TANA TARE DANI 75.....
TANA TARE DA NI... PAGE 75 BY MIEMIEBEE Sede still bayason miyan kukan yafison ire-iren abincin daya saba ci a London su burger, pizza, bufallo wing, glorified rice, louisiana da sauransu. Datazo sake basa hannunta ya rik’e “na k’oshi a banza bakin mutum ya fara warin kukan nan” “Ai sekayi brushing bale ma bawani warin nan, open up” “Na k’oshi” “Dameh?” Ta tambayesa. “Wannan” ya nuna mata da yatsa. “Haba Habeebi guda biyar fa kacal kachi yi hak’uri ka k’ara nasan kana jin yunwa yi hak’uri Baby” haka tariga lalashinsa kamar d’an yaro tana basa abincin da wayo cikin k’issa kafin su hankara har yagama plate nasa bakinsa ta wanke masa da kyau se anan ta tashi mai daga chinya dan chin nata itama. Tana tashi shima ya mik’e zasa toilet ya k’wak’ulo amai. “Mine ina zakaje? Bade toilet ba! Please karka je ka harar da abincin nan.” “Ohh! Flower ni barin iya zama da wannan kukan acikina ba.” “Nasani hak’uri zakayi Habeebi na zauna a parlour kajirani I want us to play a game today.” “Wani game?” “Just wait for me.” “Toh naji excuse me” nan ya juya. “Baby promise baraka je ka harar ba.” Shiru yayi yana nazari. “Baby please.” “Okay okay I promise shikenan?” Nan ta gyad’a kai bayi ya nufa yayi brushing shi wai a dole miyan kuka nasa bad breath (warin baki) dawowansa ya zauna kan d’aya daga cikin sofas na parlour’n tare da kunna cinema. Kasa kallon news d’inma yayi se kallon Fannah yake yadda take chin tuwon sekace wani abun arziki me dad’i. Da idanunsu ya had’u ya wani yamutsa fuska “zaka k’ara neh?” Da sauri ya kad’a kai “a’a banaso thank you.” Murmushi ta saki “karka damu gobe dashi zamuyi breakfast zanyi mana d’umamensa.” Blue eyes nasa ya k’wararo “zaki d’uma meneh?” “D’uma wannan ko bakasan meh d’umameh ba? Zan sake reheating tuwon mana muyi breakfast dashi.” “Keda wa?” Ya sake tambaya “Nida Habeebi na.” Kai ya gyad’a “lallai kam zaki nemi new Habeebi dan ni barinci d’umamen wannan abin ba.” “LOL” tad’an murmusa “ai kai ne kad’ai Habeebin nawa, trust me d’umamen ma yafi dad’i yafi taste kasan da me yau zamuyi dinner?” “A’a bansani ba and banason sani ki rik’e please ni kawai zansha coffee in kwanta barin chi komai ba.” “Kai Habeebi d’an wake de zan mana inyi slicing egg and cabbage akai its way yummy. Gode kuma in Allah ta kaimu miyan kub’ewa zanyi” Yamutsa fuska yayi “a’a Flower please kiyi abinki ke kad’ai naji yunwa ko sausages zan soya inchi.” “Oho nide d’an wake zamuci da Baby na.” Be sake ce mata komai ba har tagama chi ta tattara dining d’in sannan ta dawo ta samesa da paper dakuma biro biyu a hannunta, gefensa ta zauna. “X and O zamuyi.” Yana jin haka ya kad’a mata kai dan ko sam be iya game d’inba bayason kuma yayi losing a gabanta ta raina sa kokuma ya fad’a mata be iya ba ta masa dariya. “Baby kayi shiru.” “Barinyi ba ki kawo wani game daban wannan ba dad’i.” “Toh Habeebi ni shi kad’ai nasani Allah da dad’i lets try kaga.” “Ohh!” dabara ta fad’o masa “ni se yanzu ma na tuna inada aikin da yakamata inyi attending to a laptop” ya k’arisa maganan yana k’ok’arin miqewa hannunsa ta riqe ta dakatar dashi “Habeebi I can tell you are lying kode kana tsoron kar inyi winning naka ne” tamasa gwalo. “Ke kiyi winning d’ina? Impossible lets play it muga.” Nan da nan ta