shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 13 March 2017

Kukan kurciya 17&18🐾KUKAN KURCIYA.......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Assalamu alaikum. muna mi'ko gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyanmu aduk inda kuke,, kuyi ha'kuri dabaku pages ďai2 damukeyi kullum, littafin namu gajeren labarine,, insha ALLAHU muna gab da kammalashi,, mungode da 'kaunarku garemu,,, luv u oll😍😍😍😘😘. Page1⃣7⃣&1⃣8⃣ ..........jikinta sai rawa yakeyi cikin kuka take bashi ha'kuri dan bataji daďin yanda tayi masa 'karyaba, kayi ha'kuri yayana wlhy badan banida gskya yasa na 6oyemaka sirrinaba akwai wasu dalilai masu yawa,, amma ina ro'konka da ka gafar ceni, insha ALLAHU wanan shine nafarko na 'karshe dazan yimaka 'karya akan abinda yashafi rayuwata, ta ďago tana kallonsa sai taga shikuma hankalinsa yana kan babanta dake tsaye a'kofar gida yana cin goro. yayana!! tafaďa cikin sanyin murya, ahankali yajuyo yana kallonta cikin in ina ya ce, "beauty waye wancan??, babanane tafaďa cikin 'kwarin gwuywa. Tafďijan yafaďa azuciyarsa, Ameeda ta ce, "koshima kasanshi ne??, A'a yafaďa a ta'kaice amma idanunsa nacigaba da kallon malam dauda. Ameeda tabuďe motar tafice tana faďin to sai mun haďu gobe ko?, okey karki damu kijirani agida insha ALLAHU 'kar fe biyu zanzo miki da abu uwan mamaki, kinsan masu iya magana sunacewa KUKAN KURCIYA JAWABINE.......Ameeda ta'karasa da faďin "mai hankaline yake ganewa yayana, murmushi yayi tareda mi'ka mata dubu biyar ya ce, "sai kinjini, okey bye tafaďa tana ďaga masa hannu. Koda tashige gida yadaďe zaune amota yana karema malam dauda kallo, daga baya yafice yabar anguwar, gida yaje yay wanka yanufi filin jirgi sai abuja. Da wuri ya isa yauma mutanen gidan sunyi farincikin zuwansa, bayan yaci abinci ya huta, suka haďu afalon daddy, daddy ya ce, "Muzzaffar kace mana a kwai magana amma munjika shiru. Muzzaffar ya murmusa, tabbas daddy akwai magana, dan yau na'kara gano abin mamaki kamar yanda na faďa maka awaya, inaso ka shirya mana tafiya kano muduka harda hajiya babba. Bangane mikake faďaba Muzzaffar???, daddy zaka gane amma sai goben.........momy ta katse musu zancen da faďin a'a muje mu kaďai idan komai ya bayyana sai azo har inda take, kasan halinta sarai, kuma batason zuwa kano da kowa. Gsky ne daddy yafaďa, yanzu saimu kwana cikin shirin zuwa kano insha ALLAH. Washegari sukai 'kaura zuwa kano, dayake jirgi sukabi har saida suka huta agidan muzzaffar, kamar yanda yay mata al'kawari 'karfe biyu suka iso anguwar dan masallataima sunata sallar karfe biyu, amotar suka zauna babu wanda yafita sai muzzaffar, kansa tsaye yashiga cikin gidan saboda anyi masa iso, tunda yashigo iya abu tayi mutuwar tsaye, cikin in ina take nuna Muzzaffar Ameeda ina kika san wanan👉🏻🙎🏻‍♂??. Ameeda dake tsaye tana kallonsu ta ce, "iya Shinefa Muzzaffar ďin danake gaya miki, kumafa kece kikace ya shugo, ganin ta rikice da ganinsa sai Muzzaffar ya basar ya tsugunna har 'kasa yana faďin mama ina yini?, cikin rawar baki ta ammsa, baibi takantaba ya haye tabarmar da'aka shinfiďa masa ya zauna. Ana cikin haka baba ya shigo gidan shima yarikitu da ganin