shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 21 February 2017

KUKAN KURCIYA 7-10 ๐ŸพKUKAN KURUCIYA....๐Ÿพ NA MUH'D ABBA GANA✍๐Ÿป & BILKISA IBRAHIM {Bily}✍๐Ÿป (Mrs Abdus'salam) Page7⃣&8⃣ Sai yamma can Ameeda ta tashi daga nannauyan barcin daya d'auketa, takai dubanta ga agogon dake manne a d'akin falmata, 5:56pm ta zaro idanu tareda fad'in nashiga uku ni Ameeda ko sallar azahar banyiba, ta zabura daga gadon tana maida numfashi, bandaki tashige tayi wanka tareda yin alwala. D'akin tadawo tafara ramuwar sallah. Bata bar wajenba har saida tayi sallar isha'i, tun tana kabbaran farko takeji ana buga k'ofa bayan ta kammala ta saka kayan falmata sannan ta bud'e d'akin tafito. Tayi turus dan ganin Naseer zaune, shima ayatsine yake kallonta yanata wani mazurai. Ta daure ta ce, "sannu da zuwa. Harara ya watsa mata taredajan tsaki, ya ce, " 'yar rainin hankali, shine kika wani kulle d'aki, anata bugawa kinyi banza da mutane. Ameeda tad'an tab'e baki kayi hakuri ina sallah ne. A'a d'awafi kikeyi, tun karfe 1 narana nake zarya agidannan falmata ta ce, "mini kina d'aki kwance, dan iskanci inata buga miki kinki ki bud'e. Lah wlhy barci nakeyi, kwata-kwata banjikaba, kaima kasan danaji zan bud'e aii. Harara ya zabga mata, yau kika fara shiga d'aki ki kulle ayita bugawa kiki bud'ewa, zaki kawomin wani tsarin banza. ka yi hak'uri, yanzu mike tafe dakai?? Saida ya kurb'i giya sannan ya ce, "nazone dama nafad'a miki gobenefa zuwa abuja d'innan, dan haka ki kwana da shiri, dan kinada matuk'ar muhimmanci awajen faty d'inanan, kinsan dai yanda nake da ANAS, baikuma dace ace babu baby na awajen birthday d'insaba. Ameeda tad'an murgud'a baki, nidai tun ranar nagaya maka bazan jeba, dan haka kabar zancennan kawai, banaso yakawo mana b'acin rai, tafad'a tana mik'ewa, ni bari na wuce gida dare yanayi. ke k'aramar 'yar iska har kin isa nabaki umurni ki bijire? kodan kinga ina lallabakine??. Ameeda tayi masa kallon sama da k'asa ta ce, "To Nas kai ubanane dabazan bijirema umar ninkaba, kaima kasan idan har na ce, "bazanyi abu ba, to bazanyi d'inba", dan haka ka saurara mini, ina sauran 'yammatan naka kad'auki d'aya acikinsu mana ta rakaka. Nas ya finciko Ameeda cikin xafin nama ya had'eta da bango, cizo ta galla masa ahannu, da sauri ya saketa, ta nunashi da hannu kai Nas kasan nasha fad'a maka, duk iskancinka kadaina gigin tab'amin jiki, wlhy kashiga hankalinka, idan har bazaka iya fad'a min magana daga nesaba to ka saurara, niba 'yar iska bace kajiko!!. tana gama fad'a ta fice, atsakar gida ta tarar da falmata itada bad suna hira, kallo d'aya tamusu ta d'auke kai tana tsaki, daga nesa ta ce, "falmata nawuce gida saida safe. Falmata ta ce, "kai Ameeda bazaki kwanan anan bane??, ko yau bazakije club bane?. Ameeda ta yatsine fuska tana fad'in bazanjeba, inaso naje gida dan nafad'ama iya cewa zan dawo dawuri. To shikenan saida safe, falmata tafad'a. Bad ya ce, "Ameeda abin ko