TANA TARE DANI 73......
TANA TARE DA NI... PAGE 73 BY MIEMIEBEE Hannu yasa ya share hawayensa tare da jan numfashi sannan ya soma maganar a hankali cike da nadama. “Mami tabbas na tafka babban kuskure a rayuwa na, kuskuren da har a yau ina nadaman aikatasa but believe me when I say this wallahi nima ba’a son raina hakan ya faru ba. Kuma wallahi tun ranan da abin yafaru nakasa samun sukuni a rayuwa na akullum ina tunanin wani hali na jefa yarinyar if only I can reverse time da nayi dan daidaita komai. Mami shekaru bakwai da suka wuce ni nayi raping Fannah, nine nan silar duk wani abin takaici da bak’in cikin rayuwa da kukayi witnessing dan Allah kuyi hak’uri...” Kuka ne yafi qarfinsa yakasa k’arisa maganan duk anan Mami batace masa ko k’ala ba ido ta zuba masa ga wani uban tausayinsa dake shiganta, Fannah dake gefenta ba abinda take itama se kuka daga bisani ya cigaba “kuyi hak’uri dan Allah Mami wallahi inason Fannah karku rabani da ita, ni na raba ta da budurcinta kuma zan cigaba da zama da ita kar a rabani da ita dan Allah na tuba...” Ya k’are maganar cikin sautin kuka. “Naji bayanin ka Anas kuma na gamsu hak’ik’a ka tuba kuma kayi nadama tunda har ka iya ka yi confessing babban laifi irin wannan tabbas ka tafka babban kuskure amman tunda kayi nadama komai ya wuce yanzu sede abu d’aya da nakeson sanar dakai shine shi muslimi da tawakalli aka sansa, Fannah tamin bayanin komai na maka k’arya akan bata fad’a min ba saboda inason ji daga bakinka inkuma tabbatar da eh ka tuba dagaske kuma kayi. Hak’ik’anin gaskia ba na mijin da zeyi zaman mutunci da Fannah kamar yadda zakayi Anas hasali ma mune da godiya zanyi iya qoqari na dan ganin Fannah ta koma gidanka amman barin tilasta mata ba saboda abinda yafaru a tsakaninku da ciwo Anas she needs some space kuma ni na yafe maka duk mun yafe maka ina fatan Fannah ma zata yafe maka wannan abu yazame sirri a tsakaninmu ko Babansu barin sanar dashi ba zan barku tare” tana kai nan ta mik’e haka Fannah ma. Da sauri ta dakatar da ita “A’a Fannah ki zauna ku gana kikuma yafe masa kinji Habibiti?” Kai kawai take girgizawa tana hawaye “yi hak’uri ki zauna” nan ta shige d’aki. Itama Fannar hanyan d’akinsu ta kama bi dan ko batasan me zata fad’a mai ba, kamar a kyaftawan ido Anas ya mik’e ya riqo hijabinta “Fannah dan Allah karki tafi I’m sorry please forgive me.” Har a yanzu takasa furta koda ‘A’ a nitse ya juyo da ita suna fuskantar juna yunk’urin sauk’a kan guiwoyinsa ya gwada tasa hannu da sauri ta tarosa cikin sautin kuka tace “Anas dan Allah kabari dan Allah stop it na gamsu da tubar da kayi kuma na yafe maka zaka iya tafiya.” Hannunta daya gwada tab’awa taja da sauri tak’unsa cikin hijabinta. “Fannah thank you, thank you so much yanzu ne zan iya samun sukuni a rayuwa na, I can be free now amman dan Allah karki barni Fannah lets go home please I love you.” “Anas I can’t dan Allah kabarni katafi please” tana kaiwa nan ta fisge hijabinta ta shige d’akinsu. Kuka sosai ya tsaya yatayi awajen Mami ce tafito ta riga basa hak’uri takuma tabbatar masa cewa Fannah zata dawo a garesa saboda tana sonsa da k’yar ta iya tura Anas ya tafi koda yafito beyi takansu Afrah ba motarsa ya nufa ya wuce a 360 isarsa gida keda wuya ya had’a akwatin kayansa dawani duk abinda ze buk’ata ya rufo gidan ya wuce paint house nasa daga ranan ya soma rayuwa achan abinci ma ba ci yake ba se