shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 7 September 2016

TANA TARE DANI...21--25

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 21
BY MIEMIEBEE


Yusuf nada mutunci sosai cikin d’an k’ank’anin lokaci suka saba da juna, dake yanada surutu sekuma gashi shekarunsu d’aya, ma’aikaci ne shima a company’n. Har kitchen d’in ya kaita yajira bayan ta gama had’awa ta bashi ya amshi yakai wa Anas sannan ya dawo dan rakata har waje. wajen wata elevator suka nufa wanda is different from na d’azu dan haka ta tambayesa ko ina zasu. Murmushi yamata sannan yace, “sauk’a zamui zuwa first floor saboda in fita dake kar ki b’ata a wannan babban gini.”
     Murmushin ta maida masa “amman naga ba tanan muka hawo da Mr. Fauzi ba.”
    “Hakane, ta private elevator’nsa kuka hauro wannan kuma da zamu shiga shine na public, wancan nasa ne shi kad’ai ke shiga you are lucky ma kinsamu kin shiga wancan.” Ya mata bayani. ‘yar murnushi tayi tabi bayansa har waje ya rakota ya tsara mata napep sannan ya koma ciki. Daga can kasuwa ta wuce ta musu siyayyan abinci sosai tunda sun samu kyauta.

      Isarta gida keda wuya ta tarar da ‘yan sanda tsaye daga gani ita suke jira fuskar su Mami duk ya jik’e da hawaye. “Yawwa ga ta nan” cewar wata nurse.
    “Ku tsaya please.” Fannah tace da polisawan.
    “Dalili?” Cewar nurse d’in.
      “Ga kud’in kunan nasamu dan Allah” nan ta irga dubu goma ta bata sannan suka fice. Godiya Mami tayi wa Allah da gudu ta ruga tayi hugging Fannah.
     “Fannah dan Allah kiyi hak’uri ban tab’a san d’aya daga cikin abubuwan da suke faruwa dake su kasance haka ba dan Allah kiyi hak’uri.”
     “Haba! Mami wace erin magana kike inda kunji good news danake tattare dashi ma da duk kunbar kukan nan. Ga nan siyayya na mana nasamu aiki!!”

       Atare duk sukace “dan Allah???” “Alhamdulillah.” cewar Afrah.
    “Aina?” Mami ta tambaya.
    “A Flames Enterprises wallahi Mr Fauzi ya d’aukeni aiki wai zanna had’asa masa coffee...” nande ta musu bayanin komai. Sosai Mami sunji dad’i musamman ma dasukaji albashinta dakuma kyautan da ya mata. Nasiha sosai Mami tama Fannah dukda cewar tasan Fannah da hankali. Albarka tata sawa Anas data ta tsine masa da a baya.

   ***
     Tun k’arfe  4:40PM Fannah ke rik’e da wayarta gudun karta k’ara ko minti d’aya kan lokacin da Anas ya bata. 4:50PM na yi ta kirasa yana kwance kan gado alokacin call d’in yashiga yana gani yagane ita ne beyi picking ba instead seya katse nan yayi saving number’nta da *COFFEE MAKER* cike da mamaki ta sake kira mesa ze katse bayan shi yace ta kirasa  be d’aga ba sansa ya kusan tsinkewa. Cike da tsiwa yace “ke baki gane kan aiki ne? Kinga nayi declining call meaning na gane kece kenan haba!.”
  “I’m so-” bata k’are maganar ba ya katse wayar. Miyau Fannah ta had’e ita kam Allah bata ikon jure wulak’anci da masifan Anas.

     _Washegari..._
    Da safe da misalin k’arfe 7:40AM Fannah da Aiman da Afrah suna kwance kan katifarsu se bacci suke rafkawa an samu an k’oshi jiya wayar Fannah yasoma ringing firgit ta farka dake wayar na k’ark’ashin pillownta a gigice ta d’aga ganin sunan daya bayyana kan screen d’in ya wassakar mata da bacci. MR. FAUZI giara muryanta tayi sannan ta d’aga.
    “Assal-” be jira ta k’are sallaman ba ya katse ta “be here in my office at 8:00AM. Don’t be late” kafin tace “okay” ya katse wayarsa. Ita ba ma wannan ba duban agogonta tayi taga 7:42PM
“YA SALAM!!” ta d’anyi ihu “yaushe zanyi wanka in karya in tsari napep in isa har NEW GRA cikin minti 18 wayyo Allah help me.”

     Ko tafasa ruwan zafin wankanta batai ba da ruwan sanyi tayi wankan anayi ana ihu har ta k’are tafito ko shafa mai batai ba, da k’yar da fad’a da kokuwa tasamu ta kama gashinta hakan ma be kamu ba sakwa-sakwa kawai de aje ne. Tea da biredi ta karya da, ba Butter bale Jam haka gayansa taci ta saka wata maroon material lace da farin hijabi nan da nan ta d’au wayarta tajefa cikin jakarta da d'ari biyar ta fice. Duban agogonta tayi taga 7:53AM ji take kamar ta fire kafin ta sami keke napep har da 55 yayi. A takaice de se 8:20PM ta isa New GRA. Lattin minti ishirin tayi, imagining kalan masifan dazata sha gun Anas kawai take dan sanda ya fad’a mata baya tolerating late coming.

     Da Yusuf ta fara yin karo shiganta ciki ko gaisuwan arziki bata tsaya sunyi ba ta shige elevator se sauri take yayi ya ruhu, yana ruhuwa kuwa yafara tafiya sama ji take kamar ta fire sama bayan ya bud’u tafita da sauri gudu tayi ta k’arisa bakin k’ofar ta bud’e a hankali ta shiga tsaye ta gansa bayansa na fuakantarta sanye yake dawata pitch long sleeve shirt wanda yad’anyi rolling sleeves d’in zuwa k’ark’ashin elbow nasa. Waya ne rik’e a kunnesa se faman masifa yakeyi fitsari Fannah tasoma ji take tun kafin a fara mata nata bayan ya k’are wayar ya buga wayan kan table d’in tare da jan tsuka.

    B’ari take tayi “zaki k’ariso nan ne kokuma senayi firing naki!” Ya daka mata wata erin tsawacaccen tsawan da be tab’a mata ba. Tuni hawaye suka ciko idanunta tafiya take k’afafunta suna rawa har ta k’ariso gabansa kanta a k’asa ko fuskarsa bata kalli ba. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri wallahi unguwar danike da nisa daga nan kafin insamu abin hawa har in zo nan-”
   Katse yayi dawata tsawam sede bekai na d’azu ba “shut up! I don’t care. Koda a wani planet kike bandamu ba in na kiraki you have to be here at the exact time kina jina!?”
      Hawaye na gangarowa kan kumatunta ta giad’a kai “I’m sorry.”
    “Wuce ki had’a min coffee make it quick” ya fad’i yana k’ok’arin zama. Kallonta yake sanda takai bakin k’ofa sannan ya tsaida ta. “Ina kuma zakije?”
   
     Hannu tasa ta share hawayenta “kitchen.”
      “Okay, wannan kuma fa? Na kwalya ne shi?” Juyowa tayi ta dawo cikin office d’in tana kallon direction dayake nunawa da yatsansa, coffee machine tagani.
     “Ban gani bane” tace a hankali.
      “Banasan surutu get on with it duk abinda kike nema akoi cikin fridge d’incan.” Kai ta giad’a seta tuna da halin sa tace, “toh.” A sanyaye ta k’arisa wajen fridge d’in ta bud’e, kwalb’an giyan data gani ba adadi ne ya mugun razanar da ita. Hannu tasa bibbiyu ta rufe bakinta dan hana ihun dake k’ok’arin fito mata. A razane ta juya tana kallonsa shima kallon nata yake.
   
     “Lafiya? Gawa ko jini kika gani ciki?”
    Kasa fad’in komi tayi har yanzu takasa believing abinda tagani. “Ke! Tambaya nake miki.” Kasa amsa sa tayi nanma sanda ya tashi ya nufo wajen, fisgan murfin fridge d’in yayi ya duba cikin. Nanne yagano giyan data gani ciki ne ya razana ta. Kallo ya watsa mata “acikin rules dana fad’a miki sanda na ce miki banasan shisshigi abinda ya kawo ki kawai zakiyi so get on with it.” Yana kaiwa nan ya koma ya zauna. Da k’yar Fannah ta dawo da hankalinta gu d’aya taciro abubuwan da zata had’a masa coffeen da, tare da rufo fridge d’in duk hankalinta bai jikinta bata ma san me take had’awa ba haka ta kwarara sugar ciki tagama takai masa se mamaki take. Yanzu na miji kyakkyawa kamar Anas amman ya b’ata rayuwarsa da shaye shaye? Meyake nema a duniya? Ga kyau ga kud’i mena shaye shaye? Meyake nema? Me yasa yake shaye shaye?

      Anas na kai coffeen bakinsa ya sake maidashi cikin cup d’in dan uban sugar ga coffeen datasa ciki yayi yawa. K’aran da glass cup d’in yayi sakamakon fashewan da yayi k’asa ya dawo da Fannah daga duniyar tunanin data fad’a a firgice ta mik’e daga kan kujerar data ke zaune tana b’ari, hannunta biyu dafe kan bakinta se raba ido take.
     “Meh wannan kika had’a min? So kike diabetes yakamani da zaki d’ura min wannan sugar a coffee?”
     “Sir dan Allah kayi hak’uri my mind was carried away, zan sake had’a maka kayi hak’uri.” ta fad’a tana b’ari.