Muzzaffar amma sai muzzaffar ya fuske ya'ki bada kofa koďaya ta alamun yasansu, nanma rissinawa yayi ya gaida baba, atsorace ya amsa tareda faďin yaro mike tafe dakai ne???. Murmushi Muzzaffar yayi ya ce, "baba nidai sunana Muzzaffar nafito ne daga 'kasar kamaru, ALLAH ne ya haďani da Ameeda naji kuma inasonta, wani ďan aikine yakawoni Najeria saidai bansan ko inaba bankuma san kowaba akasar sai Ameeda dana fara karo da ita. Ajiyar zuciya baba da iya abu suja lokaci ďaya itadai Ameeda duk kanta a ďaure yake, tana mamakin miyasa yayi 'karya??, bayan ita yafaďa mata iyayensa suna abuja. baba ya ce, "yaro kana nufin kaiba ďan kasarnan bane??, eh hakane baba, niba ďan nan bane, domin a kamaru ďinma ba anan na girmaba a london na girma, lokaci ďaya suka washe baki iya abu ta ce, "masha ALLAH aimu wlhy sai kayi mana kama dawani damuka ta6a sani. Ayya aidama haka rayuwa tagada mama, saikiga baka haďa komai da mutumba amma kuna kama da juna, nima haka mutane sukecewa ina kama da Ameeda sosai tamkar jini ďaya muka fito????. Idanu suka zazzaro tareda haďa baki wajen faďi kuma???. Ya ce, "ai ikon ALLAH kenan kawaidai kamace, ya za'ayi muzama jini ďaya bayan tana Najeria ina kamaru koma nace london, wanan shine karo na farko dana ta6a zuwa 9ja. Ajiyar zuciya suka 'kara saukewa sukace eh gskyar ka kuma. Ya ce, "to nazo neman aurenta ne indai zaku bani, amma inaso asadani da ainahin iyayenta. Iyayenta kuma???? suka haďa baki wajen faďa suna kallon juna. Muzzaffar ya ce, "eh ina nufin kanin baba ko yayansa tunda sune masu ďaura aurenta. Eh kayi gaskiya yaro suka faďa suna sauke ajiyar zuciya. Muzzaffar yasake faďin saidai abinda yabani mamaki ko kaďan bakwa kama da ita anya kuwa ba sato................da sauri sukace satowa kuma yaro??????, nanama suka faďa suna dafe 'kirji. A'a bahaka nake nufiba, ina nufin kota sato kamannin wanine a danginku???. Ohhhhhh yaro kace wani abu, tana kamane da kanwar kakar baban babana ce. Ayya ammadai tayi 'ko'kari data ďakko gida, dan ance duk wanda yabar gida gidafa ta barsa, saidai inane asalin 'kauyen naku, dan can yakamata akai kuďin aurena. Kallon juna sukayi Yaro kauye kuma???,,, suka faďa suna haďa baki. Eh baba wai ina nufin asalinku, dan inaso na auri 'yar dangi mai asali kuma. To to to wannan magana da girma take yaro. Miye girmanta baba???, kodai dangin kune a abuja dan naga kamarsu da Ameeda, tayi kama sosai dasu. Abuja kuma yaro???? suka faďa kamar zasuyi kuka. A'a kukwantar da hankalinku nifa nayi muku hannunka mai sandane, yanzu ina tareda iyayena zasu shigo idan kun basu izini dan sunaso ku gana kamar yanda al'adar kasarmu kamaru take kenan, dan gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kamaru. To sushigo mana bari asaka musu tabarma. Duk abinnan da akeyi Ameeda tana zaune kamar gunki tana kallon alamomin rashin gsky kuru kuru a idanun iyayennata, lallai yau akwai abubuwan mamaki masu kamada almara agidannan, ita harma tarasa yanda zata fassarasu. Shin kodai ya Muzzaffar yasan wani abu gamedasune??, miyasa yakema iyayenta wanana tambayoyin ma wai??, miyasa sukan rikice aduk lokacin da yay musu tambayar ne???, gaba ďaya takula