shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 7 September 2016

TANA TARE DANI...46--50

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 46
BY MIEMIEBEE

    Wajen elevator’nsa ya jata bayan sun shiga tace, “Mr. Fauzi where are you taking me to?” Be amsata ba illa wayansa da ya ciro daga aljihunsa yayi waya wanda ga dukkan alamu da polisawa ne. Bayan ya gama Fannah ta maraice “Mr. Fauzi not again please, kayi hak’uri dan Allah.” Beko saurare ta ba. Bayan da elevator’n ya bud’u yaja hannunta daidai gaban motarsa ya tsaya tare da bud’e k’ofar gaba wa Fannah. “Enter” yace ba tare da ya kalleta ba. Dakewa tayi “barin shiga ba Sir, kabari mana dan Allah duk abinda ka masa yanzu nasan Ya Farouq he will fight back, fad’an ya cigaba kenan kuma.”
     “Get in the damn car!!” ya fad’a a tsawace. Ta tsorta iya tsoro amman kuma tak’i shiga.
   “Miss Aleeyu I said get in, karki bari raina ya b’aci in d’aga ki in saki ciki da kaina.”
   “Sir promise me ba wajen Ya Farouq zamuje ba.” Kai ya giad’a.
    “Promise?” Ta tambayesa. “Yes” ya bata amsa nan ne tashiga bayan ya rufo k’ofar ya zaga ta driver’s side yashiga shima. This is the first time yake driving nasu bibbiyu. Ganin hanyan gidansu yake nufa tace, “Sir you promised kace ba wajen Ya Farouq zamuje ba dan Allah ka juya.” Banza da ita yaui sanda suka isa gidan yayi parking tare da fitowa a fusace ya zaga ya fito da Fannah hannunta rik’e cikin nasa tayi tayi ta k’wace amman ta kasa. Ai kaman an turo Farouq se gashi ya yanko corner’n gidan hankalinsa kwance yana tafiya idanunsa suna sauk’a kan Anas yaga yadda yawani rik’e hannun Fannah. Ita kuwa ganin Farouq ta cigaba da k’ok’arin k’watan hannunta daga na Anas amman ta kasa. “Stop it” yayi warning nata. “Sir please ka sakeni kafin ya k’ariso.” Nan da nan Farouq ya iso gabansu se nishi yake kaman zaki dan wani bak’in kishin daya rufesa.

       Hannun nasu ya sake kalla sannan ya kalli Fannah, kanta ta sunkuyar tare da lab’ewa bayan Anas a hankali tace, “Ya Farouq I can explain this dan Allah kayi hak’uri, Mr. Fauzi please ka sakemin hannu.”
     “Bakaji me tace bane?” Ka sake mata hannu.
    “Banji ba” Anas yace kamar kyaftawan ido ya sake hannun Fannah tare da cikumo kolar rigan Farouq punches guda uku lafiyayyu yakai masa har k’asa Farouq ya sauka se zuban jini fuskarsa yake. Binsa k’asan Anas yayi tare da tsugunawa a kansa da k’afafunsa side-by-side na Farouq. Nan ma be bar kai masa bugin ba. Fannah dake basa hak’uri har bakinta yayi dogo “Mr. Fauzi please ya isa.” Se huci yake yana dukansa ba makawa. Hannun Mr. Fauzi ta gwada rik’ewa ya k’wata abinsa da zafi sauran kad’an ta fad’i k’asa. Ganin an kusan sumar da Farouq Fannah ta ruga a guje tare da hugging Anas ta baya cije da tashin hankali, abinda kad’ai yazo mata kai kenan duk da tasan yin hakan haramun ne, in bahakan tayi ba tana ganin Anas ze iya kashe Farouq da yadda yake ta kai masa bugi. Hannu ya d’aga ze sake kaiwa Farouq punch yaji jikin Fannah a nasa, wani irin electrification ya jiyo a jikinsa tun daga tsakiyar kansa har k’afa, wanda be tab’a ji ba tunda yasan kansa. Hawaye take sosai wanda har kad’an daga ciki ya tab’a rigarsa “Mr. Fauzi please ya isa dan Allah kayi hak’uri in ka cigaba zaka kashe sa ya isa dan Allah, please...” Se kuka.

     Ganin jikinsa ya mutu ta matsa baya tana share hawayenta mik’ewa yayi ya nufa wajenta “is okay kukan ya isa kinji?”
     Numfashi take ja dan yadda tasha kuka “please ya isa Sir karka sake tab’a masa.” Kai ya gyad’a mata “stop crying.” Itama kan ta giad’a masa. Da k’yar Farouq ya mik’e se jiri ke k’ok’arin d’ibansa, fuskar nan nasa ya ninka abinda yasa a kayi wa Anas, kayan sa duk ya b’aci da jini, da k’yar yake maganar a wahale. “Wallahi Mr. Fauzi you won’t get away with this, Fannah tawa ce! Fannah mata tace! Ni zan auri Fannah!”
 
     “No Farouq you are wrong *FANNAH TAWA CE! FANNAH MATA TACE! NI ZAN AURI FANNAH* and not you.” Shi kansa besan sanda yafad’i wannan kalamu ba. Fannah kam mutuwan tsaye tayi. Daidai lokacin motan polisawan suka iso guda biyu. Handcuff aka sawa Farouq a hannu “wallahi Mr. Fauzi kasani you won’t get away with this, duk ranan da na fito se na k’wato Fannah daga gareka, sena kashe ka in ban kashe ka ba sena kashe ta dan in barin samu Fannah ba, bawanda ze same ta.” Kansa aka tusa cikin motar. Daidai lokacin Ya Khaleel ya hallaro shima, ganin d’ansa cikin motan polisawa ya falfala da gudu izuwa wajen.

    “Officer ina zaku kaimin d’a dan Allah ku sako shi kuyi hak’uri. Farouq me kayi?” Nan ya juyo wajen Anas da Fannah. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri kasa su sake min d’a wayyo Allah! Kayi hak’uri dan Allah bare sake ba.”
    “Ka sake had’a ni da Allah believe me kaima zaka bisa cell d’in. Take him away” yace da polisawan.
    “Fannah dan Allah karki bari atafi miki da miji ki rok’i Mr. Fauzi please.” Hawaye sosai Fannah take dan tausayi irin nata setaji duk she is ready to forgive them abubuwan da suka mata. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri.”
   “NO” yace mata a tsawace “take him away, NOW!” A 360 suka bar wajen da Farouq. Kuka Ya Khaleel yake “Allah ze sak’a min wallahi, d’a na be maka komai ba kasa aka tafi dashi simply because kaga baida gata in shaa Allahu zan tara kud’i inyi bailing nasa, kekuma Fannah kisani Farouq shine mijinki ba wannan dayake miki wasa da hankali ba.” Yana kaiwa nan ya fice.

    Kuka me sautin gaske Fannah ta fashe da, “Mr. Fauzi why? Dan Allah ka dawo dashi I beg you please, banasan ka mutu, banasan wani abu ya tab’a ka. Ni nace zan aure sa ka sa a sakar dashi, ka sakar min miji.”
    “*Nine mijinki Miss Aleeyu* and that stays that.”
    Cikin kuka tace, “what are you saying Mr. Fauzi kana cikin right mind naka kuwa taya zakace kaine mijina? Ko baka san ba’a wasa da kalman aure bane? Ni ka sa su sake Farouq kawai dan Allah.”
    “Yes Miss Aleeyu nasan me nake fad’a ni zan aureki ba Farouq ba, you are going to be my wife” hannunta yaja tare da zaunar da ita cikin motar. Shima ya zaga ya zauna.

     Hawaye take sosai “Miss Aleeyu for goodness sake kukan ya isa. I’m going to marry you so as to protect you from Farouq atleast duk rashin kunyarsa inyaga ke matar aure ce ze saurara miki koda Babansa yayi bailing nasa, marry me Miss Aleeyu.”
    Kai take girgizawa continiously No! No! No! This can’t be happening bareyi in auri Boss d’ina koba dan haka bama bareyi in barsa ya aureni ba, BANIDA BUDURCI, BANIDA MARTABA duk ranan da Mr. Fauzi ya gano hakan ze tsaneni fiye da yadda ya tsani mutuwar sa, I can’t marry him saboda barin iya fad’a masa sirri na ba kamar yadda barin bari yagano hakan ba da kansa kuma.

     “No Sir I can’t marry you, I can’t dan Allah kabar wannan magana, ni kawai release Ya Farouq.”
   
