shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 7 September 2016

TANA TARE DANI...26--30

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 26
BY MIEMIEBEE


Bayan Anas ya gama shafa maganin kan ciwonsa ya kurb’e coffeen sa hankali kwance. Yana gamawa yasa kaya yaja motarsa zuwa gida. Amal na tsaye bakin k’ofa tana jiransa. Ko gama fitowa daga mota beyi ba tayi kansa tana masa oyoyo a garin haka tad’an fama masa k’onuwansa. K’ara yasaki kad’an.
    “Ya Anas kaji ciwo ne?”
    Murmushi ya mata “a’a angel ba ciwo bane.”
    “Toh Ya Anas kayi ihu fa, mugani.” Tana k’ok’arin d’aga mai T-shirt. Hannunta ya rik’e “don’t worry angel ba ciwo bane.”
     “Toh Ya Anas ina mayafina daka ce ka siya min zaka taho min dashi.” Nan ya tuna mayafin nata ya bawa Fannah. “Ya Anas kayi shiru ko dama wasa kake baka saya min ba.”
    “Angel na saya miki mana, naga bashida kyau ne shine na kyautar ma wata mata akan layi but don’t worry zan k’ara saya miki wani kinji?”
   Kai ta giad’a a hankali tana turo baki.
    Ganin haka yace da ita, “dauk’o mayafin ki muje mu siyo miki wani yanzu, infact shopping ma zan kaiki ki saya duk abinda kikeso.”
    “Yeyy! Ya Anas!” dagudu ta shiga ciki ta d’auko mayafinta suka fice.

    **

    Afrah kuwa ta k’osa Fannah tabata labarin abinda ya faru cikin tsakaninta da Anas d’azu, tun a hanya take ta damun Fannah sanda suka iso gida Fannah ta labarce mata komi. Ido wuru-wuru Afrah ta zaro. “Ya Fannah wallahi Mr. Fauzi na sanki irin wanga kallo haka?”
    “Kefa akuya ce” cewar Fannah “Mr. fauzin yasoni? Impossible tense kenan! bakiga uban rashin mutuncin dayake suburbud’a min bane wallahi.”
     “Ke baraki gane irin san bane-”
   Katse ta Fannah tayi “ni banasan ji sekace baki san banida martaba ba aiko da ace ma sonan yake bare aureni ba muddin yaji labarina kamar yadda nima baran auri masifaffen mutum kamar Mr. Fauzi ba. Kinga tashi ki rakani muje mu siyo wa Baba magunansa tunda mun samu kud’i.”
     “Amman Ya Fannah a gani na ba sekin bar aiki da Mr. Fauzi ba.”
   “Kamar ya Afrah? Ke bakisan Mr. Fauzi bane wai? Ai barin aiki dashi consider it done monday monday’n nan zan fara nema in Allah ya taimakeni nasamu ai na huta.”
   “Tunda haka kikace, Allah sa hakan yafi alkhairi.”
   “Ameen” Fannah tace sannan suka je suka siyo wa Baba magunansa.

      Wahsegari ma haka ya kirata kan taje ta had’a masa coffee a paint house nasa tun 8:00AM ya kirata amman se kusan to 9:00AM ta isa saboda ta raka Mami kai Baba ganin likita daga can ta biya gidan Anas tare da mayafin daya bata, ta wanke sa harda guga. Hijabi har k’asa take sanye dashi yau. Bayan ta danna door bell ta tsaya jira shiru dan haka ta sake dannawa nan ma shiru, yin haka sau uku taga ba motsin mutum gidan ta d’au wayarta ta kirasa alokacin da ya soma ringing kuwa wayan na hannun Amal tana game.

    “Ya Anas coffee maker na kiranka” kafin yace, “mik’a min” ta d’aga “hello coffee maker.” Ido wuru wuru Fannah ta zaro wato ma da coffee maker yayi saving lambarta, Allah shirya toh. “Hello Amal” Fannah ta gaisheta.
    “Laaa kinsan suna na taya ya?”
   “Bani wayar Amal” cewar Anas.
    “Ya Anas gashi ta kira suna na wacece ita?” Nan ta dawo kan wayar “Hello coffee maker ya sunanki?”
    “Fannah ce Amal.”
   “Laaaa! Fannah!!” ta daka ihu “ya kike?”
   “Lafiya, kefah?”
   “Amal kawo wayan nan.” Nan ya mik’e da nufin ze karb’a ganin haka ta mik’e a guje kafin tace me ya kamata ya k’wace wayan.
 
    “Yes? Kud’inki ne baki gani ba komeh?”
  “Mr. Fauzi gidan a rufe ne.”
   “Kin gwada bud’e k’ofar ne kika ga a rufe?”
  Nan tasa hannu taga a bud’e a kunyace tace, “a’a.”
    “Good kud’inki na kan dining table don’t call me again.” Kafin tayi magana ya katse wayar. Kallon wayar ta tsaya yi lallai ma wannan Mr. Fauzi wallahi da girman kai na kisa da ka juma da mutuwa. Tsuka taja sannan ta shiga ciki...

**
     “Ya Anas shine kace min bakasan wace Fannah ba ranan dana tambayeka.”
   Kallon Amal ya tsaya yi yana tunanin wani k’arya ze mata can yace, “eh mana ban santaba, ni banma san asalin sunan ta ba se yanzu, bakiga da coffee maker nayi saving number’nta ba.”
    “Toh Ya Anas mesa ta kiraka?”
    “Aiki zatamin.” Ya amsa ta a takaice.
  “Toh Ya Anas bani lambarta inasan muna waya da ita.”
   “A’a Amal, Fannah is not a good person bana san kuna zumunci da ita.”
    “Mesa Ya Anas?”
   “Just trust me kinji Angel?”
   “Okay Ya Anas” ta masa murmushi “bani wayar in cigaba da game d’in toh.” Ba gardama ya mik’a mata “zan d’an fita in kin gama ki had’amin a charging kinji?” Kai ta giad'a “and also karkiyi recieving min calls, Angel am serious.”
    “Ya Anas barin yi ba seka dawo.”
   “Yawwa Angel!” Be zarce ko inaba se paint house nasa alokacin kuwa Fannah har ta gama had’a masa cikin flask ta ajiye kan dining ta tafi. Dad’i yaji dan ba san ganinta dama yake ba sesa ma yace tazo time da bayya nan. Tun jiya daya ganta ba mayafi ya riga tunaninta wanda ya mugun basa haushi. Nutsuwa yayi ya sha coffeen sa sannan ya taho da flask d’in da ze dawo gida.

      **

     Fannah na zaune ita kad’ai a d’aki tun dawowarta take zaune shiru kasancewar Afrah ma ta tafi yawonta, su Mami kuwa basu dawo ba. Dadai zata d’au wayarta dan buga game kenan wayar ta soma ringing ganin sabuwar lamba ta tsaya nazarin kowaye amman sam bata san lambar ba sanda ta kusan tsinkewa ta d’aga nan ma batace komi ba, familiar voice taji “Fannah” aka kira sunanta.
   “Na’am Amal ce?”
    “Kin gane ni kenan?”
          “Eh!” Fannah ta fad'i cike da mamaki. “Ina kika samu number na?”
    “A wayan Ya Anas karki fad’a masa munyi waya fa kinji? Besan na d’auka number’nki ba.”
    “Toh Amal barin fad’a masa ba. Mesa kika kirani?”
    “Kawai I want you to be my friend.”
    Cike da mamaki Fannah tace, “toh nikuma? Ai na miki babba.”
  “To ki zama big sis d’ina” Amal ta fad’i tana turo baki.
   “To Ya Anas fa bare miki magana ba?”
    “Ai bare ma sani ba dan ni ba fad’a mai zan ba, kamar yadda kema baraki fad’a masa ba koh?”
    “Sosai” Fannah tace tana dariya “toh little sis barin fad’a masa ba.” Hira sosai suka sha suka riga tambayan juna questions akan rayuwarsu suna amsawa se can sukayi sallama.

    Washegari...
     Kasancewar yau Monday Fannah ta tashi tayi shirin zuwa office tare ta taro credentials nata dan daga can tana san ta wuce neman aiki. Takwas da ‘yan mintuna aka ta isa office bayan tayi knocking Anas yace, “come in.” Kanta sunkuye tashiga ta gaishesa be amsa ba bale ya kalleta, matsowa kusa da shi tayi alokacin ne ya d’ago kai yana kallonta.

        Jakarta ta bud’e taciro gyalen daya bata kafin ta ajiye kan table d’in ya dakatar da ita. “Wannan kuma fa? Kar ki ajiye min kan table” Ya tambayeta.
        Cak! Ta dakata “Sir mayafin daka bani shekran,jiya ne thank you, shine zanyi returning maka yanzu.”
          “Inada ido ai, banaso, bana buk’ata. Ko ki cigaba da ajiyewa wajenki ko kuma ki jefar ya rage miki. Make me coffee.” Mamaki ne yacikata bata ce masa komi ba ta mayar cikin jakarta sannan ta ajiye ta wuce ta had’a masa coffee bayan ta ajiye ta kallesa “Sir excuse me zan d’an fita but in shaa Allah zan dawo kafin azahar.”

