina. Ya ce, "ku 'kyaleni harni wannan ďan iskan yaron zai shigoma gida da bindiga?, to anufinsa nizai kashe kenan ko iyalina??, Sayeed ya fashe da kuka yana faďin nibanzo danna kashe kowaba dady, kaduba kagani babu bulet cikin bindigar, nazone gareka domin nayi maka godiya nakuma baka ha'kuri akan abinda maciya amana sukai maka. Tuni jikin daddy yayi sanyi da abinda yayma Sayeed, ya kamoshi dakansa yatayar zaune, to amma Sayeed miyasa zaka shigo da bindiga??, yanzu dakasa nayi maka abinda yafi haka aiban 'kyautaba. Murmushi Sayeed yayi karka damu daddy nayi maka uzuri, kobaka aikata komai akainaba 'yan sanda zasuzo su kamani yanzu babu daďewa. Atare suka ce, "yan sanda kuma???........ kafin surufe baki wayar daddy tafara wringing yaďaga tareda sallama, basu san mi akace masaba sungadai ya ajiye wayar. Yadawo da kallonsa ga sayeed, sayeed mika aikatane haka da zafi??, murmushi Sayeed yayi ya ce, "daddy nakafama maciya amana tarihine, na nuna musu kuskurensune, na harbi 'kafafunsu mamane da waďanda sukace su iyayenane, harda ďan iska Naseer. Harbi sayeed miyasa ka aikata haka??. Dady hakane yadace dasu, domin nina sun taka rawar gani wajen lalata min rayuwa nida 'kanina, munaji muna gani Sadiq yazama ri'kakken ďan iska, nikuma kuga yanda rayuwa ta maidani, shaye2 ya lalatani, babu abinda nake aturmrai sai iskanci da shan giya da koken, yafashe da kuka, daddy su mama masifane adoron 'kada, sonaima nafasa kawunansu da bulet suyi mutuwar jakuna abola, amma saina canja shawara na hahharbe musu 'kafafu da hannuwa ta yanda bazasu sake moruwaba, koda wanan ba'kincikin nabarsu zanji sanyi, dan haka dady dan ALLAH ko ankamani karkayi belina kabarni acan na 'kare rayuwata gabaďaya, banaso kokaďan wani yasake taimakona, ya mi'ke dazummar ficewa amma sai ya Muzzaffar ya ri'keshi, haba Sayeed baikamata ka yankema kanka irin wanan hukuncinba.....murmushi Sayeed yayi tareda dafa kafaďar ya Muzzaffar ya ce, karka damu Muzzaffar abinda yadace damai irin halina kenan. Tun farko iyayena sunrigaya sun ruguzamu, sun sayar da rayuwarmu akan kuďi kuďinma daba nasuba, wlhy daza abarni ayanzu saina ida ďauke ragowar Numfashinsu kowa ya huta...ya fisge hannunsa yafice. Basuda za6i face take masa baya, yana fita 'yansanda suka cikuykuyesa, suma su dady mota suka shiga suka bisu. Tuni ankwashi su iya abu zuwa asibiti dan sayeed ya faffasa musu kafafu da hannaye da bulet abun babu 'kyawun gani, sai kuka da dana sani suke, nikam gsky banji tausayinsuba saima ALLAH ya'kara danayimusu. Su daddyma asibitin suka Nufa hankalinsu yatashi daganin 6arnar da Sayeed yayi, (lallai KUKAN KURCIYA JAWABINE, sun raini abunda zai halakasu, sun gina ramin muguntar saka wani, sai duk suka afka batareda sun saniba, ALLAH sarki dady shine yabiya akai musu aikin cire bulet ďin. Bayan kwana biyu daddy yayi ciku2 aka fito da sayeed, saidai kasha Sayeed ya rasu, batareda kowa yasan yanda abun yafaruba, ALLAH sarki gsky bamuso hakaba domindai Sayeed abin tausayine ALLAH ya yafe masa), agidan dady akai masa sutura ananma akai zaman makokinsa, to ALLAH yaji'kan musulmai. BAYAN lafawar komai aka shiga shirin bikin su ya Muzzaffar da Ameeda, lallai naga bikin 'yan gata kam, dan shiri ake bana wasaba. Zuwa sanan an sallami su haj hassana daga asibiti, saidai suduka sun rasa 'kafa da hannu, lallai suna danasani akan 6arnar dasuka aikata, kukakam sunyi harsun rasa hawaye. ALLAH yataimakesu ma haj kaka tahana daddy yakaisu kotu, amma kamar yanda Naseer yay hasashe hakane tafaru, domin kuwa abokan daddy duksun rasa aikinsu, ga haj hassana takar6i takardarta sakinta uku ahannu, komaidai ya lalace musu basuga tsuntsu basuga tarko, su iya abu kam aisunfi kowa asara, domin sun rasa 'ya'yansu duka biyu, Sayeed ya rasu Sadiq kam bama asan inda yakeba saidai gyaran ALLAH. BIKI BUDURI. dahaka dai aka fara shagalin bikin su Ameeda, Naseer yayi kuka sosai na kubcewar Ameeda daga gareshi, har kano Ameeda taje ta gayyato Falmata, wadda itama ayanzu ta yanke shawarar yin aure, harma tafara istibira'i. Bikidai ya kankama don yaune aka ďaura aure, bayyana muku yanda ake shagalinma aii 6ata lokacine ammafa anan kwasar shoki, bakin ango da amarya yaki rufuwa, hakama dady da momy daduk wani masoyinsu, aranar da daddare aka sada amarya da ďakin mijinta ya Muzzaffar. To masha ALLAH komaidai yayi dai dai dominko amarya da ango sun riski rana mai cike da farinci saimuce ALLAH yasanya alkairi. Itamaidai falmata ALLAH ya haďata da abokin ya Muzzafar wato Ahmad kuma sunyanke shawarar yin aure, dan haka dady yahanata komawa kano yari'keta awajensa, idan biki yataho zasuje har Barno wajen mahaifinta. To saimuce ALLAH yasanya alkairi baki ďaya. BAYAN WASU SHEKARU. Mun isa gidansu ameeda domin ziyara, amma sai abubuwa dayawa suka bamu mamaki, domin kuwa mun tarar da ameeda da yara har huďu duk tagwaye, mace da namiji sai maza kuma, abin sai wanda yagani yara 'kyawawa abin sha'awa da birgewa, muna nan zaune saiga falmata itama danata yaran har uku, lallai masha ALLAH aure yayi riba. Saimuce ALLAH yabar zaman tare da 'kaunar juna. A6angaren su iya abu kuwa komai ya lalace, dan tuni malam dauda yasaketa yakoma 'kyauyensu, itakam tana kano tana bara dan tazama gurguwa, hajiya hassana kam ciwon 6arin jikine ya kamata saboda ba'kincikin rashin cimma burinta, to saimuce ALLAH yakara, dama ance idan zaka gina ramin mugunta to saika ginashi gajere dan bakasan mai faďawaba, kuma KUKAN KURCIYA JAWABINE.....😁👌🏻. TAMMAT BI HAMDULLAH. Nan muka kawo 'karshen wanan ďan takai taccen labari namu, ALLAH yabamu ladar abinda mukayi dai2, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana. Muďinnedai naku masu sonku da 'kaynarku. ABBA GANA. & BILYN ABDUL. muna mi'ka ďunbin godiya gareku masoyanmu saboda hakurin bibiyarmu da kukayi, ALLAH yabar 'kauna, saikunjimu asabon littafi mai zuwa. Mungode sosai❤❤❤❤❤😍😍😍 򖀽򖀽򖀽򖀮 Hikayarmu ©2017


---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Monday 13 March 2017

kukan kurciya 19---26


[2/24, 6:11 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA..........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Page1⃣9⃣&2⃣0⃣ .........