      “Fannah Aleeyu in kinsan you are not ready for this job ki tattara kanki kibar min office, NOW!” Ya daka mata tsawa. Hawaye ta soma yi take.
    “Mr Anas I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri zan sake had’a maka wani” da sauri taje ta tsuguna ta soma tattara broken glasses d’in acikin yin haka d’ayan ya yanke ta sosai a yatsar ta.
     “Arghhhhhh!!!” Ta saki k’ara a firgice Anas ya taso tare da kama ta da hannunta daga sama da k’arfi sosai ya mik’ar da ita. K’ara ta sake saki se hawaye take ganin yadda jinin jikinta ke d’iga sosai a k’asa. “Bakida hankali ne?” Ya daka mata tsawa.
    “Kin tab’a ganin ana tattara broken glasses da hannu? Mschww.” Hannunta ya ja da k’arfi ya kaita bathroom ba abinda Fannah keyi se kuka ita ko noticing na mijin daba muharraminta ya kama mata hannu ma batai ba dan azaba.

       Famfo ya bud’e yasa yatsan nata a k’ark’ashi ruwa na tab’awa ta sakar da ihu “arghhhhhh!!!” Kallonta yatsaya yi se hawaye take wanke mata yankan yayi sannan ya zaunar da ita kan toilet sit. Har yanzu se hawaye Fannah take bayan ya fice da ‘yan mintuna ya dawo da first aid box hannunsa bayan ya d’iga spirit jikin auduga ya gwada d’aga hannunta seta kankame se yanzu hankalinta ya dawo jikinta ta hanasa rik’e hannun nata dan haramun ne. Kallo ya bita dashi sannan yaja tsaki ya finciko hannun nata da k’arfi ya danna spirit d’in kai ihu ta sake saki “arghhhhh!!! Wayyo Allah zaafiii!!!” Be cire ba sanda ya tabbata spirit d’in yashiga sosai. Sannan ya ciro plaster ya b’are ya nannad’a mata a hannun.

      “Get up!” Yace da ita tana kuka tabi bayansa suka koma cikin office d’in coffeen ta wuce zata had’a masa sabo. “Meh kuma zaki yi can?”
    Murya na rawa tace, “zan sake had’a maka wani ne.”
     “Saboda ki sake yanke hannunki koh? A jinki nid’in ina san rik’e hannun ki ne? Mschww” Matsowa kusa da ita yayi ta matsa baya take “be telling me the procedure in had’a.” Haka tana fad’a masa abinda zeyi step by step har ya had’a sede ko daya tab’a nasan be masa dad’i kaman nata ba.
    Tsuka yaja. “Ba dad’i” ya fad’i a hankali.
    “Sorry sir me kace?”
   Tsawa ya daka mata “nace ba dad’i! Damn it!”
    “Sir! But yadda nake had’awa fa haka kayi.”
    Juyowa yayi ya galla mata kallo “so kike kiji mesa nawa be kai naki dad’i ba? Ehh? Saboda kin fini iya had’awa saboda your hands are special when it comes to making coffee. Dang it!” Ya buga hannunsa jikin bango wanda ya mugun firgita ta. Komawa yayi kan sofa ya zauna tare da sake necktie nasa. Numfashi ya saki “mik’o min bottle na giya d’aya cikin fridge d’in.”

     Ido Fannah ta zaro waro waro. Se salati take a zuci. “Bakiji me nace bane?” Ya fad'i a tsawace.
    K’arya tayi, “na’am banji ba.”
     “Nace ki mik’o min bottle d’aya na beer (giya).”
     “Wayyo Allah!” Fannah tace a zuci “yau za’a sha giya a gabana Ya Allah kace da wanda ya sayar da wanda ya raba da wanda yasha duk sunada zunubi. Wayyo ya zanyi?”
    “Don’t let me repeat myself!” ya fad’i a tsawace. Bata san sanda ta d’auko ta kai masa ba. Fisga yayi ya  bud’e tare da yin wulli da murfin daya kafa a bakinsa be cire ba sanda yashanye rabi. Take idanunsa suka soma juyawa wanda ya mugun firgita Fannah wai a ina tasan wannan idanu? Se yanzu ma take k’ara ji a jikinta sun tab’a had’uwa. B’ari take sosai.

     Bayan ‘yan mintuna ta kira sunan sa “Sir?” Shiru kukeji. “Sir?” Tasake kira “uhmmm” ya amsa a gigin bacci. Gabansa ta k’arisa tasa hannu tana waving a iska ko kad’an be motsa ido ba da alama bacci ya sacesa. Giyan hannunsan ta gwada karb’a ya damke a jikinsa da k’yar tasamu ta karb’e a hankali ta je ta juye a bayi tayi flushing data dawo kuwa ta samesa yana bacci a karkace, kansa yayi gefe guda har ta kai bakin k’ofa zata fita sekuma ta tuna yadda yamata treating ciwonta dukda yata mata tsawa, be kamata tabar sa haka ba shima tabbas inya cigaba da kwanciya haka ze tashi da ciwon wuya komawa tayi ciki dan giara masa kwanciyar, sede bata san ya zatayi ba saboda batasan tab’a sa. Tsayawa tayi kansa tana nazari...

 
© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 22
BY MIEMIEBEE

Ta kai kusan minti biyu tsaye kansa tana nazarin abin yi, chan ta shiga d’akinsa tafito dawata sweet pillow dashi ta riga tura kansa dashi har sanda ya fad’a ya kwanta kan kujeran da k’afafunsa k’asa. Nanma ta juya zata fice ta sake dawowa, tasan inta barsa haka kunkuminsa ze iya masa ciwo kasancewar kujerar dogo ne, tunanin ya zatayi ta mik’ar dashi take. Ido kawai ta rufe tana “astaghfurillah astaghfirullah astaghfirullah” ta d’aga dogayen k’afafunsa ta ajiye kan kujerar duk se bacci yake me uban nauyi ko jin abinda ake mai baiyi. Takalmansa ta cire masa.

         Bayan ta koma d’akinsa ta d’auko masa pillow, nazarin ya zata sa kansa kai take amman takasa, ganin ba mahilicci se Allah kawai nan ma ta rufe ido tana “astagfirullah” ta d’aga kansa, lis hannunta yashige cikin wavy long hair nasa me uban laushi, bayan ta aza kan nasa kan pillow’n ya cigaba da bacci abinsa a hankali. Kallonsa ta tsaya yi sam sekace ba shiba in yana bacci, sam bara’a ce shine me masifa da cin mutunci ba, he is looking so innocent in yana bacci.
 
      Fita tayi daga office nasan ta sauk’o k’asa can ta hango Yusuf nan ta nufa wajensa yana ganinta ya kira sunanta. “Fannah bade tafiya zakiyi ba?”
    “A’a” ta kad’a masa kai. “Mr. Fauzi yana bacci.”
   Ido wuru wuru Yusuf ya zaro. “Bacci? Kin masa wani abu ne?”
   “Mesa kace haka?” Juyawa yayi left and right ganin ba wanda ke zuwa sannan yace, “a iya sani na Boss baya bacci a office fashe an b’ata masa rai seya sha abinda ya saba sha dan ya gusar masa da b’acin ran.”
   “Kana nufin haka yake always kullum yana sha?”
   “Ehh amman kija bakinki kiyi shiru kinga kap nan ba wanda yasan yanayi nima dake abokin k’aninsa ne saisa na sani.”
    Cike da mamaki Fannah ke kallonsa “amman ko kasan dalilin dayasa yake shaye shayen? Naga ba abinda Mr. Fauzi ya rasa kyau, kud’i mesa zena shaye shaye?”
   “Shhh! Fannah kinsan in aka ji muna wannan magana firing namu za’ayi.
     Nide iya abinda na sani shine yanada horrible and terrible past, ance past d’insa ne yasa yake duk wani abinda yakeyi yau, dakuma mutuwan da Babansa Mr. Muh’d yayi a hannunsa. kika lura Boss baya dariya, murmushi ma se in takama.” Kai Fannah ta giad’a nufin tagane inda ya dosa.
     “Allah sarki amman baka da idea mene ne yafaru a past nasan ko mutuwa wani ya masa?”
     “A’a Fannah abinda nasani de wai mahaifiyarsa has something to do with it.”
    “Ayyah” Fannah tace “toh shi be iya rungumar k’addara bane?”
    “Ai da ya iya da bare na yin abinda yakeyi ba. Kinga lets keep quiet kar a jiyo mu yanzu ayi waje damu.”