    Yana sipping coffeen sa tare da duban wasu files “wannan kuma keya dama, iyaka in bakizo on time bane inyi firing naki” ya fad’a mata ba tare da ko ya kalleta ba. A ranta tace ka kwantar da hankalinka ina samun aiki zanyi resiging a nan. Jakarta ta ja ta fice neman aiki ta tayi amman ba sa'a kafin azahar ta dawo ta sake had’a masa coffee.
 
    Haka de tun daga ranan Fannah ta shiga neman aiki ba wasa. Mayafin kuwa ta adana sa gu d’aya dukda bata da niyyar sake sawa. Anas kuwa be canza ba baya shiga harkanta amman ko d’an k’aramin mistake tayi ze balbaleta ya tsawa ta mata, kuka take sosai duk sanda ya masifeta sam takasa sabuwa da masifar Anas, shiko kukanta sam  be d’aga sa bale ya nana sa a k’asa. Shak’uwa sosai yashiga tsakanin Fannah da Amal wanda har yau Anas be sani ba. A yau wata d’aya da sati biyu kenan tana masa aiki.

     Yau ranar ta kasance Wednesday, dawowar Fannah daga aiki kenan idanunta duk sunyi ja saboda kuka.
    “Fannah ya haka?” Mami dake fitowa daga kitchen ta tambayeta.
    Kare fuskarta take “ba komai Mami dutse ne yashiga min ido amman yafita karki damu.” tamata k’arya.
    “Are you sure?”
   “Eh Mami ina Aiman da Afrah?”
   “Sun shiga nan mak’ota.”
  “Okay barin watsa ruwa toh” nan tayi hanyan d’akinsu. Bayan tafito daga wanka tajiyo alert a wayarta tana dubawa taga message daga d’aya daga cikin ma’aikatan datayi applying FCB ltd. Tsalle ta daka ganin aiki suka bata kuma akan abinda ta karanta finally zata samu tayi amfani da ilimin data samu a jami’a.
   Afrah na dawowa ta labarta mata komi sosai Afrah ta mata murna. Ga albashi me kyau daidai N50,000.

       Bayan ta sa kaya taje tayi printing resignation letter’n da zata kaiwa Anas gobe. A hanyar dawowarta gida Amal ta kirata bayan sun gaisa take fad’a mata kan tabar aiki a Enterprise na Anas tasamu aiki. Amal ta mata murna kam sede bataji dad’in barin aikin Fannah gun Anas ba. Sau dayawa tana zuwa office na Anas ita da Fannah su fita suje suta hira ba tare da sanin shi Anas d’inba.
   
     “Ya Fannah amman mesa zaki bar aiki da Ya Anas? Ya miki wani abu ne?”
    Murmushi Fannah tayi sam halin Anas da Amal ba iri d’aya bane, kamanninsu ne kawai d’aya. “Ba abinda yamin Amal kawai nasamu better job ne.”
   “Yanzu shikenan bara mu sake had’uwa ba?” ta fad’a kamar zatayi kuka.
       “Nima banso hakan ba Amal, amman ai zamu na waya ko?”
   “Eh amman its still not enough ko zaki na zuwa gidanmu?”
    Danqaree Fannah tafe a zuci. “A’a Amal bareyi inje gidanku ba saboda Ya Anas.”
        “Ba abinda Ya Anas ze miki dan Allah kinji?”
    K’arya ta mata “naji zanzo in shaa Allah. Ina kan hanya bari in na isa gida zan kiraki.” A haka sukayi sallama.

     Washegari Fannah tasha baccinta a cewarta ta bar masa aiki se lokacin data ga daman zuwa office zata takai masa resignation letter’nta. Da misalin k’arfe 9:30AM Fannah ta iso building na Anas. A first floor ta had’u da Yusuf ta sanardashi great news na aikin data samu sosai yaji mata dad’i kuma ya mata murna. “Barin haura inkai wa Mr. Fauzi resignation letter na ina zuwa.” Da “toh” ta shige elevator. Zuciyarta fal da farin ciki ba me sake sata kuka yanzu dan ta tabbata ba worse Boss kamar Anas. Knocking d’aya tayi a bakin k’ofar yace, “come.” Cike yake da ita wato yau se 9:34AM Fannah taga daman zuwa masa office, she will get it from him.

        Bayan ta k’ariso ciki ta gaishe sa ko amsa ta beyi ba kallo ya watsa mata wanda yasa k’afafunta shaking. Ya bud’e baki ze soma suburbud’o mata masifa kamar an turosa kawai k’ofar office d’in ya bud’u wanda ba kowa ke shigowa haka ba illa Amal. “Ya Fannah!” tayi ihu ganin Fannah tsaye da gudu ta nufa wajenta tayi hugging nata. Baki wangalau Anas ya bud’e yana kallonsu. Wato Amal bata je school ba yau, bama wannan ba yaushe suka san juna da Fannah har suka shak’u haka? Tambayoyin da yayi wa kansa kenan.

     “Ya Fannah yanzu dagaske kike zaki bar aiki nan? Dan Allah kiyi hak’uri.”
     Kunnensa ya bubbuga ko halan ruwa ya shiga yau da yake wanka, barin aiki Fannah zatayi zuwa ina? Ta samu wani aiki ne? Coffee na fa? Bece dasu komi ba sanda suka gama hoge-hogensu. Bayan Fannah ta ciro letter’n ta matso kusa da table na Anas. “Mr. Fauzi wannan resignation letter na ne. Thank you for giving me the oppurtunity to work for you.” Letter’n ya d’aga yana k’arisa masa kallo sannan ya d’ago blue eyes nasa yana kallonta “are you really sure about this? Na barin aiki a nan?” ya tambayeta ba tare da ya nuna damuwa ba dukda kuwa ya damu sosai.

      Kai ta giad’a a hankali. “Kin samu wani aiki ne?” Nanma kai ta kuma giad’awa. “A ina?”
    “A FCB ltd.” ta amsa sa.
   “Ohhh, nawa ne salary’n naki?”
   K’arya tayi masa “nima bansani ba tukunah.”
   “Yayi kyau zaki iya tafiya.” Amal dake kallonsu ne tace, “Ya Anas ka hana ta tafiya ka k’ara mata salary se kar ta tafi.”
    “A’a Angle barta ta tafi. Ni ban hanaki alak’a da ita bama?” Ya tambayeta ba alaman wasa a tattare dashi.
    “Ya Anas kayi hak’uri.”
    “Zan hak’ura if only kika dena alak’a da ita, kingani ai barin aiki tayi.”
  “Mr. Fauzi-” cewar Fannah be saurareta ba ya daka mata tsawa “just go, leave, bana san sake ganinki.”
   “Amal na tafi” nan ta juya.
   “Ya Anas-” itanma tsawa ya daka mata for the first time. “Enough Angel kije ki samu Yunus yakira Shettima yazo ya d’auke ki.”

    Ita kanta tsoro taji sosai bata tab’a ganin mood na yayanta haka ba. Wajensa ta nufa tayi hugging nasa “Ya Anas I’m sorry, bansan me Ya Fannah tayi ka tsaneta haka ba, tanada kirki fah but tunda baka sona tare da ita, I’m sorry.”
     Bayanta ya shafa “is okay je gida ki huta nima I'm sorry for shouting at you.” Bayan Amal ta fice Anas ya d’au resignation letter’n Fannah ya yayyaga into pieces, zuciyansa se tafasa yake. Yarasa me ke damunsa mesa ma nake damuwa dan wata wai ita Fannah tabar min aiki? Nawa suka fi ta komi kuma na koresu, toh se meh dan kin bar min aiki? Mschww dama dan coffee ne kuma akoi masu neman aiki anan dubu. Wayarsa ya d’au ya kira Ahmad. “A buga a news ina neman masu aiki wanda suke da degree inma da hali har da masters kan had’a cofee.” Cike da rashin fahimta Ahmad yace, “Boss coffee kuma? Anayin course akan coffee ne?”
    A fusace Anas yace, “in baka aiwatar da abinda na saka kayi ba a yau a bakin aikinka.”

    Tuni Ahmad ya amsa “yes ofcourse Boss”  “Good, kuma ka turo cleaners suzo share wannan gabbage” yana nuni da resignation letter’n Fannah daya yayyaga “and also ka turo min number’n manager’n FCB ltd”


© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 27
BY MIEMIEBEE

Ko cikakken minti d’aya ba’a yiba Ahmad ya turo masa lambar PA’n Manager’n FCB ltd kasancewar Manager’n ya canza number kuma bayi sabon. Nan Anas ya kira PA’n ringing d’aya biyu PA’n ya d’aga gaisuwa ya fara wanda Anas ya dakatar dashi ransa se tafasa yake dan yadda ya b’aci. “Ka kai wa Boss naka wayan” ya fad’a authorititavely.