Bayan an yayyafama Ameeda ruwa ta farfaďo, ya Muzzaffar ya zaunar da ita, ruwa dady ya mi'ka mata tasha tana hawaye, cikin kuka ta ce, "ya suwaye waďannan dan ALLAH???. karki damu 'kanwata ashirye muke damu sanar dake komai, dan haka ki kwantar da hakalinki. Dubanta ta maida gasu iya abu dake durkushe sunata rawar jiki harda kuka, ahankali ta matsa kusadasu tana faďi iya miyake faruwane agidabnan??, shin kunsansu ne?? Idan kun sansu suwaye su??. Babu wanda yabata amsa acikinsu saima rawar jikinsu dake 'karuwa, ta ďauke kai daga garesu ta maida kan Nas dake tsaye shima tamkar gunki daka gansa kasan arikice yake, jira kawai yake yasami hanyar dazai arce amma babu dama, dan tuni polis sun dunkare 'kofar gidan. Waya daddy yayi tareda faďin kushigo ku kwashesu dan yanzu zamu koma abuja acan zamuyi komai daya dace. Okey sir suka faďa suna ďirarowa cikin gidan tamkar tururuwa, tamau aka dam'ke iya abu da malam dauda da Naseer aka yayibesu sai mota, 'kofar gidan cike yake da al'ummar annabi sai kallo da dariya akema su iya abu, su mutane azatonsu wajen kwaďayin 'yarsu ta auri mai kuďi suka kwaso wanda yafi 'karfinsu, mota aka cimimiyasu suna kuka da ro'kon ayi hakuri babu wanda ya sauraresu saima wani ďansanda daya kwalama iya abu bakin bindiga a 'kafa, tako daddage ta kwala ihu. Acikin gidan kuwa tuni Ameeda ta ruďe tana kwasar kuka dakyar suka lalla6ata tayi shiru, momy ta ce, "idan kinada wani abin bu'kata ki ďauka dan daga nan har abada bazaki sake zuwa gidanan ba, cikin mamaki Ameeda take kallonta amma babu damar tambaya dan tana tsoron kar itama asaka 'yan sanda cimimiyar ta yanzunan. Kayanta ta haďo dady yakama hannunta haba baby indai sutturace abinda kike bukata kawai to kibarta mu tafi komai kike bu'kata zamu yimiki da izinin ALLAH kinji. Kai ta jinjina tareda ajiye jakkar kayan ta ďauki ďan abinda ba'a rasaba suka fice, har yanzu mutane suna tsaytsaye a kofar gidan dan su iya abu ana motar 'yan sanda, suna shiga motar polis suka take musu baya sai abuja garin naira. Koda suka iso 'yan sanda wucewa sukayi dasu iya abu polistion sukuma suka wuce gida. Aljannar duniya ameeda tafaďa azuciyarta, gaba ďaya tazama 'yar 'kyauye, taga gida tamkar baza'a mutuba, saida momy takamata ta zaunar sannan, mizzaffar sai dariya yake mata, tana kallonsa amma tayi burus dashi tanabin ko ina da kallo, ruwa 'yan aikingidan suka kawo musu tareda kayan motsa baki, ďaya acikin 'yan aikin ta rissina tana faďin momy akawo abincine??. Momy ta girgiza mata kai, a'a magajiya abarsa saimunyi wanka sanan, to hajiya afito lafiya. Muzzaffar yami'ke yana faďin kunga nayi nana. Momy ta ce, "to saura kuma ka kwanta barci, kanayin wanka kazo kaci abinci, karki damu momyna kibani minti talatin. Kai ta ďaga masa tana dariya, saida ya haye samansa sanan ta kama hannun Ameeda tana murmushi babyna zomuje kiyi wanka kinji, itadai ameeda tamkar makaho da ďan jagora haka takebin momy har zuwa ďakinta. Yasalam ameeda tafaďa azuciyarta, bedroom ďin yatafi da imaninta wani abin kallo sai a bathroom tamkar wajen cin abinci, bayin ya haďu, itadai haka tayi wanka tafito, saimada momy tanuna mata yanda zatayi sanan. Bayan futowarta momy ma tashiga wankan, bayan ta nuna mata kanayan kwaliya dakuma kayan sawa data ajiye mata akan gado. Tashirya tsaf cikin jar doguwar rigar mai adon fararen duwatsu abinka ga fara tayi mata ďas kamar dan ita akayi. Momy ma tafito tashirya, sukayi sallar la'asar dan tama ďan shige lokacinta. Afalo suka tarar da ya Muzzaffar da dady suna jiransu a dinning. Momy tazauna kusada dady, itama ya Muzzaffar ya nuna mata kusadashi, babu musu taje tazauna, aka haďama kowa abinci agabansa sanan sukai bismillah suka hau ci. Itadai ameeda akunyace takecin abincin har saida daddy yay mata magana, babyna kodai dakaina zan baki abincinnan dai?, hannu tasa tarufe fuska tana dariya a'a dady zanci da kaina. To yakamata kam, kisaki jikinki baby nan gidankune, bakida inda yafinan kinji, dummm taji kanta yayi, wai ita wane irin ruďani ake shirin sakatane??, tagaza gane wanan rikitaccen al'amarin??, ya Muzzaffar ya ta6ata, taďago tana kallonsa da ido yay mata alamar taci, ďan murmushin ya'ke tayi tacigaba dacin abincin. Su momy suna kallonsu. Dahaka dai suka gama cin abincin suka tashi, dady ya haye samansa sukuma suka zauna suna 'yar hira, wadda duk anayine dan ameeda tasaki jikinta. Momy taje ďakin daddy, ta ce, "Alhaji nifa yau tareda baby zan kwana nayimaka yaji, yay murmushi a'a hajiya ainima ban yardaba saidai tazonan mukwana tare, murmushi momy tayi ta ce, "to inaga hakan zaifi sau'ki kam. Ranar agado ďaya ta kwana da momy da dady, sukasakata tsakkiya, (araina nace kai 'yan boko sai abarsu, wananan gandamemiyar budurwar za'a kwana gado ďaya da ita in bandadai.........baridai nayi shiru, ALLAH yashiryemu).............✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝 [3/1, 11:30 AM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA..........