shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 24 September 2016

TANA TARE DA NI... PAGE 86

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 86 BY MIEMIEBEE Take idanun d’an banza da sukaji rauni suka kad’a sukayi wani irin jaaa, hannayensa biyu na akan hannun Mr. Fauzi dake wuyansa yanata k’ok’arin cire hannayen amman ko kad’an yakasa dan bayida k’arfi ko kad’an Anas ya riga ya masa liqis. “An.. An... Anas ple...” Tari yafi k’arfinsa har anan Anas yak’i sakesa as ya d’au alwashin seya kashesa. Wani irin nishi Farouq yasoma ja da k’arfin bala’i. “ANAASSSSS!!!!” yajiyo muryan Abuu from far. “Anas don’t kill him ka sakeshi” yayi maganar yana gudu har seda ya iso wajen, k’ok’arin jan Anas daga kan Farouq yake amman ya kasa, “Anas ka sakeshi karka kashesa” seda wasu police guda biyu suka sa hannu sannan aka samu aka d’aga Anas daga kan Farouq. “Noo kubarni in kashe bastard d’innan, he dsereves nothing than to die. Let me go! Ku sakeni!” turesu gabad’aya yayi harda Abuu sannan ya sake komawa kan Farouq yakuma shaqure masa wuyan again, tsantsan azaba k’afafun Farouq se dancing suke, sake binsa su Abuu sukayi sunata k’ok’arin d’ago Anas har a yanzu Abuu bega Fannah ba se da ya juya kansa yaganta kwance so lifeless a k’asa gakuma jinin dake ta fitowa daga jikinta har yanzu. “Fannah!!” Ya kira sunanta da k’arfi hakan yasa Anas dawo da kallonsa wajen shima. “Anas ka sake Farouq its Fannah you need to focus on Anas matarka!” Da k’yar suka d’aga shi, da gudu yayi kan Fannah ya tattara ta a hannunsa se cikin motarsa a yayinda Abuu ya tsaya da police d’in ana carrying investigations, jakan kud’i da komai da komai duk aka sa cikin motar police daga k’arshe Farouq aka d’aga shima aka kaisa asibiti dan ko bara a iya hukuntasa a haka ba dole se ya samu sauk’i. An hour later... Baba, Mami, Afrah, Aiman, Abuu, Anas, Ummie, Shettima dakuma Amal duk zaune suke a harabar d’akin Fannah dukkaninsu fuskokinsu cike da damuwa, daga masu kuka se wanda suka had’a tagumi babu kaman Anas da ya kasa zama gu d’aya se pacing yake. Abuu ne ya miqe ya nufa inda Anas keta jeka ka kadawo tare da dafe kafad’ansa. “Anas you need to calm down in shaa Allah Fannah zata samu sauk’i muna nan muna mata addu’a taho muje ka zauna.” “Abuu I can’t wallahi in wani abu ya sami Fannah ko abinda ke cikinta I must kill Farouq with my own hands.” “Kabar magana haka in shaa Allah ma ba abinda ze samu Fannah” ya kwanto da Anas jikinsa yana bubbuga bayansa a sannu sannu yaja Anas suka koma suka zauna. Hannu yasa ya share hawayensa “Abuu mesa za’a kawo wancan son of a b*tch d’in nan asibitin? Mesa basu kaisa wani asibitin ba? Abuu why? Infact bekamata ma akawosa asibiti ba compared to abinda yama Fannah.” “Anas muyi focussing akan Fannah yanzu Farouq will follow afterwards.” 5 minutes later... Red globe dake a saman k’ofan d’akin da Fannah ke ciki ne ya d’auke in some seconds k’ofan ya bud’u atare duka families d’in sukayi wajen Anas ne a gaba. Cike da tashin hankali yake maganar “D... Dr... Dr how is she? How is my wife?” Ganin yadda Anas ke cikin tashin hankali Dr’n ya dafesa a kafad’a “Mr. Fauzi calm down karka damu your wife’s condition is stable zaka iya shiga ganinta bayan nan duka family zasu iya shiga ganinta also.” “Alhamdulillah! Dr. What of the baby? Shima ya rayu? Were you able to save my baby?” Kai kawai ya iya ya girgiza masa. “No Dr dan Allah karkace kun kasa saving babyna please...” ya k’are maganar cikin sautin kuka. “I’m so sorry Mr. Fauzi there is nothing we could do saboda anriga anyi terminating cikin ba yadda za’a iya saving baby’n it was destroyed already tun kafin kuzo nan, maganin Misoprostol da aka bata yagama aiki, maganin nada k’arfi sosai and yana leading to hard and painfull miscarriage we should be thankful ma maganin be b’ata mata hanji ba saboda overdose da aka bata.” “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” kad’ai ke tashi awajen se kuma sautin kukan da yabiyo baya Mami nayi Baba bata hak’uri haka Ummie da Amal ma, Afrah kuwa Shettima ne ke condoling nata. “I’m sorry excuse me please” yana kaiwa nan ya fice. Anas kuwa kasa