in yunwa ta gasa sa. Koda su Ummie suka mai waya za suzo dubansa da Fannah kuwa k’arya ya musu yace sunyi tafiya basu gari. A kullum cikin tunanin Fannah yake har kamar ya fara zarewa dan yana zaune shi kad’ansa seyaji wai Fannah na kiran sunansa cikin sarqarqiyar muryarta me bala’in masa dadi hotunanta ne suka zamo masa farillah dan a kullum pictures nata na a gabansa yana kalla. Akwai lokacin da damuwa suka ma Anas yawa kad’an ya rage ba’a koma gidan jiya ba tunda ya sanar da Mustea halin da yake ciki Mustea ya k’arfafa masa guiwa kan yanemi syrup kawai yasha amman dan promise daya d’aukar wa Fannah ya hana kansa da k’yar, bare iya explaining how much yayi missing Fannah ba duk yabi ya rame ya fita daga kamanninsa gabad’ai office ma yabar zuwa duk yamusu k’arya yace yayi tafiya. Morning, afternoon and night messages kam bebar sending ma Flowersa ba dukda ba replying nasa take ba. Ya kirata har ya gaji amman bata picking koda ya kira ta wayar Afrah dan a had’asu ma nan bata karb’a. A takaice de rayuwar wannan masoya biyu ya jagule cikin sati biyun da sukayu batare da sunsa juna a ido ba. Ba aikin Fannah a kullum se kuka, bata tab’a sanin tanason Anas ba seda ta dena ganinsa a ganga da ita da daddare kuwa kullum tazo bacci seta rungumo pillonta setanaji kamar Anas nata ne. Wayarta na maqale a hannunta a koda yaushe tana karanta lovely heart touching messages da Anas yake mata sending wanda take matuk’ar jin dad’insu amman batajin zata iya replying nasa back aduk lokacin da tunanin abinda ya faru tsakaninsu yayi crossing mind nata. Ba yadda Afrah batai da ita ta gaya mata meke faruwa ba amman tak’i ta d’au alk’warin riqe wa mijinta sirri. Abinci kam ba takansa take ba se sunyi fad’a da Mami take chi shid’inma kad’an take tab’awa. Akoi lokacin da su Mami sukayi Eghusi soup da pounded yam tana gani kawai ta tuna da Anas ta tuna da yadda yakeson miyan kawai ta b’arke musu da kuka. *** “Fannah! Fannah!” Kiran Mami daga d’akinsu da Baba. Fannah dake d’akinsu miqe kan sallaya tana aikinta na kullum wato kuka tayi saurin share hawayen ta danko in Mami taganta zasuyi fad’a. “Na’am” ta amsa agigice tare da zabura ta nufa d’akinsu Baba chan ta samu Mami. “Bade kuka kike ba?” Cewar Mami kafin Fannah ta amsata ta cigaba, “karki damu na riga na ma Anas waya yau zezo ya d’aukeki kowa ma ya huta kinsan gobe Babanku ze dawo-” katseta Fannah tayi. “Mami dan Allah karkimin haka ko kwana biyu kibarni in k’ara anan.” “Nak’i Fannah ke wai bakida tausayi ne? Kinsan irin halin da kika jefa Anas tafiyarki kuwa? Yaron nan ya tuba mesa baraki yafe masa kukoma ku cigaba da zaman ku tare kamar yadda kuka saba ba? Ko wai acewarki akoi d’a namijin da ze kula dake ne kamar yadda Anas zeyi? Tun ina ganin abin naki da hankali na dena yanzu maza wuce ki shirya kayakin ki da La’asar Anas zezo ni na fad’a miki.” Har k’asa Fannah ta sauk’a tana had’a Mami da Allah amman ko a bakin zaninta ta fice tabar mata d’akin. Seda tayi me isarta sa’annan takoma d’akinsu takasa koda shirya kayakin nata zube take kan gado tana kukan da ita kanta batasan dalilinsa ba tana cikin haka taga call daga Anas bayan ya kwana biyu be kiranta se saqonnin dayake mata me zece mata yau? Ze zo ya d’auketa ko meh? Tana gani har yamata 2 missed calls tak’i picking bada jimawa ba ya turo mata message. Flower please don’t be mad I’m sorry and I love you #kisses