shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 21 February 2017

KUKAN KURCIYA 11-16


[2/14, 5:57 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KIRCIYA........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 {☆Bilyn Abdul☆} Page1⃣1⃣&1⃣2⃣ Babu daďe tadawo hannunta ri'ke da ledar indome, sanda tadawo iya abu ta tashi dan haka tashige ďakinta itama, tana tunane2 yanda iya abu ta ruďe lallai awai wata magana a'kasa,, amma zatayi 'ko'kari tonota insha ALLAHU. Hakadai tacigaba da tura indomi ďin badan tana mata daďiba, bayan tagama ci tafita wanko hannunta,, harta kai gab da 'kofa zata shige saitayi saurin jan birki danjin ana magana 'kasa2 a ďakin iya abu, ta matsa ahankali gefen 'kofar baba taji yana magana cikin ruďewa. Abu!! data tanbayeki mikika cemata??. Why malam bance mata komaiba saboda matu'kar razana da maganar ta sakani, iya abuce ke magana cikin rawar murya. Baba ya ce, "lallai wannan magana takai arazana, to wai ya akayima wananan yariyar harta iya wanan magana??, kodai Nasuru ne ya kitsa mata hakan??. Kai malam kaima kasan nasuru bazai faďaba, dan yanama abuja, nasan Nasuru bazaiyi irin wannan kato6ararba. Baba ya sauke numfashi tareda yarce gumin daya wanke masa fuska, ahankali ya furta lallai idan mukayi sakaki tofa allura zata tono garma..........da sauri iya abu ta katseshi haba malam daina yimana wanan fatan mana, ai har abada babu mai tono mana daďaďďen sirrinmu, wanda dagamu sai ALLAH saikuma hajiya. Baba ya jinjina kai, to ALLAH ya tabbatar mana zainabu. Tunda Ameeda ta'iso wajen tsaye take kamar gunki, zuface keta ambaliya adukkan sassan jikinta, maganganun su iya abu sun rikita mata kwakwalwa, tarasa yanda zata fassara zancen nasu dan ta fahimta. Da sauri tashige ďaki danjin motsin babanta zai fito, ta faďa saman katifarta tana fidda numfashi, afili ta furta wanne irin 6oyayyen sirrine su baba basa son nasani, minene ma'anar allura zata tono garma idan sukayi sakaki???, miyasa suke zargin kuma Nas shiyya sakata wanana tambayar???? Shin wai miya haďa Nas ma da sirrinsu??, kodai Nas yasan wani abu gameda family ďinsu ne???,, tadafekai tana jijjigashi kamar mai shirin hawa bori, hawaye suka fara silalowa akumatunta, itakam tana kallon rayuwa a baibai, lallai akwai mayan 'kalubale dake bibiyar rayuwarta ta baďini data zahiri,, yanzu tawace hanya yakamata tabi domin binciko boyayyen sirrin iyayen natane dasuke 6oye mata akan aslinsu da tushensu???, da sauri kanta yake sarawa kamar zai faďo 'kasa. Jakkarta ta raruma tafara zazzagewa amma bataga abinda take nemaba, ta koma cikin kayanta, cikin sa'a tayi tozali da kwalbar sirob guda uku, da hanzari take 6alle murafan ta juye maganin abakinta, ta yarda kwalaben gefe dan bai ishetaba, kwalaben ďazu ta đauka tana 'kara kalacewa anan barci yay gaba da ita. WASHE GARI. Da'kyar taiya tashi tayi sallah tayi wanka tana cikin shafa mai kiran falmata yashigo ta ďauka murya aďashe tana faďin falmata ykk??. Lfy lao Ameeda kema ykk?, ina lfya, dama sonake kizo kirakani wani waje dan ALLAH, okey babu damuwa dama shirin zuwa gidanki nakeyi,, to shikenan ina saurarenki. Bayan wani ďan lokaci tafito saye cikin atanfa zani da riga ta yafa mayafi, atsakar gida taga iya ta gaisheta sanan ta ce, "zanje gidan falmata saina dawo. Cikin rawar jiki