   “Yes, yes you will marry me Fannah Aleeyu. In ma tunani kike ko wani abu ze shiga tsakanin mu ki kwantar da hankalinki. CONTRACT MARRIAGE zamuyi.”
   “Contract marriage?” Ta tambayesa cike da rashin fahimta.
   “Yes contract marriage nima some weeks ago Abuu yace se nayi aure, seya aura min wata ‘yar uwarshi Falmata saboda yana ganin I’m still young wataran baran iya managing Enterprise d’ina ba kuma wai ban gama mallakin hankali na ba so yakeson yamin aure, nikuma nace masa barin aureta ba, mukayi deal dashi akan in 6 months time zan nemo mace in kawo masa gida wanda zan aura. Ni koda nan da infinity, k’arshen duniya za’a bani banga macen da zata min ba har inji ina sonta zan aureta ba, I will use you  Miss Aleeyu and fake up a relationshop with you. Ni a rayuwa na banason aure, duk abinda ze had’ani da mace ma hasali banaso ke kad’ai ne...” Ya nisanta “when it comes to you I just don’t feel thesame way. Mu rufa wa junan mu asiri and help each other. Zan aureki for just 6 MONTHS TIME after then semu rabu ince wa Abuu kinci amana na kin tafi kin barni, kince you don’t love me anymore, you see daga lokacin nan bare sake tak’ura na da zancen aure ba zece I’m broken I cannot move on kamar yadda shima har yau yakasa sake aure tunda Ummimi ta tafi ta barsa. Ke kuwa kinga nasan by 6 months time d’innan Farouq halan ya gaji da jira ya koma inda yafito kinga seki cigaba da tafiyar rayuwarki kamar yadda take da. Nikuma I promise you a k’arshen 6 months d’innan bayan munyi ending marriage d’in zan baki 6 million tunda dama contract marriage ne.” Ido sosai Fannah ta zaro 6 million???? Ta fad’i a ranta.

   
        “Kinga inma so kike kubar garin nan da family’nki zuwa wani garin zaku iya, yadda Farouq bare sake tak’ura muku ba. Kuma a kowani k’arshen wata zanna biyanki albashinki na aiki N500,000 sede bawai zakina min aiki bane still, zan sauk’e ki daga zama min PA, bareyi ace mata ta PA ta ba. I’ll get the papers ready gobe, all you have to do is sign them So what do you say?”

     Shiruu tayi dan tunanin ma ta kasa. Taya zatayi agreeing wa qudurin nan? Contract marriage, how? Setayi decieving kowa kenan tasa su yarda eh soyayya sukayi da Mr. Fauzi har ya kai ga aure? Kuma seya b’ata mata image gun iyayensa, yace taci amanar sa? Gaskia baratayi ba amman kuma intayi la’akari itace ma zata fi benefiting. Dubu d’ari biyar sau 6 miliyan uku kenan plus miliyan shida daze bata ta tashi da miliyan tara kenan. Wow! Zata samu takai Babanta har k’asar waje ayi masa aiki takuma tattara family’nta subar Maiduguri su koma ko Kano ko Kaduna inda su Farouq bara su sake saminsu ba. Zata samu ta sa Afrah ma a makaranta. To yanzu ya? Ta yarda kenan?

     “Miss Aleeyu?” Ya tsamota daga cikin duniyar tunanin data wula. “Have you make up your mind?”
    “Sir naji komai amman seka b’ata min image gaban iyayenka ne su d’au mutumiyar banza ce ni?”
    “Yes Miss Aleeyu this is the only way zan kub’uta, the only way Abuu zeji tausayi na bare sake min maganar aure ba har se in ni na masa.” Kai ta gyad’a a hankali “Sir amman baramu na had’a kwanciya bako?”
    Lallai ma yace a ransa, shi d’inda ko wace mace nada burin ganinsa kan gadonta ita tasamu zata tsaya tana masa tsiya.

     “Miss Aleeyu nima ba so nake ba dan yazama dole ne, ofcourse we will share a bed amman ba abinda ze shiga tsakanin mu, in ma gudun abinda kike kenan, kisani banida interest cikin wancan abin ko physical contact ban yarda ba, lokacin da zamu iya tab’a juna shine only if either your family or my family visits saboda kar su gane faking auren mukeyi.”
     “Sir you mean barin sanar da su Mami ba? Ai ya kamatasu su sani-”
     “Bekamata ba” ya katse ta. “Ko Afrah ban yarda ki fad’a mata ba, this is our secret dan the moment kika sanar da mutum d’aya kin mana ruining komai kenan. Don’t tell anyone, clear?”

    Kai ta gyad’a tana nazarin ya zata soma b’ullo wa family’nta da wannan zancen auren Mr. Fauzi. Ai se suce dama tuni soayyaya ke kai ta office nasa ba aiki ba.
     “Good” yace. “So starting today zakiyi faking zama girl friend d’ina saboda kar mutane suyi suspecting relationship namun bana gaskia bane.”
       “Is that necessary Sir? Senayi pretending zama girlfriend naka a idan mutane?”
     “Yes Miss Aleeyu kidena san abu kina kaiwa kasuwa, bakiya san zama girlfriend d’inan ne? Sure kinaso so stop pretending and let urself celebrate.”

    “No ni banaso” ta kare kanta.
   Wani shu’umin murmushi ya saki mata. “In ma saboda Yusuf saurayin kine kike wannan abu gwamma tun wuri ki bari, kije kiyi breaking up dashi dawuri dan baraki b’ata min reputation ba ace kina dating d’ina kuma kina dating me aiki k’ark’ashi na ba.”
     “Sir Yusuf ba saurayi na bane.”
   “Allah sa” yace ba tare da ya nuna danuwa ba. “So ki bud’e kunnwanki da kyau ki jini, akwai rules da zan kafa miki regarding wannan aure;.
   Na farko shine don’t fall for me, saboda fake relationship ne I will show you love and care amman kisani bana tsakani da Allah bane, so in kika yi falling min ba ruwa na ke zaki karya wa kanki zuciya dan ni ba sanki zanyi in return ba.” Dad’in abin ba yau ta soma jin munanan kalamunsa ba so ko damuwa batai ba. “Ka kwantar da hankalinka Sir ni barin tab’a falling maka ba, business is business”
         “Allah sa ki iya ignoring beauty na. Na biyu we will be hanging out tare, duk inda zanje tare zamuna zuwa irin su dinner ko lunch da ake inviting d’ina so as inyi introducing naki wa bussiness colluegues d’ina. Inada business trip nan da 1 month da 2 weeks zuwa Morocco dake zanje.
   Na uku, I will re transform you, you are now my girlfriend ya kamata ki fara sa kayaki masu tsada saboda mu nuna wa public kin kai ince ina sonki.” Wannan wace erin zagi ne? Meyake nufi? Kaya masu arha take sawa kenan ko meh? Baki ta bud’e zata masa gana. Ya dakatar da ita ta hanyan aza hannunsa kan lips nasa “shh! Bangama ba karki katse ni. I know kinasan kice you are not ashamed, if you are not toh ni I am and that stays that. Hope am clear for now, more rules will follow afterwards...”

© miemiebee

TANA TARE DA NI...

 TANA TARE DA NI... PAGE 47
BY MIEMIEBEE


     “Baki jini bane?” Ya tambayeta tare da d’age gira.
   “Naji Sir” ta amsa a hankali. “Good and one more thing, learn to call me Anas in public. Bareyi kina kiran boyfriend naki sir ko Mr. ba. Am I clear?” Wani banbarak’wai maganganunsa suka sauk’a a kunnenta, ita rabuwan ta data kira sa da asalin sunan sa tun kafin ta fara masa aiki ta riga ta saba da Boss ko Sir ko Mr. Fauzi. “But Sir na riga na saba.” ta fad’a.
    “Seki saba da Anas d’in shima. Yanzu rufo min k’ofar mota.” Ba gardama ta rufe, basu tsaya ko ina ba se babban shopping mall dake Maiduguri bayan yayi parking ya juyo ya kalleta kallonsan take itama amman take ta kau da kanta. “So kinga cikin mutane zamu shiga am now your boyfriend dan haka karki kirani da wani suna banda Anas, clear?” Kai ta giad’a a hankali. “Me zamuyi anan amma?” Ta tanbayesa.
   “What else? To shop for you.” Ta kai da bud’e k’ofarta kenan ya dakatar da ita “wait, I’m your boyfriend ko kin manta ne? Let me.” Hannunta ta mayar tana jiransa bayan minti d’aya k’ofarta ya bud’u. Hannunsa ya mik’o mata a yayinda ta tsaya tana kallansa dan bata san me zata masa ba. “Grab my hand” yace da ita romantically.
    “Sir-” kallo ya watsa mata “I mean Anas kai fa kace ba body contact.”
     “If we are alone ba, yanzu kuma cikin mutane zamu shiga we have to pretend like other lovers do, now grab my hand.”
     “Sir I mean Anas amman haramun ne ba kyau, you are not yet my husba-” bata k’are maganar ba yakama hannunta tare da fito da ita daga motar. Janta ya fara suna tafiya se k’ok’arin k’watan hannunta take takasa, bece mata komai ba sanda suka iso daidai gaban k’ofar ya tsaya ya kalleta. Chak itama ta tsaida damben k’watan hannun ta datake kanta a sunkuye.
     “Fannah” ya kira sunanta abinda be tab’a yi a gabanta ba. “Stop it okay? Behave yourself.” A haka suka shiga cikin mall d’in idanu ne sosai akansu dan ko ba’a tab’a ganin Mr. Fauzi da mace ba segashi yau da PA’rsa. Wani business colleague nasa ne dayazo shopping shima da family’nsa ya gansa.

       “Mr. Fauzi” ya danna masa kira from far behind atare Fannah da Anas suka juya suna kallon inda suka jiyo muryar. Anas na ganinsa yakira sunansa shima “hey Mr. Mahmoud!” bayan Mr. Mahmoud sun k’ariso da matarsa sukayi hand shake sannan akayi gaisuwa. “This is Miss Aleeyu your PA ko?” Mr. Mahmoud ya tambaya.
     “Yes this is Fanna”  ya sake rik’o hannunta gam da nasa yana mirzawa a hankali, electric sparks Fannah tajiyo cikin jikinta. “My girlfriend.”