Wani sabon kukan ta fara seda tayi ta godewa Allah sannan ta tashi ta jawo akwatin ta sam takasa cika kayakinta ciki daidai nan da shigowar Mami kenan baki ta sake ganin akwatin Fannah empty batako soma shirya kayakin nata ba. “Yanzu Fannah baki ko fara shirya kayakin naki ba bayan kinsan La’asar ya kusa?” A marairaice ta d’ago idanunta tana kallom Mami. “Mami dan Allah kibari ko gobe se in tafi.” “Mschww! maganan banza” wardrobe nasu tanufa ta bude tare da ciro kayakin Fannah kap tasasu cikin akwatin tayi zipping se roqarta Fannah ke amman ko ta kanta Mami batai ba tsab ta had’a mata kayakinta masu dotti tasasu cikin leda ta had’esu gu d’aya. 4:12PM Shigowar Anas gidansu Fannah kenan Mami kanta data gansa seda ta tsorata tana cewa Fannah ta rame ta lalace amman farillah ramanta yake aganga dana Anas sam kamar ba shiba bayan gaisuwa Mami ta sake basa hak’uri sosai sannan kuma ta masa nasiha daga nan tashiga dan fito da Fannah drama sosai suka riqayi sannan da qaqani qaqa tasamu ta fito da ita, akwatin ta Anas ya amsa. Wa’azi me ratsa jiki Mami ta musu sosai duk jikinsu ya sake mutuwa barin ma Fannah, da k’yar tafito daga gidan iya bakin k’ofa Mami ta musu rakiya ta koma ciki. “Fannah please lets go kinji? Kiyi hak’uri kibar kukan nan please lets go.” Sam tayi kamar bada ita yake ba sun kusan minti biyar tsaye wajen ganin batada niyyan ko motsawa ya finciko hannunta. “Anas ka sakeni ka sakeni nace” da dambe ya k’arisa motan da ita ya bude’e mata gidan gaba yasata sannan ya sanya jakarta a baya yazagayo shima ya shiga. Tunda suka fara tafiya take masa kuka a mota koda suka isa gida kuwa tafito bata ce masa komai ba akwatinta taciro ya karb’e mata. Shigarta ciki ta nufa d’akinta ta baje kan gado, bayanta yabi yakai mata akwatinta. “Flower kinci abincin rana?” Ya tambayeta baya ta juya masa. Nufowa gabanta yayi nanma ta sake juyawa “Flower meh kikeson ci? Yi hak’uri ki fad’a min” nanma banza dashi tayi haka yata suratansa har yagaji bata tanka sa ba seda ya fita ta mik’e tashiga bayi ta watsa ruwa fitowarta yayi daidai da shigowar Anas da plate na kaza a hannunsa. A farko tayi niyyan komawa cikin bathroom d’in dankuwa gajeren towel ne ajikinta daga baya data tsaya tayi tunani cikin d’an k’ank’anin lokaci kuwa setaga yin hakan bayida amfani tunda ya tab’a ganinta ba kaya ma a jikinta. Ignoring nasa tayi ta nufa wajen dressing mirror har anan bebar kallonta ba he can’t explain how much he missed her body. Daga bisani ya girgiza kai “Fannah I’m sorry bansan...” Sekuma yayi shiru yaja k’ofar ze rufe kenan ta ce dashi “ba komai.” ba tare da ta kallesa ba. Sam be yarda da abinda kunnuwansa suka jiye masa ba be d’au Fannah zata sake masa magana bama, lallai inta haka he has a chance. A nitse ya k’ariso cikin d’akin “gashi incase you are hungry eat please” ya ajiye mata plate d’in kan dressing mirror. Seda ya kai da bakin k’ofa sannan tace masa “nagode.” Dad’i sosai yaji “you are welcome Flower.” Yana kaiwa nan ya fice yakoma parlour ya zauna yana jirar ko zata fito. Bada dad’ewa ba k’ofarsu yayi k’ara yana dubawa yaga sabin fuska guda biyu da alama ma mata da miji ne wani button ya danna se main gate ya bud’u nan ya fito dan tarerayarsu. Bayan ya shigo dasu sika gaggaisa. “So gidanmu ne kusa da naku by the left lokacin da kuka zo nan munyi tafiya nida HASKE NA dawowan mu kuma mukaji wai kuma kunyi tafiya