riqesa k’afafun sa sukayi suuul ya sulale k’asa da wuri Abuu ya sake Ummie ya tarosa. “Ya kashe min baby Abuu he murdered my child.” “Shhh! Anas kayi hak’uri” A fusace ya miqe Abuu da Shettima suka soma kiran sunansa suna binsa, gudu yasa be tsaya ko ina ba se a d’akin Farouq. Banging k’ofar yayi take Ya Khaleel dake zaune gefen Farouq da kayinsa duk bandage hannunsa kuwa handcuff ne had’e da gadon dayake kwance akai. Kamar a kyaftawan ido Anas ya had’e Ya Khaleel da jikin bango tare da shaqure masa wuya Abuu da Shettima ne suka shigo da wuri suna k’ok’arin karb’e Ya Khaleel amman sun kasa dan yadda Anas ya rik’esa. “Ina kaga abinda shegen d’anka yayi wa Fannah? Kagani koh? And you are the one responsible irresponsible father kawai, wallahi both of you must pay.” da k’yar Ya Khaleel ke maganan “Anas dan Allah ka sakemin wuya dan-” tari ne yafi k’arfinsa da k’yar da taimakon wasu doctors biyu aka k’wata Ya Khaleel se shafa wuyansa daidai inda Anas ya kama yake idanunsa sunyi wuru-wuru. Kamar me aljanu Anas yayi kan Farouq da rai ke a hanun Allah ya shaqe masa wuya shima da wuri aka k’wato sa. “Anas get your senses kowa yasan abinda suka maka da zafi amman in ka kashe Farouq yanzu babban matsala ne a garemu, kotu ne zasu hukunta Farouq bamu ba.” “Nasani sede kafin nan inason inbawa d’an banza kashi” nan yasake yin kan Farouq sede kafin yamasa wani abun aka taresa. Cikin wani irin sauti Farouq ya soma magana “duk kaine Baba wallahi duk kaine barin bari akaini prison ni kad’ai ba.” “Meh kake cewa haka Farouq?” Cewar Ya Khaleel cikin rud’ani yana matsowa kusa da Farouq gudun kar ya tona masa asiri. “Aikasan me nake nufi, da tun farko baka fiddoni daga prison d’inba daduk haka be faru ba.” “So its true!” Cewar Anas “I knew it dama ai na fad’a maka Abuu wannan” ya nuna Ya Khaleel da yatsa “munafiki ne, zakusan no one messes with Mr. Fauzi or his property, musamman kai Farouq” yanuna sa da yatsa “Shariah Court zankai ka su yanke maka hukuncin kisan kai kamar yadda kayi murdering min baby kaikuma uban banza sena tabbata an yanke maka shekaru da dama a gidan yari anan ne zan iya samun peace of mind.” Wani wawan dariya Farouq ya b’arke da, “ko a babu nasan na rabaka da source of happiness naka.” Daidai Anas zeyi kansa dan kai masa punch su Abuu suka riqesa “lets go Anas mu fita kaje ka duba Fannah kabar nan” da k’yar aka samu aka fiddo shi daga d’akin. ** A hankali ya bud’e k’ofan d’akin da Fannah ke ciki. Kwance yaganta bisa gado abin tausayi, besan a lokacinda idanunsa suka cike da hawaye ba if only ze iya amsan rashin lafiyan da yayi, ina ma ace ze iya karb’an duk wani pain da takeji right now da yayi. Kujera ya matso dashi kusa da gadon nata tare da zama. Ko hannunta yakasa riqewa dan tausayi, hawaye yake sosai a hankali ya d’aga hannunta ya had’a da nasa tare da pecking hannun. Da alama bacci take dan kuwa bata bud’e ido ba har a yanzu. D’ayan hannunsa yakai kanta yana shafa uban gashin dake kwancd akan goshinta, ya d’au tsawan minti uku yana ahaka sannan a hankali Fannah tasoma bud’e idanunta har ta bud’esu duka. “Habeebi” tace cikin dashasshiyar muryarta duk yadda yayi dan stopping hawayen nasa ya kasa kai ya miqa yayi pecking nata a goshi. “Flower welcome back” yayi maganar yana mata murmushi itama murmushin ta miyar masa a wahalance. Data gwada zama kuwa sam takasa dan zafin da takeji daga k’asan mararta, wani irin wahalallen k’ara ta saki da sauri ya sake kwantar da ita. “Not yet Flower don’t move kinji? am here sweetheart” ya sake pecking nata a goshi. “Habeebi mesa kake kuka?” Tayi maganar idanunta na cikowa. “Babu, am just happy you are back baki tafi kin barni ba, Flower I love you so very much” ya matse hannunta cikin nasa. “I love you so much more Habeebi barin tab’a barinka in shaa Allah.” “I know Flower nasan baraki barni ba I was just scared.” Yasa hannu ya share mata hawayenta “karkiyi kuka kinji? Its bad for your condition.” Kai ta gyad’a mai, “Habeebi what of our baby? Yana nan?” Ta tab’a kan cikin nata tana shafawa a hankali. Shiruu Anas yayi danko besan ta ina ze fara mata bayani ba. “Habeebi mesa kayi shiru? please tell