    “Your girlfriend?” Mr. Mahmoud ya nanata abinda Anas ya fad’i cike da mamaki a iya saninsa de Anas baida time na girlfriends.
   “Yes!” Anas ya jaddada masa, “she is no more my PA right BABE? ” Ya juyo yana kallon Fannah. Rasa na cewa tayi chan k’asa k’asa cike da kunya tace, “yy..yyess” ta nisanta “honey ” Wani shu’umin murmushi Anas ya saki. “So Mr. And Mrs. Mahmoud semun sake had’uwa girlfriend ita tanada gajan hak’uri kar mu b’ata mata lokaci se anjima.”
    “Ayi shopping lafiya Mr. And Mrs Fauzi.” A haka sukayi sallama, hannunta rik’e cikin nasa suka nufa wajen inner wears. Me kuma zamuyi anan? ta tambayi kanta a zuci. Me kula kayan wajen tana ganin Mr. Fauzi ta soma washe hak’wara “Mr. Fauzi you’re welcome have a sit please.”
   “No thanks” yace mata tare da k’arisowa gabanta da hannun Fannah cikin nasa. “Dubata wani size ne ze mata.” Baki wangalau Fannah ta bud’e cike da mamaki da kunya gabad’ai wai mesa Mr. Fauzi baida kunya ne? Hijabinta ta hura sede its too late matar ta riga tayi figuring out komai. “Lets say maxi B cup.”  “Okay thanks” yace da ita tare da jan hannun Fannah suka shige ciki, wajen bra zalla ya kaita bi yake yana duba tags na jikin bras d’in har ya kai kan tag B hannunsa ya raba da nata tare da d’iban bras d’in ba iyaka ya jibge mata ajiki, da sauri ta tare a hijabinta.

    “Sir I mean Anas meh haka? Its embarrasing dan Allah ka bari.”
     “What so embarrasing Fannah? You are my girlfriend me aciki dan na saya miki inner wears?” Wani sabon row ya kwasa ya sake zuba mata cikin hijabinta. Janta yayi zuwa side na panties yana duddubawa chan ya d’aga guda d’aya yana duddubawa a sama “Mr. Fauzi I mean Anas dan Allah kabari kar a ganka.” Banza yayi da ita tare da ajiyewa, wani daban ya sake d’agawa shima da be masa ba ya sake d’ago wani.

     “Saboda Allah Mr. Fauzi kabari.”
    “I won’t stop se kin fad’a min size naki.”
    “NOO!!” ta fad’a da ihu.
   “Then fine haka zan cigana da nema har sena samu.” Haka yatayi har wucewa ake ana nuna su. Ganin ba mahalicci se Allah ta rufe ido kawai “Sir size na hannun kan ne.” Juyowa yayi kalle ta dawani shu’umin murmushi a fuskarsa. “Good” ya ce da ita kalan size d’in ya riga d’iba har rows uku ganin kayakin sun soma mata yawa ya buk’aci akawo masu trolley dam ya cika d’aya da inner wears zalla sekace kayan lefe ze had’a. “Anas ya isa please ina zan kai wad’annan kayaki?”
   “Basu miki bane akawo wasu desingers d’in daban?”
  “NOOO MR. FAUZI!!!” Ta masa ihu, trolley’n yaja tare da rik’e hannunta wajen biya suka nufa ya ajiye tare da jawo wani trolley’n daban. Siyayya na fitan hankali yayi wa Fannah tun tana yabari har tagaji, shi kansa be bari taji total amout d’in ba. Har gaban gida ya kaita yasa yara suka shiga da kayakin ciki. “So are you telling Mami ko in shiga in fad’a mata da kaina?”

    “Zan fad’a mata da kaina.”
   “Yaushe yanzu?”
    “A’a se in bikin ya kusa.”
   “Kina nufin har se na gama gina gidan tukunnah?”
   “Yes Sir.”
   “Lallai kam!” yayi exclaiming. K’ofarsa ya bud’e yafita tare da bud’o nata. Hannunta yaja ya fito da ita sannan yasoma janta zuwa cikin gidansu. “Mr. Fauzi dan Allah kar ka shiga zan fad’a mata da kaina.”
    “When gobe jibi? I don’t have that time.” Already su Mami suna tsaye jikin kayakin duk mamaki ne d’auke karara a fuskarsu da Afrah harda Aiman. “Laaaa Mami kiga harda bressier” cewar Aiman. D’aya taciro “kuma wallahi daidai dana ya Fannah ne ko Ya Afrah.” Daidai lokacin su Anas suka iso tsakar gidan bra d’in Mami ta amsa tare da b’oye wa a bayanta ganin Mr. Fauzi.

      “Sannu dazuwa” ta musu duka. Bayan an shimfid’a musu tabarma suka zazzauna, sede Anas yak’i sakin hijabin Fannah dan dolenta ta zauna kusa dashi. Mamaki ne yacika Mami, Afrah kam gani take kamar a mafarki. Gyaran murya Anas yayi;

    “Ermmm Mami you must be wondering me ya kawo ni nan as well as kayakin chan ko? Well Fannah and I have been wanting to tell you amman Allah be bamu iko ba.” Ya juya ya kalli Fannah tare da mata wani killer smile dataji zuciyarta na k’ok’arin fashewa dak’yar ta iya ta mayar masa da murmushin itama. “We two... We two...” Sekuma yakasa k’arisawa nanne Mami tagano bakin zaren.
   “Ya Anas soyayya kuke da Ya Fannah?” Aiman ta tambaya, bakinta Mami ta buge “tashi kishiga ciki.”
   “Mami nayi shiru.”
   “Tashi nace!” Mami ta bud’e mata ido, a sanyaye ta tashi tashiga d’akin Baba.
    “Toh Anas shine har se kai da kanka zakazo ka fad’a min? Ke Fannah meya hanaki fad’a min iyyeh?”
    Kame kame ta soma “erm.. Erm...” Anas ne ya karb’eta “Mami ni na hanata saboda nayi laifi nafara soayyaya da ‘yarku ban tambayi izini wajen ki ko Baba ba, I’m sorry please.”

      “Bakomai Anas nasan bada gangan kayi hakan ba, toh inde blessing d’ina kuka zo nema ni kam na baku, Allah sanya alheri, naji muku dad’i sosai.”
    “Mungode Mami” cewar Anas a kunyace. “Yau ma Baba yana bacci ne inasan mu gaisa.” ya tambaya cike da girmamawa.
   “A’a idansa biyu barin masa magana” nan ta fice. “Congratulations to you two” cewar Afrah. Kallo Fannah ta watsa mata a yayinda Anas yace, “thank you sistaaa.”
   “Toh Ya Anas, Fannah kad’ai aka sani aka ma siyayya mufa?”
    “Ke Afrah bakida hankali ne?” Cewar Fannah tana zaro mata ido.
   “Toh ke me ruwanki?” Anas ya katse ta “don’t worry Afrah” hannu yasa cikin aljihunsa yaciro bundle na d’ari tare da mik’a mata. “Gashi gobe keda Aiman kuje kuyi shopping kinji? In ya kasa muku ki karb’i number na wajen Fannah ki kirani se in k’ara muku kinji?”

      “Yeyy! Ya Anas mungode.” Daidai da fitowar Mami kenan “bismillah Anas kashigo” a hankali ya saki hijabin Fannah tare da mik’ewa ya nufa d’akin. “Ya Fannah ya akayi Ya Anas yasan size naki naga harda bressier ya sayamiki.”
       “Afrah wallahi in baki rufa min baki ba sena cicci miki.”
   “Uuuhhh! Kode harda panties ne? Soyayya dad’i” hannu Fannah ta d’aga zata bugeta take ta gudu d’akinsu wane ta cinye kud’in.

   Bada dad’ewa ba Anas ya fito murmushin dake d’auke a fuskarsa kad’ai amsa ne game da tambayan ya had’uwansa da Baba ya tafi, it was a success. Mami ce ta rakosa waje “toh Anas kaide kullum seka mana wahala mungode Allah saka da alheri ya k’ara bud’i.”  “Ameen Mami ni zan wuce.”
  “Toh masha Allah Fannah baraki raka Anas nakin bane?” Mami ta tambayeta tana mata murmushin tsiya.
   Kamar tace barin raka sa ba sekuma ta fasa tace “zan raka sa Mami.” “Yawwa toh mungode ko Anas a gaida gida.” A sanyaye ta mik’e ta bi bayansa bayan sun fito gaban gidansu yace da ita “toh Mrs. Fauzi thank you koma ciki.”
    “Niba Mrs Fauzi bace tunda ba’ayi auren ba tukuna.”
  “Ohonki nide adena so ana kaiwa kasuwa. Cikin jakar inner wears d’in akoi kud’in d’inki ciki also akwai wani paper da phone number rubuce ajiki, number’n tailor’n Amal ne naga yana k’ok’rin d’inki seki kirasa kuyi magana, okay?” Can k’asa k’asa tace “okay nagode” tare da ficewa.