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Page 2⃣1⃣&2⃣2⃣ ........Washe gari bayan sun kammala breakfast suka nufi polistion, itadai duk abinda ake ameeda binsu kawai take da kallo cikin mamaki, tarasa gane kan wannan lamari, har yanzu bata fahinci inda suka dosaba, gashi kowa ya'ki bata damar tambaya, dahakadai suka 'karasa, tunda suka shiga 'yansanda suke 'kamewa daddy, watodai afahimtar ta daddy ďansanda ne kuma babba, shiyyasa yaja rundunar 'yansanda har kano suka yayibosu, towai misuka yimusu?, mi iyayenta sukai misu ne?, komadai miye ai yanzu zata gani, wani 'kayataccen office suka isa, mutummin dake saman kujerarsa ya mi'ke tareda sarama daddy, daddy yay masa umarni daya zauna, suma duk suka zazzauna asaman kujerun da aka 'kawata office ďin dasu domin saukar ba'ki, wanda suka tarar a office ďin yakira waya taraeda bada izinin shigowa dasu iya abu. Babu daďewa aka shigo dasu kallo ďaya ameeda tayi musu hankalinta yatashi, daka gansu kasan sunci ďan karen duka, duk raunuka ajikinsu, dareďaya sunyi wujiga2 kamar waďanda suka shekara akulle. Gaban dady da momy suka zube suna kuka da ro'konsa gafara, alhaji dan girman ALLAH kayi mana rai wlhy ka 'kara barinmu awajennan kashemu zasuyi, wlhy munyi nadamar abinda muka aikata, kuma ashirye myke mu faďa muku gskyar lamari, dan ALLAH kace karsu kashemu.......dakatar dasu dady yayi tahanyar ďaga musu hannu, ruf suka rufe bakinsu tamkar ruwa yacinyesu, office ďin yay tsit, dady yay gyaran murya tareda faďin musa ai inaga kawai zamu tafi dasu gidan dan kes ďin nagidane, dama nabari kakawosu nanne dansu dan nasan kai tsaye bazasu amsa laifinsuba sai sunji wuya, musa D.P.O yace babu damuwa sir bari nasa akai makasu, ai tun daren jiya suka faďi laifinsu kuma sunce basu kaďai bane suma sakasu akayi. Dady yajinjin kai ya ce, "shiyyasa nace zamu je gida dasu dansu nuna mana waďanda suka sakasu ďin dady yafaďa yana mi'kewa. 'Kara cimimiyar su iya abu akayi zuwa wani haďaďďen gida shima babu nisa da gidan dady, dady ne yafara shiga, da wata dattijuwa yafara karo, dakaganta kasan ba 'karamar masifaffiya bace, dan ko sallamar dady acinkushe ta amsa masa kuma cikin yanayin masifa, doguwace fara 'kya'ky'kyawa, tahaďu sosai dan tafi momy 'kyau nesa ba kusaba, daddy yazauna yana faďin ya gidan??, ta yatsine fuska tareda ta6e baki, yaukuma mafarkinmu akayi da sassafen nan??, ďan murmushi kawai daddy yayi dama sainayi mafarkinki nake zuwa ganinki, ba jiya dasafe nabar gidanba, nanma baki ta ta6e ai nasan idan kana gidan 'yar gold mantawa kake da kwa da komai, yanzuma da safennan sayeed yayo waya wai yana bu'katar kuďi, dady ya haďe fuska wane kuďi kuma yake bu'kata? Kofa sati uku banyi da tura masa dubu ďari biyarba, shin kuďin abincine??, bare ace suyakeci? Haba alhaji yanzu dan ALLAH dan yace yanason katura masa kuďi saiya zama abin faďa, sukenanfa ALLAH yabaka su biyu dukiyarnan fa tamkar tasuce tunda idan kamutu sune zasu gada, bare kace za'aci da ha'kkin 'yar gold, murmushi dady yasaki tareda gyara zama nibama wannan yakawoniba hassana, ta watsa masa kallon rainin hankali to da wacce kazo??, kodami kazo ashirye nake dakai alhaji ta'kare maganar cikin 'kufula. Kallon k kika sani yay mata sanan yaďauki wayarsa yay kira, kushigo kawai yace ya kashe, tami'ke tsaye afusace, wakuma ka kawomin har cikin gida, kaifa nakula kullum rainin hankalinka 'kara yawa yake, wlhy Alhaji har yanzu ina nan amatsayin hassanata daka sani, babu abinda yarage ahalina.............maganar ta kakare mata ama'koshi dan ganin masu shigowa, saikuma jikinta ya hau rawa dataga su iya abu, gabanta sai dukan tara2 yakeyi, tadaka musu tsawa kai kukuma daga ina? gayyar tsiya arna a idi, babu wanda ya kulata saima neman gurin zama dasukayi, Nasir ne 'karshen shigowa falon, ta gwalalo idanu tareda faďin Nasir kaikuma daga ina?, ina kasamo waďannan kara da kiyashin? Gaba ďaya aruďe take maganar, baice mata komaiba yanemi guri shima yazauna. Dady ya kalleta ya ce, "hassana yakamata kizauna, da'karfi tace bazan zauna ďinba munafuki, to wannan gayyar dakayomin ta micece??, tsawa dady yadaka mata tareda faďin karki zauna ďin, ai zaki zauna da tsiya, ana cikin haka saiga wani dattijo shima yashigo, shimaďin arazane yake bin mutanen falon da kallo, yanan tsaye wata tsohuwa tashigo tareda wani dabaikai su dady girmaba, saikuma mata su uku sumadai da'alama akwai dangan taka tsakaninsu da dady dan naga kama, sudai nakula kowa hankalinsa akwance yake. Duk guri suka nema suka zauna, hajiya hassana ce kawai a tsaye, da'alama tana samun hanya arcewa zatayi waje, saikuma dattijon nan dayaketa zufa da rawar jiki, sai kulmawa su iya abu idanu yakeyi, falon yay shiru babu abinda ake sai kallon kallo musamman ma Ameeda da kanta yake shirin tarwatsewa saboda mamaki wanan irin taron dangi haka duk na miye??.....maganar dady