TANA TARE DANI 72.....
TANA TARE DA NI... PAGE 72 BY MIEMIEBEE Wani irin wawan mutuwa jikinta yayi ga kuma wani erin tausayin Anas daya kamata lokaci guda mara misantuwa. Kasa ce masa koda uffan tayi, alokaci d’aya k’wak’walwarta ta toshe, ta rasa me zatayi ta zauna ne kokuwa ta tafi? Kalamunsa duk sunbi sun kamata batason tafiyarta ya kuma canza mata shi ya koma gurb’arcacciyar rayuwarsa na da. In hakan ta faru barata tab’a iya yafe wa kanta ba. Hawayen da suke gangarowa kan kumatunta se k’aruwa suke a yayinda zuciyarta ke k’ona in ta tuna ta auri mutumin daya jefa mata rayuwa cikin k’unci, worst part d’inkuwa shine irin zazzafar soyayyar da take masa wanda bata zaton ta tab’a yima wani mahaluk’i ba, soyayyar da bata tsammanin akoi takwabin daze iya kashesa tasani ba na mijin da ze zauna da ita da mutunci kaman yadda Anas zeyi aduk fad’in duniya tunda gashi da gaskia ya bayyana ma ya nuna yana sonta kuma ze cigaba da zama da ita still kuma koba dan haka bama tunba yau ba yake bata labarin yarinyan cewa duk lokacin da ya sameta zeyi all he can ya yafe mata amman ita batajin zata iya cigaba da zama dashi saboda abin da zafi kuma da ciwo. Sun d’au tsawon lokaci suna ahaka sam Anas yakasa sake ta k’ak’am ya matse ta jikinsa wane za’a k’wace masa ita, itako takasa hugging nasa back tana manne kawai a jikinsa se chan a hankali ta zagaye hannayenta bibbiyu a bayansa duk suna feeling turaren jikin junansu me tafiyar masu da imani, hugging juna suke cike da so da k’auna kowannen su na fatan ina ma ache wannan moment will last forever. Cikin sautin kuka ta kira sunansa. “Anas.” Kamar me jira takirasa ya amsa “na’am Fannah.” “Anas promise me baraka sake tab’a giya ba.” Bayanta yake shafawa, “Fannah anything for you I’ve promised you before and zan sake yau barin sake tab’a giya ba in shaa Allah I promise please don’t go.” “Promise me baraka sake firing workers naka ba” “Flower barin k’ara ba I promise.” “Promise me baraka sake aikata wani aikin haramun ba” “Flower I promise.” nanma yace. “Thank you” ta fad’a a hankali. “Does this mean zaki zauna dani? Baraki tafi kibarni ba?” Da k’yar ta iya ta raba jikinta da nasa ta d’ago jajayen idanunta da suke tsiyayar da hawaye har ayanzu ta kafasu kan fuskar Anas sosai shima idanun nasa suka kad’a hannu yasa ya share mata hawayen ‘yar murmushi tasaki masa sakamakon hakan wanda yasa yaji sanyi sosai aransa. “Fannah I love you so much.” Hannun sa ta sauk’e daga fuskarta a hankali tana murzawa sannan ta d’au d’ayan hannunta ta aza a nasa fuskar. “I love you too, I love you so much Anas.” Ta miqa kai tayi pecking nasa a kumatu. “But I have to leave” kamar a kyaftawan ido taja jakarta ta juya. Sauri sauri take ta bud’e k’ofar ta fita. “Fannah!” Ya kira sunanta da k’arfi cike da tashin hankali tare da shawo gabanta. “Fannah you musn’t go dan Allah ki zauna please.” Hawaye ya ke sosai kamar yadda itama take sam batason tafiyar dan de batada wata mafita ce a tunaninta. “Anas dan Allah karka hanani tafiya inhar kanaso na