        “Wa ke magana please?” Cewar PA’n saboda bada layin office Anas ya kirasa ba.
     Ba k’aramin fusatar dashi tambayan PA’n yayi ba. Cike da b’acin rai yace, “Tambaya na ma kake wake magana? Inba wai so kake ka rasa aikinka a yinin yau ba give the damn phone ro your Boss.” Ya sake daka masa tsawa.
    “Sir I’m sorry but ya kamata insan wake magana kafin in maka abinda kake buk’ata.”
     “You’re stupid kajini? Nace you are stupid, ANAS IBRAHIM FAUZI ke magana CEO’n FLAMES ENTERPRISES.”
     “Omg! Sir dan Allah kayi hak’uri wallahi ban san kai bane,my apologies please kayi hak’uri.”
    Tsuka Anas yaja “mschww damuwanka wannan kuma, where is your boss ka kai masa wayan.”
    “Sir d’azu da safe Boss d’ina da family’nsa suka tafi trip zuwa Hungary.”
   “Meaning what? Meaning baraka kirasa kace inasan masa magana ba kenan ko meh?”
   “Sir I’m so sorry amman sanda ya fad’a min koda wasa kar na kirasa in batun aiki ne dan Allah kayi hak’uri. Hutu ya tafi”
     “Lalle kanasan rasa aikin ka nace call your Boss kace masa ina san masa magana.”
   “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri wallahi banasan rasa aiki na.”
    “Damn it!” ya buga hannun sa kan table, “what of business kuna running har yanzu ko shima kun dakatar?”

          Dadai lokacin knock yashigo daga k’ofar office nasa “come” yace bayan an bud’e k’ofar cleaners mata biyu suka bayyana. Tun daga bakin k’ofa suke gaishesa har suka k’ariso ciki. Papers d’in ya nuna masu nan d’ayan ta hau sharewa kallonsu ya tsaya yi bayan yayi holding call dayakeyi da PA’n.
      Har sun kai da bakin k’ofa ya kirawo su, dawowa sukayi suka tsaya gabansa “yyyess Sir” har i’ina suke dan tsoro. “Haka ne kin share nan wajen?” Yana nuna wanda ta share wajen “bakiga wancan paper’n bane?” Ya nuna mata wani piece na paper a k’asa. “Me amfaninki a nan in har shara ma baki iya ba se an koya miki? Eh?? Useless kawai.”

          “Boss dan Allah kayi hak’uri” tana b’ari taje ta share gudan paper’n kallonta yake sannan cike da nuna rashin damuwa yace, “you are fired ki tattara kanki kibar min building kije kisamu Adam yayi settling miki salary’nki. You are dismissed.” Kuka ta fashe da “Boss dan Allah kayi hak’uri wallahi ban gani bane hakan bare sake faruwa ba.” D’ayan ce tasa baki dan ganin yadda ‘yar uwarta ke kuka. “Boss dan Allah kamata hak’uri bada-”

       Mugun kallo kawai ya mata wanda yasa take tayi shiru. “Kekuma waya jefa bakinki cikin wannan matter? Nasan kinada dogon baki ba sekin nuna min ba I have eyes to see. You two dukan biyu are fired, kuje kusamu Adam yayi settling muku albashinku now leave my office.” Suna kuka suna had’asa da Allah amman ko a kwalan rigarsa tashin hankalin Fannah tabar masa aiki bame had’asa masa coffee ke damunsa nan ya dawo kan wayar.

         “Nace kun rufe business naku ne ko kuna running har yanzu?” Ya tambayi PA’n.
    “Muna running Sir komi munayi.”
    “Good” Anas yace, “kwanan nan kukayi hiring ma’aikata koh?”
    “Eh Sir just jiya muka musu sending letter ran monday zasu soma aiki.”
     “Ka bud’e kunnuwanka da kyau kajini. Inasan kaje kabi list d’in kayi firing FANNAH ALEEYU. kajini?”
   “Naji Sir yanzu zanje in samu secretary in masa magana in shaa Allah za’ayi firing natan. Amman mesa Sir?”
           “Wannan kuma ba damuwanka bane, inajiran feedback nanda like 10ninutes”
         “Okay Sir” nan Anas ya katse wayar. Bakinsa ya cize yana murmushin mugunta. Telephone na office nasa ne yasoma ringing nan ya d’aga.

       “Hello Boss an buga a press da jaridu gobe in shaa Allahu masu degree da masters harda PHD ma zasu soma applying batun coffeen”
     “Good banasan failure.”
    “In shaa Allah Boss.” Shide Ahmad mamaki yake har yanzu wai yaushe aka soma yin degree kan had’a banzan shayin da ake had’awa kan tebur akan layi safe rana dare, wani abu se Boss.
   Kai ya jingina jikin kujerar sa yana juyawa a hankali chan ya mik’e ya bud’e fridge tare da ciro barasar sa kusan rabi ya kurb’e ya koma d’aki ya baje ya kwanta ko problem nasa ze d’an tafi. Sanda ya kusan kai minti goma sannan yasamu yayi bacci abinda kullum daya sha befi minti uku bacci ya rufesa. Bacci me nauyi ne ya rufesa wayarsa dake kan table se ringing yake PA’n Manager’n FCB ltd ke kira. Two missed calls yamasa sannan ya hak’ura.

     Bayan minti ishirin da kwanciyar Anas, Kacallah ya taho yana knocking bakin k’ofa se sauri yake kwata kwata ya manta Anas nada board meeting da zeyi attending yau saboda yadda aiki ya masa yawa gashi in less than 10 minutes za’a fara. Knocking yake sosai Anas dake bacci ko kad’an baiji daga k’arshe shiga kawai yayi yana kiransa da “Boss” shiru kukeji. D’akin ya lek’a yaga Anas yayi ruf da ciki se bacci yake sha harda minshari necktie nasa yayi gefe guda takalmansa ma d’aya na kudu da’aya kuwa arewa. Ido ya zaro wuru wuru mekuma yasami Boss nasa yake bacci in the middle of the day.
      K’arisawa cikin d’akin yayi shi kansa tsoron tada Anas yake gudun kar ya rasa aikinsa dan kuwa yaga Hussaina da Zainab da akayi firing d’azu se kuka suke. A hankali ya tsuguna gaban fuskar Anas. “Boss!” ya fad’i murya na b’ari. “Boss!” Nan ma shiru dan haka yad’an jijjik’a sa ko kad’an Anas be motsa ba se bacci yakeyi. “Boss!” Kacallah ya kira sa sosai cikin kunnen sa nan ya yamutsa fuska. “Boss kayi hak’uri ka tashi akoi board meeting da za’ayi wanda yazama dole kaje you are needed please.”

     Cikin bacci yace, “dole? Se a sani inga. Barin je ba leave ko baka ga bacci nakeyi ba?” Pillow yaja ya rufe fuskarsa. Fuskar Kacallah kan wanda zeyi kuka “Boss kayi hak’uri ka tashi please you have to be there.”
     “Wake magana?” Anas ya tambayi Kacallah fuskarsa rufe da pillow dan yama kasa recognising muryar meshi.
   “Kacallah ne Boss, Kacallah ne.”
   “Kacallah kanason aikinka?” Anas ya tambayesa fuskarsa cikin pillown har yanzu.
    “Eh Boss inason aiki na sosai” ya fad’i yana giad’a kai.
    “To ka tashi kabani waje, fita min daga office in na sake jin muryaraka you’ll be fired.”
    “Fired?” Kacallah ya nanata a zuciyarsa. Meyayi zafi harda firing. Da sauri ya tashi ya bar d’akin hak’urin da yakeson badan ma yafasa dan ko Anas yace baisan sake jin muryar sa. Bayan ya isa office nasu na ma’aikata ya zauna kan table nasa tunanin wani k’arya ze had’ama wanda zasui meeting d’in yake chan ya d’au telephone ya kira assistant coordinator’n meeting d’in bayan ya gaishesa ya fara kamar haka;

        “Uhm Sir dan Allah kayi hak’uri for the inconvenience da aka samu.”
   “Wani incovinience kenan?” Mutumin ya tambaya.
      “Boss d’ina ne mahaifiyarsa ba tada lafiya, bareyi yasamu attending meeting d’inba, kuyi hak’uri please.”
     “Toh Allah sawak’e amman gaskia bareyi ace Flames Enterprises basu hallaci wannan meeting ba saboda  na board ne gabaki d’aya, ka turo d’aya daga cikin staffs naku ya ko ta wakilce sa.”
       “Yes Sir thank you so much.” Nan ya katse ya kira wata ma’aikaciya Suwaiba dake 6th floor yamata bayanin komi take ta shirya ta tafi zuwa meeting d’in. Nanne Kacallah yad’an samu peace of mind se addu’a yake Allah sa kar emergency ya taso dan besan ya zeyi ba Boss yace bayasan sake jin muryarsa.

          Bacci sosai Anas yasha kusan to 2:00PM ya tashi da k’yar yayi alwala yayi sallah yayi ordering  kawo masa abinci daga kitchen, a lokacin ya duba wayarsa yaga missed calls from PA. Nan ya kirasa, “hello Sir good afternoon.”
   Ba takan gaisuwar yake ba dan haka ko amsa sa beyi ba, “yes anyi firing natan?”
     “Unfortunately Sir wallahi secretary’n yace ba abinda tayi wai bareyi firing nata ba-”
   “What!??” Anas ya daka tsawa. “Bareyi firing nata ba? Waye shi?” Daidai lokacin knock yazo daga k’ofa ransa b’ace yace, “who is it?”
      Tana b’ari tace, “Boss Leemcy ce abincin ka na kawo”
      “Banaso, get the hell out of my office you are fired kije ki samu Adam.” Aguje ta koma k’asa tana kuka. “Kace meh? Bareyi firing nata ba? Kai masa wayan.” Bayan minti d’aya aka kaiwa secretary wayar.
   “Hello yace.”
   “Hellon k’aniya?” Anas ya tambayesa “kasan dawa kake magana?”
   “A’a seka fad’a” cewar secretary’n.
   “Nonsense you are speaking with ANAS IBRAHIM FAUZI.”
   “Sir! Ran ka ya dad’e kayi hak’uri dan Allah wallahi Kabir be sanar dani wane kai ba.”
    “Yanzu daka sani seka yi abinda ya kamata” amsar da Anas ya basa kenan.    “Yes ofcourse Sir yanzu zan tura mata message d’in.”
   “Good, inajiran feedback nanda 5minutes.” Karap yayi hanging call d’in.