     _3 hours later..._
    Da misalin k’arfe 11:30AM zaman kad’aici ya isa Fannah, Yusuf ya wuce 4th floor yana aiki. Tashi tayi daga inda take zaune ta wuce office na Anas a hankali ta bud’e k’ofar dan masa sallama zata tafi. Yadda ta barosa haka ta samesa. K’arisawa tayi ta d’au jakarta dadai tazo fita seta tsaya kansa tana kallonsa tana tuna abinda Yusuf ya fad’i mata nan Anas ya bud’e blue eyes nasa suna had’a ido ta kau da kanta cike da kunya. A razane ya mik’e ya zauna yana tuna abinda ya faru. Kafin tace “ni zan tafi” ya riga ta fad’in “me kikeyi anan?”
Baki na b’ari tace “ta..tafiya zanyi nazo d’akuja jakata ne.”
    “Tafiya zakiyi? Da izinin waye? Wait! Ma tukun” Ya tsaya ya kalli k’afafunsa ba takalmi. A gefe guda yagan su. “Waya baki izinin tab’a ni har kicire min takalmi? Wait wannan pillow fah? Waya baki legal right da zaki d’aga min kai ki aza kan pillow?”
    “Ss..sir” tayi i’ina “I’m sorry.”
    “Ina kuma kika kaimin bottle na giyan dake hannuna?”

    “Sss... sir I’m sorry.” Ta fad’a kanta a k’asa.
   “Meaning?” Ya tambayeta a takaice.
    “Na zubar.”
    “Kin meh? Kinsan ko nawa na saya?”
    “Kayi hak’uri dan Allah.”
     “Ba nasan jin komi d’au jakanki kibar min building you are fired.”
   “Sir plea-”
     Katseta yayi “Now!” Ya daka mata tsawa. Fannah bata san sanda ta fara kuka ba, “sir dan Allah kayi hak’uri it won’t ever happen again karka koreni please.”
    “Then ki dena min shisshigi.”
   “Nadena daga yau dan Allah kayi hak’uri.” Kai ya giad’a mata “you’re dismissed for today tunda hannunki is useless baraki iya aiki dashi ba.”
    “Sir I can, in had’a maka coffee ne?”
    Kai ya giad’a mata. Jakarta ta ajiye a yayinda ya zabura yashige d’akinsa to bathroom. Kafin yafito har ta had’a masa ta ajiye kan table bayan ha zauna ya jawo cup d’in yana sha yana aiki a laptop nasa Fannah kuwa kallonsa ta tsaya yi har yanzu maganan Yusuf ya tsaya mata a wuya so take taji mesa yake shaye shaye.
     Ba tare da ya kalleta ba yace, “the next time kika sake kallona zan koreki daga nan.”

      Ji tayi kamar ta nitse a k’asa. Da k’yar tayi k’arfin hali tace, “zan iya tafiya?”
     Ba tare daya amsata ba yacigaba da abinda ke gabansa can Kacallah ya shigo ya kawo masa wasu files yayi signing. “Boss Mr. Nazeef ne yakeson ku had’u dashi akoi wani presentation dayakeson maka regarding project na building drawing d’incan nasan you’ll be busy through out wannan week amman dan Allah consider him na had’a muku appointment tun last 2 weeks yakeson had’uwa da kai.”

      “Kacallah bareyi mu had’u dashi ba, I will be very busy through out this week kabari ko zuwa next week.”
    “Boss kayi hak’uri please wallahi dak’yar nasamu na had’a muku please.”
     Hannu Anas yasa cikin gashinsa yana hargitsawa “ohhh! Kacallah I’m not in a good mood yau please go I’m sorry.” Nan yagama signing wa Kacallah ya fice. Fannah kam mamaki Anas yake bata wai mutum ata had’asa da Allah amman baiji da sauri ta kawar da kanta daga kansa kafin ya koreta. Ana cikin haka wayarsa ya soma ringing nan Fannah ta d’ago kai tana kallonsa bayan ya duba yaga wa ke kira yaja tsaki ba tare da ya d’aga ba. Call d’in na tsinkewa aka sake bugawa a fusace ya d’aga wayar yasoma magana a tsawace “Aleeya please karki sake kira na, wace erin super glue ce ke? nace miki banasan ki I don’t love you ki hak’ura mana! Don’t ever call me again ni na fad’a miki.” Karap ya katse wayar.
 
     Baki wangalau Fannah ta bud’e tana kallon Anas dukda cewar batasan meya had’asa da budurwar tasa ba setaji ta tausaya mata aiko ma me tayi bekamata yamata haka ba, yayi hurting feelings nata yayi yawa haba mana.

       “Lafiya?” Ya tambayeta tare da dawo da ita daga duniyar tunanin data fad’a. “Eh..ehh lafiya” ta fad’i a rikice.
     “Then stop starring at me, kidena kallo na haka please!” Ya daka mata tsawa. Kuka ta soma take tasa hijabinta ta rufe fuskar ta dashi. Ita dama ya sallameta taje gida tagaji da zama nan. Bayan kamar minti goma akayi knocking bakin k’ofar office na Anas a lokacin kuwa yana kan waya nuni yayi da ido kan Fannah taje ta bud’e. Hawayenta ta gama sharewa sannan ta mik’e taje ta bud’e wani ne bata tab’a ganinsa ba.
   Bayan Anas ya kammala wayan ya d’ago blue eyes nasa ya aza kan yaron “yes Haruna wani abu ne?”

      “Boss yanzu wani ya kawo wannan flowers wai daga Aleeya kan kayi hak’uri ga letter nan manne a jiki.” Nan ya matso kusa da table na Anas da nufin ajiyewa.
    “Ka kuskura ka ajiye wannan gabbage (bola) a gabana you’ll be fired.” Ai tsam Haruna ya rungume flawan a jikinsa. “Boss dan Allah kayi hak’uri.”
    “Ka fita dashi bana san ganinshi cikin office d’ina.”
     “Yes Boss. Dama kitchen ne ya d’an kama da gobara amman an samu an kashe da wuri, b’arna kad’an yayi wanda ya kamata a kira me giara da wuri.” Ya fad’a yana b’ari dan ya karanci yau Anas is not in a good mood.
   “Meya jawo gobaran?”
      “Chef (me girki) Zainab ce ta manta tabar cylinder a bud’e se gas yayi flowing amman bada sanin ta bane.”
    “Kaje kayi firing nata now wannan ganganci ne, kace mata inji ni ta tattara kanta tabar min building.”
    “Yy.. Yes Boss” take ya juya ya fita. Fannah kallon Anas take cike da mamaki mesa zuciyarsa take da tauri haka?
 
     “Kinada abin cewa ne?” Ya tambayi Fannah ba tare da ya kalleta ba. “A’a” ta amsa a takaice. Tun k’arfe 2:00PM Anas ya tattara kayakinsa yasoma shirin tafiya gida. Coffee cikin flask yasa Fannah ta had’a masa takuma kai masa har cikin mota sannan ya fice koda ya isa gida Amal kawai ya kula ya wuce d’akinsa. Ba komai ne yasa Anas acting haka ba kuwa a ranan se dan mafarkin Ummimi dayayi.

      Fannah kuwa isarta gida duk su Mami suka soma jero mata tambayiyi ya sabon aikinta, k’arya tayi tace musu great, alhamdulillah.

   _Washegari..._

     Tun k’arfe 7:00AM Fannah ta gama shirinta dukda kuwa Anas be kirata ba amman dan gudun kar tayi latti. Se 7:30AM ya kirata. Tana d’agawa kafin ta gaishe sa yace, “ina jiranki by 8:00AM in kika k’ara koda minti d’aya a bakin aikinki.” Kafin tace, “okay” ya katse wayar. Daman tagama shirinta kud’in transport kawai ta d’auko ta fice daidai 7:55AM ta isa office kasancewar hold ups. A gigice tashiga ciki ta yi elevator daidai 7:58AM tayi knocking bakin k’ofar office na Anas shiru taji ba amsa tayi knocking kusan sau uku ba response wayarta taciro ta duba agogonta taga har 8:00AM yayi daidai nan personal elevator’n Anas ya bud’u tare da bayyano da Anas. Sanye yake da black suit farin shirt da red necktie sosai yayi kyau.

     Bayan ya k’ariso ta gaishesa ba tare da ya amsa ba yasa card nasa ya bud’e ko’far tana a bayansa suka shiga office d’in. Jakarsa ya ajiye kan table sannan ya juyo tare da crossing hannayensa kan k’irjinsa yana kallon Fannah dake sanye da jan hijabi da torches na black tanajin idanunsa kanta ta sada kanta k’asa tana wasa da yatsun ta.
   “Kin karya min doka.” Ya fad’a ba tare da yanuna damuwa ba.
     A razane ta d’ago kai “Sir wani doka?”
     “Kinzo nan before time which means kin karya min doka 8:00AM nace kizo nan ba kafin 8:00AM ba. Take not banasan shisshigi next time.”
   Kai ta giad’a a hankali “okay sir.”
    “Good make me coffee.” Jakarta ta ajiye kan kujera ta nufa fridge d’in ta bud’e tare da ciro abubuwan da zata buk’ata within 2 minutes ta had’a masa taje ajiyewa kan table d’in amman hannunta se b’ari yake garin haka coffeen ya zube saura a jikinta saura jikin Anas saura kuma kan wasu papers.