kamar yadda kake fad’a let me go please.” ta sanar dashi tana k’ok’arin shanye kukanta tare da bin gefensa, hijabinta ya riqo “I can’t let you go Fannah barin iya rayuwa ba keba dan Allah kiyi hak’uri niko da barakina min magana ba but please don’t go stay with me.” K’arfin hali tayi ta fisge hijabin nata dayayi yunk’urin sake tab’ata ta tsawata masa “DON’T TOUCH ME ANAS! DON’T!” mutuwan tsaye yayi a wajen yana hawaye kamar ba gobe yana kallonta tana jan akwatinta har ta fice masa daga kallo. “Fannahhhhh pleasssseeeeeee don’t gooooo...” yana sauk’a k’asa yayi wannan magana kuka yake kamar d’an yaro abin tausayi. Tana fita tasamu adaidaita sahu ta shiga ciki ta tsaya kuka kasa koda fad’a masa inda takeso ya kaita tayi tafi minti ishirin zaune ciki tana kuka sannan da k’yar ta sanar dashi a sannu sannu yakaita har gaban gidansu d’ari biyar ta dank’a masa ba tare da ta jira amshan chanjinta ba. Tana shiga ta tarar da Mami da Afrah da alama sun dawo daga rakiya ne. Mamaki ne ya mamaye fuskarsu duka ganin Fannah da akwati ba saqe-saqen da basuyi ba daga bisani Mami ta nufa bakin k’ofar ta rik’o Fannah ganin jiri nason d’ibanta, Afrah che ta amshi akwatin nata sukayi da ita d’aki. Har a yanzu ba wacce ta iya tambayar Fannah meke tafe da ita duk hankalinsu yabi yanayin datake ciki. Wani erin nishi take da inta ja d’aya ciki kamar na mutane goma sosai Mami ta tsorata ba kamar Afrah dake kuka already. Hijabin jikinta aka tub’e mata tare da k’ure fankan d’akin. Se anan bakin Mami ya bud’u “Habibti kukan ya isa dan Allah ya isa haka kinji? Yi shiru” ta sanar da ita tana jijjik’ata da k’yar kukan ya lafa sekuma ciwon kai bayan tasha magani ta d’an dawo hayyacinta Mami ta zaunar da ita. “Fannah meke faruwa? Ya na ganki haka? Kimin magana Habibti.” Wani sabon kukan taji ya faso mata, kwantar da ita Mami tayi a jiki tana bubbuga bayanta “fad’amin kinji?” Ba yadda Mami batai da ita ba amman Fannah tak’i tanka ta se kuka ba sauti da take tayi, tabari akira Anas ma tak’i duk tasasu cikin rud’ani da kuma san jin meya faru tsakaninta da Anas ga dukan alamu ba lafiya ba. Se chan Mami ta tura Afrah waje ta zaunar da Fannah tata yi mata magana cikin wani irin salo tana rok’arta. Se anan bakin Fannah ya bud’u “Mami ina Baba?” abinda ta soma tambaya kenan. “Yayi tafiya zuwa Bama Habibti kinason masa magana ne?” Kai ta kad’a “Mami banason Baba ya sani dan Allah kiyi min alk’awari baraki fad’a masa ba kosu Afrah ma baraki sanar dasu ba kuma baraki kira dangin Anas ki sanar dasu ba suma wannan abu da nakeson sanar dake yazama tsakani na dake ne kawai banason wani ya sani” ta k’are maganar hawaye na cikowa a idanta. “Fannah na d’au alqawarin dukda bansan me kikeson fad’a min ba amman na d’auka barin sanar da kowa ba. Meya faru?” Hawaye na tsiyaya a idanunta tace, “Mami shine mutumin, shine...” sekuma ta fashe da kuka. Cike da rashin fahimta Mami ta d’agota daga jikinta “wani mutumi Fannah kuma waye mutumin?” “Mami shi, shine mutumin wallahi shine.” “Fannah ki kwantar da