shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 18 September 2016

TANA TARE DA NI...77

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI... PAGE 77 BY MIEMIEBEE Wajenta ya nufa ya tab’a body tempreture nata nan yaji ya d’anyi rising. “Flower bakida lafiya” yayi concluding. “Habeebi kawai stress ne bawani abu ba.” “Wani aikin kikeyi in natafi? Ba girki bane kawai? Toh wani stress kike nufi Flower? Tashi muje asibiti sekace me sleeping sickess ko da yaushe bacci.” Juyowa tayi tana kallonsa “Baby wai me haka? Yanzu bacci ma barin iya yiba sekace seka kaini asibiti? Lallai fah Allah kacika bin diddigin abu, nikam ma inda zani” tana kaiwa nan ta juya tacigaba da baccinta kallonta ya tsaya yayi sannan ya zagaya ya sameta suka kwantan tare. “Flower I’m sorry didn’t mean to upset you.” “You didn’t my Lion nima I’m sorry.” “Your Lion is hungry.” “Baby kaifa kace kachi abinci a meeting yanzu kuma kana jin yunwa?” “Flower bana son tsiya fa sarai kinsan kalan yunwan da nake nufi feed me.” “Ni gaskia bansani ba” tana kaiwa nan ta juya masa baya chan k’asa-k’asa tace “mutum sekace sex machine ni barin iya ba.” Murmushi sosai ya saki lallai kuwa rabuwansa da ita 2 days now shine take wannan magana? “Nafa jiki Flower najiki da kyau kuma fushi zanyi.” Take ta juyo “a’a karkayi dan Allah yanzu bacci nakeji kabari ko anjima yi hak’uri lets sleep yanzu koh?” Shiru... “Koh Habeebi? Wallahi ji na nake ba k’arfi” Kai ya gyad’a mata ta matso kusa dashi ta kwanta. ** Bayan sun idar da Maghrib Fannah ta wuce kitchen dan soya musu scrambled egg a yayin da Anass ke parlour as ysual da laptpp nasa, tana cikin fasa k’wan d’aya ya fad’i ya fashe a k’asa aiko take kitchen d’in ya soma k’arni kafin ta hankara taji bakinta ya cike da amai. Guest toilet ta ruga a guje nan Anas dake parlour shima yabi bayanta. “Anas please karka shigo ka tsaya daga chan” ai kaman shigo tace masa ya k’ariso ciki yana shafa mata baya a hankali se aman take tayi se datayi sosai sannan ya taimaka mata ta wanke bakinta suka fito idanunta se wani kafewa suke a kan 2 seater suka zauna. “Flower whats wrong? Nafa fad’a miki bakida lafiya.” “Baby k’wai ne ya fashe so se k’arnin ya fitine ni dalilin aman kenan if not ba abi-” bata k’are maganar ba ta fad’a jikinsa dan wani jiri datake ji yana d’ibanta ko a zaunen ma. “Baby hold me kaji?” ta buk’ace sa. Hannayensa ya zagaye a bayanta “I’m here karki damu” bayanta ya riga shafawa up-to-down na zuwa wani lokaci. “Flower” ya kira sunanta shiru yana leqa fuskarta yaga tayi bacci mamaki ne sosai ya rufesa Ipad nasa ya jawo ya sake daidaita kanta a k’irjinsa sannan shikuma ya kishingid’a jikin kujerar. Nan ya shiga google yasoma browsing abubuwan dake jawo yawan bacci dakuma amai abubuwa da dama ne suka fiffito masa wanda one by one yake bi yana karantawa dayazo kan wani point seya tsaya yana nazari sekuma ya dawo da kallonsa kan Fannah “it might be true ban tab’a neman Flower tak’i ba se d’azu itan da sometimes ma take nema da kanta, ga wani kasalan da takeji dashi 2 days, ga baccin asara dakuma amai. Flower are you pregnant?” Ya tambayeta chan ciki-ciki. “Kai anya? Na kusan zama DADDY kenan?! Flower!” yayi whispering a kunnenta “na’am” ta amsa. “Please Baby barin d’an kwanta kad’an wallahi I’m weak.” “Kiji nace when last kika ga period naki?” “Baby meya kawo maganan period d’ina kuma anan? Dan Allah barni in kwanta” matso rigarsa tasakeyi a hannunta tare da sake daidaita kanta kan k’irjinsa ta cigaba da baccinta. Duk wannan magana da take kuma idanunta a rufe suke. Jijjik’ata yayi seda ta mik’e ta zauna. “Ohhh! Habeebi