     Nan da nan yasa akayi typing message na Fannah daidai lokacin za’a tura Manager’n wajen ya turo sak’o kan kar a d’iba kuma kar a sakar da masu aiki saboda wasu k’wararrun dalilu. Aiko ba halin korar Fannah. Nan ya kira Anas ya masa bayani.
    “What rubbish are you saying? Ku had’ani da manager’n naku.”
    “Sir wallahi kayi hak’uri nan da sati biyu ze dawo in ya dawo everything will go your way, sosai Boss yana mutunta ka duk abinda kakeso shi zai maka, ka k’ara hak’uri please ni da kaina zan sanar dakai duk sanda yayi landing.” Dan haushi bema amsa sa ba ya katse wayar. Zuciyarsa tafasa yake kamar ze k’one “mstchwww.” Ma akan Fannah da bata kai ta kawo ba yana ta tada hankalinsa inde coffee ne ai yasa job on sale daga gobe za’a fara applying, se meh dan Fannah tabar masa aiki, aikin banza. Tun lokacin tashi beyi ba ya tattara wayoyinsa ya sauk’a. Chan ma by mistake wata ma’aikaciya tasha gabansa saboda saurin da take tayi submitting wasu files take aka buga mata fire! Itama. A ranan Anas yayi firing mutane ba adadi kowa mamaki yake at thesame time being cautious kuma shima kar a koresa. Kacallah de ba halin yima Boss magana dukda there is so much to tell.

     Washegari ta kasance thursday ‘yan garin Maiduguri kap angani kuma an karanta a news cewa Flames Enterprises suna neman masu aikin had’a coffee. Zokuga yadda maza da mata suka taru bakin building na Anas yau. Da k’yar yasamu passage. 10-10 ake d’ibansu ake kaisu kitchen kowa da coffee machine dakuma ingredients na had’awa. First set suna gamawa Mr. Fauzi ya sauk’o tasting na wanda yafi masa dad’i seya samu aiki ya maye gurbin Fannah dan ko bacci ya kasa jiya se tunanin coffeen Fannah yake duk yadda yayi ya mance coffeen Fannah ya kasa, he is addicted to it dak’yar yasamu yayi bacci bayan syrup dayasha.

    Yana kai na farkon baki ya mayar cikin cup d’in “meh wannan? Ruwan wanki ko meh? take her out.”
    “Yes  Sir” cewar Adam. Nan na biyu ta matso itama yana kaiwa baki ya mayar cikin cup d’in “ke kinma san meya kawo ki nan kuwa? Take her out.”
  “Yes Sir.”
    Na uku ma takawo nata shima yana kaiwa baki ya miyar cikin cup d’in. “Take her out bana san sake ganin fuskarta.”

     Haka de bayin Allah suketa shigowa anayin round-round, na mutane 25 maza da mata Anas ya tab’a dukka ba wanda ya masa koda kusa da na Fannah ne.
      “Fire them all, duk ka koresu bana san sake ganinsu. Fire them now!” Yaja tsuka sannan ya shiga elevator’nsa ya haura zuwa office. A ranan yayi firing ma’aikantansa guda biyar plus na jiya abin de ba dad’in ji. Hankalin kowa tashe yake abu kad’an kayi a danna maka fire. Yau yini biyu kenan Anas be sha coffeen Fannah ba amman ji yake kamar shekaru aru aru ne. Yarasa ina ze sa kansa, abinci ma ba sosai yake ci ba koda ya gwada had’a coffeen baya masa dad’i bai ma iya sha gashi wannan karan ko Shettima ma be sanar dashi abinda ke damin sa ba kamar yadda ya hana Amal ma. Kawai in an tambayesa cewa yake rasuwar Baba (Mr. Muh’d) ya tuna.

      Yau k’imanin sati kenan da barin Fannah aiki gun Anas, k’imanin sati be d’and’ana coffeen ta me dad’i a bakinsa ba. Ba yadda beyi ba dan mancewa da coffeen nata amman yakasa shi daga baya nema yagano ba coffee natan kad’ai yake missing ba ita kanta Fannan ma missing nata yake, yes yayi missing Fannah, yayi missing innocent face nata, yayi missing kukanta dakuma muryarta me dad’in gaske, yayi missing kamilallen shirinta na kullum, komai yayi missing akan Fannah. Yabi ya k’osa next week ya iso ya kira Manager’n FCB ltd.

       Fannah kuwa rayuwarta ta juma batayi dad’i kamar yadda take ba yanzu, ba ruwanta da wani tashin hankali, aikinta tana yinsa me kyau ba ruwan asst. Manager’n ta da shiga harkar mutum bale ma ya mata masifa. Sosai take jin dad’i aiki wajen. Amal kuwa duk da erin warning da Anas ya mata ta kasa dena kiran Fannah saboda hankalinta. Wannan shine karo na farko da take sab’awa umurnin Anas.

 
  © miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 28
BY MIEMIEBEEDa yammacin ranar Juma’a bayan Anas ya dawo daga office yayi firing mutane 6 shida ranan. Kwance yake kan gado a d’akinsa ya zura wa ceiling ido yayi zurfi cikin tunani. Har Shettima yayi sallama ya shigo beyi noticing ba. D’an tab’a sa yayi a hannu firgit ya dawo daga duniyar tunanin daya fad’a. “Ya Anas yaukuma tunanin me kake haka? Na Ummimi kokuma na yarinyan?” ya tambayesa yana k’ok’arin zama kusa dashi.
    “Ko d’aya” ya amsa sa alokacin dayake k’ok’arin zama.
    “Then mene? Kasan ban maka magana bane amman Yusuf yabani labarin abinda kake tayi a Enterprise naka, me yayi zafi ace cikin sati kayi firing mutane 31 haba Ya Anas.”

    “Oh haka shi Yusuf nakan yace? Allah kaimu monday shima ya jira nasa.”
     “Ya Anas wai me haka, friend nawan zaka kora? Wace kuma Fannah?” Cike da mamaki Anas ya kewayo da blue eyes nasa kan Shettima. “A ina kuma kaji wannan batu? Still gun Yusuf?”
    “It doesn matter Ya Anas saboda ita kake firing ma’aikatan ka kana kashe Enterprise naka da kanka, ajinka yanzu in za’a dawo da Baba zeyi appreciating abinda kakeyi ne?”
         “Toh yimin lectures Shettima, please ni banasan maganan nan excuse me.”
    “Saboda yarinyan ne Ya Anas, kanasan ta dawo maka aiki ne? Do you miss her?”
      A fusace yace, “Yes Shettima I do, I miss her.”
     “Toh mesa kake treating nata badly lokacin da take nan? Kaifa kasa tayi resigning tabar maka aiki.”
    “Shettima ni ba abinda yake damuna ba kenan, abinda yake damuna shine tadawo.”
    “Toh ta yaya?”
    “Ta duk yadda nasan zan iya.”
   
        Shiru Shettima yayi yana nazarin wani abu. “What are you thinking of?” Anas ya tambayesa. “Ya Anas kode san ta kake? Yaushe ka fara damuwa da rashin mutum a kusa da kai?”
     “San ta? Are you kidding me Shettima? Me zan so a jikinta? Ni kawai I miss her saboda coffeen da take making min.” Yama Shettima k’arya dan shi kansa yanzu yasan ba coffeen Fannah kad’ai yake missing ba no matter how yayi denying Fannah ta daban ce, kayan duniya be dame ta ba, kyansa dayasa mata suke binsa ma be dameta ba yaci ace Fannah ta kamu da ciwon sansa amman ko kad’an beyi noticing hakan ba a tattare da ita.

           “Amman da akoi abin duba anan mata nawa wanda suka fi Fannah komai suke fad’in suna sanka baka tab’a saurara musu ba hasali ma koda sun shigo rayuwarka k’ok’arin koransu kake amman when it comes to Fannah, ita ta tafi da kanta but kanasan dawo da ita. Ya Anas ina yarinyan dakace _TANA TARE DA KAI?_ Ko hala itace Fannan.”
 
        “Non sense. Wani erin jagual guale kake fad’i Shettima? That girl can’t be Fannah in da ace itace da nayi recognising nata. Ka manta lokacin da abinda ya faru a buge kake?”
     “Toh ita fah? Ai in ni a buge nake ita ba’a buge take ba, da itace da ta gane ni.”
   “Not really” Shettima ya fad’a yana kad’a kai.
        “Noo Shettima wancan yarinyan ba Fannah bace kadena had’ani da Fannah please ni ba wai santa nake ba, batta,da abinda zan gani har ince inaso duk mata ma ba wacce take dashi illa yarinyar dake *_TARE DA NI._* so please kabar had’ani da Fannah, coffeen ta nakeso ba itaba.” Shettima ze sake magana Anas ya katse sa “maganan Fannan kuma ya isa please. Zan kwanta excuse me” kallonsa kawai Shettima yayi ya kad’a kai sannan ya fice.