hankalinki ki sanar dani gwara-gwara” tasa hannu ta share mata hawayen nata. “Anas, Anas ne Mami shi ne mutumin.” Kai Mami take gyad’awa nufin tasoma fahimta. “Anas ne wani mutumi Habibti?” “Shine mutumin mafarki na, shine wanda yayi raping d’ina a Bama Mami shine silar komai” ta fashe dawani irin matsanancin kuka. Salatin Mami kawai ke tashi a d’akin kwanto da Fannah tayi a jikinta tana bubbuga bayanta tana fad’a mata dad’d’un kalamu sam takasa yarda da abinda takeji. Anas? Yanzu Anas dama shi yama ‘yarta kaca-kaca haka? Shi ya lalata wa Fannar ta rayuwa sannan kuma yazo ya aureta yanzu ya sako ta kenan komeh? Gaskia Anas yacika butulu. Seda ta tabbata kukan Fannah ya d’an lafu ta d’agota daga jikin nata. Cikin wani erin salo cike da tausayi ta kuma kwantar da ita a jikin nata tana bubbuga bayanta itama kukan taji na k’ok’arin fin k’arfin ta inta tuna kalar wahalar da Fannah tasha shekaru bakwai da suka wuce (masu karatu kuka lura zaku ga d’ayan wajen nasa 5 yrs mistake ne) yadda suka tsinceta kwance a walaqance. Kukan Fannah ne ya tsananta da k’yar tasamu tad’an rage kukan. Cike da tausayi Mami ta tambayeta “Fannah kin tabbata da hakan kuwa? Taya ma hakan ta faru? Had’uwanku da shi Anas d’in tun yaushe ace baki ganesa ba be gane kiba se yanzu? Anya kuwa Fannah ba b’atan kai kikayi ba? Ace yadda Anas yake da mutunci da hankali gakuma daga gida me mutunci yafito ace har yasan yayi raping mace? Habibiti anya kuwa?” “Mami wallahi shine...” Nan ta labarta wa Mami kap abinda ta karanta cikin diary’n Anas bata bar komai ba harda labarin Ummimi komai ta kwashe tabawa Mami dasu shaye-shayen da Anas yakeyi wanda bayayi yanzu sam bata bar komai ba. Mamaki ne yacika Mami sosai takasa koda furta ‘A’ duk wani haushi da takaicin datake ma Anas kuma gabad’aya taji ya koma kan Ummimi itace silar komai dukda kuwa shima Anas da nasa laifin amman Ummimi ce me babban laifi anan. Wace erin uwa ce? Ance Uwa Uwa ce amman ba’a sa jerin kalan su Ummimin Anas ciki. Talauci hauka ne? Taya zata tafi tabar ‘ya‘yan data tsuguna ta haifa taya zata k’yamaci abunda yafito daga jikinta? Aiga irin abinda ya haifo nan tasa d’anta yata aikata haramun ko kad’an bata ga laifin Anas ba laifin sa data gani na k’in tawakalli da qaddara, nak’in accepting faith nasa shine kad’ai laifin daya tafka ita bama wannan ba yanzu nan tabar sak’e-sak’en zucin da take. “Fannah yanzu ya kenan? Sako ki Anas yayi bayan da gaskiya ya bayyana? Shi ya koreki? Bayan shi ya rabaki da budurcinki ya koro ki yanzu? Kuma kice kar in sanar da iyayensa abinda yayi? Wallahi a’a Fannah inke bakisan ciwon kanki ba ni nasani ina wayata.” Hannunta Fannah ta riqo “Mami calm down Anas bashi ya koreni ba hasali ma yanzu haka nasan kuka yake saboda yana cikin hakan nafito na barsa.” Komawa tayi ta zauna “ban fahimce kiba Fannah.” “Mami ni na k’are zamana da Anas yak’i bani takarda na shiyasa nadawo hakan.” Mamaki ne kwance a fuskar Mami. “Kinsan ban fahimce kiba har yanzu” abinda ta iya cewa kenan. Nan Fannah ta kwashe