       Tana dawowa taga su Afrah kan kayan se bud’e bud’e sukeyi. Sanda ta ganta sannan ta soma maganar; “ai dama Mami na fad’a miki akoi b’oyayyen al'amari tsakanin Ya Fannah da Ya Anas bakiga kullum tana zuwa office ba.” Yi tayi kamar bata jita ba takai da shiga d’akinsu kenan Mami ta kira sunanta “Fannah! tsaya” chak ta tsaya. Mami ce ta k’ariso wajen ta “mu shiga daga ciki.” Bayan sun shiga suka zauna kan gado Mami tasa hannunta cikin na Fannah.
   “Fannah shin kin sanar da Anas labarinki kuwa? Banasan ku gina relationship kan k’arya ki fad’a masa komai akanki please dukda da k’yar ne agane wani d’a na miji ya tab’a shiganki amman yakamata ki sanar dashi, k’arya ba abar yi bace.”
 
     Rasa na fad’i tayi.
     “Fannah Habibti kinyi shiru ko baki fad’a masa bane?”
  Qarya ta mata; “ko kad’an Mami,  karki damu na sanar dashi komai ahakan kuma yace yana sona ze aureni, ya kuma buk’ace ni da kar in sake kawo masa zancen koda wasa same goes to you to please Mami, maganan ya wuce kar mu sake d’agowa.”
    “Toh Alhamdulillah na matuk’ar jin dad’i wallahi, mahak’urci mawadaci kinga amfanin hak’uri kenan. Yanzu koda Ya Khaleel ya dawo se mu fad’a masa kinada mijin da zaki aura.”

    “Mami Baffah Khaleel ma bare sake dawowa ba sabida a yanzu haka Ya Farouq yana cell...” nan ta labarta wa Mami komai. Ba abinda Mami ke inbanda sunbud’a wa Anas albarka.

**

    Shima Anas d’in daga gidansu Fannah gida ya zarce cinye sa ne kawai su Ummie basuyi ba dan murnan ganinsa da sukayi. Abuu, Shettima kowa yaji dad’in ganinsa. Bayan sun gama cin abinci ya dawo d’akinsa ya jinguna jikin gado, besan dalili ba kawai ya tsinci kansa cikin nishad’i da jin dad’i musamman inya tuna reaction na Fannah data fad’a masa size na panties nata. Knock ne yazo daga k’ofar sa. “Come” yace.
    Shettima ne yashigo ya nemi waje ya zauna kusa dashi. “So Ya Anas ina kashiga kwana biyu ka kusan sama Ummie hawan jini Amal kuma ciwon hauka?”
    “Nowhere maza just that I needed space to think.”
    “Sure?” Ya tamabayesa yana wani murmushin tsiya.
    “Yau kuma dawani surutun ka taho?” Ya tambayesa.
  Well d’azu aka kirani w“ai an ganga a mall kai da Fannah kuna shopping.”

    “Mutane da gulma!” abinda yace kenan.
    “Aww dagaske ne kenan?”
    “Nima ban sani ba” ya amsa sa a takaice. “Tashi ka fita ma please don’t ruin my day. Nifa na fad’a maka ba san Fannah nake ba I’m just using her and thats all.”
    “Toh in tayi tsami mua ji nide a dage ko weekend ne a kawo mana ita muyi spedning.” Pillow Anas ya d’aga ya wulla masa wanda Shettima yasamu yayi dodging ya fice a guje yana dariya. Shikansa Anas dariyan yake.

***
 
    Da tunanin Fannah wanda keson zama masa jiki yayi bacci. Sede mafarkin Ummimi daya kwan biyu beyi ba yayi yau. A firgice ya tashi yana gumi yana nishi, k’ark’ashin gadonsa inda yake adana bottle d’aya zuwa biyu saboda situations like this in yayi mafarki yasha ya d’au d’aya ya bud’e. Har ya kai baki sekuma ya kasa sha yayi promsing Fannah bare sake sha ba, rufewa yayi. Wata zuciyar tace masa toh ai ko kasha barata sani ba tunda ba ganinka take ba. Nan ya bud’e ya sake kai baki nan ma yakasa sha. “Oh God! NO!!!” Toilet ya nufa ya juye a bathroom yayi flushing haka yayi da d’ayan ma, sannan ya koma ya kwanta. Ina fa, bacci ya gagara, mafarkin Ummimi se hunting nasa yake.

   Wayarsa ya d’ago daga kan side drawer yaga k’arfe 1:20AM. Miyarwa yayi ya sake kwanciya daga ya rufe ido se mafarkin Ummimi ya dawo daga inda ya tsaya. Yayi hakan sau uku kawai ya hak’ura da baccin inda giyansa na nan da yana sha nan da ‘yan mintuna zeyi everlasting bacci, duk laifin Fannah ne ita tasa sa yayi making promise kan bare sake shaye shaye ba, yanzu haka ita tana bacci shi yana nan yana wahala sede ayi  2-0. Wayarsa ya sake d’agowa yaga 1:40AM kan lambarta yakai ya danna mata kira.

    **

   Fannah na cikin baccinta me dad’in bala’i tajiyo ringing na wayarta ita tama rasa meya hanata sawa a silent har yagama ringing bata d’aga ba se a karo na biyu. Cikin bacci ta d’aga “hello” dan ko duba wake kira batai ba.
    “Miss Aleeyu” ya kira sunanta ai take ta nemi baccin nata ta rasa.
   “Mr. Fauzi”,takira sunan sa cike da mamaki. “Me ya faru da daren nan?” Torchi ta haska taga k’arfe d’aya ne.
   “I can’t sleep” yace da ita sincerely.
   “Toh Mr. Fauzi nikuma me zan maka?”
     “Nima bansani ba all I know is that is your fault.” Hamma ta saki tare da zaro idanu “nikuma Sir? Mena maka?”
   “You made me promised to you that barin sake shan wani abu ba, I’m badly in need of that now kuma na kasa sha, because I can’t break my promise to you!” ya fad’a ad’an tsawace.
 

        “Is okay calm down Mr. Fauzi, calm down okay? Karka sha please, zaka iya tashi zuwa kitchen?” ta tambayesa a hankali cikin murya me sanyi.
  “Yes” yace mata.
   “Good you are going to make your coffee, trust me in kasha you’ll go back to sleep peacefully but please kar ka sha wancan abun you promised, kaji Mr. Fauzi?”
   “Naji” yace tare da mik’ewa zuwa kitchen d’in. Haka tana fad’a masa directions d’in yana bi har ya had’a sede koda ya tab’a be kai nata dad’i ba.
  “It didn’t work Miss Aleeyu, ni barinsha ba.”
    “Yi hak’uri kasha, first thing gobe I’ll come to your office in had’a maka kaji? Yi hak’uri kasha wannan d’in  please will you do that for me?” Shiru yayi bece komai ba “please” ta rok’esa.
   “Okay” ya fad’a can k’asa k’asa.
    “Sleep good okay? Gobe da safe zan zo in had’a maka coffeen kaji?”
     “Naji” yace karap ta katse wayar. Da k’yar ya iya shanye rabin coffeen. Kasancewar ba Fannah ce ta had’a masa ba, sam ya kasa bacci amman dan yadda muryarta ke yawo masa a kai besan lokacin daya koma bacci ba.

© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 48
BY MIEMIEBEE


     _5:00AM_
  Shettima ne ke knocking bakin k’ofan d’akin Anas, bacci Anas yake sosai wanda ya jima beyi erinsa ba ko jin knocking d’in baiyi. “Bam bam bam! Ya Anas katashi Asubah yayi.”
   Cikin gigin bacci yace, “naji seka b’alla k’ofan neh?”
    “Ya Anas bazaka masallaci bane?” Shi se yanzu ma ya tuna ana zuwa masallaci bayan na juma’ah.
   “Barinje ba zanyi a gida.” Dama amsan da Shettima ke jira kenan, Ya Anas baisan zuwa masjid inbanda na juma’ah daya zamo masa dole sekuma in Abuu ya tilasta masa. A sanyaye ya juya Abuu dake tsaye a parlour yana jiransu ya tambaya, “ya ina wan naka?”
    Qarya Shettima ya masa, “wai kansa ke ciwo zeyi a gidah.”
   “Toh Allah sawaqa.” Da “Ameen” da Shettima ya amsa sa suka fice. Se 5:15AM Anas ya tashi yayi sallah bacci ya koma se 7:00AM ya tashi ya soma shirin office yau kawai yaji yanasan sa jampah kasancewar yau Juma’ah. B’angaren da yake adana jampopin nasa ya bud’o suna nan turum ba adadi, dubawa yake chan yaciro wani sky blue half jampa yasa, se inche tunda nasan Mr. Fauzi be tab’a yin kyau kamar na yau ba, ba k’aramin amsar kayan yayi ba, cufflinks nasa masu tsada yasa. Fefes yafita bayan yagama feshe kusan rabin designer turarukan sa, jakar laptop nasa ya saqalo daidai yafito yaga Abuu zaune kan dining yana shan coffee. Cike da girmamawa yagaishe da Abuu tare da nufan dining space d’in shima dan had’a tea.