     Tsawa ya daka “WHAT IS WRONG WITH YOU? Meke damunki? Bakida ido ne. Mschww” harara ya watsa mata “you’re so clumsy.”
    Hawaye take sosai “Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri.”
    Ba tare da ya tanka ta ba ya mik’e a fusace ya shige d’aki tare da bankad’o kofar wanda ya sake razanar da Fannah. Kamar tasan yau ma seya sata kuka ta taho da handkerchief nata danko jiya ta b‘ata farin hijabinta da kwalli. Hawayenta ta share tarasa dame zata goge kan table d’in dan tasan sarai ya dawo ya iske wajen haka ze k’ara mata wata masifan. D’an kwalinta kawai ta cire ta goge wajen. Bayan ‘yan mintuna Anas yafito dawata farar T shirt da ¾ wando wanda ya mugun amsar sa, koda yafito kuwa be tambayeta dame ta goge wajen ba zama yayi kan kujerar.
   
     “Me kuma kike jira baki had’a min wani coffeen ba miss clumsy?”
    “I’m sorry” ta fad’a tare da d’aukan cup d’in se b’ari take ta juya kenan hijabinta yakama kujera take ya sunb’uce daga kanta daman wuyan ya mata yawa. A garin haka ribbon nata data kama kanta sakwa sakwa dashi shima ya fad’i gashinta me uban waya ya bayyana. Take ta tsuguna ta d’au ribbon d’in tana k’ok’arin miyarwa amman dan yadda ta rikice dakuma yadda takejin idan Anas kanta yasa tama kasa kama kan se fad’i k’asa ribbon d’in yake ta mayar da hijabin kuma be zo hankalinta ba.

      Tunda Anas yake be tab’a ganin gashi kamar na Fannah ba duk zaman da yayi cikin turawa be tab’a ganin erin gashin nan ba ko gashin Ummimi da Amal ma bekai wannan ba. Shi bama tsayin ba uban cikan ne sekace aljanah. Ganin ta kasa kamawa shikuwa ba taimaka mata zeyi ba ya d’au wayarsa ya kira wata. Bayan  minti d’aya akayi knocking “come in” Anas yace. Nan wata ‘yar budurwa ta shigo.
     “Yes Boss.” Da yatsa ya nuna Fannah “help her ku kama mata kanta” cike da mamaki Fannah ta d’ago kai tana kallonsa. Ta rasa gane wani erin hali ne da Anas sometimes seyayi mutunci. “Okay Boss” cewar ‘yar budurwan. Ita kanta gashin Fannah ya bata mamaki sanda ta yi dagaske ta kama mata. “Nagode” Fannah tace mata, murmushi tama Fannah sannan ta dawo da kallonta kan Anas dake d’an rubuce rubuce. “Is that all sir?”
    Kai ya giad’a mata. “Ungo wannan papers kikai wa Salees ki ce masa ya sake printing yanzu wannan yarinyan ta zubar da coffee kai.”
    “Okay Boss.” Amsa tayi ta fice.
   “Thank you” Fannah tace masa.
   “For?” Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba.
    “Da ka kirata ta tayani kama kaina.”
    “Ni bana buk’atar godiyan ki kuma bawai na kirata bane dan ta taimaka miki, ganin gashin kinne banaso.” Har cikin zuciyarta ta ji zafi wannan munanan kalamu amman ya ta iya? Dama shi neman kud’i haka yake.

     Mik’ewa tayi taje ta had’o masa coffeen wannan karan bata zubar ba. Bayan ya shanye tace, “Mr. Fauzi inasan in d’an fita.”
       Ba tare da ya kalleta ba yace, “ni ba hana ki fita nayi ba just kisani in na kiraki baki zo a dadai lokacin ba kawai ki tattara kanki kibar min building.” Tasan sarai Anas ze aikata abinda ya fad’i ya korata kamar yadda ya kora wata me girki jiya. Zaman kawai ta cigaba da yi. Kai ya d’ago yana kallonta da blue eyes nasa “well? Kin fasa fitan ne? ”
    “Eh zan zauna.”
   “Better” yace ya cigaba da abinda yakeyi. Bada jimawa ba wayarsa ya soma ringing yana ganin Angel ke kira ya d’aga take “Hello my Angel” ya ce. Baki wangalau Fannah ta saki tana kallonsa cike da mamaki. Anas d’in ke kiran wata mace da Angel? Lallai kam koma wacece ita she must be lucky. “Yau ziyara zaki kawo min?... Okay ina jiranki... Oh! Har kin shigo? Toh ina jiranki.” Bada jimawa ba k’ofar office d’in ya bud’u  Fannah ta zuba ido tana jiran taga wata babbar budurwa kawai taga d’iyar da k’anwarta ma tafita komi. Da gudu tayi kansa tana masa oyoyo! Zama tayi kan cinyarsa “Ya Anas shine yau ka taho office baka tadani munyi breakfast ba.”
    “Haba! Angel bacci kikeyi sesa banso tada ke ba.”
    “Toh ya Anas karka sake kaji? Nifa har yanzu banyi breakfast ba kuma barin yi ba.”
    “Haba my Angel yi hak’uri. Tare kuka taho da Shettima ba? Kice masa ya kaiki duk eatery’n da kikeso kiyi breakfast in na dawo zamu fita tare.”
    “Yeyy! Ya Anas” tayi hugging nasa “I love you.”
   “I love you too Angel.”

    Fannah harda d’igan miyau dan mamaki wai Anas ke dariya yau haka? Bama murmushi ba? Kuma ba k’aramin kyau dariya ke masa ba ga dimple ga fararen hak’wara. Kallonsu ta tsaya yi yadda suke kama nema yasake burgeta.

© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 23
BY MIEMIE


     “Ya Anas wace wannan tamin kyau.” Cewar Amal da suka had’a ido hud’u da Fannah dake ta kallonsu.
   “Wannan?” Ya nuna Fannah. Kai ta giad’a “ai kin fi wannan kyau Angel.” Fannah dake murmushi take yanayinta ya soya jin abinda Anas yace. “Dagake Ya Anas?”
     “Sosai ma Angel wannan ai bata da kyau.”
    “To Ya Anas wace ita? Metakeyi anan?”
     “Nima bansanta ba tana aiki anan ne.”
    “Nikam tamin kyau Ya Anas.” Nan ta mik’e daga kan cinyarsa ta nufo wajen Fannah. “Hi” tace da ita. Fannah na murmushi tace, “hello beautiful.”
    Amal ta murmusa sosai “dagaske ina da kyau kamar yadda Ya Anas yake fad’i?”
     “Sosai Ya Anas naki beyi k’arya ba.”
   “Toh me sunanki?”
   “Fannah kekuma fah?”
    “Amal amman Ya Anas na kira na da Angel.”
   “Nice name Amal.”
   “Amal kije kiyi breakfast kinji? Karki biyeta da surutu kinji Angel d’ina?”
    “Okah Ya Anas, Fannah ba-bye.”
     “Ba-bye” Fannah tamata sannan ta fice. Ita ina ma yadda halin Amal ke haka halin Anas yake dataji dad’i, kawai se tana murmushi wa kanta.

      “Kuma murmushin me kike?”
     Babu ta amsa sa a takaice. Kallo ya watsa mata sannan yaci gaba da abinda yakeyi. Coffee sau uku ta had'a masa a ranan sannan da yazo tafiya ta had’a masa cikin flask kamar jiya.

   ****

     Fannah da Afrah ne zaune tsakar sede kallo d’aya Afrah tamata tagano Fannah ta wula duniyar tunani.
    “Wai Ya Fannah tunanin me kike haka?”
    “Aww ni!” Ta fad’i a birkice. “Ba komai.”
      “Oh common kidena min k’arya dan Allah. Bade kema kin kamu da san Mr. Fauzi ba?”
     “Ya Salam!!! Afrah wai giya kike sha ne?”
    “Toh fad’a min tunanin me kike?”
       Numfashi Fannah taja, “kinsan wani abu ne Afrah?” Kai Afrah ta kad’a Fannah ta cigaba; “ni al’amarin Mr. Fauzi mamaki yake bani kinsan ban tab’a ganinsa yana dariya ba ke ko murmushi bayya yi kullum cikin masifa da tsawace mutane yake, amman yau da wata k’anwarsa tazo bakiga yadda yake dariya ba wallahi-”
    Afrah ta katse ta “sekuma ya miki kyau kikaji dama kema yana miki dariyan koh?”
    “Ke Afrah anyi mutum wallahi.” “Nama fasa baki labarin.” cewar Fannah.
      “A’a yi hak’uri Ya Fannah please.”
       Fannah ta cigaba, “kinsan wani biggest secret nasa kuma?” Kai Afrah ta kad’a mata.
      “Dan Allah karki fad’awa kowa, Mr. Fauzi yana shaye shaye.”
    “Iyye!” Afrah ta zaro idanu waje. “Yana mene? Shaye shaye fa kikace?”
    “Ke da Allah kiyi a hankali kar a jiyo mu. Yana shaye shaye amman kuma danayi tambaya se akacemin wai yanada horrible past, akoi abinda ya tab’a faruwa a rayuwarsa can baya wanda yasa yake duk wani abinda yakeyi yau kuma kinsan the most interesting part of it? Duk tsiyar Mr. Fauzi wallahi when it comes to family yanada kirki sosai kiga yadda yabani bandir na N200 mana.”