ce ta 'katseta, sallama yay musu tareda godiyar halartar kiransa dasukayi, kowa ya amsa. Tsohuwar nan ta kalli dady tareda faďin Hamza ina kasamo wannan yarinyar??, ta nuna ameeda, naga ita kaďaice ba'kon ido afalonnan gashi? kuma ina jin wani abu gameda ita"".. Dady yace mama ai akantane akai wannan taron, insha ALLAHU yanzu zamu fiddaku aduhu. Kallonsa ya maida gasu iya abu ya ce, "abu munason jin wani abu daga bakinki keda malam dauda, malam dauda yay saurin 'kar6e maganar da faďin wlhy alhaji banida laifi kona sisin kwabo, kaga wanan munafukar ya nuna iya abu, to duk wani kulli ita tasanshi tareda hajiya matarka da alhaji Tasi'u yayanka da matarsa, saikuma abokanka uku da 'kanwarka matarka hajiya sadiya, saikuma Nasir kanin matarka, duk wani bayani abakin waďannan mutanen dana lissafa zaka sameshi dan sune suka kulla abinsu, nima saboda hakane aka danneni da asiri nakasa ta6uka komai arayuwata. Dady ya ce, "malam dauda su waye abokannawa??, malam dauda ya ce, "alhaji safiyanu da marigayi alhaji lawan da alhaji mansur......atsorace dady yake kallonsa saikuma yazaro waya da sauri batarda yayi maganaba ya hau kiransu ďaya bayan ďaya da bu'katar son ganinsu, cikin minti goma sha biyar suka iso kusan atare, ba abunda sukayi zaton ganiba kenan dan haka dasuka shigo duk sai suka rikice bayan sun gama bin falon da kallo, dady ya ce, "kuzauna mana, amnafa kuyi ha'kuri bansanar daku dalilin kiranba. Tsohuwa ta katse musu zance da faďin wai mike faruwane, nifa sai "kara rikitar dani kukeyi da sakani aduhu,, kiyi hakuri mama yanzu zaki fahimci komai, abu bismillah...ina kika samu wannan ďiyar??????. Ďagowa tayi tana kallon ameeda, muryarta na rawa ta ce, "hajiya ce tabani.......................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!!. 💖abba gana💖 💝bilyn Abdul💝 [3/1, 11:30 AM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM (☆bilyn Abdul☆) Page2⃣3⃣&2⃣4⃣ .......gaba ďaya falon suka maida kallonsu ga iya abu, dady ya ce, "wace hajiyar? Ta ce, "hajiya hassana, gaba ďaya falon suka ďauki sallallami tareda tafa hannye, tuni hajiya hassana ta zauna jagwaf tana zufa, dady ya ce, ta yaya tabaki ita?. Iya abu ta matso hawaye sanan tafara bada labari daga tushe. Kamar yanda kuka sani hajiya hassana itace matar alhaji ta farko, sunkai tsawon shekara ashirin ALLAH bai basu haihuwaba, gashi kuma ALLAH ya azurta alhaji da tarin dukiya, yana cikin damuwa ta rashin haihuwa amma baita6a yin'kurin 'kara aureba, har saida mahaifiyarsa ta taursasashi, alokacin 'yan uwa sun goya masa baya da'kin amincewa dan bayason 'kara aure saboda 'kaunar dayakema matarsa hajiya hassana, saidai dukda haka acikinsu akwai masu goyama mama baya, akan alhaji ya 'kara aure, ba 'karamar fama akayiba kafin ya yarda ya 'kara aure, ya auri hajiya saliha wato momy, tunda ya auri hajiya salaha zaman lafiya ya 'kaura agidansa ta 6angaren hajiya hassana, kwata2 bata 'kyaunar tabuďe ido taga hajiya salaha agidan, abinda yasa duk nasan wanan shine tun ina yarinya aka kawoni wajen hajiya hassana amatsayin 'yar aiki daga 'kyauyen kokai, hajiya hassana tanada faďa sosai da kalolin shirya makirci iri2, to sai akayi sa'a halinmu yazo ďaya, ganin haka yasa tasakani cikin lamuranta sosai, duk wani mugun abu na asiri kona tsafi dazata kulla akan alhaji to da sanina harma da taimakona, ganin na kwarance awajen mugun hali yasa hajiya tasa dauda mai gadi ya aureni dan bataso nayi nesa da ita ko kaďan, dauda baya sona alokacin amma saida muka shiga muka fita yasoni, alhaji yabamu BQ Muka zauna, babu daďewa da aurenmu ya auro hajiya saliha. Wanan aure ba'karamin girgiza hajiya hassana yayiba dan tasan saboda bata ta6a haihuwaba aka saka alhaji 'kara aure, alokacinne muka 'kara haukacewa da bin bokaye da malam tsibbu, gaba ďaya magana ďaya suke gaya mana shine hajiya saliha zata haihu kuma zama daram agidan alhaji. Hankalinmu yayi matu'kar tashi domindai hangen hajiya hassana bai wuce dukiyar alhajinba, wadda take ganin tareda ita aka tara, amma tana ji tana gani zata zama 'yar kallo akan dukiyar, dan yana mutuwa 'ya'yan hajiya saliha zasu gajeta saidai abata tumilin takaba, duk da haka bamu daina bin malamaiba saima abinda yay gaba, akuma lokacinne nasamu ciki na sanar da hajiya hassana, tayi farinciki sosai da wanan ciki wanda har hakan yafara bani mamaki, amma saidaga baya tasameni da wata shawara itada alhaji Tasi'u yayanka. Sunce zasuce maka hajiya hassana tanada ciki, sunyima wani dector magana zai bata magani tazama kamar mai ciki, nikuma ina rainon ciki, idan nakusa haihuwa zatayi dabarar dazamu bar 'kasar na haihu acan sai ace itace ta haihu, nima na haihu ďan baizo da raiba, dafarko na nuna kin amincewata amma dasukace zasu bani miliyoyin kuđi bayan ankasheka saina amince. Kwana biyu da faruwar haka saiga zance yafito hajiya saliha tanada ciku, lallai alhaji yayi farinciki hakama sauran dangi amma