meneh?” Ta k’arisa maganan tana k’ok’arin zama, idanunta da take ta k’ok’arin bud’esu kuwa se kafuwa suke. “Good kinga period naki watan nan?” “Mesa kakeson sani?” “Flower mesa kike rashin ji ne waikam? Two days se misbehaving kike kode shima yana cikin symptoms d’inne?” Ya tambayi kansa kasancewar tana kusa dashi yasa tajisa. “Symptoms name Habeebi?” “Bansani ba ki amsani first.” “Babu bezo ba amman nasan sooner or later zezo saboda atimes haka yake min, se yayi skipping 4-5 days.” “Kin tabbata?” “Eh mana shikenan? Zan iya komawa baccin?” “A’a kitchen d’infa? Wa zeyi mopping wajen da egg d’in ya fashe?” Fuska ta maraice “Baby wallahi k’arnin amai yake sani kuma ma banjin inada k’arfin mopping inaji na ba k’arfi ko kad’an ji nake kamar nayi aikin d’aga block please kabari gobe in masu aiki suka zo senayi kaji Baby?” “Another symptom” yace da kanshi nanma ta jisa. “Wai wani symptom Baby?” “Flower look at me” nan ta maido da kallonta a agaresa. “Don’t you think you are pregnant? Mun kusan zamowa Daddy and Mammy?” Cike da rashi yarda tayi maganan, “Kana nufin wai ciki ne dani?” Ta k’are maganar hannunta kan flat cikinta, hannun sa shima yabi ya aza akan nata dake cikinta “sosai ma kuwa Flower karanta nan kiga” nan ya miqa mata Ipad d’in data gama karantawa kuma setaga almost all yadda take feeling haka aka yita bayani ciki toh ko dagaske ne tana da ciki? Ta kusa zama Uwa kenan itama? “Flower what do you think?” maganarsa neya tsamota daga tunanin da takeyi. “I think yes!” Ta fad’a delighted cike da jin dad’i. “I think so too Habeebi I might be pregnant!” “Yes Flower” hannunta yacire daga cikin nata ya sa nasa kai “we have a baby in here.” Hannunsa ta cire ta aza nata kan cikin “tsaya let me feel it.” “No!” ya zare hannunta ya d’aura nasa kai “ki tsaya inyi feeling first bani ne babba ba?” Nan ta sake cire hannunsa “sekaci girma ai kabarni inyi feeling nasa first, nida ciki na abeg d’aga min hannunka.” “Cikinki ko cikinmu?” Haka suka tayi Anas yak’i cin girma yabar Fannah ta fara feeling Babyn nasu kamar yadda itama tak’i cin k’ank’anta. Seda tagaji ganin Anas baida niyan barinta kawai ta barsa yafara feeling hannunsa yafi minti biyu kan cikinta yak’i d’agawa. “Toh ai haka yayi nima let me feel my Baby.” “Flower Allah kika sake cewa Babynki zamu b’ata. Its our Baby.” “Toh our Baby, kasan meh?” Kai ya kad’a mata. Matso da kansa tayi ta rad’a masa wani abu a kunne. “LOL yes I am Flower, so gobe zamuje asibiti?” “Muje muyi meh kuma Habeebi?” “Muje mu tabbatar da cikin naki mana ayi scanning.” “Shine se munje asibiti? “Yes Flower.” “A’a nikam barinje ba zan saya pregnancy test strip in gwada da kaina a gida ba se munje asibiti ba.” “I know Flower but still yakamata muje kinga zamu san how many weeks ne pregancy nakin and za’a bamu shawarwari dayawa kinga this our first time.” “Nikam gaskia Baby kayan kunyan nan badani ba.” “Wai wani kayan kunya Flower? Ciki abin farin cikin ne kuma abin kunya yanzu?” “Eh mana Baby kowa de yasan ta yadda ake samun cikin nan ni kawai mu rufa wa kanmu asiri kar muje.” Dariya sosai ya tsaya yanayi “Flower you are too much to meh? Suma haka akayi aka haifesu kowa ma haka akayi aka haifesa I see nothing wrong with that.” “Nide ba ‘yar iska bace barin jeba” tana kaiwa nan ta mik’e aiko seconds talatin batayi ba ta fad’a kujeran ta dan jiri da sauri ya taro ta. “Flower fa dole muje asibiti final decision.” Chak ya d’agata yakaita d’aki black tea ya had’o mata bayan tasha yajasu Sallah wanda rabinsa ma a zaune Fannah tayi dan jiri. Washegari... Asuban fari Anas ya tashi bayan yayi alwala ya