iya tace to saikin dawo Ameedan baba, batabi takantaba tafice daga gidan. Koda taje sai suka nufi inda zasu, gidan wata 'kawarsu sukaje sukai mata ALLAH yasanya Alkairi, dan tayi aurene itamadai irinsu ce ALLAH ne yay mata gyaďar dogo tasamu miji tayi aure. Daga nan asibiti suka nufa domin yin dubiya, bayan sungama dubiya suka fito, arikice Ameeda taďago domin ji tayi karo da mutum lokaci ďaya suka ďago suna kallon juna, ahankali tafurta yi ha'kuri dan ALLAH. Ko motsi baiyiba saboda shiga wani matsanancin ruďani, kallonta yakeyi ko 'kyafta ido bayayi, falmata taja hannunta suka bar gurin................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝 [2/14, 5:57 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 Page1⃣3⃣&1⃣4⃣ ........har suka tsaida adai2ta sahu suka shiga yana kallonsu, da hanzari ya tsaida wata shima ya hau, ya ce, "mai adai2ta wancan matan zamubi, to mai babur yafaďa, haka sukaita binsu Ameeda lungu da sa'ko har 'kofar gidan falmata, daga ďan nesa dasu suka tsaya, saida yaga inda suka shiga sannan yace mu juya kawai, mai adai2ta ya juya kan babur ďinsa suka koma. Koda suka koma asibitin bai iya shigaba sai kawai ya shiga motarsa ya fice, wani ďan matsaicin gida yayo fakin cikin hanzari yashiga, agurguje ya haďa kayansa akwati guda ya kinkimo zuwa mota, komawa yayi ya kulle gidan sannan yadawo yayma motar key yafice daga angiwar,, babban titi yahau yarin'ka sharara gudu(araina na ce, "waishi wanan mike damunsane). Hanyar kaduna yanufa daga kaduna yaďau hanyar abuja, 'karfe uku a abuja tayi masa saboda uban gudun dayayta shararawa ahanya, wata haďaďďiyar anguwa yashiga woow!! Nafaďa azuciyata lallai anguwar tahaďu masu karatu, hon yayi a'kofar wani 'katon gate, dagudu mai gadi yabuďe masa ya danna hancin motar ciki yana ďgawa mai gadi hannu, a yalwatacciyar harabar gidan yayi fakin ya sakko daga motar yana mi'ka dafaďin Alhmdullh, ya lankwasa yatsunsa sukayi 'kara sannan ya shiga cikin ainhin gida. Da sallama yasbiga 'katon falon daya tsaru da kayan more rayu babu kowa sai ac daketa faman aikinsa tv falonma tanata 6a6atu, ya wuce abinsa zuwa ciki,, nanma wani falinne ysararre annan ya tarar da mutanen gifan, dagu wasu yara 'kyawawa kansu ďaya sukazo suna faďin unvle oyoyo,, yataresu cikin farinciki tareda ďagasu ďai2 yana sumbatar kumatinsu, suma yabasu nashi suka sumbata, gaban wata matsakaiciyar dattijuwa yaje ya tsugunna yana gaisheta, ta amsa fuskarta ďauke da murmushi Muzzafar ďina lafiya kuwa naganka agida kuma yau ba weekend ba??. Kansa yashafa yana murmushi, wlhy kuwa momy hakanan naji ina marmarin ganinku shiyyasa nataho,, kumani wlhy zaman kano ďinnan ya isheni sonake adawo dani nan kusadaku. Murmushi dattijuwar tayi tana tashi zaune daga kishingiďar datayi karka damu Muzzaffar insha ALLAHU kwanannan zaka dawo abuja da aiki, dan har nayima kawunka maganama, yauuwa momcyna yafaďa yana kwantar da kansa gefen kafaďarsa,, momy ta shafa kansa to kaga tashi kaje ďakinka kayi wanka saikazo kaci abinci ko??, dama kamar nasani nasaka hama ta gyara maka ďakinka,, fuska yaďan yatsine kai momy banace 'kazamar yarinyarnan tadaina shigar mini ďaki bane??, da'kuwa momy tayi masa kaci gidanku muzaffar bana haka wanan halinbane??, yaďan shagwa6e fuska tareda hađe hannayensa biyu yana