shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 17 September 2016

TANA TARE DA NI... 70

tana-tare-dani.jpg TANA TARE DA NI... PAGE 70 BY MIEMIEBEE Miyan kap jikinta ya zube shima Anas yad’an tab’a sa kad’an. Irin rikicewa da b’arin da Fannah keyi ko gamo mutum yayi da aljan bareyi irinsa ba take ta tsuguna tasoma tattarawa abinda Anas ya tsana kenan ya washi yaganta tana picking broken glasses da hannu. Kafin yace tabari ko ya d’aga ta aikin gama ya riga ya gama kyat! Ta yanke a yatsanta k’ara sosai ta saki kamar a kyaftawan ido ya k’ariso gabanta hannayensa na sauk’a akan jikinta ta tsala wani irin rikicaccen ihun da shi kansa seda ya firgita. “Fannah please what is wrong with you? Anas nefa ba wani ba, its Anas your husband mesa kike haka da zaran na tab’aki ki rikice? Muga hannun” da zaran ya matso ze tab’a ta seta sa ihu ko magana takasa masa duk tabi ta tsure ta gefensa tabi da gudu da sauri ya cafko ta da hannu ya dawo da ita baya. “Fannah what is your problem why are you acting like this? Mena miki kike gudu na kamar kinga mala’ikan d’aukan rai, what is it tell me?!” Ya k’are maganar cikin sautin tsawa saboda he can’t take it anymore taya matarsa zata na gudunsa haka. Hannun nata take ta k’ok’irin fisga amman takasa hawaye kam sekace lalacaccen famfo. Bright blue eyes nasa da suka zamanto dull and weak dan tsantsan tashin hankali ya d’agosu a maraice yana kallonta se k’ok’arin karb’an hannunta take amman takasa. “Fannah mena miki? Ki fad’a min please, OMG!” Yayi exclaiming alokacin dayaga yadda jinin jikinta ke zuba a k’asa. Hannunta yasoma ja zuwa d’akinsa. Sam tak’i bud’e baki ta masa magana se hawayen da takeyi ganin sunkusan kai ga d’akinsa ta ja hannunta da k’arfin da Allah yabata seda ta fisge daga rik’onsa. “Fannah please don’t go…” bata ko sauraresa ba ta ruga d’akinta a guje tare da sa lock. Har k’asa ya sauk’a wasu irin zafaffun hawaye na maza suna sauk’owa tsili-tsili a fuskarsa. “Why Fannah? Mena miki? Your silence is killing me why are you punishing me like this?” Itama Fannar ba abinda take banda kuka, wanke ciwon nata tayi se kuka take ga wani irin yunwan dake azabartar da ita batajin zata iya kwana inbatasa wani abu acikinta ba. Rarrafawa tayi zuwa fridge na d’akin hamdala ta saki ganin da akoi cookies da drinks uku ciki. Ledar cookies d’in ta ciro ba makawa ta soma kaiwa cikinta seda taci fiye da rabi sannan ta kora da fanta nan ne tad’anji dama-dama. K’aran shigowar sak’o taji a wayarta kamar wacce barata duba ba sekuma ta miqe ta bud’e taga saqo ne daga Anas ta karanta kamar haka; Fannah please in wani abun na miki ki sanar dani stop punishing me like this zuciyana bare iya d’auka ba please Flower I’m missing your smile, body, and fragrance already open the door for me please. I love you #crying Wani sabon kukan ta fashe da har k’asa ta sauk’a tana birgima a kan rug na d’akin. Anas dake bakin k’ofar ji yake kamar ya b’alla k’ofar yashiga if only he could. “Fannah please stop crying kinji dan Allah kibari... Kidena please stop it” yayi stating cikin sautin kuka. Zama yayi bakin k’ofar yana hawaye tana kuka. Isha nayi ya rok’eta da ta tashi tayi Sallah ba