taimakawa Fannah ma tayi suna idar da Sallah suka koma suka kwanta sede unlike jiya yau jikin nata da zafi amman ba chan chan ba gudun karwani abu yasamu lafiyan babynsu yasa Anas yabata paracetamol kad’ai tasha cikin ikon Allah yamata aiki kuwa, k’arfe shida ta tashi as always taje ta had’a musu breakfast hancinta toshe da hanky dan gudun k’arnin fashasshen k’wan bayan tagama ta jera dining sannan taje ta tada Anas. “Baby katashi kayi wanka kaji?” Bayan ya bud’e idanunsa ya k’are mata kallo bakomai ne d’auke a idanunta ba banda kasala. “Flower kinyi wani aiki neh?” “Breakfast kawai na shirya mana se ruwan wankan ka tashi kashiga.” “Flower why? Daga yau banason ki sake yin wani aiki kinji? Its not fit for your condition.” “Baby bamu ma tabbata ko cikin ne dani bafa tashi kayi wanka” towel nasa ta mik’a masa nan danan yayi wanka yashirya sannan yafito suka fara breakfast kad’an daga cikin fried egg d’in Fannah taci ya sata amai aguje ta ruga bathroom shima Anas yabi bayanta yana shafa mata baya, amai ta rigayi abin tausayi, data gama ya tayata kimtsa kanta suka fito tana manne a jikinsa dan jiri. “Flower bara muje asibiti ba?” Kai kawai ta iya ta gyad‘a mai. “Sorry kinji? I can’t leave you alone like this.” “Me kake nufi Baby?” “Nafasa zuwa office I will take care of you.” “Common Habeebi karka damu I will be fine je ka gama breakfast naka kaji? I love you” peck ta manna masa a kumatu da k’yar tare da komawa ta lume cikin kujeran. “Flower in kaiki d’aki?” “Nanma yayi kayi sauri.” Mik’ewa yayi yaje d’aki yafito da blanket bayan ya kunna AC ya lullub’eta dashi sannan yayi pecking nata a goshi. Dining ya koma yayi rushing ya gama breakfast nasa, wayarsa ya d’aga dan kiran Kacallah ya fad’a mai bazasa office ba yau yaga Kachallan na kiransa. Bayan yayi picking Kacallah ya gaishesa “Sir na kira ne dama in tuna maka meeting da zakuyi da board of directors na F&C Enterprises regarding 2% shares nasu da zasu siyar mana dakuma investing da zamuyi.” Kallon sa ya miyar kan Fannah ji yayi bare iya barin ta haka ba dan kuwa batada lafiya. “Hello Sir?” Cewar Kacallah dan jin shiru. “Kacallah baraka iya presenting d’ina ba? My wife is sick I’m afraid barin iya barinta ita kad’ai ba.” “Ayya my regards please kuma Allah ya sawaqa unfortunately I can’t Sir dole se kai in ba haka ba barasu siyar mana ba kuma kasan we can’t lose this oppurtunity please Sir.” “I will see to it” nan yayi hanging. Wajen Fannah ya nufa ya zauna a gefenta. “Flower” ya kira sunanta. “Na’am” ta amsa a kasalance. “How are you feeling? Ki fad’a min tsakanin ki da Allah karkimin k’arya.” “Baby kasala ne kawai sekuma zuciya na dake yawan tashi thats all.” “Bakiya feeling feverish? (zazzab’i)” “Kad’an ba.” Ta amsa shi. “I can’t leave you like this zanyi canceling meeting d’in.” “Wani meeting Baby? Bade na F&C Enterprises ba!” “Shi Flower barin iya barin ki haka ba.” Juyowa tayi tana fuskantanshi “please kar kayi haka kaji? Karkayi losing wannan oppurtunity, karka damu dani in nasamu na kwanta I will be fit.” “Kinsan fa ba ke kad’aice ba yanzu akwai little one namu.” Wahallalen murmushi ta saki “don’t worry I’ll take care of it for its Daddy, off you go kaji? Best wishes I love you.” “I love you too Flower” yayi maganan yana gyara mata blanket d’in “take care of yourselves for me ko in kira Afrah tazo ta tayaki zama?” “A’a karka damu I can manage.” “Sure Flower?” “Yes Baby.” Brushing light kiss ya mata a baki “I love you okay? Ki kirani in wani abu na daminki kinji?” “Yes Sir!” ta masa murmushi har ya miqe sekuma ya dawo ya zauna “kinga banyi greeting baby naba” hannunsa