faďin sorry momy bazan sakeba. Yauwa ďan albarka jekayi wankan kaji. Ďakinsa yanufa wanda ya tsaru shima komai na ďakin farine tas, na ce, "lallai kanada tsafta malam,, dan 'kazami baya maida komai nasa fari haka, ďakin sai tashin 'kamshi yakeyi, ya vire kayan jikinsa ya ďaura farin tawul yanufi bayi,, komai na bayinma farine tasa masha ALLAH, babu 6ata lokaci ya salla wankansa yafito ya shirya cikin wando fari iya gwuywa da pink ďin riga 'karama, ya gyara sumarsa tareda feshe jikinsa da turare sanan yadawo falon. Dinning yanufa wanda aka cika taf da kayan abinci saikace zasuvi su goma, 'yan yaran ďazu sukazo suka haye saman kujerun dinning ďin suna faďin uncle muma zamuci, murmushi yayi musu tareda jan hanvinsu to my dota's, dakansa yazuba musu sukaci suka 'koshi bayan sun kammala suka dawo falon kusada momy suka zauna, suna nan zaune suna 'yar hira har aka kira sallar la'asar, tashi yayi yanufi masallavi suma su momy suka nufi ďaki domin gabatar da tasu sallar. Bayan yadawo kai 'tsaye ďakin momy yanufa tana zaune saman sallaya tana lazumi yawuce bakin gadonta ya kwanta saida ta idar sanan ya ce, "momy ina yini?, lafiya lao muzzaffar ya gajiyar tafiya??, to Alhamdllh momy,, to masha ALLAH ai haka akesonji. Ya ce, "momy nifa wani abun mamaki nagano akano yau, da sauri momy ta ce, "wane iri muzzaffar?, kasa yasakko ya zauna kusada ita, wlhy momy natafi zan shiga asibiti sainayi gamo dawata budurwa mai tsananin kama dake kamar antsaga kara an karya. Arazane momy ta ce, "muzzaffar da gsk kakeyi kokuwa wasa??, yaďan jinjina kai wlhy momy da gsk kinsandai ban ta6a kawo miki makaman ciyar wanan maganarba, ta mayso kusadashi cikin zumuďi ta ce,, "kasan daga ina take??, kai ya sake girgizawa A'a momy amma fai naga inda suka shiga itada 'kawarta,, masha ALLAHU yarona kayi "kan kai, gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kano. Da sauri ya ce, "A'a momy bama saikinjeba kibari nagama biniyar yarinyar, idan naďan gani wani abu gameda sirrinta saimuje harda dady, kinga babu dađi kiyi tafiya yanzu dady bai saniba ko, shikenan muzzaffar kaima kakawo hanzari maikyau momy tafaďa cikin taunin murya. Labarai masu daďi yayta kwakwaloma momy danta saki jikinta, yansan yanzu saita burkice musu, dama kwanan suka samo kanta da'kyar akan wannan matsalar, saida yaga tasaki jikinta sanan yatashi yafice daga ďaki, daga nana addu mamy tacigaba dayi ALLAH yatabbar musu da farincikin dasuka rasa na shekar masu yawa,, ALLAH yakawo musu'karshen wannan damuwa tasu. (Muka ce, "amin momy, dukda bamusan wacce irin damuwace ta dabai2 bayekuba). Itako Ameeda tunda suka loma gidan falmata tafaďa duniyar tunani kokađan fuskar saurayin dasukayi karo takasa 6ace mata, duk wani motsinta yana kan tuna fuskarshi,, har falmata saida talura da damuwarta, kusada ita tazo tazauna, cikin sigar lallashi ta ce, "haba Ameeda wai saiyaushe zakibar sakama kanki damuwa akan abinda bake kika ďorama kankiba,, yakamatafa ki zubar dakomai agefe kiji daďin rayuwarki, dagafa duniya sai kaduna,, watarana bazamuyi abinda mukeyi yanzuba. Murmushi Ameeda tayi tana mai kallon fuskar falmata ta ce, "falmata ai bazamuyima ALLAH wayauba,, nida ke duk bamusan ranar da mala"ikan mutuwa zaizo kanmuba, wlhy ina matu'kar shiga cikin damuwa da halin danake ciki. Sai kuma