     “Ya jikin naka?” Ya tambayesa.
  Jiki kuma? ya tambayi kansa kode qaryan da Shetitima yayi dan rufa masa airi batun zuwa masjid d’azu kenan? “Da sauk’i.” ya amsa.
       Good, Anas I hope kana tsokaci da lokacinka, yau sati d’aya ya tafi cikin 6 months dana baka, kasani ko minti d’aya barin k’ara maka akai ba.” Ko uffan Anas bece masa ba, amman take blue eyes nasa suka k’ada ransa ya b’aci, se faman had’a tea’n sa yake.
   “Anas dakai nake magana.”
   “Naji” yace tare da ajiye flask d’in, tean ma ya fasa had’awa ya gommaci ya tafi da yunwa. Ficewa kawai yayi ransa na tafasa. Yawonsa ya fice se to 8 ya isa office ko amsa gaisuwan da ake masan ma beyi. Ganinsa cikin jamfa duk ya basu mamaki se kallon sa suke.
     “Sir you are looking awesome” cewar Mubarak. Wani kallo Anas ya watsa masa. “You are fired!” Ya daka masa tsawa. “Sir I’m sorry dan Allah kar kayi firing d’ina.” Bello dake gefensa ya basa tausayi. “Sir he is sorry please, consider this.”
    “Kaima kanada bakin magana kenan? Follow him you both are fired kuje ku samu Adam.” Nan ya nufa wajen elevator’n sa ko ya akayi yaga d’an wani stain kan floor d’in oho. “Wa yayi mopping floor d’innan yau?” Baki na b’ari Abdul Hamid dake gefensa yace, “Boss Yakurah ce.”
    “Jeka sameta and tell her she is fired inform Adam yayi replacing nata now, am I clear?”
   Baki na b’ari yace, “yy..yyes sir” nan Anas ya haura zuwa office nasa se huci yake shikad’ansa gawani uban yunwan dayakeji dan rabuwansa da abinci tun jiya da rana.



     *****

      “Ya Fannah kisa wannan d’in mana wallahi yayi kyau kuma ai Ya Anas zeji dad’i idan ya ganki dashi tunda shi ya siya miki.” Cewar Afrah tana mik’a mata wata electric blue gyale.
    “Banaso! Ha’an! Barin sa,ba kema kinsan ba burgeni gyalen nan yake ba, hijabi na mutunci na.”
     “Haba mana Ya Fannah ace saurayinki ya siya miki abu kik’i sawa? Gaskia ba haka ake soyayya ba.”
    Kuma fa haka ne, Fannah ta fad’i a ranta, inhar ta cigaba da behaving bata damu da Mr. Fauzi ba definately Afrah da gane ganenta zata gano bakin zaren wataran. Kai amman kuma bata so, bata son sa gyalen.

      “Barin sa ba ki miyar” ta bata amsa tana k’ok’arin ciro hijabinta daga cikin drawernsu, daidai lokacin Mami tashigo. “Ya Fannah amshi kisa mana.” Cewar Afrah.
   “Meke faruwa ne?” Mami ta tambaya tana k’arisowa cikin d’akin.
  Kafin Afrah tayi magana Fannah ta tareta “ermm babu komai Mami dama Afrah na tambaya ko gyalen hannuntan ya tafi da kaya na.”
   “Eh sosai ma ya tafi, yau kuma gyale za’a sa neh?”
    A kunyace tace, “eh mana Mami ko kin manta Anas ne ya kawo min.”
    “Toh yayi kyau Allah kiyaye hanya.”
   “Ameen Mami.” Gyalen ta amsa gun Afrah dake mata murmushin tsiya yafawa tayi harda rufe kai dashi. “Haba Baaba, meh haka sekace goggo? Ai tsofi aka sani da yafa gyale haka kawo kiga.” Nan Afrah ta tsara mata gyalen sosai tayi kyau.

    “Meh haka?” cewar Fannah tana kallon kanta jikin madubi. “Sekace neman miji zani? Batsan yayi yawa mana Afrah.”
  “Wallahi beyi ba Ya Fannah, dan Allah karki b’ata kibari a hakan.” Da k’yar Fannah ta yarda ta fice, tafi minti biyu tsaye bakin k’ofar Enterprise d’in amman takasa shiga se kunya takeji. Da k’yar ta iya ta shiga Yusuf ta soma tararwa da sauri ya nufi kanta “Fannah barka da kika zo! Dan Allah kije ki ba Boss hak’uri wallahi da safen nan yayi firing mutane uku.”
   
    “Mutane uku?” Fannah ta zaro ido. “Dalili?”
    Nan ya labarta mata komai... “kinsan haka yake in ransa a b’ace, please talk to him.”
   “Karka damu I’ll try.” Nan ta haura sama, jan bakin da Afrah tasa ta sawan dolen ta sa hannu tana gogewa sede koda ta ciro madubi ta duba taga yana nan kan yanzu ta shafa saboda 24hours ne. Tsuka taja, a hankali tayi knocking bakin k’ofar san. “Enter” yace. A hankali ta waina k’ofar ta shiga alokacin ko juyawa yaga waye ne beyi ba as ya zage se masifa yake kan wayan da yakeyi. Kallonsa Fannah ta tsaya yi dan yadda jampan jikinsan ya mugun amsar sa bata tab’a ganinsa da jamfa ba kuma setaga kamar jampan ma yafi amsar body figure’nsa. A’a to kodan bata tab’a ganinsa dashi bane? Wow! amman gaskia yayi kyau kasa kallonsa tayi musamman yadda gashin kansa ke sheqi.

       “Fire them dukansu ukun, fire them and replace them with better ones, am I clear?” Ding! Ya katse wayar. Nan ne ya juyo dan ganin ko waya shigo. A hankali blue eyes nasa suka sauk’a kan Fannah kallonta ya tsaya yi dan wani kyan da tayi, daga kan d’aurinta, yadda ta yafa gyalen, lace d’in jikintan, d’inkin da komai ya masa kyau. Fuskarta kuwa ba inda yakaisa yin kyau, dark red jambakin da tasa ba k’aramin haska skin nata yayi ba. Kallonta yake itama tana kallonsa duk suna admiring kyan junansu sekuma gashi kamar sun had’a baki duk suka sa blue kaya sede nashi light nata dark.

      Haushin da Abuu ya tusa masa ya nema ya rasa daga ganin Fannah. Ita ta fara kau da kai sannan shima ya kawar. A hakali ta tako izuwa gaban table nasa “good morning Mr. Fauzi.” Ta gaishesa beko amsa ba, kallonta kawai yake kai ta d’ago a hankali tana kallonsa taga shima ita yake kallo kuma koda suka had’a ido beji kunya ya kawar da idanunsa daga gareta ba. Ganin kallon bana k’arewa bane tace, “ermmm let me make you coffee sir./ Be ce mata komai ba ta juya.

    2 minutes later ta gama had’awa ta kawo masa tare da ajiye wa agabansa. Ganin baida niyan sha tace, “please take it sir” magana take masa a hankali dan abinda Yusuf yace mata kan ran Boss a b’ace yake yau. Sip d’aya ya kai baki tana tsaye a kansa. “Sir” takira sunansa cikin siririyar muryarta. Be amsa ba illa dawo da kallonsa dayayi a gareta.

   “Ermmm nace can you do me a favour?” Shiru yayi chan yace, “what is it?”
    “Sir please kadawo da wad’anda kayi firing... Please.”
    “No barin dawo dasu ba, bana son shisshigi, just make me coffee and leave ga chan flask d’in achan” ya nuna mata da yatsa.
   “Please fa nace, do this for me please, will you?”
   “No Miss Aleeyu, they are useless workers sesa nayi firing nasu.”
  “Sir saboda ance maka kayi kyau? Is it a crime? Yanzu nima in nace maka kayi kyau sekayi firing d’ina?” Ta tambayesa, shiru yayi bece komai ba.
  “Toh Mr. Fauzi kayi kyau yau, kayi kyau sosai. Is that it? Fire me toh.”

    “No Miss Aleeyu stop it! I can’t fire you, I just can’t.”
   “Why Mr. Fauzi? kamar yadda suke mutane nima haka nake, abinda zaka musu shi zaka min, be fair please.”
   “No Miss Aleeyu, you are diffrerent, kidena had’a kanki dasu. Kina min abubuwa da dama dayaci ache nayi firing naki amman I can’t.”

     “Toh kayi hak’uri ka dawo dasu please kaji Mr. Fauzi? Yi hak’uri this job is their only source of income yi hak’uri zasu kiyaye nan gaba.” Shiru yayi bece komai ba kuma bayida niyyan magana.
   “Mr. Fauzi must I beg on my knees zaka dawo musu da aikinsu? I’ll do it.”

    “No don’t! Zan dawo musu da aikinsu, don’t kneel.” Yayi warning nata dad’i taji sosai. “Sir are you serious?”
    “Yes kije kice Adam ya dawo dasu.”
   Cike da jin dad’i tace, “thank you sir, thank you” nan ta fice taje ta sanar da Adam godiya duka suka riga mata kamar su cinye ta. Bada jimawa ba ta dawo office na Anas. Coffee ta had’a masa cikin flask sede duk sanda ta d’aga kai ta kallesa shima ita yake kallo, har ya soma sata feeling uncomfortable. Gyalen nata tayi yunk’urun d’agawa zuwa kanta.