me baby na nanan kokuwa ya tafi?” Nanma shiru kuka ta soma sosai “Habeebi kafad’amin please, tell me my baby is still with me, tell me burin Ya Farouq na rabani da baby na be cika ba please Habeebi.” “Shhhh!” Ya aza yatsansa kan lips nata “bar kuka kinji?” Ya share mata hawaye. “Habeebi please tell me” seda yayi kissing forehead nata sannan yace, “Flower ki kwantar da hankalinki kinji? I’m so sorry nayi delaying time, da a lokacin da kika turo min da saqon nazo dana hana aukuwan wannan abu, am sorry please.” Maganansa ya tabbatar mata ta rasa babynta. “Habeebi so the baby is gone?” Ta tambayesa. “Ka fad’a min please.” Cikin wani erin salo ya gyad’a mata kai “baby ya tafi ya barmu Flower, we’ve lost our baby all because of me, I’m sorry.” “Habeebi ba laifinka bane laifi na ne, da ban had’iye maganin ba da babynmu be tafi ya barmu ba, ni na kashe babynmu da kaina...” ta rushe da kuka. “Shhh!” yasa hannu yana share mata hawaye “don’t ever talk like that Flower ba laifinki bane, mugodewa Allah you are back, mugodewa Allah Farouq be samu ya kaiki wani wajenba in shaa Allah, Allah ze kawo mana wani baby kinji? Kibar kuka and I promise you Farouq will come nowhere near you again ko fuskarki bare sake kalla ba.” Kai ta gyad’a masa cikin kuka yana share mata hawaye seda ya tabbata tayi shiru ya kirawo su Abuu da su Baba duk suka shigo suka gaishe da Fannah. ★★★★ Tun daga nan aka soma jinyan Fannah, sosai take samun kulawa gun Maminta, Ummie ma kusan a asibitin take yini se dare take tafiya haka Anas ma kullum yana gefen Fannarsa yana bata iya kulawan daze iya, office gabad’aya yabar zuwa yabar Kacallah in charge. Kamar yadda yayi promising kuwa seda ya cika, Shariah court yakai Farouq inda achan aka yanke masa hukuncin rataya na kisan kai dayayi, kafin nan Abuu yace inhar Farouq ze bawa Anas hak’uri yanemi gafararsa za’a janye zancen amman ina Farouq taurin kai wane tsohon k’adangare yace ya gommaci ya mutu daya bawa Anas hak’uri haka a idan mutane aka mai rataya ya wuce lahira. Ya Khaleel kuwa 10 years imprisonment aka basa na bada goyin bayan kisan kai da yayi, daga nan aka rufe chapter’n Farouq da Ya Khaleel. (NOTE: ga masu fad’in kar a hukunta Farouq kusani hukunci ne me tsauri wato kisan kai ya dace dashi saboda yayi aborting baby wanda yake daidai da committing murder, inkuma har wai ba kashesa akayi ba aka yanka masa wasu shekaru a gidan yari toh definately wata rana ze fito kuma ze cigaba da hunting Fannah) *** 1:05PM A yau aka sallami Fannah daga asibiti sosai Dr yabasu shawarwari ciki harda hutun ‘yan watanni da Fannah ke nema kafin ta sake d’aukan wani cikin. Bayan isowansu gida Fannah taga security men as in k’warraru designed security men guda biyar bakin k’ofar. “Habeebi wannan mutane fah?” “Your security men Flower in shaa Allah from now no harm will come to you.” “Habeebi ai dama enemy d’in d’aya ne Farouq kuma he is gone yanzu ba me sake tak’ura mana.” “Even still Flower I want to keep you safe, ban tunanin zan iya yafe wa kaina in wani abu ya sake samunki, you are a like Flower da ba’ason abinda ze tab’a sa” murmushi ta saki masa, bayan yashigo yayi parking motar sannan ya ciro luggages natan yayi ciki dasu, da kansa ya cirota daga motar yakaita har d’akinsu. “Thank you Habeebi.” “Always Flower” yayi maganar yana ciro mata towel nata daga wardrobe “gashi kiyi wanka semuci abinci I cooked your favorite.” “Favorite wanne kenan? louisiana?” “Yes sweetheart kishiga kiyi wanka ko in miki?” Towel d’in ta fisga daga riqonsa “haka kawai seka haumin wanka?” “Barin iya bane?” “Eh” ta fad’a tare da murgud’a mai baki. Gabanta yasha tare da d’agata sama chak! be direta ko inaba se cikin jacuzzi sannan yasoma raba ta da kayan jikinta. “A’a Habeebi wallahi zaka iya kayi hak’uri kabari please.” “LOL shegen kunyan kinnan bansan ranan barinsa ba, ina jiranki” nan ya manna mata peck a kumatu sannan ya fice. Cikin kwanciyan hankali ta samu tayi wankanta ta fito zaune ta tarar da Anas gefensa wani baggi T shirt ne baby pink in color da hoton birds da flowers akai. “Come here” ya buk’ace ta, ba gardama taje ta zauna gefensa, akan cinyansa ya