shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 28 March 2017

Kukan kurciya 27&28 (END)
hausa novels https://mrsbilkisa.blogspot.com 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul)

 Kuyi ha'kuri da jinkirinmu wasu 'yan dalilaine suka kawo haka 🔚 Page2⃣7⃣&2⃣8⃣ ........Arikice Ameeda da ya Muzzaffar suke kallonsa, bindigarsa ya saita sosai akan ya Muzzaffar da Ameeda, hazbinallahu wani'imal wakil kawai suke ambata a zuciyarsu, ya Muzzaffar yay 'karfin halin faďin Sayeed mimuka yimaka? Yaushema kadawo 'kasar??. Cikin sanďa daddy yabiyo ta bayansa ya daki bindigar ta faďi (karku manta daddy babban ďan sandane) mari ya wankama sayeed ya'kara wanka masa wani, tuni sayeed yazube awajen saboda zafin mari, da'kyar momy da Ya Muzzaffar suka ri'keshi saboda sai kaima Sayeed duka yake tako ina. Ya ce, "ku 'kyaleni harni wannan ďan iskan yaron zai shigoma gida da bindiga?, to anufinsa nizai kashe kenan ko iyalina??, Sayeed ya fashe da kuka yana faďin nibanzo danna kashe kowaba dady, kaduba kagani babu bulet cikin bindigar, nazone gareka domin nayi maka godiya nakuma baka ha'kuri akan abinda maciya amana sukai maka. Tuni jikin daddy yayi sanyi da abinda yayma Sayeed, ya kamoshi dakansa yatayar zaune, to amma Sayeed miyasa zaka shigo da bindiga??, yanzu dakasa nayi maka abinda yafi haka aiban 'kyautaba. Murmushi Sayeed yayi karka damu daddy nayi maka uzuri, kobaka aikata komai akainaba 'yan sanda zasuzo su kamani yanzu babu daďewa. Atare suka ce, "yan sanda kuma???........ kafin surufe baki wayar daddy tafara wringing yaďaga tareda sallama, basu san mi akace masaba sungadai ya ajiye wayar. Yadawo da kallonsa ga sayeed, sayeed mika aikatane haka da zafi??, murmushi Sayeed yayi ya ce, "daddy nakafama maciya amana tarihine, na nuna musu kuskurensune, na harbi 'kafafunsu mamane da waďanda sukace su iyayenane, harda ďan iska Naseer. Harbi sayeed miyasa ka aikata haka??. Dady hakane yadace dasu, domin nina sun taka rawar gani wajen lalata min rayuwa nida 'kanina, munaji muna gani Sadiq yazama ri'kakken ďan iska, nikuma kuga yanda rayuwa ta maidani, shaye2 ya lalatani, babu abinda nake aturmrai sai iskanci da shan giya da koken, yafashe da kuka, daddy su mama masifane adoron 'kada, sonaima nafasa kawunansu da bulet suyi mutuwar jakuna abola, amma saina canja shawara na hahharbe musu 'kafafu da hannuwa ta yanda bazasu sake moruwaba, koda wanan ba'kincikin nabarsu zanji sanyi, dan haka dady dan ALLAH ko ankamani karkayi belina kabarni acan na 'kare rayuwata gabaďaya, banaso kokaďan wani yasake taimakona, ya mi'ke dazummar ficewa amma sai ya Muzzaffar ya ri'keshi, haba Sayeed baikamata ka yankema kanka irin wanan hukuncinba.....murmushi Sayeed yayi tareda dafa kafaďar ya Muzzaffar ya ce, karka damu Muzzaffar abinda yadace damai irin halina kenan. Tun farko iyayena sunrigaya sun ruguzamu, sun sayar da rayuwarmu akan kuďi kuďinma daba nasuba, wlhy daza abarni ayanzu saina ida ďauke ragowar Numfashinsu kowa ya huta...ya fisge hannunsa yafice. Basuda za6i face take masa baya, yana fita 'yansanda suka cikuykuyesa, suma su dady mota suka shiga suka bisu. Tuni ankwashi su iya abu zuwa asibiti dan sayeed ya faffasa musu kafafu da hannaye da bulet abun babu 'kyawun gani, sai kuka da dana sani suke, nikam gsky banji tausayinsuba saima ALLAH ya'kara danayimusu. Su daddyma asibitin suka Nufa hankalinsu yatashi daganin 6arnar da Sayeed yayi, (lallai KUKAN KURCIYA JAWABINE, sun raini abunda zai