zazzana musu sannan ta mik’a masa pen d’aya zuciyan Mr. Fauzi fa se bugu yake dan sam be iya game d’in ba at all. “So deal d’in shine if I win zan d’aneka anan” ta nuna goshinsa. Shiru yayi yana nazarin yau d’ani nawa zesha gun Flower. “Baby kayi shiru ko kanajin tsoro ne? Karka damu I’ll take it easy on you” tana masa wani shu’umin murmushi. Ina irin shikuma bari ya nuna mata shina miji ne bayajin tsoron nan. “Ba tausayi in na nad’e ki se goshin naki yayi ja.” “Haka kace?” “Yes Flower haka nace.” “Fine lets start.” Shi yafara placing X bayan yayi itama tasa O kafin ya hankara Fannah ta masa baki biyu kafin yace meh tariga tayi crossing ta chi sa. Tsalle ta daka “yeyy! I won nachi!” “Taya ya kikaci? Ai wannan cuwa-cuwa ne niban yarda ba.” “Kamar ya Baby? Gashi nan nacika kuma kana gani bring your forehead.” “Gaskia ban yarda ba asake wani kinyi magud’i anan.” “No vex asake wanin.” Hankali sosai ya miyar yana coffan yadda tayi d’azu shima dan mata baki biyu sede nan ma kafin ya hankara tasake chi nanma tata daka tsalle “yes!! yanzu ka yarda na cika?” “Ni fa gaskiya ban yarda ba kina min cuwa-cuwa ne kawai.” “Koma me ka kawo goshinka saboda deal ne.” Fuskarsa ya ajiye mata daidai tsakiyan goshin sa tasa hannu ta danna masa d’ani me uban zafi take wajen yayi pink. K’ara ya saki “argghhh!” “Aww” tayi pouting bakinta “da zafi ne Baby?” “Nima bansani ba” ya watsa mata kallo. Zuciya yayi “lets play again I must win this time.” Nanma da suka buga ita ta sake chi haka ba yadda ya iya ta ya sake a jiye mata goshinsa ta d’anesa fiye dana d’azu nanma k’ara ya saki sosai amman kamar maye yak’i hak’ura shi a dole seyaci ta aiko sun buga har sau 7 duk Fannah kechi gashi ko saurara masa batayi tunda yace no pity haka take d’aninsa da zafi-zafi goshin Anas daga fari yakoma pink yanzu jazir ya koma duk yabi ya galabaita. “Mschww! Ni na fasa game d’in.” a fusace ya mik’e yashiga d’akinsa. Murmushi kad’an tasaki sekuma ya bata tausayi ga dukkan alamu be iya game d’in bane daman shegen ajeboncin sannan dama ina ze iya? K’aramar hand towel da warm water tasa a bowl tabi bayansa mik’e kan gado ta tarar dashi yana ganinta ya juya mata baya a nitse ta k’ariso ta ajiye bowl d’in akan side drawer sannan ta zaro robe daga ciki ta ajiye a gefe. “My Baby” ta kira sunansa. Ko juyawa ya kalleta ma beyi ba. “Habeebi yi hak’uri ka juyo kaji inga goshin naka.” Nanma shiru ya mata. “Yi hak’uri mana Baby.” “Me zaku gani? So kike ki gani kimin dariya komeh?” “Ko kad’an Habeebi taya zan maka dariya? Gani zanyi kaji yi hak’uri kajuyo.” Ganin baida niyan juyawa tasa hannu ta juyo dashi a hankali tare da aza kansa kan cinyoyinta ita kanta seda ta tsorata ganin abinda ta mai da goshi, wani erin fata ne dashi sekace na mace da baison wahala haka? “Ya Salam Baby I’m sorry bansan haka goshin naka yayi ba.” hannunta ta miqa ta tab’a goshin nasa k’ara ya saki sosai. “I’m sorry kaji? Kai kace fa no sympathy ba tausayi shiyasa.” “Toh kuma seki yarda? Aikinsan in nine barin miki haka ba.” yayi maganar kamar wanda zeyi kuka. “Baby I’m sorry da ka fad’a min baka iya ba ai.” “Flower its embarrassing ace ban iya playing simple game kaman wannan O and X d’inba.” “Baby its X and O ba O and X ba.” “Naji whatever” kansa ya d’ago daga