yasa cikin kayanta yashafa kan cikin. “Good morning my baby your Daddy loves you so much.” Murmushi kad’an ta saki dukda kuwa yabata dariya sosai. “Habeebi nothing is certain yet fah kar muta hoping muzo kuma abu yayi turning out in a different way.” “I still don’t care, I love you bye.” Jakansa ya d’aga ya fice a yayinda ta rufe idanunta tare da aza hannunta kan cikinta tana shafawa a hankali da murmusi fal kwance a fuskarta. ** Sosai d’an baccin da tayi ya taimaka mata dan kuwa ta samu k’arfin jiki takuma warware, d’aya daga cikin masu aikin nata ta aika chemist ta siyo mata strips guda biyu, bayan ta kawo mata tashiga toilet tayi carrying out test d’in se bugawa zuciyarta ke bayan daya gama reading ta bud’e ido d’aya da rabi ta leqa tana ganin ‘P’ ta bud’e duka nan ta karanta ”POSITIVE” ta karance. Tsalle ta daka “yeyyy!!! I’m pregnant!! I’m pregnant!!” A gurguje tafito daga bayin ta d‘au wayanta ta kira Anas sede har ya yanke be d’aga ba kasancewar yana a meeting 2 missed calls tamasa ganin be d’auka ba tamiyar da wayar ta ajiye. 1:50PM lokacin da Anas yafito daga meeting d’in ya duba wayarsa yaga missed call na Flower ba tare da b’ata lokaci ba ya kirata back daidai lokacin da take fitowa daga wanka kenan a dole tayi zuciya tak’i picking se a karo na biyu ta d’aga nan ma tak’i cewa komai “Halo Flower?”,nanma shiru. “Flower don’t be mad I was in a meeting kinji? Yi hak’uri kimin magana.” Se anan ta sauk’o. “Ya meeting d’in?” “Alhamdulillah yanzu muka fito, ya jikin ki?” “Da sauk’i me kakeso kachi yau?” “Babu karki dafa komai zan saya mana lunch banason kina wani aiki yanzu.” “Hunmm! As you say Mr. Fauzi yau inada suprise maka.” “Really Flower? I hope ba irin suprise na miyan kukan da kika min ranan bane?” Dariya ta saki “ko kad’an Habeebi” “Toh tell me meh suprise d’in?”,Baki ta cuno. “Suprise nefa Habeebi ai ba’a fad’a seka dawon de, k’arfe nawa zaka shigo?” Rolex agogon hannunsa ya duba “erm... Zuwa 3 haka.” “Okay toh sekazo.” “Wait.. Wait fad’amin kinji meh suprise d’in? Ko hint ne kibani.” “O’o seka dawo I love you!” Bata jira ya sake magana ba ta katse wayar tana murmushi shima murmushin yake. Had’ad’d’iyar kwalya ta tsara tasa wata had’ad’d’iyar light purple lace da torches na fari da dark purple d’inkin peplum da skirt. Bayan nan ta kafa d’aurin network nata me kyau sannan ta feffeshe da turarukan ta meh yima Anas dad’i. Game ta zauna tata bugawa chan takira gida suka gaggaisa. 3:15PM nayi ta b’allo sabon strip ta sake carrying out test d’in ta ajiye 3:20PM Anas ya dawo gida k’ofa na bud’uwa Fannah ta bayyana a bayansa kallonta yake wane a mafarki sekace ba itace ke kwance ba lafiya ba d’azu. Another symptom yace a ransa morning sickness. Bayan ya shigo ya miyar da k’ofan sannan ya juyo yana kallonta har a yanzu tunanin wani kalma ze furta wanda ze dace da kyan da Fannah tayi yake. “Flower you are looking extra ordinary spectacular, you’re looking amazing.” “Thank you Sweetheart” ta fad’a tana mai murmushi matsowa kusa dashi tayi seda ta rufe gap dake tsakaninsu nan k’amshin jikinta me haukatasa ya buga masa hanci besan alokacin daya fara bin wuyanta yana shunshunawa ba. Hannu tasa ta shuresa da k’yar “Baby waittyy manaaa” bata bari ya sake komawa jikinta ba ta mik’a masa strip dake hannunta. “What is this Flower?” Ya tambayeta. “Pregnancy test strip.” “Kina nufin har kinyi carrying out test d’in without me?” “Yes Baby I’m sorry duba kaga result d’in.” Da hanzari ya maida kallonsa kan bar d’in “POSITIVE” yaga rubuce kai. © MIEMIEBEE

Share:

11 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).