gaisuwa?,. "O, sorry ban kula dakai bane ykk?". Ya ce, "lfy lau, ya garin. Gaba tayi abinta ba tare da ta amsashiba. Bad yamaida kallonsa ga falmata, wai ita wannan k'awar taki miye damuwarta, kodai Nas ne ya b'ata mata rai??. Falmata ta ce, "k'ila hakane amma dama tun d'azu ranta ab'ace yake, shine dalilin dayasama ta d'au caji. Bad ya ce, "wlhy dani nakeson yarinyar can datuni na shak'ama shegiya koken, nayi abinda zanyi, narasa mike damun Nas da har yarinyarnan tafi k'arfinsa. Hummm kajika dawata magana, tunda bataso yazaiyi, wlhy nakula Ameeda bata buk'atar wannan harkar, dan ALLAH ku barta, indai dan ALLAH yakesonta to ya aureta kawai, amma indai ta wannan hanyarne bazai tab'a samun Ameeda yanda yakesoba. Habawa falmata bakisan Nas bane kawai, na tabbata wataran sai yakaiga samun nasara, kedai kisa idanu kisha kallo kawai. Dariya kawai falmata tayi dan tasan hakan bamai yuwuwa bane, tasan tasha cin kud'in Nas akan yanaso ta shawo masa kan Ameeda ta yarda dashi, amma takasa. Aban garen Ameeda kuwa tana fita ta samu adaidaita ta hau, sai gida, sallama tayi tare da shiga cikin gidan babu kowa a tsakar gida, d'akin iya tanufa, amma babu kowa, saita wuce d'akinta kaiwai. Tacire kaya ta kwanta, babu dad'ewa ta fada duniyar tunani, tabbas indai tana tareda Nas bata tunanin zata shiryu, lokaci yayi dazata nisanta kanta dasu Nas, to amma iyayentama suna taka rawar gani wajen lalacewarta, kenan suma dolene ta nisancesu?, to inta bijire musu ta tafi ina zata?, a kano tatashi tayi wayo harta mallaki hankalin kanta, itadai batasan wasu 'yan uwansu dasuke nesaba, to miye mafita??. Zata cigaba da zama dasune?, kokuwa zata kama gabanta domin daidaita rayuwarta?, kullum shekarunta k'ara ja suke, tanaso tayi aure ta haifi yara, amma bata fata Nas yazama mijinta uban 'ya'yanta, wace hanya yakamata tabi domin gujewa auren Naseer??. Tajuya kwanciyarta zuwa rubda ciki, wayarta tad'anyi k'ara alamar shigowar sak'o, ahankali takai hannu ta d'auka, Nas ne yaturo mata sak'o. Ta ajiye wayar batareda sha'awar duba sak'onba, sai kuma ta d'auka ta duba. Ga abinda ke ciki.... Hy babyna Plz kiyi hak'uri da abinda nayi miki, nayi miki alk'awarin bazan sakeba, amma dan ALLAH kiyi hak'uri ki halarci birthday party d'inan, dan wlhy duk cikin 'yammatan kece mai kala, kin fisu aji, kuma kece nake burin ki zama uwar 'ya'yana, dan nasan zasuyi alfahari dake a matsayin uwarsu. Saina jiki. I luv u my dear. Naki NAS!!!. Tsaki tayi tana fad'in shasha sha ai wlhy duk dad'in bakinka babu inda zanje, kuma ni bana fatan kazama mijina, dan 'ya'yana bazasuyi alfahari dakaiba a matsayin ubansu. Taja tsaki tareda wurgar da wayar saman katifar ta. Iya talek'o tana fad'in Ameeda sai yanzu??. Ameeda ta tashi zaune wlhy kuwa iya, amma nad'an dad'e da dawowa na lek'a d'akinki bak'ya nan. Eh naje gidan malam D'anladi, matarsace ta haihu d'azu. Ayya ALLAH yaraya, mi'aka samu. Mace ta haifa tanana sarga d'ed'iya, iya tafad'a tana