halakasu, sun gina ramin muguntar saka wani, sai duk suka afka batareda sun saniba, ALLAH sarki dady shine yabiya akai musu aikin cire bulet ďin. Bayan kwana biyu daddy yayi ciku2 aka fito da sayeed, saidai kasha Sayeed ya rasu, batareda kowa yasan yanda abun yafaruba, ALLAH sarki gsky bamuso hakaba domindai Sayeed abin tausayine ALLAH ya yafe masa), agidan dady akai masa sutura ananma akai zaman makokinsa, to ALLAH yaji'kan musulmai. BAYAN lafawar komai aka shiga shirin bikin su ya Muzzaffar da Ameeda, lallai naga bikin 'yan gata kam, dan shiri ake bana wasaba. Zuwa sanan an sallami su haj hassana daga asibiti, saidai suduka sun rasa 'kafa da hannu, lallai suna danasani akan 6arnar dasuka aikata, kukakam sunyi harsun rasa hawaye. ALLAH yataimakesu ma haj kaka tahana daddy yakaisu kotu, amma kamar yanda Naseer yay hasashe hakane tafaru, domin kuwa abokan daddy duksun rasa aikinsu, ga haj hassana takar6i takardarta sakinta uku ahannu, komaidai ya lalace musu basuga tsuntsu basuga tarko, su iya abu kam aisunfi kowa asara, domin sun rasa 'ya'yansu duka biyu, Sayeed ya rasu Sadiq kam bama asan inda yakeba saidai gyaran ALLAH. BIKI BUDURI. dahaka dai aka fara shagalin bikin su Ameeda, Naseer yayi kuka sosai na kubcewar Ameeda daga gareshi, har kano Ameeda taje ta gayyato Falmata, wadda itama ayanzu ta yanke shawarar yin aure, harma tafara istibira'i. Bikidai ya kankama don yaune aka ďaura aure, bayyana muku yanda ake shagalinma aii 6ata lokacine ammafa anan kwasar shoki, bakin ango da amarya yaki rufuwa, hakama dady da momy daduk wani masoyinsu, aranar da daddare aka sada amarya da ďakin mijinta ya Muzzaffar. To masha ALLAH komaidai yayi dai dai dominko amarya da ango sun riski rana mai cike da farinci saimuce ALLAH yasanya alkairi. Itamaidai falmata ALLAH ya haďata da abokin ya Muzzafar wato Ahmad kuma sunyanke shawarar yin aure, dan haka dady yahanata komawa kano yari'keta awajensa, idan biki yataho zasuje har Barno wajen mahaifinta. To saimuce ALLAH yasanya alkairi baki ďaya. BAYAN WASU SHEKARU. Mun isa gidansu ameeda domin ziyara, amma sai abubuwa dayawa suka bamu mamaki, domin kuwa mun tarar da ameeda da yara har huďu duk tagwaye, mace da namiji sai maza kuma, abin sai wanda yagani yara 'kyawawa abin sha'awa da birgewa, muna nan zaune saiga falmata itama danata yaran har uku, lallai masha ALLAH aure yayi riba. Saimuce ALLAH yabar zaman tare da 'kaunar juna. A6angaren su iya abu kuwa komai ya lalace, dan tuni malam dauda yasaketa yakoma 'kyauyensu, itakam tana kano tana bara dan tazama gurguwa, hajiya hassana kam ciwon 6arin jikine ya kamata saboda ba'kincikin rashin cimma burinta, to saimuce ALLAH yakara, dama ance idan zaka gina ramin mugunta to saika ginashi gajere dan bakasan mai faďawaba, kuma KUKAN KURCIYA JAWABINE.....😁👌🏻. TAMMAT BI HAMDULLAH. Nan muka kawo 'karshen wanan ďan takai taccen labari namu, ALLAH yabamu ladar abinda mukayi dai2, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana. Muďinnedai naku masu sonku da 'kaynarku. ABBA GANA. & BILYN ABDUL. muna mi'ka ďunbin godiya gareku masoyanmu saboda hakurin bibiyarmu da kukayi, ALLAH yabar 'kauna, saikunjimu asabon littafi mai zuwa. Mungode sosai❤❤❤❤❤😍😍😍 򖀽򖀽򖀽򖀮 Hikayarmu ©2017


---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

1 comment:

  1. Thank you very much for sharing information that will be much helpful for making coursework my effective.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).