       “Mesa Shettima zece inasan Fannah? Mesa yake tunanin itace yarinyar da nake nema har yau, eh nasani yarinyar _TANA TARE DA NI_ amman ba itace Fannah ba, banasan Fannah barin tab’a santa ba coffeen ta kawai nakeso. Coffeen ma daga yau zan dena missing saboda in manta da ita a rayuwa na forever”

         Washegari ya kasance Asabar ko tashi daga kan gado Anas beyi ba ya fara tuna Asabar daya kira Fannah zuwa gidansa had’a masa coffee, k’irjinta daya gani tun ranan har yau yakasa deleting image d’in daga k’wak’walwar sa. Kai ya kad’a dan ya gusar da tunanin nan ya mik’e ya shiga bathroom ya kunna shower yabar ruwan na sauk’a kansa. Duk yadda yayi ya mance Fannah ya kasa, yarasa dalili is not as if yasan how it feels to be in love.

   _One week 2 days later..._

      A shekaran jiya Manager’n FCB ltd ya dawo tun a ranan secretary’n yama Anas sending number’n Boss nasa as promised sede abin mamaki har yau Sunday Anas be kira manager’n ba. Kwance yake a d’akinsa da wayarsa a hannunsa ya zura wa lambar Manager’n ido yakasa kira. Anas ya koma wani abu daban. Sati biyu ne tun rabuwarsa da Fannah amman seji yake kamar irin shekara da shekaru. Abin nasa se worse yake dukda maganar da Shettima yamasa amman ina. A yanzu haka yayi firing about 60 something staffs nasa kullum cikin kawo sabi ake, hankalin kowa ya tashi a office sede ba kamar yadda na Anas ya tashi ba. Mutuwa ne kawai beyi ba dan hana kansa tunanin Fannah da coffeen ta. Yanzu haka ma ga number’n Manager’n amman ya kasa kira dan girman kai.

      Seda yammacin ranan ya danna wa manager’n kira, he can’t take it anymore. Manager be d’aga ba a karo na farko se ana biyu nan ma sanda ya kusa tsinkewa.
   “Hello” Manager’n yace bayan ya d’aga.
   “Mr. Azeez, Anas Fauzi ne.”
    “Ohh our youngest billonaire! Kwana dayawa.”
    “Alhamdulillah tun last 2 weeks nake neman ka akacemin ka tafi trip hungary, I had to wait ka dawo.”
    “Taya Kabeer ze maka haka? Besan ko waye kai bane? Ai be fad’a min ba I’m sorry.”
   “Ba komai ya wuce dama aiki nakeson baka.”
   “Toh billonaire inaji...”
  “About last 2-3 weeks kukayi employing ma’aikata koh?”
    “Eh suna nan ma munajin dad’in aiki dasu musamman wata Fannah something yarinyan akoi hardwork ina tunanin k’ara mata matsayi ma.”
      D’an murmushi Anas yayi “ita nakeso kayi firing Mr. Azeez.”

     Ido wuru wuru ya zaro “inyi firing nata kuma billonaire? Mesa?”
   “Saboda ni nace.”
   “Toh nawa kuma zaka bani wannan karan?”
    Murmushi yasaki kad’an again. “Miliyin d’aya yayi?”
   Mr. Azeez lips nasa ya tand’e tas “amman barin samu k’ari ba?” saboda yasan irin kud’ad’en da Anas yakeda.
    “Inde zakayi firing nata zan k’ara maka 1.5 yayi?”
    “Wow! consider it done Mr. Fauzi saisa nakeson aiki da kai wallahi. Gobe gobe za’ayi kamar yadda kakeso.”
   “Good” Anas yace yana me jin dad’i “amman kasan be kamata kayi firing nata haka kawai ba zan turo maka 50k akai se ka bata please make sure ka bata, banaso na bata kud’i dayawa tak’i dawowa wajen aiki”
     “Karka damu Mr. Fauzi zan san yadda zan b’ullo mata da lamarin ta yadda barata fahimci you have something to do with this ba.”
   “Good nagode.”
    “Ai ba godiya tsakanin wa da k’ani. Take care” ahaka sukayi sallama.

    Sosai Anas yaji dad’i dan dolen Fannah ta dawo masa aiki yanzu kuma wannan karan ma better job ze bata yadda bara ta sake tunanin tafiya ba, yasamu yasha coffee iya san ransa. Aiki kamar Personal Assistance nasa tunda dama baida shi. Jira kawai yake gobe ko jibi yayi Fannah ta dawo masa aiki.

    **

       Fannah na zaune d’aki ita da Afrah se hira sukeyi cike da nishad’i. Har wani fresh Fannah ta k’ara dan yadda batta da wani matsala yanzu. Wayarta ce ta soma ruri nan da nan ta duba ganin Yusuf ke kira yasa ta d’aga da wuri. “Assalamu alaikum Yusuf”
   “Wa’alakissalam Fannah ya kike? Ya aiki?”
    “Lafiya qalou, aiki alhamdulillah, naka fah?”
    “Fannah wallahi wajen aiki ya zamo kamar hell.”
   “Mesa kace haka Yusuf?” Ta tambaya cike da rashin fahimta.
    “Wallahi Boss ne Fannah, Boss yazama wani abu daban tun tafiyar ki, da barin ki office d’in wallahi yayi firing mutane sittin da abu ka.”
     “What! Allah shirya!” Fannah tayi exclaming cike da mamaki. “Sittin da abu? Dalili?”
   “Saboda ke mana Fannah, wallahi Boss yayi missing naki frustration na rasa ki yasa yake duk abinda yakeyi.”
    “A’a kam bade ni ba, nikuma me had’ina da Mr. Fauzi? Ai Allah ya riga ya rabani dashi har abada in shaa Allah.”
   “Fannah ki tausaya mana ki dawo please, wallahi kina dawowa komi ze dawo normal.”
  “Yusuf!” Ta kira sunansa cike da mamaki “nima ka tausaya min mana, ashe de baka sona kafi kowa sanin abinda Mr. Fauzi yakemin ni barin aiki dashi shine mafi alkhairi a gareni kukuma Allah k’ara maku hak’uri amman inde dan in dawo aiki k’ark’ashin wancan mugun mutumin ne ka kirani I’m sorry I can’t.” Karap ta katse wayarta.

   “Wani mara imanin ne Ya Fannah?” Afrah dake game a wayarta ta tambayeta.
     “Yusuf ne wai in dawo aiki a Flames Enterprises...” nan de ta labarce mata komi.
   “Ayya amman sun ban tausayi gaskia shege Mr. Fauzi an gasu!” ta fad'a tana dariya. Dariyan itama Fannah takeyi “ai ya gasu ya k’one Allah ya riga ya rabani dashi har abada!”

    Washegary...
 
    As usual k’arfe takwas dadai ya cika wa Fannah a office kap co workers nata suna santa dan hali irin nata me kyau. Chan around 10:30AM tana zaune tana faxing wasu papers aka danna mata kira daga Manager’s office zuciyarta fal taje sam basu tab’a samin matsala dashi ba tun dawowarsa ita ta d’au ma batun promotion dayace ze mata ne. Bayan ta shiga office nasan ta gaishesa cike da girmamawa kamar yadda ta saba da fara’a ya amsata sannan ya nuna mata kujera ta zauna. “Fannah Aleeyu kamar yadda kika sani kina d’aya daga cikin hard working employees d’ina ko kad’an bansan rasaki amman in yazama dole kinga ba yadda na iya.”
   Murmushin dake fuskarta ne ya gushe a hankali. “Bangane ba Mr. Azeez.”
    “Fannah babban matsala na samu da wannan organisation namu wanda yazama dole in rage ma’aikatan da aka d’iba last 3 weeks wanda nakeso da alkhairi kenan wanda kuma ba haka ba, zasu cigaba da aiki nan amman ba albashi. Inasan ki da alkhairi Fannah sesa zan fara sallamar ki and already na riga na samo miki aiki ma me kyan gaske.”
     “Allah sarki Mr. Azeez ni ko ba albashin ‘yan watanni zan maka aiki karka damu, inasan aiki anan sosai.”
    “A’a Fannah” I insist please. “Ga wannan” nan yaciro envelope “dubu hamsin ne ciki albashinki na wata gabad’aya.”
   “Mr. Azeez ai banyi aikin wata ba kayi deducting please seka samu ka biya wasu dashi..”
   “Ni na baki Fannah ki rik’e karki damu”
   “Toh nagode sosai Allah saka da alkhairi, matsalar da organisation naka yasamu kuma Allah takaita.”
   “Ameen” yace yana mata murmushi
  “Toh Mr. Azeez ina ne inda kace ka sama min aikin?”
     “Ba ko ina bane se Flames Enterprises.” Take taji zuciyarta ta buga ai ba Flames Enterprises ba sunan chan wajen, hell shi yakamata ana kiran wajen da.
 