     “Gaskiya ne amman Ya Fannah wallahi tausaya miki nake, shaye shaye fa in randa ya bugu ya miki wani abun fah? Ki nemi wani aiki please banasan abu ya tab’a ki.”
       “Karki damu Afrah in shaa Allah ba abinda ze min, ni so nake naji me tarihin sa mesa yake shaye shaye. No offense amman Mr. Fauzi kyakkyawan namiji ne da duk macen data gansa (musamman ‘yan matan miemie bee novels group LOL) zataji tana sonsa kotaji ya burgeta ga kyau ga kud’i ga class ba abinda ya rasa mesa zena shaye shaye? Dole da akoi k’wararren reason and I must find out wayasani ko in giara masa rayuwa.”

      Cike da mamaki Afrah ke kallon Fannah, yaushe rayuwar mutane ya soma damun Fannah’n da bata shiga cikin jama’a. Ahhh! gaskia Mr. Fauzi ya k’ure ta fannin had’ewa. “Toh kekuma tanan kika b’ullo yau? Ai bari ya cigaba da saki kuka ni ba ruwa na. Ina ruwanki da shaye shayensa yaga dama ya dawwama dashi mana. Nikam gaskia ina ji miki tsoro.”
    “Worry not Afrah.”
 
    Washegari ma tun 7:00AM Fannah tagama shirinta se jiran call daga Anas take amman shiru 7:30AM nayi kawai ta tsari napep ta k’arisa office nasa koda datayi knocking bakin k’ofar kuwa ba response ta gwada bud’ewa ma a rufe waje ta nema ta zauna daga gefe tana jiran dawowansa.

   8:00AM on the dot k’ofan elevator ya bud’u Anas ya bayyana daga bayansa. Cike da mamaki Fannah ke kallon Anas dake sanye da suit as always. Wai shi jira yake ne se takwas d’in daidai ya cika ya shigo a’a kokuwa kawai perfect timer ne? Binsa da kallo take tana wannan nazari har ya iso bakin k’ofar bata sani ba.
      “Incase kina mamakin ko tsayawa nake se daidai 8:00AM yayi nake iso nan toh you are mistaking kuma wai ban hanaki kallo na haka ba?”
      “I’m sorry” ta fad’a a kunyace.
     “Ba abinda na tambaya ba kenan.”
     “Ka hana...” Ta fad’i kanta a k’asa.
      “Then kidena, saboda ke barin fara sa niqaf ba. Mschww!” nan ya bud’e k’ofar office d’in yashiga, Fannah na biye a bayansa. Bayan ya ajiye jakansa ya juyo tare da crossing arms nasa a chest nasa yana kallonta.

       “Waye ya gayyace ki nan?” Sam bata fahimce sa ba. Hijbanta me hula ta sake ja tare da rufe mata kusan rabin fuskarta, ta tsani taji wannan blue eyes nasa kansa.
      “So kike na sake repeating kaina?” Ya sake tambayarta yana mata wani erin kallon rashin isa.
    Murya ciki ciki tace, “Sir ban fahimce ka ba.”
    “Dama ina zaki fahimta? Uban wa ya gayyato ki nan yau? Ni na kiraki nace kizo?”
  Kai ta kad’a masa “Sir naga yau thursday ne kuma ranan aiki ne shiyasa.”
       “So what? Nifa sanda na fad’a miki banasan shisshigi, wai ku mata duk haka kuke ne? Tunda kin kawo kanki off you go, make me coffee. Kuma wannan fuskarki da kike rufewa ki bud’e is not as if I’m interested in looking at it.”

     A hankali ta mayar da hijabin daidai sannan taje ta ajiye jakarta ta had’o masa coffeen yauma sauran kad’an ta sake zubarwa. “Wai wace erin clumsy mutun ce ke? Ehh? Am teilling you yau da wannan coffee ya zube kan wannan building drawing sekin re drawing min I don’t care baki iya ba. Mschww!” fisgan cup d’in yayi daga hannunta wanda a garin haka ya tab’a mata yankanta dake kan warkewa. K’ara ta sakar amman ko a kwalan rigarsa komawa tayi ta zauna kan kujera tana kuka. Anas be ma san tanayi ba can da kukan ya ishesa yace, “ke!” A hankali ta d’ago jajayen idanunta ta a zasu kansa. “K’aran kukan nan na distracting d’ina ko kiyi shiru kokuma ki fita.”

      A hankali ta mik’e ta sauk’o k’asa inda ta saba ganin Yusuf yau ma can ta samesa. “Fannah ya haka idanunki duk sunyi ja? Kin ji ciwo ne.”
     Murmushi ta k’irk’iro “a’a ba komai.”
      “A’a da akoi komi keda Boss ne?”
    Kamar ta masa k’arya sekuma ta fad’i gaskia kawai. A hankali ta giad’a kai hawaye na sake cikowa idanta.
      “Haba! Fannah I thought you were a fighter, ai in kikace zaki biye wa Boss kullum kina cikin kuka kenan, haka shi yake in ya bak’anta wa mutum rai ne yake jin dad’i, hak’uri zakiyi kina basa uzuri, wallahi kina ganin Boss haka ne he is weak kawai pretending yake to be strong, past d’insa kullum bibiyarsa yake zuwa present kinga ko dole yana sauk’e haushinsa kan mutane. Kiyi hak’uri.”

     “Toh amman Yusuf mesa duk tsiyarsa naga yafi wa mata kan maza mesa?”
     “Nima bansani ba Fannah wannan lamari se Allah. Barinje inyi arranging wad’annan a file room.”
     “Muje tare ba abinda nakeyi nima.” Haka duk inda ze je Fannah tana biye dashi, sosai ta zagaya building d’in ranan floors kad’an ne batayi exploring ba. Duk wani walak’anci erin na Anas ma ta manta dashi se enjoying kanta take gun Yusuf gashi da surutu da kayan ban dariya. Abinci ma tare sukaci bayan sunyi sallan azahar tama manta yakamata taje ta had’a wa Anas coffee tunda azahar tayi.

      Anas na zaune kan table nasa bayan ya idda sallah se zanen building drawing d’in yake. Bayan ya gama ya soma modeling zanen, zane ne me uban kyan gaske, bungalow ne amman had’ade harda underground ga garden da swimming pool ba abinda babu ciki. Jiran Fannah yake tun d’azu tazo ta had’a masa coffee amman shiru, shi yanzu ya saba inbe sha coffeen Fannah ba baijin dad’i. Inde ze sha coffeen ta kuwa be damuwa da cin abinci. Har to 1:30PM Fannah bata dawo ba.

       Wayarsa ya ja daga kan table ya yayi scrolling kan contact nata ya kira to his suprise waya ya soma ringing cikin office d’in wato ko fita da wayartan ma batayi ba. Tsuka yaja yayi hanging take ransa ya b’aci Kacallah ya kira ko ya ganta sam Kacallah yace besa ta a ido ba. Ya kira kusan mutane uku duk ba wanda ya ganta, kokuma suce d’azu sunga wucewarta. Yusuf ya kira daga k’arshe.
      “Hello Boss?” Cewar Yusuf.
     “Kaga Fannah?” Anas ya tambayesa ba wasa cikin muryarsa. Tunda Fannah taji Yusuf yakira Boss taji cikin ta ya rud’e. Kai take kad’a wa Yusuf kan yace batta nan amman inaaa shima Yusuf d’in tsoro yake kar Anas ya gano gaskia yayi firing nasa.
     “Yes Boss.”
   “Ina take then?” Anas ya tambaya almsot kamar masifa.
    “Mu.. Muna tare Boss.”
    “Aikin daka koma yi kenan ko? Toh kaji kasani nan ba wajen baza soyayya bane zaku iya yin abunku a waje amman banda cikin building d’ina.”
   “I’m sorry Boss it will never happen again.”
     “Better” cewar Anas “ita kuma budurwar taka kace mata tazo ina jiranta.” Ding! Ya katse wayar kafin Yusuf ya masa bayani, sam ya kasa kallon Fannah.
     “Yusuf meyace?” ta tambaya duk ta rud’e.
     “Karkiyi kuka please, kije yana kiranki kinyi wani laifi neh?”
    “Innalillahi!” Nan ne ta tuna bata had’a masa coffeen rana ba. “OMG! Mr. Fauzi zeyi ball dani yau wallahi coffeen sa na mance, nashiga uku” take ta soma cin faratun ta.
    “Don’t panic kiyi sauri kije kafin ya sake fusata.” A sanyaye ta mik’e k’afafunta se b’ari suke. Koda ta isa sama kasa knocking tayi bakin k’ofar already hawaye ma sun fara ciko mata a hankali tayi knocking sau d’aya shiru be amsa ba kuma sarai yaji nan tayi na biyu. “Come” yace a hankali ta bud’e k’ofar ta mayar a nitse sannan ta tako cikin office d’in ta tsaya da kanta a k’asa. Pencil dake hannunsa ya ajiye ya d’ago kai yana kallonta.