gardama ta d’au hijabin ta tayi Sallan kamar yadda shima yayi a parlour bayan yagama shafa’i da wutr nasa ya dawo. “Fannah kifito kichi abinci kinji? I get it bakison sake sani a ido, zan koma d’aki sekin gama infito kinji? I love you.” Yana kaiwa nan ya juya a sanyaye kamar wanda k’wai ya fashe mai a ciki ya nufa d’akinsa bayan minti ishirin ta bud’o d’akinta a hankali, parlour ta nufa dan tattara wajen da plate ya fashe mata d’azu to her suprise taga wajen tsaf ko alaman miya babu tsaf Anas ya share yayi mopping. Dining area ta nufa ta d’iba abincin kad’an se sauri take kar ya fito su had’u gefen flask d’in taga wani paper hannunta na b’ari ta d’aga ta karanta. Flower please wear the plaster and cover your wound please kinji? I’m sorry. Wani sabon kukan taji yana k’ok’arin rufeta ga plaster’n tana gani amman batajin zata iya d’agawa, miyar da paper’n tayi ta ruga d’akinta a guje ta baje kan gado, ta cigaba da kukan daga inda ta tsaya. Bayan shiganta da kamar minti uku Anas yafito daga d’akinsa wajen daya ajiye mata paper’n ya nufa disappointedly yaga bata d’aga plaster’n ba to ko bata fito bane? Flask d’in ya bud’e yaga da alaman ta d’iba abincin mesa bata d’au plaster’n toh? “Fannah haka kika tsaneni yanzu? Bakiya son koda help d’ina?” Ya k’are maganar da hawaye na gangarowa daga kumatunsa guda. Hannu yasa ya share ya koma bakin k’ofar d’akin ta ya zauna yana sauraron sautin kukanta yana hawaye shima har bakin sa yayi dogo da ce mata tayi shiru amman tak’i. K’arfe 9:00PM na bugawa ya mik’e “Fannah anan zaki kwana?” Ya tambayeta tana jinsa amman tak’i amsawa dan batada burin sake masa magana a rayuwarta again. “Fannah kifito muje mu kwanta kinji? I can’t sleep without you by myside please kifito.” Sautin kukanta yaji ya k’aru. “Flower kibar kukan nan please...” ba irin rok’ar duniyan da be mata ba amman tak’i bud’e k’ofar ta kuma k’i barin kukan, ga wani uban ciwon kan da ke cinta. D’akinsa ya koma ya d’ago pillonsa da bargo ya dawo bakin k’ofar d’akinta ya shimfid’a ya kwanta kai be damu da uban sauron Maiduguri ba all he knows is that he don’t want to leave his flower alone. “Fannah goodnight, I love you so much.” Alokacin da yayi maganan tana kwance kan gado ta d’au tafiya yayi wani irin tsoro taji ya ratsa ta ko kashe wutan d’akin ta kasa, duk’unk’une kanta tayi cikin bargo se b’ari take cike da tsoro. Tafi awa d’ai tana neman bacci sannan a wahale yazo mata. Anas kam sam ya kasa bacci he is missing her in his hands se juyi yake amman ya kasa bacci bare iya kwatanta how he is missing her legs wrapped around his body ba. *** 2:34AM Firgit Fannah ta farka dan wani erin masifaffen mafarkin datayi. “Anas!” ta kira sunansa da ihu take ya jiyota dake daman baccin nasa beyi nisa ba. “Fannah” ya kira sunanta tare da mik’ewa. “Fannah I’m here kinji?” Kuka take sosai cike da tsoro duk ta duk’unk’une kanta da bargonta ta cusa kanta cikin cinyoyinta se kuka me sauti take. “Anas” ta sake kiran sunansa. “Yes Fannah I’m here please stop crying bud’e min kinji please I beg you...” Har a yanzu bata bar kukan ba. Zaman gadon ne ya gagareta ta tako zuwa bakin k’ofar ta tsaya adaidai lokacin yake kiran