labarin komai tabata. “Haba Habibti! Taya zaki tafka sokanci haka? Kina ganin akwai d’a na mijin da ze rik’e ki da mutunci kaman yadda Anas zeyi ne? Wallahi babu. Tunda yayi nadama Fannah gakuma dalilin dayasa faruwan hakan ai seki yi hak’uri ki yafe masa nasan da zafi amman hak’uri zakiyi. Ni wallahi na d’au ma ko shi ya koroki dan shine babban tashin hankali, Anas na sonki so na hak’ik’a ba kowa neba ze iya yin abinda yayi ko baki tab’ajin inda za’a kama yaro nama d’iya fyad’e amman ya bushar da ido yace ba shine ba kuma ba yadda aka iya haka za’a barsa amman Anas fah? Ya yarda shi ya miki kuma ahakan kin still yakeson ki kiyi tunani Habibti.” Ta k’are maganar tare da riqo hannun Fannah cikin nata. Hawaye take sosai “Mami bawai yafiyan bane barin iya ba tsab zan yafe masa, ni nama yafe masa komu muna ma Allah laifi kuma ya yafe mana muddin mun tuba kamar yadda Anas yayi na yafe masa har abada kuma zan sanar dashi amman Mami barin iya zama dashi ba again, Mami abinda yamin da ciwo.” Kwantar da ita Mami takuma yi ajikinta. “Shhhh! na gane halin da kike ciki Habibti is not easy you need some space, da zafi sosai ace bada sanin kiba kin auri wanda ya miki tabargaza da rayuwa amman Habibti yariga ya wuce lets face the future ko ba haka ba?” Kai ta gyad’a a hankali. “Good kuma kema nasan kinason Anas ko bahaka ba?” Nanma kai ta gyad’a. “Toh alhamdulillah zaki cigaba da zama ana har nan da lokacin da kikejin zaki iya komawa d’akin ki shikuma Anas zan masa bayani.” Kai ta d’ago a raunane “Mami banason sake-” katseta Mami tayi da wuri ta hanyan aza yatsanta kan bakin ta tana kad’a mata kai. “Karkice haka Habibti karki kuskura kinji? Dole zaki koma gidan mijinki d’akinki tunda be sallameki ba kuma tambayan takarda haramun ne kema kinsani tsinuwa ake gaggautawa duk macen datayi hakan, ki hak’uri Fannah nasan yadda kikeji amman hak’uri yazama dole kinada nan da sati biyu ki huta hankalinki ya kwanta kafin Babanku ya dawo, kinsan muddin yaganki anan ze tambaya dalili, ko kinason yagano Anas ne yayi raping naki?” Da sauri ta kad’a kai. “Masha Allah kinga sekiyi hak’uri Anas nasonki Fannah godiya yakamata kiyi wa Allah ki tuna da irin walaqancin da Farouq da Ya Khaleel suke miki ada dakuma gori acewarsu ba d’a na mijin da ze tab’a aminta ya aureki karkiyi ma Anas haka Fannah, abinda ya miki ya riga ya wuce hak’uri zakiyi wannan shine jarabawarki a rayuwa kinji? Accept it Mamana.” Kai ta gyad’a a hankali badan tanaso ba. Mik’ewan Mami yayi daidai da shigowar Afrah d’akin a gurguje. “Ya haka?” Mami ta tambayeta. “Mami Ya Anas ne yazo” ta fad’a tana haqi “kuma.. Kuma.. Mami kuka yakeyi wallahi Ya Anas yazo yana kuka.” “Subhanallahi to kekuma me haka? Sekace kinyi gamo da aljan.” Kukan Fannah ne ya katse Mami daga magana. “Mami wai meke faruwa?” Cewar Afrah bayan ta kalli Fannah. “Babu kifita ina zuwa” badan tanaso ba tafice. “Fannah wai baraki bar kukan nan ba? Ko sena sa kinbi Anas kukoma tare?” Kai kawai ta girgiza mata “taso muje mu samesa.” “Mami banaso dan