washe baki. Ameeda ta ce, "masha ALLAH. Kinci abinci ko, iya ta tambayi Ameeda??. Eh, kawai Ameeda ta ce, "mata. To aii shikenan, kinga bari naje nacinye wanda na ajiye miki dama wlhy bai isheniba. Ameeda ta girgiza kai kawai, danjin furicin iya abu, ta shafa cikinta tare da fadin a cikin ranta wlhy yuwa nakeji ba k'aramaba, dan tun safe rabonta da abinci. Kud'i ta d'auka tafice, wajen wani mai shayi taje tasiyo soyayyar indome da kwai, da shayi, tazo taci takoshi, sannan tasamu sa'ida. WASHE GARI tunda safe tashirya tabar gidan, dan tasan Nas zai iya zuwa yasa su iya su tursasata zuwa Abuja. Itako wlhy bazata jeba, gidan wata aunty ta tatafi, tawuni acan sai dare tadawo. ko hutawa batayiba iya abu ta shaida mata zuwan Nas, wai haryabasu kud'i, amma ransa ya b'aci daya tarar bata nan. Baki Ameeda ta tab'e ta ce, "matsalarsa ce kuma wannan, nidai tunda nace bazaniba ai dole a sauraramini. Tamik'e tashige d'aki tana mita...................✍๐Ÿป Ku biyomu!!. ©2017 Hikayarmu!!!. ๐Ÿ’–abba gana๐Ÿ’– & ๐Ÿ’žBilyn Abdul๐Ÿ’ž ๐ŸพKUKAN KURCIYA......๐Ÿพ NA MUH'D ABBA GANA✍๐Ÿป & BILKISA IBRAHIM✍๐Ÿป {☆bilyn Abdul☆} Page9⃣&๐Ÿ”Ÿ Ameeda ta juya ta sake juyawa akan 'yar yololiyar katifarta, gaba ฤaya kanta akulle yake tama rasa irin tunanin dazatayi, da sauri ta mi'ke zaune tajawo jakarta ta hannu, kwalaben sirob taฤakko guda uku taฤan rintse ido tana mai ba'kin cikin yanda rayuwa da sakacin iyaye ya jefata, afusace tashiga 6alle marafan kwalaben kamar wadda ta tuna wani abu, jiki na rawa tashiga tuttula maganin abakinta kamar mai shan ruwa, kafin mu farga ta shanye kwalabenan ukku gaba ฤaya,, abba ya girgiza kai yana jan numfashi da sauri,, tabbas yanajin tausayin halin da ameeda take ciki,, nikam kunsan mace da rauni saida nayi kuka. Tana gama sha ta 6ingire awajen tahau barci,, muma sai muka fito guywa a sanyaye. Ameeda bata farkaba sai bayan magriba, ta mi'ke zumbur tana kallon kanta kamar wadda aka sake, takai dubanta ga agogo, ido ta zaro dan ganin yanda lokaci yatafi idan zata iya tunawa tun 'karfe tara na safe take barcinnan, ta furta na shiga uku babu azahar bare la'asar, da hanzari tafice daga ฤakin iya abu ce kawai atsakar gidan take tatar koko, ta shiga washe baki yauwa ameedan baba kin tashi??, kinga zoki 'karasa min tatar nan dama nagaji wlhy, ฤan 'karamin tsaki ameeda taja ta wuce batarda tabi takan iya abu ba bareta tanka mata, iya abu ta ta6e baki 'yar kwaya tanaji ina magana tamin shiru kai ALLAH yawadaranki Ameeda, kai kawai na girgiza ina faฤin ohni abba wanan wace irin rayuwace akeyi agidanan???, naฤanja tsaki domin babu mai bani amsa tunda bily yau bata nan nikaฤai nazo ฤaukar muku rahoto. Ina nan zaune saiga ameeda tafito daga bayi da'alama wanka tayi, ruwa ta ฤiba abuta tayi alwala, ฤaki tanufa batareda takula habaicin da iya abu take mataba,, sallolin da'ake binta tashiga ramawa, tadaฤe tana addu'a da ro'kon ALLAH ya shiryata tadena mugayen halayen datake