wani SaBON AL'AMAREE (littafin bilyn Abdul) dayake shin faruwa agidanmu, amma bansan taya zan fassara shiba, ayau kuma na'kara gamo dawani abinda ya tsayamin zuviya acikin asibiti. Falmata ta gyara zamanta sosai,Ameeda miye yake shirin faruwa agidan naku?, miye kuma kikayi gamo dashi a asibitin, shiru Ameeda tayi saikuma zuwa can ta nisa hannun falmata takama tana faďin karki damu zan sanar miki amma bayanzuba,, a asibiti kuwa mutumin damukayi karo da junane ďazu yaketa yimini gizo a idani, bansan miyasaba nakasa mantawa da fuskarsa da kuma irin kallon kurillar dayake mini. Dariya sosai falmata tashigayi har Ameeda tafara jin haushi ta ce, "k kuma miya baki dariya daga cikin maganganuna. Falmata ta tsagaita da dariyar tana bama Ameeda ha'kuri, wlhy 'kawata ganinayi kamar kin kamu da soyayyane?, tsaki Ameeda tayi ta ce, "kefa falmata watasa'in kanki a cunkushe yake wlhy,, wlhy abinda nakeji gameda mutumin ďazu yafi 'karfin soyayya, wani abu daban nakeji gameda shi, kinsan ban ta6a soyayyaba kuma har yanzu baga wanda zanyi soyayya dashiba. Falmata ta langa6e kai gefe kenan yaudarar Nas kikeyi??, tskai sosai Ameeda tayi, "o, da ke atunaninki son Nas nakeyi?, to idanma kina tunanin haka kibari wlhy banta6a jin onason Nas azuciyataba,, k ahalin yanzuma jinake na 'kara tsanarsa da duk wasu halayensa. To shikenan Ameeda ALLAH yajishemu al'kairi, Ameeda ta ce, "amin 'yar uwa. Gaba ďaya yinin yau haka tayishi sukuku kuma cikin ikon ALKAH batasha komaiba har dare, agidan falmata takwana dan kwata2 bata sha'awar komawa gidan,, koda sukaje clop da daddare batasha komaiba, bakuma tayi rawaba, gefe tasamu ta zauna abinta, kowa yasan budurwar Nas ce dan haka babu wanda ya matsa mata, dan sunsan halinsa sarai, kuma yana dawowa labari zai kai masa, ba'karamin aikinsa bane yakashe mutum. Haka rayuwar tacigaba da gudu da sauri,, babu abinda yacanja daga rayuwar ameeda saima kara ta6ar6arewa da yakeyi,, dan Nas yadawo mata dawani sabon salon na shaye2, gidansu kuwa ji ake da'ita yanzu su iya basa mata faďa bare duka, duk abinda takeso shi ake mata, ita lamarin nasu har mamaki yake bata matu'ka. Yauma haka taci kwalliya cikin doguwar riga ba'ka saidai daka ganta kasan abinda tasha bai gama sakintaba, haka tafito tana ďan dafe bango ayayin dataji zata faďi, cikin ikon ALLAH harta iso titi, tana tsaye domin jiran babur ko mota saiga wata dalleliyar mota tadawo da baya har zuwa gabanta dan da harya wuce. Ahankali aka zahe gilas ďin motar 'kya'ky'kywan saurayin ranarne ya bayyana, atsorace Ameeda taja baya tana tangaďi, yabuďe motar dasauri yafito, sorry yafaďa yana matsowa kusada ita, ta ce, "malam lafiya kuwa??, murmushi yasaki mai 'kayatarwa ya ce, "lafiya 'kalao 'yammata, ina zuwa haka??. Tai saurin dafe bangon wani shago danjin tana niyyar faďuwa, ina ruwanka da inda zani nikam banason yawan shishshigi gsky,, amamakinta saitaga yayi murmushi tareda haďe hannuwansa a waje guda yana faďin sorry madam, amin afuwa natsaya ne narage miki hanya naga kina bu'katar hakan,, hararar sa tayi tana wani lumshe idanu irinna 'yan maye, to idan banasofa?, sai incigaba da ro'konki harki amince kishiga motata beauty. Murmushi tayi saboda jindaďin sunan daya kirata dashi, ta ce, "to muje ALLAH dai yasa karka sayar mini dakai,, buďe mata motar