       “D’au jakarki kibarmin building” ya fad’i ba tare da nuna damuwa ba. A razane ta d’ago kai hawaye na bin kumatun ta “Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri please.”
     “Don’t let me repeat myself. Kin jini ki d’au jakarki ki tafi zan kira Adam ya biyaki kud’in ki. Now off you go.”
  Kuka take sosai in Anas ya koreta bata san ina zata samu wani aikin ba yadda neman aiki keda wuya “Sir please, hakan bare sake faruwa ba dan Allah kayi hak’uri.”
  Ko sauraranta baiyi “in kika barni na sake nanata kaina ranki ze b’aci.”
   “Sir dan Al-”
   Yi yayi kamar ze tashi. Har k’asa Fannah ta durk’ushe tana kuka “dan Allah kayi hak’uri wallahi in kayi firing d’ina bansan ina zan sake samun wani aikin ba, ni nake kula da family na Baba na bashida lafiya have mercy please.” Yana jin ta ambato family’nta seya nemi fushinsa ya rasa “get up” yace mata. A nitse ta mik’e tana share hawayenta.

      “For your family’s sake, zan barki ki cigaba da aiki anan.”
    Wani sanyi taji a ranta “thank you sir thank you so much.”
      “Inba wai na manta bane na hanaki min godiya.” Duk wannan magana dayake bai kallin Fannah. Se a yanzu ne yad’ago kai yana kallonta da blue eyes nasa. “Ki bud’e kunnuwanki dakyau ki jini.” Kai ta giad’a “inaji Sir.”

      “Yau shine na farko kuma na k’arshe da zaki sake zuwa wani waje kibar min wayanki a office kina jina?” A hankali ta giad’a kai. Ya cigaba “kin ajemin saboda in miki recieving calls ne?”  “A’a kayi hak’uri.”
    “Ai dama saboda na hak’uran ne saisa kike tsaye cikin office nan har yanzu. Secondly, building d’ina ba wajen yin hira da saurayi bane in keda saurayin naki kunasan spending time tare seku bari in kun bar nan banasan iskanci cikin nan aiki ya kawo ku ba soyayya ba. I hope am clear.”

        “Sir Yusuf fa ba saurayi na bane ka-” ta fad’i kanta na kallon k’asa a yayinda ya katse ta “ban damu ba koda mijinki ne, nide na fad’a miki the next time kika manta abinda ya kawo ki nan saboda hira ya miki dad’i you will be fired for good.” Da hannu ya mata nuni wuce ki had’a min coffee.

    Bayan ta had’a masa ta ajiye kan table d’in. Sosai model dayake had’awan ya mata kyan bala’i sarai ya gane abinda take kallo kenan. “Cikin rules naki I made it clear banda shisshigi so mind your business please”
   “I’m sorry” tace sannan ta koma ta zauna tare da ciro wayarta tana game ita ta k’osa ma lokacin tashinsu yayi  ta tafi gida. Tana cikin yin game a wayarta Anas ya buga table da k’arfin daya firgita ta. “Kashe game d’innan” ya fad’i ransa b’ace.
     “Sir I’m sorry amman fa nasa a silent.”
    “Meaning baraki kashe ba kenan?”
    “A’a zan kashe” ta amsa a takaice.
    “Then make it quick.” Nan ta kashe daidai lokacin wayarsa ya soma ringing ganin Amal ke kira ya murmusa kallonsa kawai Fannah take.

     “My Angel” ya ce da Amal.
    “Ya Anas zan taho office naka yau tunda banje school ba.”
    “Angel amman fa bakida lafiya kikace.”
    “Toh Ya Anas ni banasan physics d’innan kuma har double muke dashi yau sesa nayi k’arya.”
    “Angel! K’arya!” Yayi exclaiming.
    “I’m sorry Ya Anas.”
   “Toh karki sake.”
    “Ya Anas inzo? Inasan inga wancan Fannah d’inne I want to be friend with her.”
   “Da Fannan?” Ya tambaya cike da mamaki. Jin an kira sunanta ta d’aga kai ta kallesa shima kallon nata yake take ta kau da kai.
 
   “Eh Ya Anas ita tabada hankali.”
   “A’a Angel, Fannah bata zo office ba yau kibari se watarana.”
   Cike da mamaki Fannah ta d’ago tana kallonsa toh in ba’a office take ba  ina take?
    “Yawwa ba-bye” yayi hanging. Ko kallon Fannah ma beyi ba yacigaba da yin abinda yake.

© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 24
BY MIEMIEBEE


Haka ta ta zama shiru game dayake sata nishad’in ma Boss nata ya hana ta yi. Time-to-time take satan kallonsa dan ba k'arya model dake gabansan ya bala’in mata kyau. Kafin lokacin tashin su yayi as usual ta had’a masa coffee cikin flask takai masa har mota.

          Isan Anas gida keda wuya ya wuce d’akinsa thank god Amal bata nan sunfita da Ummie da ta cika masa kunne da surutu bayan ya watsa ruwa ya  sha coffeen sa sannan ya kwanta.

   _Bawan Allah ka cuceni, ka rabani da budurcita martaba ta, ka cuceni barin tab’a yafe maka ba. Kuma ina nan kusa da kai INA TARE DA KAI..._

     Firgit Anas ya tashi daga mafarkin dayake yana nishi sosai, ga wani uban zufan dake k’eto masa. Hannunsa bibbiyu yasa cikin gashin kansa yana hargitsawa daidai lokacin knock yazo daga k’ofar d’akin. “Waye ne?” ya tambaya. “Shettima ne in shigo?”
“Eh” ya amsa a kasalance. Shettima na ganinsa ya gane mafarki yayi wajen dispenser ya nufa ya d’ibo ruwa ya kai masa bayan Anas yad’an sha ya masa godiya.
      “Mafarkin wa kayi kuma? Ummimi?”
     Kai Anas ya kad’a masa. “Shettima yarinyan... _TANA TARE DA NI_ I can feel it help me find her please. Wallahi shekaran jiya ma sanda nayi mafarkinta kuma it hurts me alot in naji tana cewa na cuce ta na rabata da budurcinta.” Kafad’arsa Shettima ya dafa “Ya Anas kai yanzu koda ka sameta me zaka mata? Kafa riga ka b’ata mata rayuwa”

     “Shettima I will seek for her forgiveness, zan nemi gafararta koda kuwa kneeling zanyi gabanta I will do it. A rayuwa inasan in karya wa mata zuk’atansu amman bawai in raba su da martabarsu ba Shettima.” Ya fad’a a hankali cike da damuwa kamar ba Mr. Fauzi da muka sani ba.
    “Toh Ya Anas what if tace bara ta yafe maka bafah? Tace sede ka aureta ofcourse kasan kowace mace zata so kasancewa matarka.”
     “I will do it Shettima inhar aurenta zesa ta yafemin zanyi, baraka gane yadda abin ke damuna ba.” Sosai Shettima yasha mamakin jin kalman ‘aure’ fitowa daga bakin Anas gaskia Anas yayi regreting abinda ya aikata yakamata yarinyan ta yafe masa duk sanda suka had’u. Kwanciya yayi jikin Shettima a yayinda shikuma ya dafa hannunsa kan kafad’arsa. “Karka damu I’m sure duk rananda kuka had’u zata yafe maka, ni da kaina zan mata explaining komai.”
   “Thank you” Anas ya ce masa tare da tasowa daga jikinsa ya kishingid’a jikin gado.

     “Toh zan wuce d’akina Ya Anas please karka sha wani abu, shaye shayen nan da kake ba shi ze warkar maka da tunanin yarinyan nan ba.”
    Kai Anas ya giad’a masa danko shi yasani sarai in be sha syrup nasa kokuma giya ba damuwansa barasu gushe ba. Shettima na fita shima ya sa kaya ya wuce paint house nasa(d’an k’aramin gida) acan ya bud’o fridge ba komi bane aciki inbanda kwalban giya masu tsadan gaske d’aya ya zaro daga ciki ya nemi waje ya zauna, ya kashe wayoyinsa tukunna yadda bara ma a damesa ba. Sannan ya shanye fiye da rabi. A hankali matsolilinsa suka soma gushewa har se sanda yajisa problem free daga nan ya samu ya kwanta yayi bacci sosai daga kan kujerar ma ya gangaro k’asa ya cigaba da baccinsa se can bayan isha Anas ya tashi nan ya biya sallolinsa.

     Yayi frying omalet yaci sannan ya k’are kwalban d’azu ya koma ya kwanta. Agida kuwa hankalin kowa ya tashi gashi in sun gwada lambobinsa duk bame shiga gashi kuma ba wanda yasan da zaman paint house daya saya wanda yake zama ciki if he wants to  be alone ko Shettima ma besani ba. Shide Shettima yasan sarai yanzu wansa is somewhere yana shaye shaye abinsa. Sosai shaye shayen d’an uwansa ke damunsa shi da yasan ina ze samu yarinyan da Anas ya tab’a raping da ya nemo masa ita, atleast suka had’u hala Anas ya rage shaye shayensa.

    Ba shi ya tashi ba se washegari da misalin k’arfe 9:30AM ko sallan asuba beyi ba. A gigice ya fad’a bathroom yayi alwala yafito yayi sallah sannan ya koma yayi wanka ko breakfast beyi ba kaya kawai yasa ya d’an gyara gashin kansa ya fice. Driving yayi da sauri cikin d’an k’ank’anin lokaci ya isa office yunwam uba yakeji ko breakfast beyi ba amman bedamu ba saboda zesha coffee. As usual yana shiga aka soma bisa da gaisuwa kai kawai yake giad’a musu har ya isa bakin office nasa can yaga su Kacallah sunyi layi kafin suyi magana yayi apoligising “I’m sorry na makara ne.”
     “Ba komai Boss tunda kasamu ka fito.” Layin kap yabi da kallo be ga Fannah ba to kode dan be kirata bane yasa bata zo ba yau? Amman ai kuma jiya ma be kirata ba kuma tazo maybe ko tana wajen Yusuf.