banda mutum uku dakuma abokanka, daga nan muma saimukace hajiya hassana tanada ciku, dayawa wasu basu yadda da zancenba, amma dayake likita ya aiwatar da komai sai alamomi namai ciki suka bayyana ga hajiya saliha; tonikuma bama kowa yasan inada cikiba tunda bana zuwa ko ina, bakuma kowa k zuwa gidanba saboda bala'in hajiya hassana, bama kowa k gane inada cikiba saboda banida girman ciki, saima mai lurane zai gane. Mun gayama dauda dukkan shirinmu amma saiya'ki yarda ya ce, "bazai ci amanar alhajiba, damukaga zai kawo mana yawa saimukayi masa abinda bakinsa zai rufe ruf koda wasa bazai sake maganarba, ALLAH kuwa ya amince mana daga nan muka samu kan dauda harma yafara taimaka mana abisa kullin namu. Gallazawar da akema hajiya saliha tasa alhaji ya canja mata gida, hajiya taji haushin hakan matu'ka, dahaka wata tara tacika, zuwa sanan ko alhaji ba'a bari yaganni ita kuma hajiya kullum tana gama da tulin tsumma aciki, wata ranar talata natashi da na'kuda, cikin dare na haifi ďa naminji, wanan lamari yayima hajiya hassana daďi dan sanan alhaji bama ya 'kasar, asirinmu rufe muka gama komai, likita yabama hajiya magani ruwan nono yazo mata tashiga shayar da jariri, nikuma ina gefe ina jiyyar kaina. Kwana biyu da haihuwata hajiya salaha ta haihu saidai ďan baizo da raiba, anyi shagali a sunan ďana wanda yake amasa sunan ďan hajiya hassana ga wanda bai saniba, yaro yaci suna baban alhaji wato usman muna kiransa Sayeed, afirgice dady yake kallon iya abu da dukkanin muta nen falon, iya abu ta share hawaye tareda ci gaba da bada bayani. Watan Sayeed uku aduniya nasamu ciki, nayi murna sosai dan koba komai nima zan ri'ke ďa ahannu, haka naita rainon ciki har wata tara sanan na haihu 'ya mace, Alhaji yay mana hidima dan acewarsa mun zama 'yan uwa. Daga nan ban sake haihuwaba har hafsa takamu da 'kyanda ta rasu, nayi kuka sosai su hajiya nata lallashina, sai bayan shekara uku muka samu ciki tareda hajiya saliha, alhaji yayi farinciki da cikin hajiya salaha dan tahuta da gorin da hajiya hassana take mata na rashin haihuwa, ALLAH kuwa ya inganta mata muka haihu tare ni namiji ita mace, a wanan haihuwama anufin hajiya ce ta haihu baniba, aka sakama ďa sunan baban hajiya wato Abubakar shine sadiq kenan, itakuma hajiya salaha aka sakama ďiyarta Khadija....bayannanma tadaďe bata haihuba, hajiya hassana ta tsani khadija sosai bata 'kyaunar yarinyar, dan haka wani daren juma'a tabama yarinyar shinkafar 6era ta mutu.......hazbinannalahu wani imal wakil aka shiga amabata afalon, arikice dady yami'ke ya sha'ke hajiya hassana cikin wata irin murya maiban tausayi yake faďin dama kece kika kashemin yarinya hassana kin cuceni kin cuceni kin cucenu....dakyar aka 6an 6areshi daga jikinta ana lallashinsa, su hajiya ansha sha'ka sai wurga idanu take kamar kwaďo aruwan zafi, iya abu tacigaba dafaďin daganan ALLAH ya'kara bama hajiya salaha ciki ta sake haihuwar mace aka sakamata khadija itama. Itama hajiya taso kasheta amma ALLAH bai yardaba, daga nan suka shirya mitin itada alh Tasi'u, alh safiyanu, alh mansur, alh lawan, sai 'kanwarta haj sadiya, haj laure matar alh tasi'u, abu, sune suka yanke shawarar sace khadija daga wajenku, dan 'ya'yanta suci gado su kaďai konace 'ya'yana, anyanke shawarar nizan ďauke Ameeda muyi nesa da abuja nida dauda karmu sake koda tunanin zuwa, duk abinda muke bu'kata za'a yimanashi, sunce mu raini yarinyar cikin rashin tarbuyya dan anaso ta tashi abauďe, inda halima tazama karuwa dukdai wani halin rashin kirki yazamto tana aikatashi, tashi ďaya miliyan uku aka bamu, to mukuma bamu ta6a ri'ke ko dubu ďari biyu ba shiyyasa muka haukace muka ruďe, akaje kano aka nema mana gida, muka gudu, rana ďaya kuka nememu kuka rasa ko sama ko 'kasa, daga 'karshema saikuka ďauka sacemu akayi, saida muka tafi dakusan wata uku sananan aka sato mana khadija aka kawo mana shiyyasa baku ta6a zargin mune muka sacetaba, amma labari yazo mana akan irin rikicewar dakukayi na rashin khadija kunshiga ruďani sosai aka sanar damu dan Alhjima saida aka haďa da addu'a. Mukuma munacan muna rainon khadija wadda muka maidawa suna ameeda, ta taso a ta6are dan babu mai kwa6arta duk abinda tayi dai2ne babu mai cemata baiyi daidaiba, 'yar tallace sosai dan ta kware tun tana 'karamarta muke ďora mata harta girma. Munsata makaranta batareda sanin su hajiyaba, daganan tazama 'yar kanta, saidai bata bin maza ko kaďan wanan yasa hajiya hassana taturo 'kaninta Naseer yashiga rayuwar ameeda sosai yakoya mata abubuwa masu yawan gsk narashin arzi'ki, harda shaye2 dazuwa club wanan shine abinda yafaru ga ďiyarku kwara ďaya tilo ameeda, duk 'karshen wata su hajiya suna aikamana da kuďi danmuyi bu'katunmu................