     “Stop, kibarshi haka” yace da ita. Yi tayi kamar bata jisa ba, se k’ok’arin d’agawa take. “Miss Aleeyu as your Boss and boyfriend I said stop it, okay?” Ya fad’a a tsawace nan ta bari wayarta dake side bag nata ne ya soma ringing nan ta ciro ganin Yusuf ke kira ta d’aga a takaice. “Hello?” On the other side yace;
  “Our life saviour!”
Murmushi ta saki wanda yasake fidda kyanta. “Kai dan Allah, ba komai don’t worry.”
    “Dama kira nayi  dan na sake miki godiya and to offer you a lunch saboda in sake nuna miki godiyata.”
    “Haba Yusuf is it necessary?” Duk wannan waya da takeyi Mr. Fauzi na zaune yana kallonta wani kishi yaji wanda be tab’a feeling ba ya tokaresa jin ta ambato sunan Yusuf wato dashi ma take wannan murmushi sekace an mata albishir d’in shiga aljannah, lallai Yusuf you wanna die ya fad’i a ransa.

     “Awwn! Lunch zaka siya min?... Aww tare zamuje muci?... Are you sure?... Toh nagode zan sauk’o yanzu... Thank you.” Nan ta katse wayar. “Mr. Fauzi zan tafi dama had’a maka coffee kace inzo yi nayi zan tafi, se anjima.”

   Bece mata komai ba as tunanin wani aiki ze bata tayi dan hanata fita da yake. Chan ya duba gaban table nasa yaga wasu mails da Kacallah ya kawo masa jiya wanda za’ayi reprinting nasu. Har takai bakin k’ofa ya kira sunanta “Miss Aleeyu!” Chak ta tsaya tare da juyowa. “Yes Sir?”
   “Come” yace da ita ba musu ta k’ariso. Pen da plane sheets guda goma ya irga ya mik’a mata tare da had’a mata da mails guda goman. “Gashi min copying wad’annan da neat handwriting don’t make any mistakes.” Kallon papers d’in ta tsaya yi sannan takoma kan Anas. “Mr. Fauzi kai kace fa am nomore your PA kuma yanzu kana bani aiki?”
 
   “Yes Miss Aleeyu, na canza mind d’ina ne yanzu in aiki ya taso zan iya saki tunda mu bibbiyu ne kawai, kiyi sauri I need them ASAP.”
    “Ayyah Mr. Fauzi kaifa kace ba aiki yanzu kuma...” Katse ta yayi “hurry Miss Aleeyu yau Juma’ah ne zanje masjid.”
   “Toh Mr. Fauzi ayi printing nasu mana ba sena rubuce su ba.”
   “Yes Miss Aleeyu rubuce su nakeson kiyi hurry up go and sit acan.” Zata sake magana yace, “now!” A d’an tsawace. Batada wani option haka taje ta zauna tafara copying tana rubutawa. Kallonta yake. Daidan ki kenan se muga ya ke da Yusuf d’in zaku fita lunch. Yace a zuci. Huh! Nima yunwa nakeji bari ta gama muje muci breakfast/lunch tare daga chan sena wuce masjid.


kuyi hak’uri abinda yasamu kenan yau
© miemiebee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 49
BY MIEMIEBEE


Kallonta yake kamar TV a yayinda take sauri sauri tayi tagama dan zuwa samin Yusuf. Guda 4 tayi cikin goma amman wani zogi hannunta ke mata saboda tsawon mails d’in, idanunta ta d’ago tareda maraice fuska koze d’an ji k’anta. Sosai shima yaji ta basa tausayi amman kuma ya ya iya? In yace tabari definately zata je ta samu Yusuf abinda baiso kenan, shikuma bayasan raini bayasan tasan kishinta yake ta d’au ko sonta yake (ni Miemie nace toh da ba sontan kake ba?) Yanason ce mata barata fita da Yusuf ba amman bayasan ta d’auka da wani manufa ta d’au ko santa yake kanta ya soma girma. Kansa ya kawar daga gareta kawai dan kar tausayinta ya kama sa tare da concerntrating akan laptop nasa.

    Bayan tasamu tayi guda takwas ta d’ago kai “Mr. Fauzi please kayi hak’uri nagaji.” Banza da ita yayi. “Mr. Fauzi please” nanma bece da ita komi ba dan yasan muddin bakinsa ya bud’u zece ta ajiye shikenan, abinda baiya so kenan. Wayarta ne ya soma ringing tana kai dubanta taga Yusuf ke kira bayan ta d’aga tace, “Yusuf I’m sorry wallahi aiki ne yad’an rik’eni amman I’m almost done yanzu zan sauk’o.” Nan ta katse.
 
       Anas dake sauraronta yace a ransa yanzu zaki sauk’o ba? We shall see. Bayan 10 minutes tagama, wani hamdala ta saki se murza yatsunta take dan azaba. “Sir gashi na gama” ta sanardashi alokacin da take tsaye gaban table nasa. Amsa yayi yana dubawa one-by-one komai yayi sede bayasan ya barta ta tafi, taya zataje tayi having lunch da Yusuf bayan gashinan, bayan tasan tare suke ci always, Isn’t he her boyfriend? Ai koda relationship nasun na k’arya ne still be kamata ba. Besan meh ba amman yanzu bayasan ganin Fannah da wani d’a na miji in ba shiba.
    “Sir can I go now?”
    “Wait” yace, tare da zaro d’aya daga cikin papers d’in “seda nace miki be careful banason cancelation kalli nan. D’au new plane sheet ki sake copying.” Kamar wacce zatayi kuka tace, “ayyaahh manaaaa Sir mana, letter ‘f’ nefa kawai nayi canceling its not looking rough ai.”

      “Ma ke kenan, to me it is morethan rough...” Yacigaba da duban sauran nan ya tsakula wasu guda ukun da tad’anyi light mistakes, in aka had’a dana farkon hud’u kenan. “Recopy them all duk kinyi omiting mistakes”
   Baki ta sake, “Mr. Fauzi wallahi barin iya ba dan Allah karka min haka.”
   “Miss Aleeyu what is wrong with you? I am paying you bawai aiki kike min kyauta ba d’auka kije ki zauna ki gama yanzu.” Ya fad’i authoritatively tare da kawar da kallonsa daga gareta. Harara mai rai da lafiya ta watsa masa ganin bai ganinta sannan ta tattara ta koma ta zauna. Yusuf takira ta basa hak’uri kan fitarsu bareyi ba seko next week saboda tasan ba yanzu zata gama ba, hannunta yayi tsami layi d’aya ta rubuta seta tsaya taja yatsunta.
     “Ba komai” yace “Allah kaimu” tare da katsewa.

   Dad’i sosai Anas yaji dayaji tace ta hak’ura. Kallonta yake tayi ta tsaya tayi ta tsaya tana gama guda d’aya tausayinta ya kama sa, tasowa yayi daga kujeran sa ya nufo gabanta, ita a zatonta ko yaga mistake na ‘a’ da ‘e’ da tayi ne yazo mata masifa. A maraice tace, “Sir dan Allah kayi hak’uri don’t make me recopy it please, wallahi guda d’aya ne kuma bara’a gane ba” ta k’are maganar kamar wacce zatayi kuka. Tsugunawa yayi a gabanta, ido wuru-wuru ta zaro meyake shirin yi? Kafin ta kawo wani abu a ranta ya ja hannunta a hankali, bugun zuciyarta taji ya k’aru, a hankali take k’ok’arin k’watan hannun nata gudun karya k’ara mata wasu papers d’in. Biron ya amsa ya ajiye tare da bud’o tafin hannunta me uban laushi yana mata tausa a hankali daga kan yatsunta har zuwa wrist nata.

      Har wani sanyi sanyi takeji saboda yadda hannun yayi tsami yana mata ciwo amman kuma be kamata  tabar masa hannunta yana tab’awa harda mata tausa ba. “Ermmm Mr. Fauzi” ta fad’i tana k’ok’arin karb’e hannun nata, sarai yagane tanason k’watan hannunta ne amman be kula ta ba, hasali yi ma yayi kamar be san tanayi ba, sanda ya tabbata ya mata tausan da yaci ace hannun ya bar zafi ya bari. Mik’ewa yayi ya koma ya zauna ba tare da yace da ita komi ba, dukda kuwa so yake ya bata hak’uri amman inaaa girman kai!
 
    Bayan ya zauna ta d’aga biron daga inda ya ajiye da nufin cigaba da rubutun tunda ba cewa yayi ta bari ba. Bece komi ba har yanzu se da yaga zata fara rubutun. “Keep the pen, stop it, don’t write.” Ya bata wannan commands. Kallonsa take  fuskarta d’auke da kan mamaki. “Sir bangama bafa-”
   “I know” ya katse ta, “just kibari don’t write again.” Dad’i sosai taji yanzu seta samu tafita da Yusuf ma tunda Boss yace tabari. Arranging papers d’in tayi ta kai ta ajiye masa kan table sannan ta koma ta d’au jakarta ta saqala, duk kallonta yake bece komai ba seda ta kai bakin k’ofa ya daka mata kira “Miss Aleeyu!” Har tsakiyar kanta tajiwo muryarsa. Juyowa tayi tana b’ari dan firgitan da tayi. Toh me tayi kuma yanzu? Da hannu yayi gesturing nata kan tazo. Taku take k’afa na rawa har takai gaban table nasa.