Allah kije ke kad’ai dan Allah.” Ba tare da ta saurareta ba taja hannunta tare da dank’a mata hijabinta “sa!” ta buk’aceta a tsawace. Da shegen tsoronta batasan lokacin da tasa suka fito ba hannunta na rik’e cikin na Mami. Zaune kan tabarman da Afrah ta shimfid’a masa suka tarar dashi ya had’a uwa uba tagumi kamar wanda yayi ciwon amai da gudawa ya zube arana d’aya tsantsan tashin hankali kawai, ko noticing su Mamin ma beyi ba tsabagen yadda ya zurfafa cikin tunani seda ya jiyo muryar Mami tana kashe wa Fannah warning hankalinsa ya dawo a garesa. “Ya isa haka!” tace. A raunane ya d’ago jajayen idanunsa ya azasu kansu Fannah. Zamansa ya daidaita ayayinda suka k’ariso kan taburman suka zauna a nitse, Fannah na a lab’e bayan Mami ko d’ago kai ta kallesa bataiba dukda jin idanunsa da take akanta. K’ok’arin dakatar da hawayen nasa yake amman ya kasa Afrah dake lab’e jikin k’ofa Mami ta umarceta da ta fice wajen gida kuma koda Aiman ta dawo karta barta tashigo se in sun gama maganan da zasuyi ba gardama ta fice. A sannu Mami ta dawo da kallonta kan Anas tana ganin yadda yake hawaye kamar ba gobe kallonta ta kewayo kan Fannah itama same story sede ma kamar Anas yafita yin kukan. Daga bisani Anas ya soma magana cikin sautin kuka cike da nadama. “Mami I’m sorry dan Allah kiyi hak’uri keda Fannah daduk wanin danayi hurting sanadin abinda na ma Fannah kuyi hak’uri dan Allah I’m truely sorry.” Sam yi tayi kamar batada labari saboda so take ta tabbatar da ko eh dagaske Anas yake ya tuba. “Wani abu kenan Anas? Meya faru? Kai kuka Fannah kuka ku fahimtar dani meke faruwa nayi nayi Fannah ta sanar dani amman taqi.” Alokaci d’aya Fannah ta d’ago kai tana kallon Mami fuska d’auke da tambaya amman kuma se tayi shiru. Idanunta na had’uwa da na Anas tayi saurin sadda kanta. “Mami kina nufin Fannah bata fad’a miki mena mata ba?” ya tambaya cikin dashasshiyar murya cike da rashin yarda da abinda Mami ta fad’a mai. Kamar ya Fannah bata sanar da ita abinda ya faru tsakaninsu ba??? “Eh Anas nide na ganta da akwati gakuma kukan datazo tana tayi shin meya faru? Sakinta kayi neh?” “Mami barin tab’a sakin Fannah ba har abada barin tab’a iya rubuta mata takardan saki ba, ina matuk’ar son Fannah fiye da yadda nakeson kaina...” Sekuma yayi shiru yana tunanin koya sanar da Mami abinda ya had’asa da Fannah ko a’a. But what if Mami tak’i yarda da tuban da yayi kamar yadda Fannah tayi kuma fah? What if ta tilasta sa seya saki Flowersa fah? No bare iya ba, he will never let that happen on the otherside kuma yanason yayi clearing komai tsakaninsu ko halan inyayi hakan Mami taji k’ansa tabarsa da matarsa. Tunanin wani ra’ayi d’aya zebi yake. Shirunsa yabawa Mami daman magana “Anas kayi shiru” dankuwa ta riga ta yanke hukuncin cewa inhar Anas bare iya confessing laifin daya aikata ba to be tuba dagaske kamar yadda Fannah ta fad’a mata ba inkuwa yayi toh Fannah is his! ina fatan each and every fan tayi sallah lafiya, Allah maimaita mana Ameen, love you loads © MIEMIEBEE
Tnk
ReplyDelete