     “Lafiya Miss Aleeyu?” ya tambayeta.
   A kid’ime tace, “a’a, a’a nagode Mr. Azeez gobe in shaa Allah zanje nagode.”
    “You’re welcome, yawwa please karki sanar da wani ko wata maganar da mukayi dake kar su gudu in rasa ma’aikata.”
   “In shaa Allah na gode da erin karamcin da ka min Allah saka.” Da “Ameen” daya amsata ta fice. Jakarta ta d’auka tama sauran ‘yan uwan nata k’arya kan zata gida.

     Bayan ta isa gida ta tarar da duka family member’nta banda Aiman dake school zaune suna hira harda Baba dad’i taji sosai Babanta na samun sauk’i. “Fannah ya haka yau?” Tambayar Mami.
  Murmushi ta musu duka “wallahi matsala aka samu da ma’aikatanmu...” nan de ta zayyana masu komi. Ba wanda yaji dad’i cikinsu saboda sun san wahalar neman aiki.
  “Karki damu ‘yata zamu taya ki da addu’a in shaa Allahu nan da lokaci kad’an zaki sake samun wani aikin.” Baba ya tabbatar mata yana me mata murmushi.
   “Gaskiyan Babanku ne Fannah karki damu akoi Allah.”
   “In shaa Allah Mami gashi kuwa ya biyani albashi na na wata kinga zamu samu mud’an yi siyayya. Afrah zo mu shiga daga ciki.” Shigarsu ciki Fannah tabata labarin aikin da Mr. Kabeer ya nemo mata a Flames Enterprises.

    K’irji ta dafe tare da zaro ido. “Kin gudu baki tsira ba Ya Fannah ya zakiyi yanzu?”
   “Nikuwa na gudu na tsira Afrah banga abinda ze sake sani ma Mr. Fauzi aiki ba. Chab! Aiko Mr. Azeez yazo ya kirani nan gaba ce masa kawai zan nasamu wani aikin daban.”
   Shiru Afrah tayi tana nazarin abu. “Tunanin me kike haka?” Fannah ta tambayeta tare da d’an bugin ta a hannu. “Something smells fishy anan.” Afrah tace tana tunani.
   “Meh kenan?” Fannah ta tambayeta a takaice.
   “Mesa Mr. Azeez ze tura ki Flames Enterprises kinsan me nake gani? Gani nake kamar Mr. Fauzi nada hannu cikin wannan abu.” Shiru itama Fannah tayi tana nazarin abinda Afrah tace. Chan ta murmusa “ko kad’an Afrah kin manta Yusuf yace kullum cikin koran ma’aikata yake ai kinga kuwa dole yana neman masu aiki safe da dare and ko ba dan haka bama I trust Mr. Azeez”

     Kai Afrah ta giad’a nufin ta gane. “Kinyi gaskia kuma fa mude fatan mu Allah baki wani aikin ba sekin wahala.”
    “Ameen Afrah gobe zan shiga nema in shaa Allah.”

***
   Tun k’arfe 9:00AM Fannah tabar gida bayan addu’o’in da su Mami suka ta suburbud’a mata. Mr. Fauzi kuwa yau office nasan ma yak’i shiga yana tsaye bakin k’ofa shi a dole yana jiran isowar Fannah dan tun daren jiya da Mr. Kabeer ya fad’a masa yayi firing nata yakasa hak’ura se Allah Allah yake gobe yayi. Mamaki ne ya cika kowa a building d’in wai yau Mr. Fauzi ke tsaye bakin k’ofa ko wa yake jira se Allah! Ganin har 11:00AM ba alaman Fannah ya dawo ciki da disappointment karara a fuskarsa. Bade ta samu wani aikin ba? In bahaka ba me ze hanata zuwa? Ai sosai Fannah bata wasa da aiki, what could be the problem? Wayarsa ya d’au ya kira Idrees bayan kamar minti biyu Idrees ya iso bayan gaisuwa yace, “yes Boss you called for me.” Giaran murya Anas yayi “aiki nakeson saka and banasan failure, kanajina?”
  “Inaji Boss fad’a min duk abinda kakeso ayi maka.”

 
© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 29
BY MIEMIEBEE


 
  “Kasan Fannah Aleeyu ko wacce ta tab’a aiki anan?”
    “Wacce take had’a maka coffee Boss?”
   “Yes ita.” ya amsa sa a takaice.
   “Sosai nagane ta friend na Yusuf ce.”
    “Toh ban tambayeka ba.” Ya tsawata masa.
    “I’m sorry” Boss ya sunkuyar da kansa.
    “You better be, bawani aiki zan baka ba illa spying akan Fannah dana keson kana min, inasan yazamo duk inda zataje dakuma duk abinda take ciki ka sani kana turo min rahoto.”
    “Okay Boss nagane.”
      “Good, karka bari ko da information d’aya ne ya wuce ka, do you get me?”
    “Yes sir.”
   “Good inka min wannan zan baka mak’udan kud’ad’e. Off you go, ga number’nta” nan ya mik’a masa rubucaccen number’n Fannah kan wata paper. “Ka kirata yanzu seka samu kayi tracing inda take.”
     “Yes Sir” nan ya fice.

   _30 minutes later..._
   
     “Hello Boss yanzu Fannah tabar state secreterial.”
    “Good ka shiga ka tambaya min ko aiki suka bata”
      “okay sir.” Nan ya katse wayar ya shiga. Tambayoyi yariga ma receptionist na wajen itako jaka ta riga basa information saboda tagansa kyakkyawa ba laifi, dama da biyu Anas yayi assigining Idrees yin aikin. “Kina nufin har kunbawa Fannah aikin kenan?” Idrees ya tambayeta.
    “Eh Idrees mun bata saboda takardun ta sunada kyau.” Ta fad’a ta na kashe masa ido
    “Okay inasan number’n Manager’n ku if possible.”
   “Sure Idrees” nan ta basa dan sokanci godiya ya mata sannan ya fice “se na kira ki koh?”
   “Okay!” tace masa tana nin dad’i. Aiko yana fita yayi blocking number’nta bata sake ganinsa ba tun daga ranan.

     Anas ya kira “hello Boss nayi tambaya wai eh tasamu aiki a ma’aikatan amman na amso maka number’n boss d’in sekuyi magana.”
     “Excellent! Ka iya aiki” yayi exclaiming “turo min lambar and kacigaba da binta aikinka na kyau.” Bayan minti d’aya Idrees ya masa sendn number’n Manager’n wajen. Da telephone office nasa ya kira Manger’n. Manager’n na ganin Flames Enterprises ya d’aga jiki na rawa.
   “Ranka ya dad’e Mr. Fauzi ina gaisuwa.”
   “Yawwa barka” straight to the point ya wuce “Fannah Aleeyu da kuka bawa aiki yanzu nakeson kuyi firing nata.”
     “Amman Si-”
    Katse sa Anas yayi “zan baka dubu d’ari biyar.”
       “Toh anyi an gama Sir bari in ta dawo gobe ina jiran alert.”
    “Karka damu just do as I say ina jiran feedback.”

       Idrees be bar bibiyar Fannah ba sanda yaga tashiga gida sannan ya kira Anas ya fad’a masa.
     Fannah ta shiga cikin gida da farin ciki fal a ranta ta sanar da family’nta aikin da ta samu sosai suka tayata murna. Washegari ta koma ma’aikatan suka tareta da sad news na fasa bata aikin da sukayi. Zuciyarta taji ya kariya. “Dan Allah kode wani abun nayi kuka hana ni aikin kuyi hak’uri, ina buk’atar aikin nan. Kefa jiya kika kai wa Manager’nku takardu na yakuma yaba, yau kuma kice kun fasa?”

    “Eh an fasa seki k’ara mai please.” Abin tausayi Fannah taja jakarta ta fice wani ma’aikatan ta wuce neman aiki take suma suka bata aiki. Bayan tafiyarta aka koma gidan jiya Idrees yabi sahu yau ma mace yasamu as receptionist d’in ya tsarata yasamu ya ta fad’a masa news dayakeso tare da basa number’n Manager’n.
     Shima kud’i da dama Anas yabasa ya yarda yayi firing Fannah.

    Duk aikin da Fannah ta samu da ta koma washegari se suce sun fasa sun canza mind nasu, sosai abin yake daminta ranan harda kuka. A inda tasamu aiki a k’arshen ne bayan tafiyanta Idrees ya shiga to his suprise yaga wani santalelen gardi as receptionist d’in yasan koda mutuwa zeyi ba basa information da yakeso ze masa ba. Fita kawai yayi ya kira Anas nan ya masa kwatancen ma’aikatan. Meeting Anas yakeda amman yayi cancelling in akan Fannah da coffeen ta ne baya wasa.