d’azu Haskena kecemin ta ga shigowarku shine nace mata yakamata mushigo mu muku sannu dazuwa.” Cewar mijin. “Suna na MUS'AB wannan kuma is my wife NAINAH” yajuyo ya sakar mata dawata lallausassar murmushi, murmushin ta miyar masa itama. Haka kawai se Anas yaji sun burgesa se ya tuna lokacin da suke a haka shima shi da Flowersa he misses her alot, da k’yar ya iya bud’a baki yayi magana drinks yayi serving nasu ganin Fannah batada niyyan fitowa ya shiga mata managa mik’e kan gado ya tarar da ita. Bayan ya k’arisa ya zauna agefenta yace, “Flower munyi bak’i neighbours namu ne suka shigo mana inda zaki iya fitowa seku gaisa da matarsa.” Kai ta gyad’a masa. Daman da hijabi jikinta bayansa tabi suka fito daya gwada yunk’urin riqe mata hannu kuwa setaja da baya. “Flower just for this once se mun nuna musu we are not on good terms ne? Please corperate” Sam tak’i barinsa ya tab’a mata hannu haka ba yadda ya iya suka fito kai a rabe idanunta basu sauk’a ako inaba se hannun Mus’ab da Nainah data gani a had’e se hirarsu suke suna dariya gwanin sha’awa a hankali ta dawo da kallonta kan Anas ita kanta she miss yadda suke a da. Ahakan suka k’ariso parlour’n suka zauna a seperate kujera tun anan hankalin Mus’ab yabasa da akwai matsala bayan sun gaggaisa cike da dabara ya buk’aci Fannah dasu shiga ciki da Nainah, hakan kuwa akayi. Alokaci guda Fannah taji san Nainah yashigeta ganin yadda take small of age amman ga hankali da ladabi da biyayya sede ashe ba Mus’ab ne kad’ai yagano abinda ke faruwa tsakanin Anas da Fannar ba har ita Nainan ma tayi. Suna zaune kan gado bayan Nainah tagama yabawa d’akin Fannah dama gidan entirely tayi gyaran murya. “Aunty Fannah” tace da ita. “Na’am Nainah” ta amsata. “Ba shisshigi ba Aunty amman senaga kamar da akoi matsala tsakaninki da Uncle.” Bata bar Fannah tayi magana ba ta cigaba “shi zaman aure se hak’uri Aunty koni da kike gani na nan inada kishiya kuma bawai shiri muke da ita ba sau dayawa tana cewa seta kasheni hakan be bani daman fad’a da miji na ba ina sonsa kuma shima yana sona kamar yadda nasan kuma kuna son junanku.” Wa’azi sosai Nainah ‘yar shekaru sha bakwai ta tama Fannah liqis ta kashe mata jiki gakuma wani kunyan dataji ache k’anwar bayanta tamata gyara bisa ganganci irin nata dan ko bata tambaya ba tasan Afrah ta girmi Nainah. Godiya sosai Fannah ta mata tare da bata kyautan wasu bangles had’ad’d’u. Shima Anas tun zamansa da Mus’ab ya riga masa wa’azi da nasiha sosai. ** Bayan sun yi masu rakiya suka dawo ciki har Fannah takai da bakin k’ofar d’akinta sekuma ta tuna alk’awarin data ma Nainah nacewa zata bawa Anas hak’uri bisa hurting nasa datayi. Seta juya zata masa magana sekuma ta kas, shiko yana tsaye a tsakar parlon ya k’ura mata ido ji yake kamar yaje yayi hugging nata ya fad’a mata how much he loves her. Da k’yar ta iya kiran sunansa muryarta se rawa take. “Anas” daman jira yake ya amsa “na’am Flower” tare da takowa har gabanta dududu space daya rage a tsakaninsu befi inches shida ba. Kanta ta sunkuyar “Anas I’m sorry kayi hak’uri” ta fad’a dashi sincerely. Hannunta duka ya rik’o cikin nasa d’aya yana murzawa a hankali tare da mata wani erin kallo alokaci guda yaji bak’in cikinsa duk sun gushe, murmushi ne fal kwance a kan fuskarsa. Dad’i yaji sosai da bata hanasa rik’e mata hannu ba. © MIEMIEBEE
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.