sun fita hayyacinsu.. Amota ya tarar dasu momy, ya kallesu yana murmushi, dady ina fatan kunajin duk yanda mukayi ta waya???, kwarai kuwa ďan kirki muna jinku, inagadai dukkan hasashenmu yazama gasky kuma ALLAH yakawo mana 'karshen damuwa ta shekara ashin da biyu dasuka wuce. Murmuahi yayi To ALLAH ya tabbatar iyayena, yanzu kamar yanda kukaji sunce ku shigo. To suka faďa suna fitowa. Duk wanan tanbayoyi da Muzzaffar yakema su iya abu wayarsa a kunne take, dankuwa kiran daddy yayi ya ajiye wayar komai sunaji har aka gama. Da sallama suka shiga gidan, iya abu da baba suna zaune yayinda Ameeda take zaune a inda suka barta kamar dutse. Tunda suka rangaďa sallama suka shigo kallo ya koma sama, dominkuwa tuni su iya abu sunyi mutuwar zaune, ko yatsun hannunsu sun kasa motsawa, Ameeda ta mi'ke zummbur dan tun shigowar muta nen biyu gabanta yake dukan uku2 tamkar zai fito waje, jinta take tamkar ba'a duniyaba, sai kawai ta yanke jiki tafaďi awajen batareda daliliba. Da gudu Muzzaffar yayi kanta yana kiran beauty! Beauty!!!. Ina beauty ta suma, jiki na rawa momy ta 'karaso wajen tana jijjiga Muzzaffar da Ameeda dake jikinsa. Acan kuwa tuni fitsari ya ji'ke wandunansu iya abu da malam dauda, tuni sunshiga cikin kogin kwadamin ruďani da kiďima, lallai yau kashinsu ya bushe, lallai yau itace ranar tonan asiri, lallai yau itace rana dubu ta 6arawo ďaya kuma tak tamai kaya, lallai yau itace rana mai firgitarwa, lalai yau itace rana ta cizon yatsa da ambatar dana sani. Lallai yau itace ake kira da 'karshen tuka tuki tikkk. Adai dai wanan lokacinne kuma Naseer yashigo gidan ko sallama babu, tofa shimafa mun lura 'kamewa yayi atsaye tamkar bishiyar da aka dasa awaje ďaya, gaba ďaya zufa ta gama wanke masa dukkan sassan jikinsa, jiyake tamkar ya saki kashi atsaye, lalaikam idan zomo na yawo tofa kerema yana yawo tabbas wata rana za'a haďu, yau itace ranar zadata girgiza mutane masu ďunbin yawa, wasu zasu rasa daula, wasu zasu rasa aure, wasu zasu rasa aiki, wasu zasu rasa mutunci, wasu zasu rasa girma, wasu zasu bakunci gidan yarinema, tofa tabbasa Nas yana ganin kila yana cikin masu ziyartar gidan yari, dan yau ranace mai kamada ranar hisabi amma na duniyyyyyyyya😜. Tofa wai miye sirrin wanan rikita2ne???, wai miye abinda ake tsoron yafarune??, wai miye dalilin shigar mutane masu yawa cikin ruďani haka?????, miye tsakanin su muzzaffar da Ameeda ne???, miye tsakanin Nas dasu muzzaffar ne???, waishin ma waye muzzaffar???, waye Naseer???, suwaye su iya abu?????, wacece Ameeda??????, miye matsayin momy & daddy awanana bada 'kala???, miye kuma ya haďa wanana ahali akarkashin runfar rikici ďayane??????????... Mukaďaine masu baku wanana amsar, dan haka ku kasance damu........................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝

---------------------------------------------------------------------------------------------
do you want to learn how to blog and also make money online check this site
Share:

1 comment:

  1. Thank you very much for sharing information that will be much helpful for making coursework my effective.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).