azata sannan yaciro lotion nata ya soma shafa mata sam bata hanasa ba bayan da yagama takallesa cike da so da k’auna tana murmushi sannan tace, “thank you Habeebi.” “Its my job Flower in tayaki sa kayan?” “A’a karka damu” a hankali tasa kayan daya cire mata wanda tsayin yamata daidai tsakiyar cinya. “Toh Habeebi ba leggings da zan sa taciki?” “Babu I missed your sexy legs so yau inason inta kallonsu.” “LOL” ta murmusa “baraka kasheni da kayan dariya ba Habeebi toh muje muci abincin” tayi maganan tana bin jikinta da turare bayan tagama ya rik’o hannunta suka fice daidai gaban d’akin babynsu ta tsaya hakan yasa Anas tambayarta ko lafiya. “Flower wani abu ne?” “Habeebi kawai na tuna da babynmu ne, I miss him/her” ta k’are maganar tare da aza hannunta kan cikin nata. Ganin zata fara masa kuka yayi sauri yayi hugging nata yana bubbuga bayanta. “Is okay Flower Allah ze kawo mana wasu in shaa Allah bar kuka kinji?” Hannayenta ta zagaye a bayansa a hankali tana gyad’a kai “I pray so Habeebi.” Sun d’au minti biyu suna manne da juna sannan Anas ya raba jikinsa da nata “muje muci abincin ko? Se kisha meds naki” “Yes amman inason inshiga d’akin first.” “A’a Flower banason kiyi kuka kuma nasan definately kika shiga zakiyi.” “Please Habeebi” badan yanaso ba yabud’e masu k’ofan suka shiga. Daidai gaban babban gadon ta tsaya tare da sunkuyawa ta ciro d’aya daga cikin cute pink teddy bears d’in tana murmusawa, hawaye kawai tasoma zubarwa, kafin tasa hannu ta share Anas ya riga ya ganta. “Flower kinga shiyasa nace banason kishigo.” “Habeebi ka tuna lokacin da nace mu sayi blue ones kace a’a pink kafiso saboda jikinka na baka mace zamu haifa? Kasan wani name ya fad’o min alokacin?” “No Flower tell me” ya juyo da ita gabansa tare da kwantar da kanta a chest nasa yana shafa bayanta. Kanta ta d’ago tana kallonsa “HANAN Habeebi. Kasancewar kanason baby girl nima na soma ji ajikina mace zan haifa and HANAN zanso muna kiranta dashi amman not anymore Habeebi...” sekuma ta rushe da kuka. Face nata yayi cupping yana share mata hawayen “kibar kuka kinji sweetheart? We will have another baby and many more kuma aduk lokacinda muka samu baby girl I promise you ke da kanki zakiyi naming nata HANAN kinji? Bar kuka.” Kai ta gyad’a a hankali tare da hugging nasa gagam a jikinta. “I love you Habeebi, I love you so much.” “I love you too Flower muje muci abinci.” Teddyn ya amsa ya ajiye sannan ya jata har a yanzu bata bar kukan ba, shida kansa yake bata abincin har ta k’oshi sannan ya b’allo mata meds nata ya bata bayan sun idar da Sallah suka fita waje garden dan shaqatawa kan wani dogon kujera suka zauna ya kwantar da ita ajikinsa me bala’in sata mance da dukkannin damuwanta. Hannu yasa cikin ¾ wandonsa yaciro wani heart-shaped pack tare da miqa mata. “Habeebi meh wannan?” “Its yours bud’e kiga.” Excitedly ta amsa ta bud’e had’ad’d’en silver bracelet taga aciki meh chain d’an dogo seda toliyar heart a k’arshen wanda yake nan d’an babba. “Wowww its a beauty!” tayi exclaiming. “Do you like it?” “I love it Habeebi.” Hannu yasa ya ciro daga pack d’in tare da d’ago siririn hannunta ya sa mata chas ya zauna. “Just as I imagined it” ya fad’a tare da kissing hannun nata. “Tsaya kiga wani abu.” Toliyan heart d’in ya bud’e mata “FAHNAS” taga rubuce ciki in italics. “Habeebi this is way beautiful” fuskarsa ta riqo tayi pressing masa appreciating kiss daya kashe masa jiki lokaci guda, koda ta gwada sakesa kuwa holding lips natan yayi ya cigaba da kissing nata seda suka ji kansu problem free sannan ya saketa, murmushi ta sakar masa “I love you my sugar lips.” Murmushin shima ya miyar mata “sugar lips?” Yayi maganar da gira d’aya a d’age “ofcourse Habeebi I missed your lips and your body” kafin ya hankara ta sake pressing masa another hot kiss, se kissing juna suke passionately and hungrily tamkar yau suka fara tasting juna**** some minutes afterwards... “I love you Flower.” yace da ita yana shafa dogon sumarta. Sake shigewa jikinsa tayi; “And I love you too Habeebi like bohot bohot!” ta sakar masa da best smile nata me mugun amsar ta dakuma birkita wa Anas lisafi. © MIEMIEBEE