   “Who asked you to leave?” Ya tambayeta yana kallon cikin idanunta. Da sauri ta kawar da kallonta elsewhere ba tare da tace komai ba. “Am talking to you!” ya fad’a ad’an tsawace duk ransa yabi ya b’aci har yanzu be yarda Yusuf nada gut daze ce zekai Fannah cin abinci ba, yaushe ma yagama ciyar da kansa kuma awani local restaurant zekaita ko hotel ma bare iya kama musu ba to talk more of ya musu reserving.

     I’ina tasoma “ermm.. Si.. Sis.. Sir naji kace in ajiye in bari kuma aikin daka sani kenan.”
   “Amman nace ki tafi?” Kai ta girgiza a hankali. “Good kinga book shelve d’in can?” Kai ta giad’a tana kallon shelve d’in. “Jeki min arranging nasu.”
      Kallon shelve d’in ta tsaya yi nakusan ‘yan mintuna sannan back to Mr. Fauzi. Itade bata ga abin gyara cikin shelve d’in ba ga books nan duk anyi arranging nasu tsatsaf. “Bakiji me nace bane?” Ya tambayeta.
   “Naji Sir amman kuma naga ba abin gyara ciki, shelve d’in is well arranged.”
    “Toh ni banasan arrangement d’in na hannun dama a k’asa nakeson su koma hannun hagu a sama. Na tsakiya ki dawo dasu second to the last row, second row ki raba into two a 4th raw...” Haka ya ringa juye-juye. Kallonsa take kamar tayi kuka, ita ba abinda taji ma inbanda na hanun dama a k’asa su koma hannun hagu a sama.
  “Well baraki fara bane?”
   “Zan fara” ta amsa sa a takaice murya k’asa k’asa. Jakarta ta ajiye ta nufa wajen book shelve d’in. A hankali ta fiddo da na saman tayi replacing nasu dana k’asan kamar yadda ya buk’ata, a yayinda shikuma ya katse duk wani abinda yakeyi yana kallonta ko kyafta ido baiyi.

   Itade Fannah arranging take yadda taga dama, chan ta tsaya admiring wani latest english novel data jima tana nema bata samu ba. «Half Bad by Sally Green» kusan na minti biyu tana kallon littafin sannan ta had’a da sauran ta cigaba. A takaice de seda ta kusan awa tagama had’a uban book shelve na Anas dake nan kamar library. Daidai lokacin k’arfe 11:30AM kenan. Tagaji iya gajiya.

     “Sir na gama” tace all exhausted, ga wani uban yunwan daya keto mata lokaci guda. Bece da ita komai ba illa d’akinsa da ya nufa bayan like 5 minutes ya fito se k’amshin turare yake, gashin kansa ma ya sake gyarawa, kallonsa Fannah ta tsaya yi. “My girlfriend” yace da ita yana kallonta dawani killer smile tattare da fuskarsa shikansa yasan yayi kyau yau. Zuciyarta taji ya tsallaka bugu uku lokaci guda, kai ta d’ago a rikice tana kallonsa da ita yake koko a’a. “Me?” Ta tambayesa tana nuna kanta.

    “Yes you, you are my girlfriend ko kin manta ne?” Lallai ma! Kallansa take cike da mamaki yanzu yagama azabar tar da ita yawani zo yana shegen murmushinsa yana kiranta girlfriend nasa. “I’m hungry muje muci abinci nasan kema you must be hungry.” Yunwan takeji amman ta dake “no I’m not ni barinje ba kawai ka sallameni in koma gida.”
    “No ba gidan da zakije, we are going to eat, oya stand up na baki 5 minutes kije ki kimtsa a office naki.” Yi tayi kamar bata ji saba.
    “Miss Aleeyu! Don’t try my patience.” Ganin bai kallonta ta galla masa harara kan zata cire idanta sannan ta mik’e tare da jan jakarta ta fice zuwa office nata wajen book shelve d’in ya nufa yad’anyi dube-dubensa. Exactly after 5 minutes d’in yafito daga office nasan itama a daidai lokacin ta fito.

     Light makeup nata ta gyara ta hanyan k’ara powder da zalla datayi sekuma d’aurinta data sake gyarashi. Gyalen nanan yadda yake d’azu ta yafasa kamar yadda Afrah tamata d’azu. Kallonta yake wane ze had’iyeta. A hankali cikin k’asaita ya tako gabanta gam ta rufe idanta tana jiran ya fara suburbud’a mata surutu setaji ya kama hannunta take ta bud’e idan so take tace masa ya sake mata hannu sekuma ta tuna there will be no point doing so dan ba jin maganarta zeyi ba. Wajen elevator’nsa suka nufa bayan daya bud’u tace, “Sir semun nunawa duka ‘yan office naka muna dating ne? Kabari in mun fita anan amnan yanzu ka sakemin hannu please.” Ko tanka ta beyi ba illa janta waje da yayi suka soma tafiya.

      Take floor d’in yakama da surutu da gulma kowa se tofa albarkacin bakinsa yake k’us-k’us dan sun san halin Boss yanzu seya buga fire! Kunya ne ya rufe Fannah kamar ta nitse k’asa yanzu shikenan zasuce daman abinda ita da Mr. Fauzi keyi kenan kullum a office nasa, soyayya. Da idansu ya had’u da receptionist kuwa harara ta watsa mata dan ta jima da fad’awa tarkon san Mr. Fauzi koda ta fad’a masa kuwa tatas ya mata ya k’yamace ta. Ignoring nata kawai Fannah tayi, Yusuf dake shigowa yanzu ne yagansu tare da Mr. Fauzi amman ko kad’an idanunsa be kai kan hannun su ba.

   “Fannah!” Ya danna mata kira a yayinda ya gama k’arisowa kusa dasu. “About the lunch I think zamu-” be k’are maganar ba idansa ya sauk’a kan hannun ta dana Boss. Ido wuru-wuru ya zaro sekace a mafarki! Me had’in Fannah da Boss to kodai soyayya sukeyi? Fannah da hanaklinta zatayi soayayya da me shaye shaye?
   “Oh I’m sorry bansani bane daban gayyaceki lunch d’inba” ya fad’a tare da juyawa. Fannah ji take kamar ta nitse k’asa. “Yusuf” Mr. Fauzi ya kira sunan sa chak ya tsaya tare da kewayo wa. “ SWEETHEART baki sanar dashi bane dama? Why?” Shiru tayi bata amsa saba. “Tell him now to clear all doubts.” Nan ma bata tanka saba.

    Hannunta dake cikin nasa ya matse yadda ze d’an mata zafi.
    “Na zata na fad’a masa, Yusuf I’m sorry.”
    “Sorry for what? Don’t apologise HONEY fad’a mashi yanzu.” Shiru tayi duk takaici yabi ya cikata.
   “ QUEEN,ko yunwan ne bakiya son magana? I’m sorry yanzu zamuje muci abincin just tell him kinji HONEY BOO? ” Wai meke damun Mr. Fauzi ne ta tambayi kanta so yake yayi ruining friendship nata da Yusuf ne ko me? In yacigaba da abinda yakeyi ai se Yusuf ya d’au k’arya ta masa d’azu batun aikin dayace ya mata yawa, se yace ko k’arya ta masa daman fita zatayi da Mr. Fauzi take b’oye masa.
 
       Ido kawai ta rufe tace, “Yusuf I’m sorry ban fad’a maka ba, Anas is now my boyfriend excuse us please zamuje muchi abinci.” Mamaki ne sosai ya ratsa Yusuf lallai ma Fannah tacika ‘yar halak.
  “I’m sorry for delaying you, by the way congratulations” a sanyaye ya juya yayi tafiyarsa, binsa da kallo Fannah tayi, ji take kamar tayi kuka, mesa Mr. Fauzi ze mata haka? Bata sake ce masa komai ba har suka isa hotel d’in shi da kansa ya bud’e mata k’ofa se dad’i yakeji saboda yasan definately yanzu Yusuf da yake zaton saurayinta ne ze rabu da ita tunda ya gansu tare.

 
     Abinci kala d’aya ya musu ordering kafin abicin ya iso ba abinda Anas yake inbanda kallon Fannah shi inama haka zata namasa shiri kullum. Duk lokacin data d’aga kai setaga ita yake kallo. Da k’yar kalamun dayakeson kiranta dasu tun d’azu da safe suka fito yanzu, “you are looking beautiful today.” Kai ta d’ago tana kallonsa da mamaki karara a fuskarta. Wayace mata tayi kyau? Mr. Fauzi? Kode k’arya kunnuwanta suke mata. “Eh sir?” Ta tambayesa.

    “Not Sir, Anas” yayi warning nata.
   “Anas me kace?”
   “Nace kinyi kyau yau.” Ido wuru-wuru ta zaro yau wata rana Mr. Fauzi ya yabata, sede bata san meh ba seta tsinci kanta cikin jin dad’i, toh se meh dan yace tayi kyau? Se komai ya faru k’wak’walwarta ta bata amsa. Murmushin jin dad’in datayi k’ok’arin kawar dashi ne ya kub’uta mata, kallon ta Anas yake dad’i yaji yasata murmushi. “Thank you” tace a hankali cikin jin dad’i, take ta nemi bak’in cikin daya tusa mata ta rasa. “You too kayi kyau.”
   “I know already ba sekin fad’a min ba, I always look good.”
   Toohhhh! Ta d’ago kai tana kallonsa yaga shima ita yake kallo, shegen girman kai tace a zuciyarta wai I always look good irin yasan shi kyakkyawan nan ne, Allah raba mutum da erin wanga hali.
   