aikatawa, dakuma ro'kon ALLAH yabata miji nagari mai sonta da gsky, ta shafa sanan tafito waje. Zuwa sanan iya abu tagama tatar kokon tana zaune tana walfar tuwo abinta, ameeda taja kujera 'yar tsugunno ta zauna agefen iya abu,, tana kallonta amma ta share tacigaba da cin tuwonta, ameeda taฤan murmusa dan tasan tana fushine akan abunda tayi mata ฤazu, cikin taushin murya ta ce, "iya ina nawa tuwon??, saida iya abu ta haฤiye laumar tuwonta jikake kutttttt sanan ta harari ameeda cikin masifa ta ce, "ban dafa dakeba,, murmushi ameeda tayi ta ce, "babu damuwa iya, taฤanyi shiru zuwa wani lokaci saikuma taja numfashi tareda faฤin iya dan ALLAH inada tambaya??, iya tai mata banza bata tankaba. Ameeda tacigaba da faฤin iya wai ina 'yan uwanmu ne??, gaban iya abu yafaฤi duuuuum arikice taฤago tana kallon ameeda data tsura mata idanu, sai fidda numfashi take da'kyar ga gumi yafara bin sassan jikinta kamar wadda tahaฤi kwaฤo,, Ameeda ta ce, "iya yayadai ko tambayata ta 6ata miki raine??, da sauri iya abu take girgiza kai saikace 'kadangaruwa, tashiga kame2 A'a ameeda babu komai tambayarki bata 6atamin raiba, miye abin 6acin rai awanan tambayar kawaidai naji xancen nakine abazata shiyyasa...... ameeda tayi saurin 'katseta to iya kibani amasa mana ina danginmu suke?, kuma mu 'yan asalin wane garine??, inane tushenmu na asali??, cikin sar'kewar harshe ta ce, "kibari ba yanzuba watarana zan faฤa miki, to waima miye dalilin wanan tambayar???. Ameeda tagyara zama tana faฤin babu komai iya,, kawaidai ina son sanine, ina kuma mamakin tunda nataso bamu ta6a zuwa wani gari danufin ziyarar danginmuba, sai nan kano kawai nasani,, ahankali kuma nafara fahimtar bawata dagantaka mai 'karfi tsakaninmu da 'yan uwanmu nan kano, musamman idan nayi la'akari da irin halin danake ciki basu ta6a nuna damuwarsuba bare su tsawatar mini. Jikin iya abu sai rawa yakeyi kamar mai jin sanyi, Ameeda tana kula da'ita, tana mamakin yanda iya abu tashiga wani hali daga tambaya. Lalai akwai alamomin tambayoyi akan iyayen nata,, akwai wani 6oyayyan abu gameda tarihinta,, lokaci yayi dazatasan mi iyayenta suke 6oye mata, lokaci yayi dazatasan inda danginsu suke, lokaci yayi dazata nisanta kanta ga iyayennata, tasan duk tsiya bazata rasa wanda zai ri'keta acikin dangin nasuba harta samu mijin aure,, tayi al'kawarin koda a'kauye dangin iyayenta suke zata zauna dasu kuma tasamu miji acikinsu tayi aure,, tagaji da wanan tam6elen datakeyi, tasan kuma indai tana gaban iyayenta bazata ta6a daidaita rayuwartaba,, ta mi'ke batareda ta tanka irin lallashin da iya abu take mataba akan taci tuwon data zubo mata,, gyale taja akan igiya tafice abinta......................✍๐Ÿป Ku biyomu!! ©2017 Hikayarmu!!!!!!! ๐Ÿ’–abba gana๐Ÿ’– & ๐Ÿ’bilyn Abdul๐Ÿ’
Share:

2 comments:

  1. Thank you very much for sharing information that will be much helpful for making coursework my effective.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).