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 💝bilyn Abdul💝 [3/4, 12:16 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Wananan page ďin nakune mmn twins & ummiyy kunfi kowa son littafinnan, mungode ALLAH yabar 'kauna😍😍😘😘 Kuyi hakuri dajinmu shiru babu posting Luv u oll😘😘😘😘😍😍 Page2⃣5⃣&2⃣6⃣ ......a haukace dady yami'ke ya sha'ke wuyan haj hassana yana kuka, yawancin mutanen falon duk kuka sukeyi musamman ma ameeda daji take tamkar ta tashi tahau su iya abu da duka, kuka take kamar ranta zai fita, jitake babu wanda ta tsana aduniya kamarsu yanzu, musamaman ma haj hassana data rabata da iyayenta tun tana 'yar 'karama, gsky bata zaton zata iya yafemusu koda nan gaba. hajiya tsohuwa ta ce, "wa ameeda zonan jikata naji ďumin jikinki kinji, dan jitake kukan da Ameedan takeyi tamkar aranta takeyinsa. Agefe kuwa ana kici2n kwace haj hassana daga sha'kar da daddy yay mata, da'kyar aka yakiceta sai hakki take da kakarin mutuwa, daddy ya ce, "wlhy kudukanku sai munshiga kotu daku babu fashi, sai an kwatar min hakkina awajenku, azzalumai, maciya amana, kekuma nasakeki sai uku!!!! Kibarmin gidana karna sake ganinki, nayi dana sanin kasancewarki matata mara imani....kuka ya sar'keshi yakasa cigaba da faďar abinda ke zuciyarsa. haj hassana sai kururuwar kuka take da bashi hakuri, Alhaji karkayimini haka dan ALLAH katunafa shekara talatin da biyar muna tare dan ALLAH karka gujeni alokacin danakeda bu'katar zama dakai, ka taimakeni alhaji ka tausaya mini....tasake rushewa da kuka tareda kama 'kafarsa, hankaďata yayi ya taka mata hannu harsaida yay 'kara yafice fuuuu...wata galabaitacciyar 'kara tasaki dan azaba, babu wanda yay yun'kurin taimakonta, bayan wasu 'yan mintuna saiga dady da gayyar 'yan sanda, yayibarsu aka sakeyi su bakwai akai ciki dasu. Bayan wasu 'yan awanni komai ya natsa, Ameeda tabasu labarin halin data tsinci kanta awajensu iya abu da yanda rayuwa tamai da ita adalilin Naseer, kuka suke sosai cike da tausayinta, ta ce, "ashe inada gata bansaniba??, ashe su ba iyayena bane?, shiyyasa suke cutar dani ta hanyar lalatamin tarbiyya, shiyyasa basu ta6a damuwaba da halin dana tsinci kaiana, ya Muzzaffar haďuwata dakai alkairine, bazan ta6a mantawa dakaiba, kataimakeni kataimaki rayuwata kacetota daga hali irinna gur6atattun mutane, ngd ngd ngd yayana abin alfaharina...ta kara rushewa da kuka, dady dake kusada ita yarungumeta yana lallashi saikace wata karamar yarinya. Tabasu tausayi kwarai da gsk, amma babu komai zasu sharemata hawayen shekara ashirin da biyu dataketa zubarwa, zasu maida ita 'yar gata kuma mai gata. Tun aranar tafara ganin gata na musamman ga iyayen nata, komai saidai ayimata, jinta take tamkar awata (SABUWAR DUNIYA littafina mai zuwa), lallai tayarda ita 'yar gatace kuma a bar so ga kowa, ranar agidan kaka ta kwana, tasha tarairaya. RAYUWAR AMEEDA A SABUWAR DUNIYA. tana zaune afalo cikin 'kayatacciyar kwalliya ta burgewa, 'yan tagwayen yarannan dabamusan ko 'ya'yan waye ba har yanzu suna gefenta suna mata surutu sai faman murmushi take dan tanason yara, ita indai yaro baida fitina to xata iya zama dashi, ya Muzzaffar yashigo falon da sallama, ta ďago manyan idanunta tana amsa masa, fuskarta cike da murmushi. Dagudu yaranan sukaje suka tarosa, ya tarbesu shima da farinciki, kusada ameeda ya zauna datake binsu da kallo cikin sha'awa da matu'kar birgewa zuciyarta na kissima mata abubuwa dayawan gsk, har yazauna kusada ita bata saniba, ya hura idananunta dake tsaye 'kyam awaje guda. Ajiyar zuciya tasaki tana murmushi, saikuma ta shagwa6e fuska kai yaya sokake idanuna su bushe??. Yay murmushinsa mai 'kayatarwa tareda juyowa sosai suna fuskantar juna, ya sanyaya muryarsa tareda faďin khadijah na mikike runanine??. Hannu tasaka tana rufe fuska ta ce, "babu komai. Hummm niko kinga nasan abinda kike tunani, taďago kai da sauri tana kallonsa to faďi naji idan kacanki gsky. Yaďan jinjina kai tareda latse baki, idan na faďa minene tukuycina??, ta rausayar da kai gefe duk abinda kabukata indai bai sa6ama shiri'a ba kuma inadashi zan maka, yasake yin murmushi mai sauti, kina tunanin inama ace su 'yan biyu 'ya'yanmune na cikinmu ya 'kare maganar da kashe mata ido ďaya, idanu ta zaro lah yaya nidai babu ruwana kuma ba haka nake tunaninba. Ya ce, "uhhmyiiim ban yardaba, kirantse indai ba haka bane, tashitai da niyyar guduwa yay saurin dam'ke hannunta, saikuma yay saurin saki, tajuyo ahankali tana kallonsa, saikuma ta tuna rayuwarta da Naseer, tatuna babu abinda yafi bu'kata arayuwarsa irin jikinta, kullum burinsa yaza'ayi ya mallaketa, ashe akwai sauran mutane masujin tsoron ALLAH da tsare dokokinsa??, ashe akwai masu gudun aikata alfasha komin 'kan'kantarta, jiki asanyaye takoma ta zauna, cikin sayin murya ta ce, "yayana inasonka ina 'kaunarka, kaine mutum nafarko dana faraso amatsayin masoyi, kaine mijin daya dace da rayuwata, kaine kaďai zaka iya saita sauran halayena dasuka nemi ku6cemin.....ta rushe da kuka mai tsuma zuciya. Xamowa yayi daga kujerar, ya tsuginna agabanta, banason ganin kukanki khadija nima nadaďe ma'kale da 'kaunarki araina kawai dan baki bani dama bane, nasan alokacin kina tsoron Naseee ne kawai, amma inaji araina kece uwar 'ya'yana, ahankali yakai hannu yana share mata hawayenta. Su momy dake la6e suna kallonsu cikin farinci da jin daďi, jisuke tamkar su tashi sama dan daďi, lalai za ayi bikin 'yan gata.........wata sallamace ta katse musu farincikin nasu, gaba ďaya sukajuyo suna kallonsa cikin mamaki da al'ajabi. Wani saurayine baki, dakagansa kasan arikice yake; kodai abuge kokuma yanada ta6un hankali, hannunsa rikeda bindiga...😳...............✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!. 💖abba gana💖 💝bilyn Abdul💝