yay tashiga yana faďin ai ki sayar da kai nakeyi bazan saida na beauty ba irinki, dariya tayi tana faďin maza akwai daďin baki. Tada motar yay sukabar titin batareda yayi maganaba. Yajuyo yaďan kalleta yayinda sukayi nisa, beauty ina muka nufane??, taďan gyara zamanta ta ce, "muje zan rin'ka nuna maka hanya, okey yafaďa yana murmushi,, lafiya lau ta nuna masa hanya harzuwa gidan falmata yayi mamaki kwarai da gsk, azatonsa yanda take abigennan bazata iya komaiba, tafito tana masa godiya, ya ce, "yanzu nan haka zamu rabu ko number bazaki baniba??, taďan ta6e baki haba malam daga haďuwa yau saina ďauki no ďina nabaka??, ya murmusa A'a beauty kindai manta yauce haďuwarmu ta biyu, kinga idan kinbani number ki duk sanda kika bu'kaci zuwa wani waje sainazo nakaiki, kinga kinsamu direba daga sama kenan. Dariya sosai tayi yareda mi'ka masa wayarta tana faďin sarkin wayo gashi kaďauka, yauwa ngd sosai yafaďa yana kar6ar wayar tata mai 'kyawun gsk, number sa yasaka sanan yakira tata yay save ďin tasa atata sanan yayitata atashi,, sallama sukayi yaja motar yatafi suna ďagama juna hannu, itama saita shige gidan falmata tana murmushi, jinta take cikin wani farinciki mara musaltuwa.............✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💖bilyn Abdul💝 [2/19, 2:39 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Page1⃣5⃣&1⃣6⃣ .......Tunda tashiga falmata ke binta da kallo dan ganin wata fara'a mara kangado datakeyi, ta zube saman kujera tana lumshe idanu dan barcin bai gama isartaba, falmata data kasa ha'kuri ta ce, "Ameeda wai miye sirrin farin cikinki ne???. Murmushi Ameeda tayi tana kallonta hummm 'yar uwa yaumafa sake haďuwa da guy ďinnan nayi, shimane ya kawoni har 'kofar gidanan. Falmata ta saki baki tana kallonta, kai haba??, ALLAH kuwa, zama falmata tayi kusada ita tana faďin to ya akayi yasan gidanku??, k ahanya ya ďakkoni yayin zuwana nan gidan, kai kawai falmata ta jinjina ta na faďin to ALLAH ya jishemu alkairi. Haka rayuwar tacigaba da gungurawa yayinda da Muzzaffar yashiga rayuwar Ameeda sosai, koda yaushe suna ma'kale da waya, ko kuma su haďu awani wajen dan bata so Nas yagane tana tare da wani, cikin hikima yake janye ra'ayinta daga barin shaye2, idanma tasan zasu haďu bata shan komai kwata2, yauma tana zaune aďakinta sai wayarta tafara ruri, takai hannu ta ďauka dan ganin sunan Muzzaffar, cikin muryarsa mai daďi ya ce, "assalamu alaiki beauty, saida tayi murmushi sannan ta ce, "wa'alaikassalam yayana, ykk?, ya aiki??. Alhmdllh wlhy, yanzuma gani ina shiri tashi daga aikin, kefa kina inane??, gabanta ne yafaďin dan batasan yazata cemasaba, tunda suka haďu baisan inane gidansuba kullum a hanya suke haďuwa ko gidan falmata, shi azatonsama nanne gidansu, yaďan yi gyaran murya yana faďin yadai beauty??? koba'kya gidane??. Ajiyar zuciya taja ta ce, "ina gida zakazo ne??, eh indai kina bu'katar ganina sainazo??, sassanyar dariya tayi aini kozaka kasance dani koda yaushe zanso haka, amma yanzu kaga kayi aiki kagaji dan haka kaje gida kayi wanka kaci abinci ka kwanta ka huta. Murmushi yayi tamkar yana gabanta, murya 'kasa2 ya ce, "ina gwauro yaga duk wanan gatan beauty!!?, dariya Ameeda tayi sosai, wlhy kanada abin dariya, yanzu dakanka kake kiran kakanka gwauro??. Shima dariyar yayi, to aii gsky ce