shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 25 January 2019

SHAWARWARI 52 ZUWA GA MATAN AURE, ZAWARAWA DA 'YAN MATA - SIFFOFIN UWA TAGARI 10

SHAWARWARI 52 ZUWA GA MATAN AURE, ZAWARAWA DA 'YAN MATA - SIFFOFIN UWA TAGARI 10

Shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani, kafin a yi auren. Ga wasu shawarwari 40 wadanda idan matan suka yi la'akari da amfani da su da yardar ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure.

     1.     Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
       2.     Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.
       3.     Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.
        4.     Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
         5.     Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
6.     Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.
7.     Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.
8.     Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.
9.     ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.
10.Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan uwansa da abokansa.
11.Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
12.Kada ki zama mai satar fita unguwa.
13.Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.
14.Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.
15.ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.
16.ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.
17.Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
18.Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.
19.Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.
20.Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.
21.Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.
22.Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.
23.Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.
24.Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.
25.Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.
26.Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.
27.Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.
28.Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
29.Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.
30.Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.
31.Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
32.Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.
33.Kada ki zama mai yin dare wajan girki.
34.kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.
35.Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.
36.Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.
37.Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
38.Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.
39.Kada ki ringa baiwa 'yan uwan mijinki labarin laifukansa.
40.kada ki ci wani abu da mijinki baya son warinsa misali tafarnuwa.

Allah ya bada iko wajen kamanta da aiki da shawarwarin.
Share:

NASIHA ZUWA GA MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 9

NASIHA ZUWA GA MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 9


NASIHA ZUWA GA MATAN AURE
Ki kasance mai yi wa Allah biyayya a bayyane da boye, shi zai hana miki cutar da wadanda kike tare da su, mutane ne ko dabbobi, ki sanya wadannan sunaye hudu na Allah a tare dake koda yaushe, su ne kamar haka: “Assamii’u – Albasiiru – Al’aliimu – Alqadiiru”. Idan ki ka sa wadannan sunaye a gaba gare ki, to zaki rabauta a duniya da lahira, domin zaki bauta ma Allah kamar kina ganinsa.
Ki kasance mai gudun duniya kada ki qwallafa wa kanki wannan duniyar, domin ida ki ka lura da ita, za ki ga cewa masu wadatar cikinta mafiya yawa ba su samun wadatar sai bayan shekara ar’abin ko makamancin haka, sai mutuwa ta dinfare su. Wadanda kuma suka same ta a lokacin quruciya sai ka ga nan da nan mutuwa ta zo masu. Amma idan ki ka guji duniya, ki ka fuskanci lahira, sai ki ga kwanakinki sun zo maki a cikin sauqi.
Ki kasance mai qanqan da kai ba mai alfahari ba, domin ki sani duk inda ki ka kai wajen wadata ko mulki akwai wacce ta fi ki, domin mafiya yawan mata akwai su da ji – ji da kai da taqama, kuma wannan ba dabi’a ba ce mai kyau.
Ki nisanci kwalliya da sanya turare yayin fita, ba ina nufin kada ki yi tsafta yayin fita ba, a’a, a yau mafi yawancin mata idan za su fita unguwa ko asibiti ko gidan suna su ci kwalliya suna bayyana adonsu, koda ko sun sanya hijabi har qasa sun sanya niqabi. Za ki gan su sun bayyana adonsu ta wurare da dama; ta wajen idanunwansu, da daurin niqabansu, da hannayensu, da qafafuwansu, tare da cewa sun kulle jikinsu duka, saboda haka ki kasance mai tsafta koda yaushe, amma ki nisanci bayyana ado yayin fita, domin wannan shi ne zama lafiya gareki.
Ki yi amfani da lokacinki wajen abin da zai amfane ki duniya da lahira, ta hanyar karatun alqur’ani, zuwa makaranta, sannan ki nisanci gulma, hirar banza, yawan surutu da dai sauran su, domin wadannan abubuwan baza su Haifa maki da mai ido ba. Kiyi amfani da lokacin ki wajen abin da zai amfane ki ya kusantar dake zuwa ga Allah.
Ki zamanto mai qarancin Magana ba mai yawan surutu ba, ki zamanto babu wata kalma da za ta fita daga bakinki sai alheri, kada a ji maganganun banza a bakin ki.
Share:

SAKO ZUWA GAREKU MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 8

SAKO ZUWA GAREKU MATAN AURE - SIFFOFIN UWA TAGARI 8

Aure dai sunna ne na manzon Allah S.A.W, don haka a kowace sunna akwai lada matukar dai an yi ta kamar yadda manzon Allah S.A.W ya koyar. Don haka shi ma aure yana da nashi ladan idan aka yi shi kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya koyar. Manzon Allah S.A.W ya yi bayanin irin ladan da ya kamata mace ta samu wajen biyayyan ta ga mijinta. Duk matar da take kyautata ma mijinta, tana faranta masa rai, tana kwantar masa da hankali, tana taya shi farin ciki a lokacin farin ciki, ta kuma taya shi bakin ciki a lokacin bakin ciki. To babu shakka itama xata ga farin ciki a duniya da lahira, Allah ya sa mu dace, amin.

Ya zo a cikin hadisin AbdurRahman Bn Auf, Allah ya kara masa yarda inda yake cewa Manzon Allah SAW ya ce "idan mace ta yi sallar ta guda biyar, kuma ta azimci azimin watan Ramadana, kuma ta kama kanta daga zina, kuma ta yi wa mijinta biyayya. A ranar lahira za a ce mata ki shiga aljanna ta kofar da kike so. Imamu Ahmad ya ruwaito wannan hadisi, kuma Albani ya inganta shi acikin SAHIHUT-TARGIB. Don haka ya kamata matan aure su kula da yin biyayya ga mazajensu. Akwai wata mata da mijinta ke bada labari: yace wata rana ya bar Abuja inda yake aiki zuwa Kaduna inda iyalinsa suke, koda ya zo sai ya kunna fanka don ya sha iska, har bacci ya dauke shi, sai aka dauke wuta, matarsa na ganin haka sai kawai ta dauko kujera da mafici ta zauna kusa da mijin tana masa fifita har sai da gari ya waye.


Da aka kira sallah sai ta tashe shi domin ya yi sallah, da ya ganta a zaune sai ya tambaye ta me ya faru take zaune kusa da shi? Sai ta ce masa ai yana kwanciya sai aka dauke wuta, don haka ita kuma tunda a wajen nemo masu abinci ne ya gaji, kuma gashi yana so ya yi barci amma zafi ya hana shi, to bari ita ta bar nata barcin don shi ya samu ya yi barci. Allah ya yi ma wannan mata albarka, Allah ya baku ikon yin koyi da ita. Dan duk matar da mijinta ya shede ta akan wani abin kirki, to lallai Allah ma zai yabe ta. Allah kasa ku kasance cikin mataye nagari. Amin.
Share:

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).