sunanta again “Fannah.” Kuka ta fashe da, yana jin muryarta kusa dashi hankalinsa ya sake tashi. “Fannah, Fannah ki bud’e min kinji? Let me in please.” Kuka take sosai ta inda yakejin sautin kukan nata ya matso tare da had’a kansa da wajen “Fannah I’m here please kibar kukan.” K’asa ta sulale kamar yana ganinta shima ya sauk’a. Hannunta ta aza jikin k’ofar tare da dafe kanta jikin k’ofar tana me cigaba da kukan. Daidai inda hannunta yake ya aza nasa shima “Flower I’m here you are not alone I’m here with you kibar kukan kinji?” A hankali taji tsoronta na gushewa da dad’ad’d’un kalamun Anas awajen bacci ya d’auketa tun Anas najin k’arfin nishinta har yazo yaji shiru hakan ya tabbatar masa tayi bacci anan ne shima yasamu ya d’an kwanta although sauro sunk’i barinsa saura na masa waqa a kunne saura suna cizon sa farin fatarsa duk yayi pink amman haka ya hak’ura dan baison barin Fannah ita kad’ai ahaka har Asuba tayi bayan ya idar da nasa ya gama addu’o’insa ya dawo ya soma kirar sunanta a hankali cikin baccin tasoma jin sunanta. “Fannah ki tashi kiyi Sallah kinji? Asuba yayi. Fannah tashi kinji?” A kasalance ta mik’e ta nufa bayi ta d’auro alwala tayi Sallah sannan ta koma kan gado ta kwanta har a yanzu Anas ya kasa bacci. Ko kad’an baijin ma ze iya zuwa office yau, bare iya barin Fannarsa awannan hali ba. Se anan ne yasamu yayi bacci shima 9:45AM ya tashi har anan Fannah na bacci tattara bargon nasa yayi ya wuce d’akinsa yayi wanka sannan yayi shirinsa na kullum fridge ya dosa ya ciro irin sliced potatoes d’innan da ake packaging ya musu frying da omalet ya had’a musu breakfast. Cikin awa d’aya dining table is set agogon hannunsa ya duba yaga 11:02AM knocking yaje yayi a k’ofar d’akinta alokacin da take fitowa daga wanka kenan. “Fannah kin tashi? If yes good morning kifito ki karya kinji? I love you” yana kaiwa nan ya koma dining ya soma zaman jirarta. Kukan dake son k’eto mata ta shanye simple doguwar riga tasa bak’i me silky jiki. Babban akwatinta ta ciro ta soma tattara kayakinta wanda zatayi amfani dasu ciki. Dam ta cika da essential stuffs nata ba mantuwan da tayi tana gama had’a akwatin ta ja ta rufe sannan ta zira hijabinta dogo har k’asa ta d’au wayarta sannan ta soma ja, a hankali ta bud’e k’ofar ta fito tafiya take kanta a sunkuye da jakarta tana ja daidai ta iso parlour ta bayyana a idon Anas. Kasa believing abinda idanunsa suke gane masa yayi. What is he seeing? Ina Fannah zataje da wannan babban akwati? Ganin se dosan bakin k’ofa take ya k’urma mata kira “FANNAH PLEASE STOP!” A guje ya nufa inda take, k’ara saurin tafiyar ta take gabanta yasha da wuri idanunsa take suka kad’a sukayi ja. B’ari bakinsa yake kalamunsa suna stammering “Fa.. Fan.. Fannah meh wannan? Ina za kije? Meke faruwa Fannah? Tafiya zakiyi ki barni? Mena miki Fannah? Dan Allah karki tafi in wani abin na miki tell me I’m sorry for everything that I’ve done I’m sorry please karki tafi.” Ya k’are maganar cikin sautin kuka. Zuciyarta taji ya karye, batasan seda hawaye suka soma ambaliya a fuskarta ba sam ta kasa dena kukan musamman ma dataga alaman cizon sauro all over his face and hands nufin a waje ya kwana yana gadinta