    Bayan like 15 minutes Anas ya iso wajen tare suka shigo cikin building d’in atare wajen receptionist d’in suka nufa. Bayan ya gaishesu Anas yace, “take me to your Manager.”
    “Sir I'm sorry amman se in kanada appointment dashi tukuna, me sunanka in duba.”
    “Tambaya ma kake waye shi? Bakasan Mr. Fauzi bane?” Cewar Idrees dake tsaye bayan Anas.
   “I’m sorry Mr. Fauzi amman bakada appointment dashi.”
    “You’re very stupid and zan tabbata an koreka daga aiki anan stupid kawai” Chan ya hango wani na wucewa “hey!” Ya danna masa kira jiki na rawa mutumin ya iso “ranka ya dad’e, sannu da zuwa yau manyan bak’i mukeda a office namu? Kai D’anladi bakasan mutane bane? Ai Mr. Fauzi ba’a had’a masa appointment. Koda yaushe yazo he is welcomed”


    “Ahto gaya masa de” cewar Idrees.

    Kallo Anas ya watsa ma D’anladin sannan ya dawo da kallonsa kan Isah “so nake ayi firing wannan mutumin.” ya nuna D’anladi da yatsa.
    Hak’uri Isah ya soma bawa Anas. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri shekaran jiya ya shigo gari, be sanka bane, kai D’anladi baraka basa hak’uri bane?” Ya daka wa D’anladi tsawa.
   “Kayi hak’uri Sir.” Kallon sa Anas yake cike da rashin isa “sede D’anladin kam. Uhm Isah Mr. Abdullahi na nan kuwa?”
    “Eh Manager na nan mu haura sama please.” Nan sukayi sama kamar yadda Anas ya saba siye mutane da kud’i haka ya siye Mr. Abdullahi. A dad’insa yanzu kap inda Fannah zata samu aiki yayi blocking batada wata option other than ta masa aiki.

  **
   Kuka Fannah take sosai Mami na bata hak’uri. “Haba! Fannah sekace ba muslima ba? Ke da nasanki da rungumar k’addara kiyi shiru kukan ya isa.”
    “Haba Mami abin ba daidai ba, ace duk inda naje se bayan sun d’aukeni in nakoma washegary kuma suce sun fasa.”
    “Ya isa Fannah akoi Allah ki dad’a hak’uri.”
     “Kiyi hak’uri Ya Fannah” cewar Afrah tana bubbuga bayanta a hankali cike da tausayi da damuwa.

    Fannah bata sake lek’a waje ba tun daga ranan. Sosai rashin aikinta yake damunta in kud’in hannunta ya k’are bata san ina zata samu kud’i tabiya kud’in asibiti da magunan Baba ba. Tasan sarai inda a yanzu zata je wajen Anas ze bata aiki amman barata iya jure wulak’ancin sa ba, mutum ne ace ko kad’an baida slightest regard wa d’an adam. Ita dashi har abada in shaa Allah ta gommaci talauci ya kashe ta data sake masa aiki.
 
     _One week later..._

    Haukacewa ne kawai Anas beyi ba yarasa me ke ajiye Fannah har yanzu batazo neman aiki gunsa ba. Gashi koya tura Idrees ce masa yake Fannah bata fita, toh why? Ta hak’ura da neman aiki kenan komeh? Bare iya explaining ya yayi missing coffeen ta ba tun rananda tabar masa aiki har ila yau baicin abinci kamar yadda ya saba ci da. Shi yanzu abu d’aya ne yasan inya aiwatar dolen Fannah zata dawo masa aiki shine in zeje gidansu, gashi dama Idrees yamasa bayanin yadda gidansu Fannah yake basuda arziki. Wayarsa ya d’auko ya kira Ahmad. “Hello Boss good day.”
   “Yawwa kaje ka d’au credit card d’ina cikin mota a bud’e ne kayi duk siyayyan dakasan magidanci zeyi wa family’nsa I mean food items, kayan sawa home appliances komi da komi ka gane?”
    “Yes Boss angama.” Nan ya katse wayarsa. “In baraki dawo ba Fannah I will force you to.”

    5 hours later...

    Anas na zaune a office nasa yana jiran call daga Ahmad baya son se Maghrib yayi, aikuwa a lokacin Ahmad ya kirasa “Hello Boss komai is in place kamar yadda ka buk’ata motan kayan na nan pake a bakin main gate.”
     “Good gani fitowa.” Turare ya sake feshe jikinsa dashi ya giara gashin kansa ya tabbata he is looking okay sannan ya fice. Motarsa ya shiga motan kayan kuwa Ahmad ne ciki yana gaba Anas na biye dashi har gaban gidansu Fannah suka tsaya. Sosai yasha mamaki ashe saisa Fannah batta wasa da aikinta ashe basu da k’arfi ne sosai. Kallon gidan ya tsaya yi dan ko a Bama gidansu yafi wannan kyau.

    Daidai lokacin Aiman ta taso daga islamiya se b’antare charbin Malam dake hannunta take tana nufowa kusa da gidan alokacin data d’aga fuskarta Anas yaga alaman kamannin Fannah tattare da ita nan take ya yanke hukuncin kasancewar ‘yar yarinyar k’anwar Fannah. Daidai tazo shiga gidan ya dakatar da ita ta hanyan kiran ta da “‘yan mata.” A hankali ta d’ago kai tana kallonsa bata gane kamanninsa ba kasancewar yasa sunglasses.
   “Wace ‘yanmatan” ta kalli left and right “ni? Barin d’an maka tambaya bature ne kai please naga kayi fari dayawa”
   Dariya sosai Anas ya tsaya yi sekace ba shi ba, kawai se yarinyan ta tuna masa da Angel nasa Amal.
   “ A’a ni ba bature bane ‘yanmata”
   “ Nifa kadena cemin ‘yanmata, ai Ya Fannah tace ni yarinya ce ba ‘yan mata ba wai ita da Ya Afrah ne ‘yan mata.”
    “Toh Ya Fannah ta miki k’arya ai ‘yan mata ce ke.”
   “Toh kaikuma fa? Samari?” Ta tambayesa tana jefa charbin malam data b’are a baki tare da taunawa.
    “Ni big uncle ne suna na Anas, kinacemin Ya Anas.”
   “Ya Anas.. Ya Anas ni Aiman a ina na tab’a jin wannan suna?” Ta tsaya tana tambayar kanta.
   Yana ciro glasses nasa aiko kamanninsa ya bayyana.
  “Laaaaa!!! Blue eyes na TV. Me kazo yi agidan mu? Ashe ba bature ne kai ba, kazo ne muma asamu a TV’n?”
   Dariya sosai yake wanda ya mugun masa kyau, fararen hak’waransa suka bayyana, dimple nasa d’aya ya lotse. “Kinasan kiga kanki a TV?”
  “Eh mana ai social studies teacher’n mu tace celebrities kawai ake gani a TV nima inasan in zama d’aya.”
   “Toh kar ki damu, yanzu kizo ki kaini cikin gidanku.”
“A'a'a'ahhhh chabdi! Ai Ya Fannah ta hana. Maza basu shiga gidanmu gaskia me blue eyes kayi hak’uri karka sace min iyaye da yayu. You are a stranger.”

   “Kefa kikace kina gani na a TV karki damu b abinda zan miki. Ahmad ina sweet d’incan?” nan Ahmad ya koma mota ya ciro packet na sweet Anas ya amshi, “ungo zo ki karb’a.” Ya fad’i yana mik’a mata.
    “Blue eyes tsakanin ka da Allah baka sa abin sace yara ciki ba?” dariya sosai Ahmad yake.
   “Kice min Ya Anas ba blue eyes ba.”
    “Toh Ya Anas.” Ta fad’a yawunta na d’iga k’asa.

      “Bari kiga” nan ya bud’e ya ciro d’aya tare da sha “kinga ba abinda yamin. Zoki karb’a se ki kaini gidanku. Ya Fannah tasanni, nine Mr. Fauzi. ”
    “Ohhh ashe kaine me sa Ya Fannah kuka.” Yi yayi kamar be jita ba yace, “karb’a mu shiga toh.” Ba musu ta amshi pack na sweet d’in “muje toh Ya Anas.” Bayan ta yabi suka shiga gidan kam ba laifi tsatsaf ba k’azanta.
    “Mami! Ya Fannah! Ya Afrah! kufito munyi bak’o kuma ya bani sweet har packet.” Fannah ce ta soma fitowa ko hijabi batada ‘yar vest ne kawai jikinta tana shan iska.

      “Aiman ban hanaki shig-” bata k’are maganar ba suka had’a ido hud’u da Anas ai a guje ta koma ciki se nishi take. K’wak’walwar Anas sanda yabar functioning na d’an lokaci ganin Fannah ba kayan arziki. “Ke Ya Fannah wa kika gani haka kike wannan nishi” cewar Afrah dake game as always. Kasa magana Fannah tayi kawai waje take nuna mata da hannu. “Meh gamo kikayi?” Kai ta kad’a mata still tana nuna waje. Kafin Afrah ta tashi suka jiyo muryan Mami na masa lale su Mami anga Mr. Fauzi. Lek’awa Afrah tayi tagansa zaune kan tabarma d’aya da Mami.