beauty, kinga da inada mata da yanzu kafin na isa gida an haďamin ruwan wanka, idan nayi kuma ga abinci yana jirana, kilama saboda gata abani abaki, to amma yanzufa?, dole duk abinda nalissafo nizanma kaina. Ameeda ta gyara kwanciyarta to yayana kadage kayi auren mana musha biki, kaga idan kayi aure to koda yaushefa ina gidanka ina taya aunty na aiki da hira kafinkadawo. Tofa yafaďa yana murmushi, beauty to idan kuma kece kika zama matar tawafa???, ido tazaro da sauri kamar tana gabansa, tabďija yayana bar wananan zance kaji yanzu dai bari nabarka sai anjima,, kafin ya farga ta kashe wayar gaba ďaya, yayita kira amma akashe, daga baya saiya ha'kura yanufo gidan falmata kawai. A 'kofar gidan falmata yay fakin yasamu yaro ya ayka dan akira masa Ameeda, shigar yaron babu daďewa suka fito da falmata, saida ta gaisheshi sanan ta ce, "ai tana gida yauma batazo nan gidanba kwata2, cikin mamaki yake kallonta ya ce, "dama tanada wani gida bayan wannan??. Lah bata ta6a gaya makabane, ainan gidanane nikuma 'kawartace, kai ya girgiza to shikenan, dan ALLAH kozaki iya yimin kwatacen gidanne??, babu damuwa ai bawani nesa baneba, kwatance tashiga yimasa, ta ce, "damma inada ba'ko dana rakaka kawai. Babu damuwa yafaďa yana tada motar, bankwana yay mata yatafi. Yazo gaf dazai fita layin ya haďu da motar Nas, bin motar yayi da kallo harta shige wanan ai Naseer ne mikuma yakeyi anan anguwar??, kardai ďan isakan yaronnan yazo yayta 6ata 'ya'yan jama'a a garinnan??. Da yayi tunanin yabi bayansa saikuma yafasa ya hau babban titi yanufi gida, yama fasa zuwa gidansu Ameedan kenan. Bayan kamar kwana biyu da faruwar hakan saisuka sake haďuwa da Naseer a anguwar, amma shi Nas baiga Muzzaffar ba, Muzzaffar ya ce, "Beauty dan ALLAH kinsan wancan guy ďinne??, cikin damuwa ta kalleshi ta ce, "miyasa kamini wanan tambayar ne??, saboda naga kina ganin shigowar motarsa kika kwantar da kujerar baya, kuma kin matu'kar shiga ruďani. Ajiyar zuciya taja tareda zubo da hawaye daga idanunta, ta ce, "karka damu dashi, a'a beauty dolene nadamu dashi dominkuwa nasansa nasan koshi waye, irikice take kallonsa cikin tsoro kuma, a ina kasansa dan ALLAH????. kansa ya maida ga titi yana faďin kifara sanar dani ala'karku sanan saina sanar dake nima,, cikin rawar baki tace shinefa saurayina danake gaya maka ďinnan, hazbinallahu wani'imar wakil yashiga ambata, arikice ya ce, "Ameeda yau inaso ki kaini ainahin gidanku. Nanma cikin tsoro take kallonsa ta ce, "badaga gidan namu mukeba yanzu,, kansa ya girgiza tareda yin fakin agefen titi, juyowa yayi sosai yana kallonta, Ameeda banan bane ainahin gidanku, nan gidan 'kawarkine falmata, amma idan kin bani dama yanzunnan zan kaiki ainahin gidanku inda mom & dad naki suke, yana gama faďa yatada motar. Gaba ďaya zufa ta wanke jikin Ameeda, tanajin kunyar 'karyar datayi masa gsky,, amma ba laifinta bane rayuwace tamaida ita haka. Tiryan2 yaringa bin hanya kamar yata6a zuwa babu indà ya tsaya sai'a 'kofar gidansu Ameeda, yajuyo yana kallonta beauty ga gidanku nan👉🏻🏚.................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝.
Share:

2 comments:

  1. Thank you very much for sharing information that will be much helpful for making coursework my effective.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).