Share:

24 comments:

 1. tank u abba muhaaa©

  ReplyDelete
 2. muhammad abba gana24 September 2016 at 14:09

  toh!!!! @habiba,

  ReplyDelete
 3. thanks u so much

  ReplyDelete
 4. jazakallahu khairat

  ReplyDelete
 5. muhammad abba gana25 September 2016 at 09:51

  ameen @maryam yusuf,

  ReplyDelete
 6. muhammad abba gana25 September 2016 at 09:51

  ameen @FATY,

  ReplyDelete
 7. muhammad abba gana25 September 2016 at 09:56

  ba komai maman irfan

  ReplyDelete
 8. muhammad abba gana25 September 2016 at 10:03

  ameen @Abdulkadir,

  ReplyDelete
 9. mun gode abba, allah ya biya (amen)

  ReplyDelete
 10. SLM Dan Allah Abba yaushe zaka kara samana cigaban sareenah katai maka Dan unguwar nagode

  ReplyDelete
 11. pls cigaban sareenah

  ReplyDelete
 12. Allah ya ja zamani dan unguwar atemaka akarasa mana sareenah Dan allah

  ReplyDelete
 13. pls abba ya aka goge novel me suna kamar kumbo kamar korensa yayi dadi sosai

  ReplyDelete
 14. Muna godiya

  ReplyDelete
 15. Allah ya qara basira

  ReplyDelete
 16. Allah ya saka da alheri

  ReplyDelete
 17. tnx alot pls acigaba da 88

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).