---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Kukan kurciya 17&18



🐾KUKAN KURCIYA.......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Assalamu alaikum. muna mi'ko gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyanmu aduk inda kuke,, kuyi ha'kuri dabaku pages ďai2 damukeyi kullum, littafin namu gajeren labarine,, insha ALLAHU muna gab da kammalashi,, mungode da 'kaunarku garemu,,, luv u oll😍😍😍😘😘. Page1⃣7⃣&1⃣8⃣ ..........jikinta sai rawa yakeyi cikin kuka take bashi ha'kuri dan bataji daďin yanda tayi masa 'karyaba, kayi ha'kuri yayana wlhy badan banida gskya yasa na 6oyemaka sirrinaba akwai wasu dalilai masu yawa,, amma ina ro'konka da ka gafar ceni, insha ALLAHU wanan shine nafarko na 'karshe dazan yimaka 'karya akan abinda yashafi rayuwata, ta ďago tana kallonsa sai taga shikuma hankalinsa yana kan babanta dake tsaye a'kofar gida yana cin goro. yayana!! tafaďa cikin sanyin murya, ahankali yajuyo yana kallonta cikin in ina ya ce, "beauty waye wancan??, babanane tafaďa cikin 'kwarin gwuywa. Tafďijan yafaďa azuciyarsa, Ameeda ta ce, "koshima kasanshi ne??, A'a yafaďa a ta'kaice amma idanunsa nacigaba da kallon malam dauda. Ameeda tabuďe motar tafice tana faďin to sai mun haďu gobe ko?, okey karki damu kijirani agida insha ALLAHU 'kar fe biyu zanzo miki da abu uwan mamaki, kinsan masu iya magana sunacewa KUKAN KURCIYA JAWABINE.......Ameeda ta'karasa da faďin "mai hankaline yake ganewa yayana, murmushi yayi tareda mi'ka mata dubu biyar ya ce, "sai kinjini, okey bye tafaďa tana ďaga masa hannu. Koda tashige gida yadaďe zaune amota yana karema malam dauda kallo, daga baya yafice yabar anguwar, gida yaje yay wanka yanufi filin jirgi sai abuja. Da wuri ya isa yauma mutanen gidan sunyi farincikin zuwansa, bayan yaci abinci ya huta, suka haďu afalon daddy, daddy ya ce, "Muzzaffar kace mana a kwai magana amma munjika shiru. Muzzaffar ya murmusa, tabbas daddy akwai magana, dan yau na'kara gano abin mamaki kamar yanda na faďa maka awaya, inaso ka shirya mana tafiya kano muduka harda hajiya babba. Bangane mikake faďaba Muzzaffar???, daddy zaka gane amma sai goben.........momy ta katse musu zancen da faďin a'a muje mu kaďai idan komai ya bayyana sai azo har inda take, kasan halinta sarai, kuma batason zuwa kano da kowa. Gsky ne daddy yafaďa, yanzu saimu kwana cikin shirin zuwa kano insha ALLAH. Washegari sukai 'kaura zuwa kano, dayake jirgi sukabi har saida suka huta agidan muzzaffar, kamar yanda yay mata al'kawari 'karfe biyu suka iso anguwar dan masallataima sunata sallar karfe biyu, amotar suka zauna babu wanda yafita sai muzzaffar, kansa tsaye yashiga cikin gidan saboda anyi masa iso, tunda yashigo iya abu tayi mutuwar tsaye, cikin in ina take nuna Muzzaffar Ameeda ina kika san wanan👉🏻🙎🏻‍♂??. Ameeda dake tsaye tana kallonsu ta ce, "iya Shinefa Muzzaffar ďin danake gaya miki, kumafa kece kikace ya shugo, ganin ta rikice da ganinsa sai Muzzaffar ya basar ya tsugunna har 'kasa yana faďin mama ina yini?, cikin rawar baki ta ammsa, baibi takantaba ya haye tabarmar da'aka shinfiďa masa ya zauna. Ana cikin haka baba ya shigo gidan shima yarikitu da ganin Muzzaffar amma sai muzzaffar ya fuske ya'ki bada kofa koďaya ta alamun yasansu, nanma rissinawa yayi ya gaida baba, atsorace ya amsa tareda faďin yaro mike tafe dakai ne???. Murmushi Muzzaffar yayi ya ce, "baba nidai sunana Muzzaffar nafito ne daga 'kasar kamaru, ALLAH ne ya haďani da Ameeda naji kuma inasonta, wani ďan aikine yakawoni Najeria saidai bansan ko inaba bankuma san kowaba akasar sai Ameeda dana fara karo da ita. Ajiyar zuciya baba da iya abu suja lokaci ďaya itadai Ameeda duk kanta a ďaure yake, tana mamakin miyasa yayi 'karya??, bayan ita yafaďa mata iyayensa suna abuja. baba ya ce, "yaro kana nufin kaiba ďan kasarnan bane??, eh hakane baba, niba ďan nan bane, domin a kamaru ďinma ba anan na girmaba a london na girma, lokaci ďaya suka washe baki iya abu ta ce, "masha ALLAH aimu wlhy sai kayi mana kama dawani damuka ta6a sani. Ayya aidama haka rayuwa tagada mama, saikiga baka haďa komai da mutumba amma kuna kama da juna, nima haka mutane sukecewa ina kama da Ameeda sosai tamkar jini ďaya muka fito????. Idanu suka zazzaro tareda haďa baki wajen faďi kuma???. Ya ce, "ai ikon ALLAH