cinyar nata ze juya mata baya kenan ta rik’o hannunsa. ”Don’t be mad kaji Habeebi? Game ne kawai ba komai ba I’m sorry kuma bar kan naka kan cinya na zan d’an matsa maka wajen ne” “Kin manta kwanaki da cintoyin sukayi tsami ne?” “Ina sane ai ba dad’ewa zakayi akai ba tsaya” Batare da yace da ita komai ba ta matse towel d’in ta aza kan goshinsa da wuri yasa hannu ze d’aga dan azaba ta dakatar dashi “sorry kaji? Nasan da zafi hak’uri zakayi” haka tata matse masa a hankali yana sakin k’ananun k’ara time to time bayan data tabbata ta matse masa ta bud’e robe d’in ta lak’uta tasa a goshin nasa tana fara murzawa yayi saurin d’aga hannunta. “Flower ya isa haka barshi.” “Habeebi ka tsaya ko kad’an ne in mirza in bahaka ba ze iya kumbura fah” “Toh ai laifin ki ne, ke kika riga d’ani na sekace ba mijin kiba” “Baby nace I’m sorry be wuce ba? yanzu tsaya mu shafa maka semu kwanta mu huta... Yawwa Baby naa” a hankali take shafa masa har tasamu ta gama taje ta zubar da ruwan sannan ta dawo suka d’aura alwala tare da yin Sallah. Gado suka haye suka kwanta tana a gefensa suna fuskantan juna. “I love you Anas.” Shiru ya mata shi a dole har yanzu yanajin haushi. “Baby baraka cemin I love you too ba?” Kai ya gyad’a. “Har yanzu wai baka hak’ura ba?” Nan ma kai ya gyad’a. Matsowa tayi gab dashi kafin ya gane me takeson yi kawai ta hau kissing nasa ganin basuda niyyan tsayawa nima naja legediz benz d’ina na bar musu d’akin gudun kar su cinye kansu a idanu na (LOL) Koda na leqosu bayan minti uku still basu bari ba haka na sake komawa nabasu minti goma anan ne dana leqo naga Fannah kwance kan k’irjin Anas murmushi fal kwance kan fiskokinsu yana shafa doguwar sumanta a hankali cike da soyayya. “So can I hear it now?” Ta tambayesa. “Yes Flower I love you too.” Dad’i sosai taji ta sake matse jikinta a nasa ahaka har sukayi bacci. *** 7:30PM Tun idar da Sallan Maghrib da sukayi Fannah ta shjge kitchen ta fara aikin d’anwake acikin d’an k’ank’anin lokaci tagama ta had’a musu dining table tayi serving kowa a saucer, Anas na ganin haka ya saci jiki ya koma d’aki ya miqe kan gado shi a dole yana bacci bare chi d’anwake ba. Har d’akin ko ta biyosa “Habeebi tashi muje dinner is ready.” tayi maganan lokacin da take tsaye akansa, shiru yayi tare da sake gamme idanunsa shi wai adole yana bacci. “Baby tashi mana” ta gwada jijjik’ashi “meneh?” Ya tambaya sleepishly. “Baby wai bacci kake? Yaushe ne muka tashi daga bacci har kake wani? Tashi muje kaci abinci yaso seka dawo ka cigaba kaji?” “Banajin yunwa Flower.” “Nasani hak’uri zakayi karfa ya huce yayi sanyi tashi kaji My Lion.” Badan yanaso ba ya mik’e yabita bayan sun zauna ta ja mai saucer’n sa gabansa “bismillah lets eat” nan da nan ta soma kai nata ciki shide kallon saucer’n nasa kawai yake seda ta kusan rabin nata taga Anas beko tab’a nasa ba. “Habeebi inzo in baka ne?” “A’a chi naki zanchi da kaina.” “Toh chi mana ai yamayi sanyi” fork ya d’aga yasa ciki tare da danno kan d’aya seya kai baki seya sake maidoshi baya da abin ya isheta seda tabari yakai baki sannan ta tura hannunsa yasa d’an waken ciki yana fara k’ok’arin fito dashi a girgiza masa kai “karkayi please gwada chi mana kaji kaikam.” Tsotse zak’in jikin yayi kap ya jawo plate ya tufar da d’an waken