Aure dai sunna ne na manzon
Allah S.A.W, don haka a kowace sunna akwai lada matukar dai an yi ta kamar
yadda manzon Allah S.A.W ya koyar. Don haka shi ma aure yana da nashi ladan
idan aka yi shi kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya koyar. Manzon Allah S.A.W ya
yi bayanin irin ladan da ya kamata mace ta samu wajen biyayyan ta ga mijinta. Duk
matar da take kyautata ma mijinta, tana faranta masa rai, tana kwantar masa da
hankali, tana taya shi farin ciki a lokacin farin ciki, ta kuma taya shi bakin
ciki a lokacin bakin ciki. To babu shakka itama xata ga farin ciki a duniya da
lahira, Allah ya sa mu dace, amin.
Ya zo a cikin hadisin
AbdurRahman Bn Auf, Allah ya kara masa yarda inda yake cewa Manzon Allah SAW ya
ce "idan mace ta yi sallar ta guda biyar, kuma ta azimci azimin watan
Ramadana, kuma ta kama kanta daga zina, kuma ta yi wa mijinta biyayya. A ranar
lahira za a ce mata ki shiga aljanna ta kofar da kike so. Imamu Ahmad ya
ruwaito wannan hadisi, kuma Albani ya inganta shi acikin SAHIHUT-TARGIB. Don
haka ya kamata matan aure su kula da yin biyayya ga mazajensu. Akwai wata mata
da mijinta ke bada labari: yace wata rana ya bar Abuja inda yake aiki zuwa
Kaduna inda iyalinsa suke, koda ya zo sai ya kunna fanka don ya sha iska, har
bacci ya dauke shi, sai aka dauke wuta, matarsa na ganin haka sai kawai ta
dauko kujera da mafici ta zauna kusa da mijin tana masa fifita har sai da gari
ya waye.
Da aka kira sallah sai ta
tashe shi domin ya yi sallah, da ya ganta a zaune sai ya tambaye ta me ya faru
take zaune kusa da shi? Sai ta ce masa ai yana kwanciya sai aka dauke wuta, don
haka ita kuma tunda a wajen nemo masu abinci ne ya gaji, kuma gashi yana so ya
yi barci amma zafi ya hana shi, to bari ita ta bar nata barcin don shi ya samu
ya yi barci. Allah ya yi ma wannan mata albarka, Allah ya baku ikon yin koyi da
ita. Dan duk matar da mijinta ya shede ta akan wani abin kirki, to lallai Allah
ma zai yabe ta. Allah kasa ku kasance cikin mataye nagari. Amin.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.