Shakka babu, a wannan zamani
'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da
rashin kwanciyar hankali, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma,
an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani, kafin a yi auren. Ga wasu shawarwari
40 wadanda idan matan suka yi la'akari da amfani da su da yardar ALLAH za'a
samu kyautatuwar zaman aure.
1. Aurenki ya zama domin neman
yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2. Kada ki zama mai kwadayi
wajen zaben mijin Aure.
3. Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta
hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da
dangantakarsa.
4. Ki zama mai hakuri da
halayyar mijinki.
5. Ki zama mai matukar biyayya
ga mijinki.
6. Ki zama kin iya barkwancin
magana wajen baiwa mijinki dariya.
7. Kada ki zama mai rainuwa a
cikin duk abinda mijinki ya baki.
8. Ki dinga wanke bakinki da
safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.
9. ki zama mai tsaftar jikinki,
gidanki, abincinki, da sauransu.
10.Ki dinga girmama Iyayan
mijinki da 'yan uwansa da abokansa.
11.Kada ki zama mai satar kayan
mijinki.
12.Kada ki zama mai satar fita
unguwa.
13.Ki guji Leke a gidan
mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.
14.Ki dinga godewa mijinki a
cikin abinda ya baki.
15.ki kiyaye abinda mijinki ya
fi so.
16.ki kiyaye abinda mijinki ya
fi sonci da safe, rana, dakuma dare.
17.Ki dinga yabawa mijinki
kwalliyarsa.
18.Ki dinga yawan neman
shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.
19.Kiyi kwalliya ki tsane tsaf
kafin dawowar mijinki.
20.Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki
kafin dawowar mijinki.
21.Kada ki bari mijinki ya dawo
ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.
22.Ki zama mai yawan canza
zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.
23.Kada ki ce mijinki sai ya
saya miki abinda ba shida ikon saye.
24.Lallai ki yi amfani da ilimi
wajen yanke dukkan wani hukunci.
25.Ki yi shiru a duk lokacin da
mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.
26.Kada ki zama Al-mubazzara
mara tattali.
27.Kada ki tara kayan wanki da
yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.
28.Ki kula da yanayin da zai
nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
29.Kada ki ringa baiwa
kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.
30.Idan zaki yiwa mijinki
magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.
31.Idan kika samu sabani da mijinki
ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
32.Ki zama mai tattali a cikin
dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.
33.Kada ki zama mai yin dare
wajan girki.
34.kada ki zama mai yawan fada
da makwabtanki.
35.Kada ki kasance mai yawan
zagi ko Ashariya.
36.Kada ki ringa baiwa Iyayanki
Labarin laifin da mijinki yake miki.
37.Ki zama mai hakuri da juriya
da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
38.Kada ki ringa daga murya
sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.
39.Kada ki ringa baiwa 'yan
uwan mijinki labarin laifukansa.
40.kada ki ci wani abu da
mijinki baya son warinsa misali tafarnuwa.
Allah ya bada iko wajen kamanta da aiki da shawarwarin.
Allah ya bada iko wajen kamanta da aiki da shawarwarin.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.