akai. Kallonsa kawai ta tsaya yi cike da mamaki, wasu biyun ya sake kaiwa baki yana gama tsotse zak’in se ya fito dasu ya ajiye. “Wai Habeebi me haka? Haka ake cin d’anwake? Ai wannan almubazaranci ne.” “Kefa kikace senaci yanzu kuma da nake ci kina min surutu.” Nan ya cigaba da abinda yakeyi, ganin yakusan kai rabin saucer’n tace, “Baby kabari mana” sake matsowa kusa dashi tayi ta danna kan d’aya ta kai masa baki gashi karb’a ba musu ya karb’a “kuma karka tsotse Baby ka tauna ka had’iye.” “I can’t.” Ya sanar da ita. “Yes you can” ta tabbatar masa. Bayan ya gama tsotse zak’in yafara k’ok’arin cirowa aiko ta rufe mai baki “Baby ka tauna ka had’iye mana ko so kake yunwa ya soma damunka? Had’iye.” Kai kawai yake girgiza mata aiko daram ta zauna kan cinyarsa “yau seka had’iye in ba haka ba...” ta matso kusa da kunnensa ta rad’a masa abu ai take ya gyad’a kai. “Goood thats my Man” anan ta sake mai baki. Goran ruwa ya jawo kamar yadda ake had’iyar magani haka ya had’iye d’an waken haka yabi sauran yariga had’iyesu sekace meshan magani. Ita de Fannah nata ido ne. Bayan da suka gama dinner ta d’anyi assisting nasa wani aikin da yakeyi se 10:30PM suka kwanta. Washegari Anas yace sam bazasa office da jan goshi bah ba yadda Fanah batayi dashi ba yafa ce shi ba office da zeje haka suka sha baccinsu se to 11 suka tashi sukayi wanka tayi musu d’umamen as promised sam Anas yak’i chi ba yadda batayi dashi baya da yachi yace bare chi ba sede in fresh new one zata dafa bayan ta karya ta masa nasa breakfast daban kasancewar wheather’n garin yayi cloudy ba rana yau yasa suka fita baya wajen garden suna shaqatawa suna hiran masoya gwanin sha’awa abinsu. Honk da ake tayi yasa Anas ya miqe ya duba ko suwaye ne ganin motar Shettima yasa ya danna wani button gate d’in ya bud’u musu duk suka d’uru sukayi ciki. Amal da ba’asan an girma ba chak ta d’ale cinyan Anas tasa Ummie kunya. “Haba Amal ya haka kuma? Sauqo kinji?” Tana maganan tana kallon Fannah. “Ayyah Ummie barta ba komai she missd him thats why.” “Laaaaa Ya Anas me haka a goshin ka?” Cewar Amal nan hankalin kowa ya koma kan goshin Anas a tare Shettima da Ummie suka ce “dagaske fa amma meya samu wajen haka yayi pink?” Hannu yasa ya rufe goshin tare da bin dukkaninsu da kallo yana nazarin wani k’arya ze had’a musu idanunsa na had’uwa dana Fannah ta kawar dakai se k’ok’arin maze dariyan dake san kub’uto mata take. “Kayi shiru Anas” cewar Ummie “meya samesa Fannah?” Ta yi redirecting kallonta zuwa Fannah. Nan ta soma raba ido dan batasan me zata ce dasu ba. “Ermm... Erm-” katse ta Anas yayi. “D’azu ne zuma suka harbeni a garden ina d’an gyaran wani flower.” “Eh zuma suka harb’esa d’azu” ta mara masa baya. “Ayya sannu” duk su uku suka ce alokaci d’aya Amal na tab’awa yaja hannunta “da zafi stop it.” “Sorry.” Hira suka sha sosai da Fannah tama Ummie tayin d’umamen kuwa tace akawo mata haka suka zauna ita da Shettima suka narki tuwon banda Amal dake nan kamar Anas itama wai batachin miyan kuka se bayan Azahar suka tafi. ** “Kai aman gaskia Habeebi ka iya had’a k’arya sosai fah” ta kwashe da dariya. Banza da ita yayi. “Habeebi is a liar.” Wani kallo ya watsa mata “ki ka sake kirana liar sena miki abinda baki tsammani Flower.” “Do your worse” tamasa gwalo “My Baby is a liar” da gudu ta wuce kitchen tasa lock a duka k’ofofin se dariya take masa. “Ai ba kwana zakiyi ciki ba, zaki fito ki sameni.” Ya fad’a mata. “Zakachi miyan kub’ewan?” “Bansani ba kikayi abinki ke kad’an ki zakichi.” “Nida Baby na zamuchi.” “Babyn da one day zaki haifa ba amman bani ba.” ** A d’aki ta samesa da laptop gabansa yana d’an aiki. “Baby fito lunch is ready.” “Banajin yunwa.” “Tun safe banda chips da kachi me ka sake kachi?” “Toh laifin wa? Ba kece kike ajeni da yunwa ba.” K’arisowa d’akin tayi ta zauna kan cinyansa tare da zagaye hannayenta a wuyansa. “Kamar ya Baby? Ni ke ajiye ka da yunwa?” “Eh manah tun jiya kike dafa kalan abincin da bana chi kuma kin sani.” “Baby ai so nake ka saba bahaushe yace ba kullum ake kwana kan gado ba yanzu for instance in one day kaje Bama ina zaka samu irin abincin nan daka saba chi? ” “Even still je kichi abincinki ni baran chiba.” Gajeren hot kiss tamasa sannan tayi pecking nasa a kumatu “tashi muje kaji Habeebi na?” Besan a lokacin da yatashi ya bita ba ita da kanta take basa, ba kamar jiyan ba yau yaci kub’ewan sosai sabida yamasa d’and’ano bayan sun k’are chi suka koma d’aki tayi assisting nasa aikin dayake kai. 10:20PM Daidai nan Fannah tagama canzawa cikin wani had’ad’d’en rigan baccinta Anas kuwa akan nickers nasa da vest as always seda ya bari ta kwanta sannan ya hauro gadon ya had’e hannayenta gu d’aya “wa kike kira da liar d’zu?” “A’a ba kai ba.” “Nide nine liar ba?” “A’a Baby ba kai ba dan Allah kar ka min cakulkuli wallahi ba kaiba please karka-” bebari ta k’arisa maganan ba ya fara mata cakulkuli dariya take tana hawaye sosai tana had’asa da Allah sam yak’i bari. Seda ya tabbata ta galabaita sannan ya sake mata hannu ya share mata hawayen. “Next time zaki sake kira na liar.” Se “wayyo cikina” take tayi har a yanzu. D’agota yayi ya kwantar da ita jikinsa seda tagama dawowa hayyacinta ta d’ago kanta “Liar nasake fad’a” bata bari ya soma mata cakulkulin ba ta rufe sa da kiss sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya har wani su juya nan su juya chan suke alokaci d’aya Anas yasoma fita hayyacinsa dan wani irin kisses da Fannah ke masa kamar yadda shima yake mata all over her face and neck, duk sun zurfafa suna romancing junansu. Yasani in beyi stopping kansa ba yanzu he can’t later in kuma hakan ya faru zeyi breaking mata promise daya d’aukar mata before nacewa seda yardan ta abu ze gudana tsakaninsu. Da k’yar ya iya ya tashi daga kanta yaja baya ya zauna. “Baby meya faru?” ta tambayesa cike da damuwa tana k’ok’arin miyar da hannun rigarta daya fad’i sannan ta matso kusa dashi ta zagaye hannayeta daga bayansa. “What is it Habeebi?” “Babu” ya amsata blankly. “Da akoi Baby tell me.” A hankali ya cire hannayen nata ya juya yana fuskantar ta. “Flower I can’t go further... I..” Sekuma yayi shiru. “Why can’t you Habeebi?” “Flower kin manta promise dana miki seda concent naki zan tab’a ki?” Kai ta kad’a nufin ta tuni. “Kinga in ban tsayar da kaina yanzu ba I can’t later lets just sleep.” “No Baby I’m ready for it.” Ido ya zaro cike da mamaki yana kallonta “Flower me kikace?” kad’ai abinda bakinsa ya iya furtawa dan yadda mamaki ya rufesa. © MIEMIEBEE
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.