    Bayan ya sallamesu Kacallah da k’yar ya kira Yusuf dan yunwa. Sam Yusuf yace be sa Fannah a ido ba.

    **

          Fannah kuwa yau baccinta tasha ba ita ta tashi ba se kusan to 9:00AM dad’i takeji yau Anas be kirata ba nufin bai buk’atar ta kenan. A dad’inta yau bara a sata kuka ba dan kuwa Fannah zata iya jure wahala da walak’anci amman banda masifa daga an mata masifa take soma kuka, Anas kuwa aikinsa kenan kullum masifa. Sun gama breakfast da d’anwanke se santi suke ita da Afrah suna zaune a d’aki Aiman ta tafi makaranta. “Afrah tashi muje mu gaishe da Baba naji Mami tace ya tashi.” Atare suka shiga d’akin Baba da Mami suka samesa a kishingid’e yana kurb’an tea. “Ina kwana Baba?” Suka gaishesa a tare.
    “Lafiya emmata na, Fannah ya gajiya kuma?”
    “Ba gajiya, Baba ya jikinka?” Nan Afrah itama ma ta tambayesa.
   “Da sauk’i sosai. Fannah Allah cigaba da miki albarka ya k’ara bud’i mungode sosai.”
    “Kai Baba dan Allah godiyan me haka?”
   “Shine ai Baba” cewar Afrah “ai nima banje makarantar bane da senayi fiye da Ya Fannah.” D’an dariya Baba da Fannah sukayi, hira kad’an suka tab’a se sanda Mami ta shigo suka fice zuwa d’akinsu.

    “Ya Fannah are you sure yau bara kije office ba?”
   “Eh mana ai be kiran ba gashi har goma da mintuna aka, baya buk’atan coffee yau.”
   “Allah sa!” Afrah tace.
   “Me kike nufi?” Fannah ta tambayeta a takaice.
    Wayar ta ta mik’a mata “duba nan kiga.”
     “Innalillahi! Na mutu!” Fannah tayi exclaiming. “4 missed calls?? Yau Mr. Fauzi zeyi ferfesu na.”
    “Akan wannan pointless suratan da kike ba gomma kin kirasa ba.”

        “Afrah wallahi baran iya ba balbale ni zeyi da masifa.”
   “Oh!” Afrah ta saki numfashi
“Ya Fannah yanzu kuka kike? Ai yaci ace kin saba da masifa tun gun Baffa Khaleel. Ki kirasa.” Kai Fannah ta kad’a, fisgan wayan Afrah tayi aiko ta soma dialing number’n Mr. Fauzi. “Afrah in kinayi wa Allah ki kashe tun kafin ya shiga dan Allah, wallahi zan kirasa ki kashe dan Allah.” Ai wayar na nuna an d’aga Afrah ta wurga wa Fannah wayar tayi bakin k’ofa jiran kallon drama tana dariya.

     B’ari Fannah take ta kai wayar kunne nan ma takasa fad’in komi, kamar yadda shima Anas d’in yayi shiru ransa b’ace se tafasa yake. “Hello Mr. Fauzi.” Tayi managing ta fad’a cikin murya me rawa.
    Cike da tsiwa yake maganar. “Se yanzu kika ga damar magana? Eh?? Me kika maidani? Toy abin wasa? Wayyo!” Ya saki k’ara tare da rik’e cikinsa dan yunwa.
     “Mr. Fauzi I’m sorry dan Allah kayi hak’uri.” Ta fad'a idanta na cikowa da hawaye.
  “Meya hanaki zuwa office yau?” Ya daka mata tsawa. Kuka take kam yanzu.
   “Si..sir naga jiya danaje baka kirani ba kace na dena ma shisshigi sesa banzo ba ya-” bata k’are maganar ba ya katse ta.
   “Nonsense na baki nan da 20minutes be at my office” karap ya katse wayar. Hannu Fannah tasa tana share hawayerta a yayinda Afrah ta k’ariso ta zauna kusa da ita. “Haba mana Ya Fannah wallahi kidena masa kuka ze raina ki.”

    “Da Allah rufa min baki ba duk ke kika jawo ba, ba abin na ja miki Allah ya isa ba.”
    “Yi hak’uri Anty babba, meya ce miki?”
Harara Fannah ta galla mata “bansani ba muguwa kawai.” Nan ta mik’e ta canza kaya ta sako red hijabi tare da jan jakarta ta fice. Afrah na mata Allah kare ma ko kulata batai ba. Bata sha wahala ba tasamu keke napep sede hold ups daya rik’a rik’e su a hanya. A takaice de lattin minti 5 tayi. Duk yadda tayi tabar b’ari takasa. Se addu’o’i take ta suburbud’owa Allah kare ta daga sharrin masifan Boss nata.

    Knocking tayi bisa k’ofar “come in” yace. Bayan data shigo tagansa yana attending wasu mutane kanta ta sunkuyar tajira har se sanda ya sallamesu. Kallonta yake bema san me ze mata ba chan yace. “In nache you are fired zaki ga laifi na?” Kai ta kad’a a hankali fuskarta na kallon k’asa se b’ari take.
             Table d’in ya buga da k’arfi a tsorace ta d’ago kanta tana hawaye.
        “Ban kuma hanaki min magana da body language ba?”
       “Ka hana” ta fad’i tana share hawayenta. “Na farko yau dagangan kik’a k’i zuwa office kika bar ni da yunwa, na biyu dana kiraki har 4 missed calls baki d’aga ba saboda kin mayar da Boss naki sa’an wasanki.”
       “Kayi hak’uri dan Al-”
Katse ta yayi a tsawace “ban baki izinin magana ba so shut up!” Hawaye se gangara suke kan kumatun ta tana sharesu “na uku da kika kirani back kika k’i magana se sanda kika ga dama. Na hud’u kikayi latti akan latti. Zakiga laifi na in nace na koreki daga nan? Am talking to you!” Ya k’ara mata wata tsawan.
   
       Hak’urin ma takasa basa se kuka takeyi shark’af shark’af. “Baraki amsa ba kenan?”
       “A’a I’m sorry” ta fad’a da k’yar muryarta na rawa.
     “Kuma kinsan me? Wannan kukan da kikeyin ba damuna yake ba, koda zaki tsiyaye hawayen ki tas barin damu ba, gara kiyi saving nasu kuma har yanzu tsaye kike?”
    Kai ta d’ago a hankali “a’a” nan ta wuce ta had’a masa coffeen bayan ta ajiye masa coffeen ta juya zata fice kenan ya finciko ta da hijabin ta da mugunta wanda sanadiyar haka ya shak’e mata wuya k’ara sosai ta saki take ta soma kuka.
    “Nan gaba zaki sake nanata abinda kikayi yau. Mschwww!” Bata ce masa komi ba jakarta kawai ta d’auka ta fice sam yi yayi kamar be ganta ba. Data sauk’o ma tana jin Yusuf na kiran sunanta ta sharesa k’ofa na bud’uwa ta fice bayan ta yabi da gudu Allah ya so ba keke napep a lokacin tsaye take tana hawaye tana kuka me d’an k’ara isowan Yusuf wajen yace, “Haba Fannah mene yafaru ina ta kirarki kika yi kamar bakiji niba. Wani abu ne?” Batace dashi komi ba se kukan da takeyi.
    “Fannah meya faru kike kuka haka?” Ya tambayeta cike da tausayi. Kukan take har yanzu kamar ‘yar yarinya tayi covering fuskarta da hannu. Hijabinta yaja a hankali ya zaunar da ita kan wata bench. Be sake ce mata komi ba har se sanda ta gama shan kukanta. “Fannah zaki iya fad’amin meya faru?”
     “Ni nabar aiki a nan.” tace tana share hawayenta.
    Cike da mamaki yace, “ban gane kinbar aiki ba Fannah kinsamu wani aikin ne?”
    “Ban samu ba amman zan shiga nema.”
       “Mesa Fannah, na miki wani abu ne?”
    “Baka min komi ba amman Boss naka yamin. Yusuf niba mutun ce me neman magana ba, nayi hak’uri da erin abinda Mr. Fauzi yakemin, I can’t take it anymore wallahi ko kashi bara’a masa abinda Mr. Fauzi kemin ba neman kud’in ba hauka bane. Ni kawai ya biyani kud’in ‘yan kwanakin dana masa aiki zanje in nemi wani.”

     “Fannah kibar magana, nasan you don’t mean what you are saying. Kinsan yadda neman aiki keda wuya ki hak’ura, sekace ban fad’a miki matsalan Boss ba? Haka yake inya k’untata wa mutum ne yakejin dad’i kiyi hak’uri. Yanzu har kika bar aikin nan baki sami wani bafah? Dame zaki biya kud’in magamunan Baba. Kiyi hak’uri.”

     “Kana nufin in cigaba da aiki k’ark’ashin Mr. Fauzi kullum yata cin mutunci na yana masifeni?”