jiya. “ Fannah please karki tafi mena miki da zaki tafi? Kiyi hak’uri dan Allah.” Hannunta yayi yunk’urin rik’ewa baya taja da wuri taja akwatin nata tabi ta gefensa da wuri ya rik’o hijabinta. Abin da be tab’a faruwa ba ya faru yau. Mr. Fauzi ya sauk’e girman kai da duk wani feeling daya keyi ya sauk’a har k’asa akan knees nasa duka biyu. Hawaye yake sosai “Fannah please don’t go dan Allah karki tafi. In wani abun na miki please let me know.” A nitse ta juyo ganinsa akan guiwowinsa ba k’aramin mamaki ya bata ba. Idanunsa a raunane ya d’agosu yana kallonta duk setaji wani iri tasa mijinta kneeling tace masa ya tashi kuma batason sake masa magana ganin yadda yake kuka itama ta k’ara k’arfin nata kukan. Juya masa baya kawai tayi batason ganin hawayensa kamar yadda shima baison ganin nata. “Fannah turn and look at me please mesa zaki tafi? Mena miki? Kinsan barin iya rayuwa ba ke ba please karki tafi Fannah in wani laifin na miki ki sanar dani dan Allah.” Juyowa tayi cikin sautin kuka ta soma magana har wani sama sama nishinta yake. “Anas are you serious? Bakasan me kamin ba? Kana nufin har a yau baka gane ni ba? Kana nufin baka san yarinyan dake _TARE DA KAI_ ba har a yau?” Cike da rashin fahimta ya taso “Fannah what are you talking about? Wace yarinya kike nufi?” Hannu tasa ta share hawayenta kamar yadda yayi shima. “Anas kaine mutumin, kai nake mafarki kullum zaka dawo ka sake azabartar dani kamar yadda kayi 5 years back. Anas don’t you get it? I’m the girl, nice yarinyan... Ni kayi raping 5 years bacm. Nice yarinya from the incident a Bama na yammacin Asabar 23rd of March...” Sekuma ta fashe da wani irin masifaffen kuka. K’wak’walwarsa kasa d’aukan abinda ke faruwa yayi. Se kai yake kad’awa yana salati a ransa da k’yar bakinsa ya bud’u cike da tashin hankali da rashin yarda yace “no you are not Fannah, you are not the girl inda kece da nayi noticing naki bake bace Fannah baki gane bane taya ma kika sani? I never told you.” “It doesn’t matter ‘cause I read your diary Anas ni kayi raping. Anas nice yarinyan da ka raba ta da budurcinta, ka cuceni Anas saboda kai nida family na muka bar Bama muka bar ‘yan uwanmu, saboda karya me bin maza da ‘yan unguwa ke kirana dashi muka bar Bama a sanadin abinda kamin, saboda abinda kamin Anas ka rabani da first love d’ina AHMAD wanda yasoni tsakani da Allah, saboda kai na rasa gatana, sabida kai Ya Farouq da Baffah Khaleel suka samu baki suke zagina suna kirana karuwa saboda abinda kamin kasa Baba ya kamu da ciwon zuciya Anas you are the source of my sorrow and fear. Mena maka Anas? Mena tab’a maka daka gommaci ka k’untata min? A rayuwa ba abinda naso kamar in gyara maka rayuwarka and I did mesa ni baka min haka ba? Mesa ka shafawa rayuwata bak’in fenti Anas? Barin iya zama dakai ba, barin iya cigaba da zama da mutumin daya cuceni kamar yadda kayi ba. Ka sallameni in tafi gida ka sallameni inkoma gun Mami na dan Allah karka hanani takarda na. Anas I’ve loved you but not anymore, I thought I could trust you why is the handsome Anas I know turning into a monster? Ka sallameni dan Allah...” © MIEMIEBEE
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).