kenan kawaidai kamace, ya za'ayi muzama jini ďaya bayan tana Najeria ina kamaru koma nace london, wanan shine karo na farko dana ta6a zuwa 9ja. Ajiyar zuciya suka 'kara saukewa sukace eh gskyar ka kuma. Ya ce, "to nazo neman aurenta ne indai zaku bani, amma inaso asadani da ainahin iyayenta. Iyayenta kuma???? suka haďa baki wajen faďa suna kallon juna. Muzzaffar ya ce, "eh ina nufin kanin baba ko yayansa tunda sune masu ďaura aurenta. Eh kayi gaskiya yaro suka faďa suna sauke ajiyar zuciya. Muzzaffar yasake faďin saidai abinda yabani mamaki ko kaďan bakwa kama da ita anya kuwa ba sato................da sauri sukace satowa kuma yaro??????, nanama suka faďa suna dafe 'kirji. A'a bahaka nake nufiba, ina nufin kota sato kamannin wanine a danginku???. Ohhhhhh yaro kace wani abu, tana kamane da kanwar kakar baban babana ce. Ayya ammadai tayi 'ko'kari data ďakko gida, dan ance duk wanda yabar gida gidafa ta barsa, saidai inane asalin 'kauyen naku, dan can yakamata akai kuďin aurena. Kallon juna sukayi Yaro kauye kuma???,,, suka faďa suna haďa baki. Eh baba wai ina nufin asalinku, dan inaso na auri 'yar dangi mai asali kuma. To to to wannan magana da girma take yaro. Miye girmanta baba???, kodai dangin kune a abuja dan naga kamarsu da Ameeda, tayi kama sosai dasu. Abuja kuma yaro???? suka faďa kamar zasuyi kuka. A'a kukwantar da hankalinku nifa nayi muku hannunka mai sandane, yanzu ina tareda iyayena zasu shigo idan kun basu izini dan sunaso ku gana kamar yanda al'adar kasarmu kamaru take kenan, dan gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kamaru. To sushigo mana bari asaka musu tabarma. Duk abinnan da akeyi Ameeda tana zaune kamar gunki tana kallon alamomin rashin gsky kuru kuru a idanun iyayennata, lallai yau akwai abubuwan mamaki masu kamada almara agidannan, ita harma tarasa yanda zata fassarasu. Shin kodai ya Muzzaffar yasan wani abu gamedasune??, miyasa yakema iyayenta wanana tambayoyin ma wai??, miyasa sukan rikice aduk lokacin da yay musu tambayar ne???, gaba ďaya takula sun fita hayyacinsu.. Amota ya tarar dasu momy, ya kallesu yana murmushi, dady ina fatan kunajin duk yanda mukayi ta waya???, kwarai kuwa ďan kirki muna jinku, inagadai dukkan hasashenmu yazama gasky kuma ALLAH yakawo mana 'karshen damuwa ta shekara ashin da biyu dasuka wuce. Murmuahi yayi To ALLAH ya tabbatar iyayena, yanzu kamar yanda kukaji sunce ku shigo. To suka faďa suna fitowa. Duk wanan tanbayoyi da Muzzaffar yakema su iya abu wayarsa a kunne take, dankuwa kiran daddy yayi ya ajiye wayar komai sunaji har aka gama. Da sallama suka shiga gidan, iya abu da baba suna zaune yayinda Ameeda take zaune a inda suka barta kamar dutse. Tunda suka rangaďa sallama suka shigo kallo ya koma sama, dominkuwa tuni su iya abu sunyi mutuwar zaune, ko yatsun hannunsu sun kasa motsawa, Ameeda ta mi'ke zummbur dan tun shigowar muta nen biyu gabanta yake dukan uku2 tamkar zai fito waje, jinta take tamkar ba'a duniyaba, sai kawai ta yanke jiki tafaďi awajen batareda daliliba. Da gudu Muzzaffar yayi kanta yana kiran beauty! Beauty!!!. Ina beauty ta suma, jiki na rawa momy ta 'karaso wajen tana jijjiga Muzzaffar da Ameeda dake jikinsa. Acan kuwa tuni fitsari ya ji'ke wandunansu iya abu da malam dauda, tuni sunshiga cikin kogin kwadamin ruďani da kiďima, lallai yau kashinsu ya bushe, lallai yau itace ranar tonan asiri, lallai yau itace rana dubu ta 6arawo ďaya kuma tak tamai kaya, lallai yau itace rana mai firgitarwa, lalai yau itace rana ta cizon yatsa da ambatar dana sani. Lallai yau itace ake kira da 'karshen tuka tuki tikkk. Adai dai wanan lokacinne kuma Naseer yashigo gidan ko sallama babu, tofa shimafa mun lura 'kamewa yayi atsaye tamkar bishiyar da aka dasa awaje ďaya, gaba ďaya zufa ta gama wanke masa dukkan sassan jikinsa, jiyake tamkar ya saki kashi atsaye, lalaikam idan zomo na yawo tofa kerema yana yawo tabbas wata rana za'a haďu, yau itace ranar zadata girgiza mutane masu ďunbin yawa, wasu zasu rasa daula, wasu zasu rasa aure, wasu zasu rasa aiki, wasu zasu rasa mutunci, wasu zasu rasa girma, wasu zasu bakunci gidan yarinema, tofa tabbasa Nas yana ganin kila yana cikin masu ziyartar gidan yari, dan yau ranace mai kamada ranar hisabi amma na duniyyyyyyyya😜. Tofa wai miye sirrin wanan rikita2ne???, wai miye abinda ake tsoron yafarune??, wai miye dalilin shigar mutane masu yawa cikin ruďani haka?????, miye tsakanin su muzzaffar da Ameeda ne???, miye tsakanin Nas dasu muzzaffar ne???, waishin ma waye muzzaffar???, waye Naseer???, suwaye su iya abu?????, wacece Ameeda??????, miye matsayin momy & daddy awanana bada 'kala???, miye kuma ya haďa wanana ahali akarkashin runfar rikici ďayane??????????... Mukaďaine masu baku wanana amsar, dan haka ku kasance damu........................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝

---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).