    “Ba abinda nake nufi ba kenan. Abinda nake nufi shine ki k’ara hak’uri, ki cigaba da wannan d’in kina neman aiki nima in shaa Allah zan tayaki. Kinga in muka samo miki seki bar nan d’in amman karki bar nan bakida wani aikin please.”
     Shiru tayi na d’an lokaci “you are right Yusuf nagode sosai.”
    “Always... Mushiga daga ciki kinji?”
   Kai ta giad’a  masa suka dawo ciki tare. Duk inda zasa tana biye dashi. Seda azahar yayi ta koma office na Anas knocking tayi yace, “come in.” Bayan ta shiga ko kallonsa batayi ba ta zarce ta had’a masa coffee.

    “Na d’au kinbar aikin ne ai.” Yace da ita yana daddana laptop. Nanma shiru ta masa ta fice ba ita ta sake dawowa ba se to 4 ta had’a masa coffeensa cikin flask ta d’auka takai masa mota. Shiko Anas ko a kwalar rigarsa daman haka yake so, tana aikinta me kyau ba shisshigi.

    Washegari ya kasance Asabar ba aiki Anas kuwa through the week yasaba da karyawa da coffeen Fannah sam yak’i cin breakfast seya sha coffeen ta tukunah. Wayarsa ya d’au ya kirata da misalin k’arfe 10:30AM alokacin se shiri suke ita da Afrah zasu gidan wata k’awar Afrah data haihu tun bata gama secondary school ba aka mata aure, zasu yin barka. Fannah tayi bala’in kyau tunda nake ban tab’a ganin Fannah tayi kyau kamar na yau ba dake Afrah ce ‘yar gayu ta mata kwalya. Brick red jan baki tasa mata da kwalli da lining sannan ta taje mata dogayen gashin idanunta da mascara ta mata brushing gira tare da shafa mata powder had’adden daya mugun amsar skin nata.

     Sanye take da blue and red atamfa amman red d’in yafi yawa dan dolenta tasa gyale sabida Afrah ta tak’ura mata. Tana zaune tana game tana jiran Afrah wayarta ya soma ringing ganin Mr. Fauzi ke kira ya mugun bata mamaki yaude Asabar ce bakuma ranar aiki ba toh me zekira yace min? Ta tambayi kanta a zuci. “Afrah kiga Mr. Fauzi ke kira meze cemin?”
    “Taya zamu sani in bawai d’aga wa kikayi ba Ya Fannah.”  A hankali ta d’aga tasa a kunne.

© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 25
BY MIEMIEBEE


“Hello” tace a hankali.
    “coffee nakeso.” Ya fad’a authoritatively.
       “Sir amman ai yau saturday ne ba’a aiki a weekends.”
     “In Boss naki yace se kinyi kuma fah? Can you say no.”
     Can k’asa k’asa tace, “a’a.”
    “Good, meet me at my paint house...” Nan yamata kwatance kafin tace, “okay” ya katse wayar.
 
     “Meh yace wai?” cewar Afrah dake d’aura kai.
     “Wai coffee yakeson sha inje in samesa a paint house nasa.”
  “Ranan Asabar d’inma?”
    “Humm! sekace bakisan Mr. Fauzi ba? Haka yake d’an ra’ayi ne.”
    “Kina nufin yanzu bara muje gidan Haleeman ba kenan?”
    “Zamuje mana ai had’a coffee kawai zan masa within 2-3 minutes nagama semu tafi yanzu kiyi ki gama shirinki muje tare.” Da “toh” Afrah ta juya ta gama d’aurin ta sannan sukayi sallama da Mami daidai gaban paint house na Anas kamar yadda ya mata kwatance suka tsaya bayan ta sallame me napep d’in suka tsaya admiring gidan dududu barefi 2 bedroom flat bane ciki fari ne tas gidan ya k’ure kalman kyau.

        “Ya Fannah wannan ne motarsa?” Tana nuni da yatsa.
    “Wai ba” cewar Fannah.
    “Wow! Wow!”
   “Ke kin fara ko? Nikam kizo mushiga”
   “Wa? ni? In shiga? Saboda ya koreni kimin dariya? Kefa kikace baida mutunci a dalilin me zan biki ciki? Nide kiyi sauri ina jiranki nan.”
    “Amman Afrah bakiyi ba wallahi ai da sekice min baraki shiga ba, da bamu sallami me napep d’inba.”
     “Oho sorry zamu samu karki damu, kiyi sauri kar muyi latti.”
     “Afrah da Allah mu shiga wallahi bansan shiga ni kad’ai.”
     “Ya Fannah dan Allah kibar had’a ni da Allah dan wallahi barin shiga ba. Off you go” ta mata gwalo. Baki Fannah ta murgud’a mata sannan tayi hanyanta ciki.

     Door bell data gani bakin k’ofar ta danna zuciyarta se bugawa yake tana jiransa. Bayan kamar minti d’aya k’ofar ya bud’u. Anas tagani tsaye jikin k’ofar ko singlet babu jikinsa bale kaya ¾ wando ne na soja jikinsa, da alama yanzu yafito daga wanka danko gashin kansa a jik’e yake kad’an kad’an ruwa na d’iga a k’asa, ga wani kyan da skin nasa yayi a jik’e har shining shining yake. Blue eyes nasa kuwa sun sake shiga ba k’arya yayi kyau sosai ga body kam masha Allah very muscular ta kasa dena kallonsa kamar yadda shima yake kallonta and for the first time bada wata manufa ba. Be tab’a ganinta da shiri irin na yau ba, kullum cikin hijabi take banda gyalen data yafa yau ga d’an kwaliyan datayi wanda be tab’a gani tayi ba. Sosai ta canza kamanni, ga yadda Afrah ta yafa mata gyalen, ta d’an bar kad’an daga cikin k’irjinta dake a cike dadai ‘yar budurwa a waje. Za’a iya ce miki kinyi kyau ya fad’a a zuciyarsa.

     Kusan a tare suka kawar da ido daga kan junansu gyalen dake wuyanta ta d’aga ta yafa kai tare da rufe k’irjinta dashi. Kad’an ya matsa gefe “come in” yace da ita a hankali ta shiga ta tsaya ba daga nesa ba “ga chan kitchen d’in” ya nuna mata da yatsa k’ok’ari tayi kar ta sake kallonsa kafin ya silleta. Kai ta giad’a nan take ta tuna dokokinsa tace, “okay.” A sanyaye tabi direction daya nuna mata ta shiga kitchen d’in komai tsatsaf ba datti ba wari. A gefe guda ta hango coffee machine gefe guda kuwa fridge. Wajen fridge d’in ta nufa ta bud’e as expected taga bottles na giya jere daban daban kai kawai ta kad’a taciro abinda zata buk’ata ta nufa wajen coffee machine d’in ta ajiye cupboards d’in tabi tana bud’ewa har tasamu na cups and spoons. Sosai ta mayar da hankalinta gu d’aya gudun kar ta fasa masa d’aya daga cikin fancy cups nasa yasata biya. Bayan ta gama had’a masa ta d’auka da hannu bibbiyu shes very careful ta bud’e k’ofar a hankali  ta rufe tana juyawa kawai taga mutum tsaye gabanta gashi har yanzu besa kaya ba ¾ wandon ne. Tsorata tayi sosai iya tsoro dayasa tayi b’arin coffeen saura suka zube a jikin Anas dako singlet baida saura kuma jikinta saura a k’asa. Da cup da plate data d’aura kai dakuma spoon d’in duka suka fashe a k’asa.

    K’ara sosai Anas yasaki dan zafin coffeen ita bata ma damu da kanta ba, batasan ma yatayi taciro gyalenta ta soma goge masa jikinsa ta cikinsa dashi ba “sorry sir, I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri” duk ta rikice. Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki tab’a masa jiki ma take, lallai kuwa. Alokaci d’aya kuma ta tsaya cak! A kunyace ta d’aga hannunta daga jikinsa ta d’aga kai suna had’a ido tayi sauri ta kawar da kanta. “I’m sorry” tace kallonta ya tsaya yi, besan meke damunsa ba, shi d’inda ko matan turawa kan bikini (pant and bra) ma basu masa ba mesa yake kallon Fannah toh? Me take dashi? Jik’ak’en mayafinta ta bud’e zata yafa ya kama karap! A razane ta d’ago kanta tana kallonsa alokaci d’aya tana k’ok’arin fisgan gyalen sede k’arfinsu ba d’aya bane.

   Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta d’aura hannayenta biyu tana tare k’irjinta da kanta k’asa har yanzu Anas be motsa ba kallonta yake sosai sosai da ta d’aga kai seta ga ita yake kallo. Da k’yar tayi gathering courage ta bud’e baki zatace masa “kabani mayafina” kawai ya juya ya fice da gyalen zuwa wata d’aki. B’ari sosai Fannah take, shikenan tabar Anas yaga jikinta duk laifin Afrah ne da hijabinta ne da asirin ta a rufe. Ido ta d’aga sama “Ya Allah ka yafemin astaghfirullah astaghfirullah.”
     Daidai lokacin Anas ya fito daga d’akin da wani leather a hannunsa baya ta juya take tana kare k’irjinta seda yagama matsowa kusa da ita ta tuna kayan tan ma show me your back ne sanda tace wa d’an iskan tell
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).