    Ashe haka bawan Allan keda kyau, yama fi kyau a fili akan a gidan TV lallai Allah yayi hallita. “Ya Fannah Mr. Fauzi nefa! Mr. Fauzi a gidanmu!” ai da gudu tayi wajen sa kayansu taciro kayan sallarta. “Ki sa hijabi mu fita mu gaishe sa. Ma meyazo yi tukun? Halan bikonki” Duk ta kidime se suratai take tayi.
      Hannunta Fannah ta rik’o “ke jakar ina ce? Ina zaki? Meh Mr. Fauzi yazo yi gidan mu? Nashiga uku Allah sa ba sharri ya taho dashi ba.” Afrah ta bud’e baki zatayi magana suka jiyo kiran Mami “Fannah! Afrah! kufito mana Mr. Fauzi nefa yazo.”
    “A’a Mami Anas de” cewar Anas sewani behaving yake kamar d’an arziki. “Kufito da sauri” Mami ta sake k’olla masu kira. “Toh” Afrah tace. “Ya Fannah kiyi sauri.”
  “O’o ni barin fita ba ni yama yasan gidanmu? Ya Allah help me!” Hannunta Afrah ta fisga daga rik’on Fannah ta fice a guje har k’asa ta gaishe da Anas ya amsa da fara’a se murmushin show off yake. “Aiman kawo wa Ya Anas ruwa kinji?”
   “A’a Mami ta bari daga office nake yanzu naci abinci.”
   “Allah Babana ko ruwa bara ka sha ba?”
   “Eh Mami, ina Baba? Ya jikin nasa?” Fannah dake mak’ale jikin window tana jinsa ji take kamar taje ta shak’uresa ji yadda yake abu kamar d’an arziki.
   “Jikin Baba da sauki. Afrah ina Fannah newai? Fannah!” Ta danna mata kira.
     “Na’am Mami” ta amsa kan wanda zatayi kuka. “Kifito mana me kikeyi ne?”
    “Mami gani nan.” Hijabi ta zumbura sewani kumbure kumbure take.
   Koda ta fito bata d’aga kai ta kalli Anas ba shikuwa idanunsa na kan ta rabuwansa daya sata a ido har ya manta.

    “Baki ga Mr. Fauzi bane da baraki gaishe sa ba?” yi tayi kamar bata ji me Mami tace ba.

© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 30
BY MIEMIEBEE


Kallon Fannah Mami ke cike da mamaki, wannan ne karo na farko da Fannah ta sab’a wa umarninta bakuma tare da ta nuna damuwa ba.  “Fannah dake fa nake magana, meke damunki ne? Baraki gaishe sa ba?” Ta sake tambayarta. Nan ma shiru tayi, a kunyace Mami tace, “Anas kayi hak’uri bansan meke damun Fannah ba.” Murmushi yake kaman ba shi ba “ba komai Mami maybe bata san yin magana ne” blue eyes nasa ya d’ago yana kallonta sosai, haka kawai yasamu kansa cikin niahad’i in yana kallon innocent face nata, sarai taji yadda yake kallonta amman ko d’aga kai batai ba. “Fannah tunda baraki gaisheni ba ni zan gaisheki ina wuni?”

     Shiru tayi bata amsa ba, Mami de tashiga cikin duhu wai ace Mr. Fauzi na gaishe da Fannah amman barata amsa ba. “Anas kayi hak’uri dan Allah bansan meke damun Fannah ba yau, Afrah ko kunyi fad’a ne?”
   “A’a Mami ba abinda ya had’a mu.” Afrah ta fad’i cike da zumud’i se satan kallon Anas take.
   Giaran murya Anas yayi “uhm Mami nasan kuna mamakin ko me nazo yi anan koh? Bikon Fannah nazo yi, dama misunderstanding muka samu tabar min aiki akan had’a coffeen da take min ne tace ta gaji dayi sede in zan bata aikin daya fisa nikuma alokacin banida aikin da zan bata.”
 
            Baki wangalau Fannah ta bud’e tana kallon ikon Allah yanzu ko kunya baiji yake wannan k’arya. Kut lalle! “Mami walla-” ta gwada kare kanta.
       Katse ta Mami tayi “se yanzu bakin ki yaga daman bud’uwa Fannah? Toh kiyi shiru Anas ya gama, ina jinka Baba na.” Idanun sa ya d’aga yana kallonta, itama kallon nasa take, murmushin mugunta ya saki mata wanda ta murgud’a masa baki in return tare da kawar da kallonta daga garesa. “Yawwa, shine tayi resigning amman yanzu da nake neman Personal Assistant (PA) kuma gashi takardun ta sunada kyau zan d’auke ta aiki. Albashi dubu d’ari biyar da kuma weekly allowances N5,000.”

          “Alhamdulillah!” Mami ta fad’i cike da murna. “Alhamdulillah! Aiki har gida Allah ya kawo miki Fannah, wallahi Anas ba abinda zance sede Allah maka albarka ya k’ara d’aukaka da girma, aiki ba inda Fannah bata nema ba amman seta koma washegari se suce sun fasa, abin de ba dad’i”
    “Fannah ke baki iya godiya bane?” Mami ta tambayeta. Shiru tayi kamar bata jita ba.
    “Mami kibar Fannah yau kawai bata san magana ne, ai mutane yanzu sun sa san kai a gaba, su yasu kawai suka sani. Se hak’uri.” Idanunsa ya d’aga yana kallon Fannah dake tsaye har yanzu ta had’e gira gu d’aya. “So Fannah zaki dawo min aikin? Tunda na canza miki post yanzu”

      “Anas yanzu har seka tambaya ko zata koma ne? Ai komawa ta riga ta koma kawai ka fad’i yaushe kakeson tayi resuming office.”
   “Mami!” Fannah takira sunanta cike da takaici. “Wai me haka?”

    Sanyi yaji a ransa jin muryarta kawai.
       “Eh mana Fannah, a jinki akoi inda zaki samu aiki me kyau haka ne? Gaskia Anas mungode sosai sosai Babansu na bacci da ya maka godiya shima.”
    “A’a Mami ba komai nine da godiya. Gobe nakeson Fannah ta soma aiki.”
      “Allah kaimu Anas, In shaa Allah a goben zaka ganta” Hannu yasa a aljihu ya ciro bandir na d’ari biyu tare da ajiyewa gaban Mami “ga wannan a saya wa Baba magunansa dashi da kuma sweet wa Aiman ko?” ya dawo da kallonsa kan Aiman dake manne a jikinsa se mamakin gashin hannunsa take.
   “Yeyy! Ya Anas nagode. Ya Fannah ba sekin sake min rowan naki ba Ya Anas yace a siya min” kallo Fannah ta watsa mata wanda batasan Anas na kallonta ba.
   “Anas Babana da wahala haka? Toh mungode Allah saka da alheri.” Fannah ji take kamar ta k’urma ihu ita wallahi barata koma masa aiki ba sede sama da k’asa su had’u.
    “Ermmm Ahmad!” ya danna masa kira nan Ahmad dakw waje yashigo bayan ya gaishe dasu Mami Anas yace ya shigo da kayakin. Dama already yariga ya tara almajirai nan suka soma shigowa da kayaki. Ba Mami kad’ai ba har Fannah sanda tasha mamaki wato siye mata iyaye zeyi da kud’i da kayan duniya, lallai kuwa.

      Kap tsakar gidansu sanda aka cika da kayaki tun Mami da Afrah suna godiya har suka gaji sukayi shiru. Addu’a sosai Mami ta riga ma Anas tana suburbud’a masa albarka ga kyautan kud’i ga kuma na kaya, abinde ba’a cewa komi. “Anas kace ko ruwa baraka sha ba? In aika Aiman ta siyo maka ko maltina mana.”
   “A’a Mami ba komai”
     “Gaskiya Anas ba abinda zance maka, ka gama mana komi naso ace idan Babansu biyu wallahi yamaka godiya, Allah saka da alheri ya k’ara  bud’i”
     “Haba! Mami ai ba godiya tsakaninmu, ya isa please.”
   “Toh ina zuwa, Afrah biyoni.”
    “Afrah kad’ai Mami nikuma fah?” Cewar Aiman “ni ma sena bi ku.” Cak ta tashi daga gefen Anas ta bi bayan su Mami zuwa d’akin Baba. Ya rage daga Anas se Fannah itama juyawa tayi zata shiga d’akinsu ya mik’a dogon hannunsa ya cafko ta da hijabi chak ta tsaya ba tare da ta kalle sa ba tace, “Mr. Fauzi ka sake min hijab.” K’in sakewa yayi, ya mik’e tare da shan gabanta yana d’auke dawani murmushin mugunta a fuskarsa.

       “Stop pretending, nasani you miss me.” Yace da ita.
         “Miss you? A dalilin me zanyi missing mutumin da yake sa ni kuka all thetime? Mr. Fauzi kasan meh? Ni barin sake koma maka aiki ba, na bari na bari forever, ko coffee maker’n ka barin sake zama ba bale PA, kuma wannan tarukucan kayakin daka kawo ka tattara ka mayar dasu inda ka kwaso su bama buk’ata.”

      “Ai aiki min kin riga kin dawo k’arfe 8:00AM gobe don’t be late, wannan kayaki kuma anan zasu zauna, tunda kikayi resigning ba tare da kin sanar da ni ba nima haka zan  dawo dake ba tare da sanin ki ba. Karki manta everything can be bought with money kamar yadda na saya family’nki yanzu. Inba wai so kike ki b’ata wa Mami rai ba zaki dawo min aiki gobe.”

     “No Mr. Fauzi you are wrong, not everything can be bought with money, aiki maka kuma na riga na bari ba dawowa.” Hijabin ta ta
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).