    “My girlfriend nasan ban isa in hanaki kallo na ba amman kallon yayi yawa unless you wanna eat me up.”
   Wai lallai ma tace a ranta wato shi ya zage yana kallona in ni nad’an kallesa yace wani na cika kallo.
    “But Sir naga nima ai kallo na kake, kuma tun d’azu tunda nashigo office naka yau.”
   “Toh ai dan na kalleki doesn’t mean anything, ni kawai kallon ki nake saboda kin d’an yi kyau yau kuma ni bada wata manufa nake kallonki ba amman kinga ke kullum cikin kallona kike, day and night kuma da wata manufa kike kallo na. I can see it in your eyes, kallon soyayya kike min nikuma nayi warning naki don’t fall for me.”

Bakin Fannah seda ya kusa fad’i a k’asa dan yadda ta sakosa. “Nide ba kallon soyayya nake maka ba.” Ta fad’a tare da kare kanta.
   “Ohonki nide na fad’a miki SWEETHEART don’t fall for me.” Dadai lokacin abincinsu ya iso. Waiter’n ranan ne ya kawo musu wanda ta tambayesa nawa ne kud’in plate. “Wow Miss Aleeyu you are looking amazing.”,Murmushin daya k’ayata ta tasaki “thank you.” Wani kallo Anas ya watsa wa waiter’n take yaji wani bak’in kishi ya tokaresa ji yake kamar ya tashi ya shaqure sa ai shi yakamata ya yaba kyan da tayi ba wani daban ba, kuma yayi.
 
  “Can I have your number?” ya tambayeta, “zanso zama abokin ki.”
   “K’ato dakai?” Anas ya tambaya a fusace, “toh barata bayar ba. Ko kunya ma bakaji ma mschww! Boss naka zan kira yayi firing naka next time baraka sake cewa kanasan wata da abokanta ba, stupid kawai.”

    “Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah naga PA’rka ce am sorry please.”
    “She is not my PA she is my girlfriend.”
   “Omg! Mr. Fauzi please forgive me wallahi bansani ba.”
   “Damuwanka, Boss naka zan kira abincin ma mun fasa ci.” Wallet nasa yaciro ya irga kud’in ya wurga masa.
   “Fannah lets go” ya fad’i a fusace. Dakewa tayi, “Anas” ta kira sunansa cikin wani irin salon muryan da bata tab’a amfani dashi ba. “Calm down kaji? Calm down please.”

    A hankali yaji hankalinsa na kwantawa. “Calm down please” ta sake fad’i. Idanunsa da suka kad’a taga sun soma dawowa asalin farin kalansu.


*© miemiebeee

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 50
BY MIEMIEBEE



Kamar wanda bareyi magana ba yace, “naji tashi mu tafi.”
    “Promise me baraka kira boss nasa ayi firing nashi ba.”
   “Thats none of your business, he deserves to be fired.”
    “Please Anas for me, please karka kira Boss nasa kaji Anas? Please.”
    “Fannah no!” Ya fad’a ad’an tsawace.
         Fuska ta maraice, “Shikenan tunda d’an wannan ma baraka iya min ba” jakarta ta tattara ta mik’e da niyyan tafiya gyalenta ya rik’o. Da k’yar bakinsa ya iya furta “no don’t go, barin kira Boss nasan ba, just don’t go.” Dad’i taji sosai da murmushi ta juyo tana kallonsa “thank you, so ka hak’ura muci abincin anan?”
 
    “No not here, lets go somwhere” be jira tace wani abu ba yakama hannunta suka fice, gidan baya suka shiga dukansu a yayinda driver ya kunna mota. Ita yanzu Fannah damuwarta d’aya ne yadda zata masa wa’azi yadena rik’e mata hannu, tana son tabisa a hankali ne kar ta had’a masa komai lokaci d’aya shiryuwan ma yace yafasa akoma gidan jiya. Gaban wani makeken hotel driver’n ya tsaya bayan ya bud’e musu k’ofa Anas yafito sannan ita, ciki suka shiga hannunta rik’e cikin nasa sede yau da mutane cikin hotel d’in zaune suna cin abinci ana ganinsu aka soma gulma k’us-k’us. Magana take iya yadda Anas ne ze jiyota.

      “Anas kad’an sake min hannu kaga duk maganan mu suke kaji please.” Banza yayi da ita ya nufa wajen receptionist. “I want to reserve this place now.”
    “Okay sir bara a sake karb’an customer ba, but bari na cikin su gama please.”
   “Kasan ko waye ni? I said reserve it now ka koresu duka I will pay you double of the money.”
   Ido ya zaro sosai jin double, “okay sir, bari amusu magana.” Haka mutanen suna ji suna gani aka kaisu wani d’an waje suka k’are cin abincin chan, aka barwa Fannah da Anas kad’ai makeken wajen. Kujeran tsakiya suka zauna ya musu ordering abincin, bayan minti uku abincin nasu ya iso spoon nasa ya d’aga ya soma ci, yayi spoons biyar yaga ko tab’a nata batayi ba.

     “Fannah why are you not eating? Acanzo miki ne?” Kai ta girgiza “Anas dole in zakaci abinci sekayi reserving ne?”
   “Yes wani abu ne?” ya tambayeta yana cin abincin sa.
    “No-” kafin ta k’ara fad’in wani abu yace, “banasan surutu while eating just keep quiet and eat okay?” Kai ta giad’a masa ta soma ci a hankali, kamar kullum yagama yayi zaman jirarta, wayarsa dake ringing ya d’aga “okay then” yace tare da katsewa. Bayan tagama ci ya biya suka fice gidan gaba ya bud’e mata cike da mamaki tace, “Anas ina driver’n yaje?”
     “He went somewhere, I’ll be the one to drive, enter.”
    “Sir zan tafi da kaina” haka kawai taji batason tana shiga mota dashi kad’ai.
    “Miss Aleeyu kina b’ata min lokaci zanje masjid get in.” Zata sake magana yace, “now” a tsawace.
        Ta tsorata amman ta dake “sir ni zan tafi da kaina.”
       “I’m your boyfriend ko kin manta? Kishiga ko in d’aga ki in saki ciki da kaina.” Miyau ta had’iye tashiga a hankali danko tasan Anas baida kunya tsab ze d’agata. Nan ya rufo k’ofar, not long enough yatada motar, agogon hannunsa ya duba yaga 15 mins to 12:55PM lokacin sallan juma’ah. “Fannah” ya kira sunanta, nan tabar kallon windown da takeyi ta juyo dad’i sosai yake mata yadda Anas ke kiran sunanta ‘Fannah’ cikin daddad’an muryarsa, har setaji ta sake k’aunar sunan nata inama dashi yake kirarta kullum. “Yes” ta amsa sa.

     “Can you wait in idar da sallan juma’ah se in kaiki gidah?” Kai ta giad’a masa daga nan be sake cewa komai ba a inda manyan mutane suke parking motocinsu yayi parking nasa a space da aka tanada masa, a kunne yabar motar dan AC’n daya kunna mata. “I’ll be right back.”
  “Okay” tace masa tana kallonsa har ya b’ace cikin mutane, shiru ta zauna tana d’an kalle kallenta chan bacci ya d’auketa wanda batasan yaushe ba. Bayan 25 ninutes Anas ya dawo yana bud’e motar yaga Fannah na bacci da wuyanta karkace gefe d’aya, gyalenta kuwa rabinsa ba’a jikinta yake ba hakan yabawa Anas daman k’are wa k’irjinta kallo, yayi kusan minti d’aya yana kallonta sannan take ya kawar da kansa yana girgizawa “no this is not approppriate.” Zagayowa yayi ta side nata ya kwantar mata da kujeran yadda zatafi jin dad’i tare da gyara mata kanta agarin haka d’ankwalinta ya kunce. “Oh no!” Anas ya fad’i k’asa k’asa. Allah yaso ribbon natan be kunce ba, yanayin gashin dake kwance kan goshinta da sajenta ya tsaya yana kallo, besan sanda ya d’aga hannunsa ya shafa kan sajen fuskartan ba, ganin ta d’an motsa yaja hannun nasa baya da sauri gudun kar ya farkar da ita. Mayafinta yaja a hankali ya rufe mata k’irjinta dashi, kanta kuwa d’ankwalin ta ya bud’a ya d’an rufe mata gashinta sama-sama sannan ya rufo k’ofar yadda bareyi k’ara ba.
   
      Side nasa ya nufa ya shiga ya zauna sede sam ya kasa kunna motan a gudunsa kar ya fara driving kuma ta tashi in suka d’an hau kan bomb. Zama yayi tare da ciro wayarsa yana chatting yana zaman jiran tashin Fannah. Bacci sosai takeyi chan ya juyo yana kallonta, kallo na sosai, cameran wayarsa yashiga yayi positioning sannan ya d’auketa picture d’aya, ganin tayi kyau ya k’ara mata d’aya kasa hak’ura yayi seda ya mata pictures kusan hams
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).